Showing 57001 words to 60000 words out of 70697 words
Chapter 20 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf
karba za a mai, shin dalilin kafa kai
da yai a jikin motar, wasu siraran hawayen nadamar rayuwar shi ke bin kuncin shi, ga rashin
abokin shi da yai, kuma kusan a gaban shi zakin nan ya kaiwa Oga Zaks cafka a wuya, what if
shima ya biyo shi? Ga Suwaiba da iyayen ta da 'yan uwan ta, maybe this is a bad idea for him
to risk there life for his mistake, he was trying to walk away, when he hered her voice, calling out
his name in a passionate way" Baby? kai ne? Kai ne da gaske nake gani? What are u doing
here?" Qarasawa tai da gudu ta fada qirjin shi tana kukan missing din shi da tai, shima rungume
ta yai kamar wani zai kwace mai ita, gyaran murya Salma tai masu," Adda a waje kuke fa, kn
san halin mutane, ba za ai tunanin mijin ki bane, za a fara qananan maganganu" janyewa sukai
daga yanda suke taja hannun shi zuwa cikin gidan su ta tsaida shi a soro, Saudat kam ta qame
qam a wajen, dan zuciyar ta bugawa kawai take, ina nata mijin? Ya akai suka rabu yau? Bayan
ta san ba sa rabuwa? Wannan tambayoyin Salihu ne kawai zai amsa mata su bayan ya samu
nutsuwa, dan ta kula shima ba a nitse yake ba, Salma da tai gaba ne ta dawo baya ta ja hannun
yayar tata sukai ciki, ta kula da cewar Saudat na cikin damuwa tin safe yanzu kuma data ga
Salihu shi daya ba nata mijin abun ya qaru mata, ko ba komai tana son mijin ta kawai halayen
shi ne yasa ta gudowa taqi komawa, what could possibly happen to him? Sun riga sunyi Sallah
gidan Juwairah dan haka bayan sun shiga sanar da Abban su sukai Salihu yazo ga kuma a
yanayin da suka gan shi, a da Abban was furious, amma da Mama Bilki ta taishe shi, akan ya
tafi cikin nutsuwa ya bude ma Salihu zuciyar shi yaji me ke tafe dashi, in yazo da rainin hankali
gidan su yazo, ta bashi goyon baya ya mao duk abin da yaso, kada kai yai cikin qunan rai ya
fita amma sai ya danne bacin ran nashi, kamar yanda matar tashi ta bashi shawara, Sallama ya
mai ya miqa mai hannu amma Salihu ya noqe, ya durqusa qasa yana mai kuka mai ban
tausayi," Abba ni mai laifi ne ba a wajen ku ba har a wajen Allah, babban mai zunubi ne,na taso
ban san menene ilimin addini ba, duniya kawai na saka a gaba, bani da ilimin addini daya ratsa
zuciya ta da zai hana ni aikata dukkan abubuwan dana aikata, dan son ka da Allah da Annabin
shi ka yafen abinda nai wa Suwaiba, ka yafewa abokina diban jinin Saudat da yai domin ya
mutu, a dazu kan na iso nan, ta hanyar hatsarin mota" wani qarar kwanuka da qarar Saudat ne
ya dawo da su daga maganar da suke, faduwa tai a wajen a sume, da gudu Abban su yai
kanta, ya daga ta yai ciki da ita, ruwa suka yayyafa mata, a hankali take bude idon ta, ya sauka
kan Salihu da ya shigo ba izini, kuka ta saka ta kai mai naushi a baki, " mugaye azzalimai,
kashe shi kuka ko? Dan na san yanda Kalla ke sona zai biyo bayana ko bajima ko ba dade,
shine kuka kashe shi?" " Saudat you have to calm down, u get it all wrong, ni da kk gani ni na
shawarce shi akan mu fita daga qungiya dan son da muke maku, da kuma tsoron Allah daya
shigeni, amma Kalla ya qi, ya mun bayanin shi akwai sauran lokacin tuba, na mai wa'azi da in
mutuwa ta riske mu kan tuban fa, yace akwai lokaci, yana fita yai hatsari mummuna, kan shi ya
fashe qafarshi ta......." " Stop it ! Stop it !" Saudat ce cikin tsawa take hana shi qarasawa, tare da
fashewa da kuka mai ban tausayi, a nan dai ya qarasa labarta masu komai daya faru har a
wajen Oga Zaks, Goggo dake gefe da ta fito cikin bala'i taji komai, sai jikin ta yai sanyi, ta koma
kwallar tausayin yaran ta, ba laifin kowa bane illa laifin ta, ba su taba sanin Saudat na son mijin
ta haka ba, kawai ta gudar wa mutuwa ne sai yau, daga ta Mama Bilki ta sa Abba yai ya kaita
dakin su, ya kwantar da ita, kuka kawai take, Mama Bilki ce ta shiga bayan Abban su ya fito"
Saudat ki hakuri , na san rashin masoyi akwai zafi, amma soyayyar da zaki nuna wa kalla a
matsayin shi na mijin ki shine addua, tinda bai sake ki ba kk qi komawa, dan haka daga yau
zaki fara takaba, har tsawon wata 4 (hudu) da kwana 10 ( goma) dan haka har abada mijin ki na
buqatar adduar ki, baya buqatar kukan ki, kinji" ta qarasa tare da shafa kanta, cikin sakewar jiki
ta dora kan ta a kan cinyar Mama Bilki hawaye masu zafi na fitowa saga idon ta, nan take ta
hau kwarorowa mijin nata addu'a, mama Bilki na amsawa, haka har ta samu sauqin zuciyar ta
itama, Salma na maqale tana tina nata mijin tana hawaye, ga tausayin Addar nata da ya dame
ta. Bayan yayi alwala yai salla ne ya kuma ci abinci Abba ya ce suje gidan Yayan shi,( gidan su
Juwairere) tafiya can sukai, a motar da ya zo da ita, sukai wa Yaya Balarabe bayanin komai, ya
gamsu sannan ya amince da mijin Suwaiba zai zauna a shagon gidan har Allah yasa su Jabeer
su koma Abuja sai su su zauna a bangaren su, Abba godiya yai wa yayan nashi, ya koma gida,
in da Yaya Balarabe yace, zai fara koya mai ilimi na addini dan ya na da qarancin shi, godiya yai
sosai, Nafee Abban su Jabeer ya kira ta gyara shagon, aka shimfida mai yaloluwar katifar da
wankakken zanin gado da pilo, sai yar sallaya, da buta, da ruwa mai kyau a bokiti rufaffe, Abban
su yace in yana buqatar zagawa zai iya shigowa cikin gidan, godiya yai ta musu kamar zai
kwanta, zuciyar shi cike da tausayin rayuwar da zai koma, sannan qasan ta kuma cike da
murnar ganar da shi gaskiya da Allah yayi.
Yau kwana tara kenan da haihuwar Juwairah, anyi suna, suna ya qayatar, dan Jabeer ya yi
qoqari sosai, ga akwati nan biyu da yai ma mai jego da jaririya, daya babba daya qarami, gobe
suke son komawa Abuja, dan wajen aikin na buqatar Jabeer, sun gama kwasar duk wani abu
da zasu dauka, sauran kayan zata barwa Addan nata da mijin ta, a haka taje gida taiwa Saudat
ta'aziyya ta kuma yi wa iyayen ta sallama, ta sha kuka kamar wadda za ai wa auren dole, da
kyae suka lallashe ta, sai da taga Jabeer ran shi ya baci da kukan ta sannan ta hakura, sun
dawo gida bayan Isha'i Nafee idon ta ya kumbura saboda kukan rabuwa da bestyn ta kuma yar
uwar ta, sannan matar yayan ta da ke son ta,Innar mu ma ba a barta baya ba wajen matse
kwalla,tana qara bawa Juwairah hakurin zaman da sukai a baya, Baba Balarabe ma jikin shi sai
da yai sanyin rabuwa da Juwairah, dan yarinya ce mai shiga rai matuqa, da kyawawan halayen
ta, da kuma iya zama da mutane, a haka aka kwana gidan kowa da abinda ke ran shi.
Washegari da sassafe, Jabeer da Juwairah dauke da Abrar suka fito suka shiga sabuwar motar
Jabeer zasu tafi, Nafee ta riqe hannun Juwairah tana matsar kwalla, Jabeer ne yace" My little
sis ki yi hakuri,kwana nawa ne zamu qara dawowa, ran da fa Saudat zata fita takaba ranar za, a
fara bikin ki ko kin manta, dan haka ki kwantar da hankalin ki, sannan wataqila ma Salma ta
haihu kafin nan zamu zo, kinji Sweery," hawayen ta ta share, tai masu adduar tafiya lfy su da
samun sa'a da nasara,Innar mu sa Baba Balarabe ma haka, sai mijim Adda Suwaiba dake gefe
shima yana masu fatan alkairi, motar ya tayar sukai gaba, cike da kewar juna, Salihu gaba daya
ya canja, fatar shi tai duhu, tumbin nan ya sauka,sai kyaun shi ya fito, ashe yana da kyau yaci
kudin haram ya gina tumbi tulele ga kumatu kamar nawa( lols just kidding nawa mai kyau
neí ½í¹„) tausayin shi ne ya kama Baba Balarabe ganin yanda ya koma a qasan ran shi
kuma yana ayyana ko zasu fara zuwa kasuwa tare ne wanjen gwanjon su da shi ne? Bayan su
Innar mu sun shiga gida ne ya same shi ya mai wannan tayin, cikin jin dadi ya amsa da zai yi ko
meye in dai halal ne ba damuwa, qasa yai da murya da kan shi" to Baba ai ban da jari kuma" "
kar ka ji komai, akwai jari a wajena ,ko da dubu biyar zaka iya farawa mu gani" godiya yai ta
zubawa kamar me, Baba Balarabe da yaga ba zata qare ba dariya yai ya shige cikin gidan ya
bar shi anan,.
Suwaiba ta tare da mijin ta,kuma kasuwanci ba laifi wataran a samu ya siyar da kayan dika,
ribar dubu biyu ko ukuma, wataran kuma su ragu, a haka shi da ya fara da capital na five
thousand yanzu ya kai seven thousand, ai an samu, kuma a ciki yake qoqarin ci da su.
Salma da Huwaila kusan ta tare suka haihu, Salma ta haifi Yaran ta biyu masu matuqar kama,
da kyau, ita kuma Huwaila ta haifi namiji, mai kama da Bangis sak, kwana tara ne a tsakanin
su,yaran Salma sun girmi na suwaiba, an yi suna in da akai suna ba komai a dukka gidajen sai
to gwanda na Salma ma, dan anci an sha,mutane ne dai ba su zo ba sosai, ita ko Huwaila ,
komqi qayau sikai sunan nasu, ga habaici da suke sha wajen yan gulmar da ke zuwar masu
barka da kuma wanda suka zo sunan, yaron Salma na mijin An sama mai Muhammad, macen
Fateema,a hakan suke kiran su, sai yaron Huwaila da aka sama suna, Umar, rayuwa tai ta
juyawa wadannan bayin Allah da dadi ba dadi duk haka ake ta fama, wanda kusan ko ina ne
dama yanzu a wannan lokacin haka ake ta fama, in da gidan Baba Balarabe ya bunqasa da
arziqi dan Salihu ya shiga gwanjo da sa'a sosai, yanzu har dila biyu yake budewa, Juwairere
kam arziqi ba a magana sai godiya, gidan su mai kyau daki biyu da dinning, sai babban palo,
mai dauke da manyan kujeru da kayan kallo, yarinyar ta sai wayo take.
Shirye2n bikin Nafeesa ne ya kama gadan gadan, in da Saudat kuma sauran kwana uku kenan
ta fita takaba, a yau din ne su Juwairah da Jabeer tare da diyar su Abrar za su zo, Jabeer ba
qaramin qoqari yai ba a yan watanni biyun, dan ita Juwairah bama ta sani ba tinani take in sun
je ina zasu sauka, bangaren su yanzu Adda Suwaiba ne a ciki, bata da masaniyat daki daya da
bandaki da palo madaidaicin da Jabeer ya masu a filin dake gefen gidan su wanda yake kamar
kango je a da, sai yar tsakar gidan qarama sosai ba wani fili sosai, ba laifi a irin gidajen cikin
gari a kano wannan yayi kyau, sai wajen azahar suka iso, wajen Innar mu ta shiga, Nafee da
gudu ta je ta rungume ta suka hau murna, bayan sun natsu ne ta miqe aka hau gyara amarya
da ita.....
*Juwaireren mama na gayyatar dukkan fans din novel din 'YAN ABUJA zuwa wajen bikin
Nafeesa, Allah ya bada ikon zuwa ameen*
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: í ½í²…í ¼í¿¼ 'YAN ABUJA í ½í²…í ¼í¿¼
BY HAERMEEBRAERH
Page 31:
A yanzu hankalin Talle ba qaramin tashi yai akan ya nemo Salma ya bata hakuri akan abinda ya
mata, dan yasan tinda ya sake ta, ga ciki tabbas tana nan qullace da abinda ya aikata mata,
kuma baya fatan ma.yace zai maida ta, saboda ba zai iya riqe ta ba yanda ya kamata, ba irin
rayuwae sa salma ke.mafarki ba kenan, " Ya Allah ka bata ikon yafe min a duk sanda na
bayyana a gaban ta ina mai neman yafiyar, ko bam samu zuwa ba na mutu.Allah ka wakilci ce
ni a zuciyar Salma ta yafe min" " Haba Talle, sai yaushe zaka daina zubda hawaye ne? Na baka
shawara mu kama akuya daya mu siyar, ka samu na mta dana guzuri, kaje wajen yarinyar nan
ka nemi yafiyar ta, amma ka kafe kace a'a to taya kudin zasu samu? In aka siyar nima ba sai na
samu na kafa wani jarin ba? Ko dari dari biyu muke samu a rana a matsayin riba ai zamu toshe
wata gabar, balle nasan zamu samu yafi haka, ga tashin hankalin batan Haule, duk da ina
kyautata zaton gajiya tai da halayen mu ta gudu wajen mahaifiyar ta, amma abun na matuqar
damuna" " ta zancen Haule kwantar da hankalin ki, ta na wajen mahaifiyar ta, da kyar suka
amshe ta, amma yanzu baki ga gatan da take sha ba, abokina da yamin hanyat auren babar ta
ta ne ya ke sanar sani hakan, yana mun godiyar kyautawa da nai na barta tazo taga mahaifiyar
ta" " Allah sarki, a gaskiya mun tafka babban kuskure a rayuwar mu Allah ya bamu ikon
gyarawa, me zai hana ka samu a islamiyyat malam Sallau kaga ana karatu kyauta, awa biyu
zamu bayar a a kwana uku kawai, dan akwai jahilci mai tarin yawa a rayuwar mu, kai kuma ka
na zuwa ta bayan isha'i kai da Yaya" " gaskiya kin kawi shawara dan abubuwan da muka tafka
da da ilimi a tattare damu musamman na addini da bamui ba, Allah ya yafe mana" " Ameen" "
ina yarinyar nan Hawaila? Ki taran su har Baban gidan zuwa anjima za ai maganar auren ta,
gobe juma'a, suna da daki, a bangaren su, da katifa dan haka ban ga dalilin ta ci gaba da zama
a gaban mu ba ko me kk ce, kin ga a hankali muka samu sai mu mata kayan daki kamar kowa"
" wannan shawarar tayi, tin da ga yaron su nan Umar Allah ya bayar gwanda ai auren gobe
komai ya wuce,Allah ya sanya mana albarka dikkan mu, ya yafe mana" " Ameen, na gode maki
da kk canja halaye daga munana zuwa kyawawa, yanzu kyaun ki ya fito matata, nima ina fatan
kin ji dadin canjawa ta?"ya fada yana mai matsawa kusa da ita, ita kuma tana wani sissine kai,
wai kunya" naji dadi mana Talle sosai, nan gaba ma swatyn nima zan dinga kiran ka irin
yanda kk cewa Salame" dariya ya kwashe da ita ta gane inda ta dosa ( Sweety) shine abinda
take son cewa.
Da yamma za a tafi dinner kowa ya sha gaye hae ya gaji, ba a cika wa Nafee irin kwalliyar nan
ta yanzu ba,ta dai sha powder da kyaran jikin da ya fito da kyaun ta, ( aikin Juwaireren mama
kenan) ba qaramin kyau tai ba, sun so kwarai a aske mata gira ai shaping din ta amma
Juwaireren mama ta hana, domin hakan haramun ne, tinda akwai abinda ake yi a danyi dabara
kamar an yi shaping din, to gwanda ayu hakan, aiko nan take Adda Suwai nonoless aka dauk
ma Nafee kwalliya, ta yi matuqar kyau, haka Saudat sa Salma maman yan biyu, Yaran su ma
sun sha gayu, ga qamshi dake tashi a jikin su mai ni'ima kowa son daukan su yake, Shamsiyya,
Innarmu, Goggo Sarai Mama Bilki da sauran dangi sun sha kwalliya suma, amma ance ba za a
je sa iyaye ba, nan fa Goggo Sarai za a fidda halin "ni dai gaskiya ko su Bilki ba zasu ba ni a tafi
dani, dan nasan irin wajejen nan akwai kwalama" wani kallo Suwaiba ta mata, " Haba Goggo
har zuwa yaushe zaki daina wannan halayen ne?" Sinne kai tai tace" Yannan wasa dama nake
ina ni ina zuwa wajen matasa" kuma a qasan rai dai ana son zuwafita tai daga dakin tai
wajen masu soyawa amarya kaji da za a tafi kaita garin Kebbi, dan hanya akwai nisa, ba tsaywa
siyan abu a hanya zasui ba, kuma a cikin garar ta Jabeer yace a saka harda kajin, can ta nufa
tace" wannan biki nanarziqi ne in ban ci a wajen ninner din ba na ci anan"( dinner). Kada kai
Salma tai da taji me take fada, mai hali baya sake hali sai dai ya lafa,in dai abun ya shige shi.
A wajen dinner wajen ya qayatu angon Nafee ba dai kyau ba shima, sai dai Nafee ta fishi kyau
da dan haske, tin da suka isa yaran Salma na wajen Suwaiba nonoless, Salma sai ta fito kamar
budurwa ba mai jego ba, kyaun Saudat kuwa itama ba a magana, anan abokan ango da suke
zaune kusa da shi suka qura masu ido kamar zasu sace su gudu, ana tsaka da rawa da
shagalin biki ne suka taso, da dukkan alamu gidan su daya, dan kamannin da suke da shi,
Sallama sukai, su kuma sika amsa, Juwairere da Adda Suwaiba tashi sukai,suna masu
murmushi, su kuma suka zauna a wajen da suka.tashi din, Saudat jikin ta har rawa yake tana
son barin wajen, dan a zuciyar ta nan take ta tino da Kalla, dayan e yace" Haba sarauniyat
kyawawan duniya ina zaki, bayan ga sarkin ki ya iso domin ya dauke ki ya kai ki masarautar
masoya?" Murmushi tayi, she us so nervous, ji take kamar ta zura da gudu, Oh duniya yau
Saudat ke jin nauyin mazaí ¾í´”komawa tai ta