Showing 51001 words to 54000 words out of 70697 words
Chapter 18 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf
komai,sai barna ta faru a zo ana dana sani wasu ma ba a sanin barna ta faru sai sun aurar da
yaran, za a duba yarinya bata kai budurcin ta gidan miji ba cousen ya dauke a cikin gida, maybe
ma a dakin uwar ta, can u imagen, wannan wace irin rayuwar zinace2 muka shiga? Mu yawaita
nemawa kan mu tsari akan zina yan uwa Allah ya kare mu) Talle ne ya amshe maganar da
gaskata yayan nashi, kuna ya basu tabbacin dawowar shi qauye da zama, don ya gama xaman
birni kenan, murna kam Marka ta yi ta da jin wannan zance, amma ba ta ce komai ba har
yanzu, a haka suka watse kowa ya kama inda zai yi cike da alhinin mutuwar Jummala.
Su suwaiba sun kammala ginin dakin su tsaf, sai dai ba flasta, ba fenti, sai ledar daki da suka
fara shimfida qaton buhu a qasa sannan suka saka ta, katifa biyu suka saka, babba da qarama
daya, sai kayan sunda suka kwaso suka zuba ciki, daki yayi ba laifi, amma ba wani wadata da
yalwa sai godiya kawai, kullum dare Suwaiba sai tai kukan rashin mijin ta da kuma yanda ta
koma, yanzj wa zai aure ta? Yaushe Salihu zai aiko mata da takardar sakin ta? Ko yazo ma ta
ganshi? Haka za tai ta saqe saqe har bacci barawo ya dauke ta. Goggo ta kamu da mummunan
hawan jini, sakamakon sanya tinani da damuwa da tai, sannan yanda ta saba Yaran ta na
manne da ita yanzu tsakanin su gaisuwa, in suka gaida ta sai dai tajiyo hayaniyar su da Mama
Bilki tana koya masu abubuwan da ya dace, suna kuma wasa da Ammar kamar ciki daya suka
fito, abun ba qaramin daga mata hankali yake ba, asibiti kam taje shi a kwanakin nan yafi sau
nawa, dan sai kawai tana zaune taji wani jiri da duhu ya mamaye ta, sai suma, haka za su kaita
a bata magani sui qoqarinnda zasui ta farfado si sallame ta Abba ya maido ta gida, takan ce a
ranta " Oh ni Sarai naga duniya, Yarana danake taqama da su a idon duniya su suka juyan
baya yanzu, Allah gani gare ka" yau Goggo ta tashi da matsanancin ciwon kai, in da ta dinga
kiran Suwaiba ta na zaune tana jin ta tai shiru, Mama Bilki ce ta leqo ranta bace tace" Suwaiba
kina son shiga aljanna kuwa? Mahaifiyar ki na kira kina ji ki shiru? Wallahi ki kiyayi Allah, ki
kiyayi fushin uwa suwaiba, meyasa kk da ruqo ne, shi wancan mijin naki mai qaton ciki ba dan
dan kyaun da yake da shi ba meye abin so a wajen shi, duk da wahalar da suka jefa ku kina
nan kina faman son shi, kina begen shi, sai uwa wadda ta haife ki, itace baki san ki yafe wa ba
ko? To na qara jin haka tana kiran ki kina ji ki zauna kiga ya zamu qare a gidannan da ke,
shashasha kawai,kin miqe ko saina kwado maki wannan murfin kwanon?" A hanzarce ta miqe
tana kallon hannun Mama Bilki mai kwanon, shigewa dakin Goggon tai tana zumbura baki"
Gani" shine abinda tace ta ja ta tsaya, " Suwaiba nice fa Goggon ki, abar son ki, Suwaiba ba
dan Adam din daya wuce kuskure, nayi kuskure, na yi nadama ku yafe ni ke da yan uwan ki, na
san ban zama uwa ta gari ba,ko wannan ciwon da nake fama da shi ya ishen ciwon kai ba
qaqqautawa, na rasa ya zan kuma duk.sanadin juyan baya da kukai ne, a tinani na a da rayuwa
mai kyau nake baku, dan Allah suwaiba ku yafe wa Goggon ku kunji?" Kuka Suwaiba take
sosai, harda majina, kusa da goggon ta taje ta zauna ta dora kanta kan cinyar goggon ita kuma
ta hau shafawa, ba wanda ya qara cewa komai, nan take Goggo sarai taji kamar ana zare mata
ciwon kanta, damuwar ta na raguwa.
Da saurin shi ya shigo gidan bakin shi washe kamar gonar audiga, qoqarin shi bai wuce yaje ga
mahaifan shi ba da matat shi, shiga bangaren Innar mu yai yaga wayam an karo qofar ba kowa,
bangaren su yai cike da doki da zumudi, durqushe ya ganta gaban ta robar da ta hada zuma da
zamzam ne da taiwa fatiha qafa bakwai take sha tinda cikin ta yai wata takwas dan samun
sauqin haihuwa, ta shan ye ya kai rabin robar, zufa ke karyo mata ko ta ina, sai addua take tana
qarawa," Allahu Allahu Allahu rabbi la ushrika bihi shai'an wa huwassami'ul aleem" shine abinda
take fada taja maimaitawa, da sauri ya isa gare ta, ruwa ya fashe mata tana wani nishi na son
ta sillubo koma meye a tattare da ita, sauri yai ya juya ta daga durquson sabida kar ta haihu a
haka ta samu mummunan tsaga a gabanta, zaunar da ita yai ta gaba ya koma bayan ta yana
qoqarin taimaka mata, dan yanda ya ganta, da yanda suke karantawa shi da uta a wani littafi na
EVERY WOMAN ya san haihuwa ta zo, ba yanda zai ya fita da ita asibiti haka, suna haka sukaji
sallamar Innar mu ta zo da kwadon zogale zata ba Juwairah, ai ko tana ganin haka itama ta
duqa ta hau taimaka masu, nan take ta fara qoqarin nishi mai qarfi...........
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ' YAN ABUJA
BY HAERMEEBRAERH
NA RIQE KU DAN ALLAH KU DAN QARA MIN HAKURI KADAN NAN DA KWANA BIYAR
INSHAA ALLAH ZAN KAMMALA 'YAN ABUJA ZAN MAYAR DOCUMENT YANDA DUK MAI SO
ZAI SAMU. NA GODE SOSAI DA SOYYAR NOVEL DINA DA KUKE NUNAWA. ME LOVE U
ALL❤
Page 28:
Kukan jaririyar da suka ji ne ya tabbatar masu da cewar Juwairah ta sauka, lfy, Yah Jabeer na
gani ya na kissing wiyan Juwairah da tai zufa iyaka, shafo gefen fuskar shi tai tana murmushi,
Innarmu ce ta dau Babyn tai gefe da ita tana " Oh yarannan ba ko kunya, ji yanda kai jage2 da
hawaye harda majinar kuka dan abin kunya, ita mai haihuwar ma tai jarumta ko kuka ba tai ba
sai kai" cikin dakewa da alamun boye halin da ya shiga ya fara magana" a gaskiya Innar mu ba
abinda zan ce dake sai ubangiji ya miki rahama, ya saki a aljanna madaukakiya, ke kuma
Juwairah Allah ya maki albarka, ya biya maki dukkan buqatun ki, ni Jabeer yau na qara
alqawarin riqe amanar ki har qarshen rayuwata" kallon Innar mu yai ya sake cewa" Innar mu da
ace mazaje suna shiga dakin haihuwa da matan su da an rage kashe2n aure da wulaqanta
mata, da maza sun daraja mata fiye da qima, Innar mu duba fa kiga irin wahalar da yarinyar nan
ta sha" ya qarasa maganar cikin tsananin tausayawa da girmama matat tashi, jikin Innarmu duk
yai sanyi itama, dan tabbas ta san iyaye mata sunyi matuqar qoqari na samar da mu dika, sai
dai mui ta masu addu'a da qoqarin yi masu biyayya," Jabeeru duk abinda ka fada gaskiya ne,
yanzu kaga yarinyar nan tana ta bushe wa, tashi ka dora mana ruwan zafi, ka zo ka saka
ganyen magaryar nan a ruwan su tafasa tare saboda ya fidda dattin jikin yarinyar sosai,
Jabeeru kazo ka dauki 'yar ma mana ka riqe mata kamar wani zai dauke ta" dariya yai yana
sosa qeya ya gyarama Juwairah zama sosai yanda zata ji dadi sannan ya isa gare su, kallon
yarinyar yake with so much love , ga wani irin kyau da Allah ya mata na musamman, wannan
kyaun daga ina ta samo shi,juyawa yai ya samo amsar shi wajen juwairah, murmushi ya mata
sannan yace" tabbas na samu amsata danake nema a zuciya ta , kyaun yarinyar nan duk naki
ne Honey" " meye wata Hamee ni ta shi ka dora ruwan ka dawo ko kuma ka gyara ruqon ta naje
na kwaso na bangare na dana zuba dazu, riqe ta na dawo" yara mai ita tai ta sa kai ta fice tana
" yara ido ya bushe ba kunya, zamani duk ya canja iko sai lillahi" zuwa tai ta zuba ganyen
magaryar a ruwan ya ci gaba da tafasa sannan ta kwaso bayan ta tace da rariya ta
taho,yarinyar ta karba ta fara wanke wa, mamaki ne ya ishe ta ganin Jabeer na gyara Juwairah,
" kai ni fa sai na bar maku wajen ku, wannan rashin kunya har ina, wa ya koya maka yanda ake
ma mai jego ni Hansai" cikin dariyar da suke mata yace" Innar mu na koya ne a wani littafin
anti-natal din ta littafai ne da suka qunshi yanda ake renon ciki da haihuwa da kuma yaran
kansu, da irin taimakon da uba zai ba uwa in ta haihu, ina fatan kin fahimta, baya daga cikin
kyautatawa namiji ya bar mace tai ta wahala ita daya bayan tate suka samar da abinda aka
haifa ko za a haifa din, yana daga cikin karamci da kyautatawa tare da soyayya namiji ya shiga
dumu2 ai komai da shi, hakan na qara ma ma'aurata fahimtar juna da so da tausayi, sai kiga
aure ya dade ba fafa ba yaji bare kai qarar miji gida" innar mu gyada kai kawai take , a zuciyar
ta tana ayyana gaskiyar dan nata, amma to be honest ita kunya suke bata, shiru tai kawai bata
ce komai ba, Jabeer ne ya kammala gyara wajen ya tallabe Juwairah suka fita tsakar gida,
kujera ya bata ta zauna ya fita wajen Innar mu ya debo ruwan zafi, ya shigo da shi cikin babban
bokiti, ya raba biyu, daya a babbar roba daya na wanka, kai mata yai ya koma daki ya dakko
ruwan kal fari, ya zuba kamar murfi uku a ruwan da zata zauna din, ya je ya fara tayata
wankan," Yah Jabeer pls i can do it my self, Innar mu na nan fa, she may not say a word amma
na san ba zata so ganin hakan ba," " ke ba abinda zata gani kar mu bata lokaci, mqza na gama
maki kan ta gama da Babyn mu," a haka ya kashe ta da zance ya mata wanka ta zauna a
ruwan taji dadi sosai, ya qaro wani, ya saka ta a ciki, ya qara ruwan kal din a ciki( ma'ul kal na
wato ruwan kal yana wanke datti shima sosai, ya fidda qarni da warin HQ sannan yana matse
mace, ya gyara ta, sai dai ba a so in ba kamar yanzu da aka haihu ba a cika amfani da shi shi
da bagaruwa, baya2 ake son amfani da su, dan kar su yi illa ma wajen, kuma ana son in ana
amfani da su a yawaita cin fruits da veges da kuma shan zuma mai kyau da zamzam, dan su
zama sun saukar da ni'ima a HQ yanda ba zata bushe ba) bayan sun gama ne ya fito kenan
Nafee ta dawo daga makaranta, shigowa tai da gudun ta, sakamakoj kukan bby da ta jiyo, ai
suna ido biyu da Juwairah ta kwasa da gudu ta isa wajen ta ta rungume tana murna, " sannu
matar Yayah Allah ya qara maki lfy ya raya mana abinda muka samu" " Ameen Nafee sannu da
dawowa" " to malama sake ta haka taji da kanta" sakin ta tai amma bakin ya qi rufuwa kamar
gonar audiga, gani tai ya dakko zanin haihuwar ya aje mahaifar a cikin leda zai wanke zanin,
maza tai ta karbe, "Yah Jabeer barmun na wanke ni ban komai ba ai" " A'a sis basshi yanzu kk
dawo skul bana son ki wahal da kanki, kayan jini ne ke kuma baki son su dan haka zanyi,
beside ni ya kamata nayi, tinda ina kusa, ta yi me wuyar da ta haifo man the queen of beauties,
shiga ki ga inda ake kyau barakallah" ai ko tini ya kwadaita mata gani yarinyat da gudu tai
dakin, tana isa ta zube gwaraf gaban Innar mu, ta gyara yarinyar ta sha kwalli, tai matuqar kyau,
idon ta bude fes kamar haihuwar sati, cikin zumudi ta amshe ta, tana mata addu'a Juwairah ce
ta shigo da sallama daki tai ta na tasbihi ga Allah tana matuqar godiya daya sauke ta lfy, Mama
Bilki ta sha addu'a yau a bakin Juwairah, ta gefen idon ta ta hango tsantsar kyau irin na
yarinyar, " ikon Allah ke nan yanzu da wanne ido zani gida na kalli Mama da Abba, wai ni ce yau
na haihu" shafa cikin ta tai da yai mata babba kamar bata haihu ba ga nankarwa da taji yayi,
murmushi tai ta qara gode Allah, nan da nan ta hau shiri, man kade ta dauka ta shafe cikin da
shi sosai ta murqe shi, dama ya sha gashi wajen Yah Jabeer, don jinin ya samu fita, bayan ta
gama murje cikin ne ta kwalama Nafee kira dan ta zo ta daure mata cikin, zuwa tai ko ta tamke
mata shi, tsam, ya koma kamar ba ta haihu ba, kayan ta ta saka atamfa riga da zani ya mata
kyau sosai, kalar atamfar akwai pink da red a jiki, geshe jikin ta tai da turarika masu dadi ta fito,
lokacin Jabeer ya gama komai yai wanka shima ya shigo, sannu tai masa da adduar Allah ya
saka mai da alkairi, yai murmushi yace" is my duty love, so ki daina damun kan ki," murmushi
tai mai da tasan yana biyan komai a wajen Yayan nata, kada kai yai alamar zamu hadu ne, kina
tsokana ta ko, daki yaje ya shorya ya fito ya same su dika a zaune, gyaran murya yai ya kalli
Abban su ya gaida shi, dan yana shiryawa ya shigo, yai ma harinya addua, Nafee na ta masu
tsiya shi da Innar mu, miqa mai ita Abban su yai shima ya mata addua, sannan ya fadi sunan da
za a ana kiran ta da shi, wato Hafsat sunan Innar mu kenan, Innar mu har kukan dadi tai,
sannan yace ma Juwairah "sai ku nema mata sunan ku na yan gayu da na san dole sai kun
saka mata," Nafee ce ta kalli Juwairah tace" matar yaya sai ki bamu suna" Juwairah tinani tai
sannan tace" Na saka mata Abrar( mao tsoron Allah)" " Oh ni Hansai yanzu ina ni ina iya fadan
Abras" dariya suka kwashe har Abba, Abban ne yace" haba Innar su, yanzu Abrah dinne zai
gagare ki?" Haba me zasui in ba dariya ba dan shima ya kwafsa, gyaran murya Jabeer yai ya
fara magana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa tare da son sanar da su abin farin cikin da
ya same su yace" Abba Innar mu Juwaireren Mama and my little sis Nafeesa, ina mai farin cikin
sanar damu ci gaban da ya same mu, a yau kuma a dazu dana dawo na zo da labari me dadi
na samun aikin da nai, a NNPC na can Abuja in da suka ban gida dake kusa da gidan man da
zan aiki, a unguwar Jabi, harda mota, sin dauken a matsayin Manager na wajen gaba daya,
sanan kuma bangaren kasuwanci na yau na biya ta kasuwa, Saifullahi dana kan bari ya min
jiran wajen in bana nan ya dakkon kudade masu tarin yawa, da kuma wasu jakunkunan da na
saro ba su iso ba daga malaysia , to a yau suka iso, har wasu yan kasuwan sun sara, shine ya
ban kudin da suka kai dubu dari biyu da talatin cif a hannuna, nan take na bashi talatin din nayo
gida da sauran" juye2 ya farayi yaga ina ya wurga ledar da yazo da ita, dubawa yai ya hango ta
can hanyar shigowa inda ya yar ya iso wajen matat shi mai naquda, kasa kudin yai kashi biyu,
sannan ya qara kasa kashi daya biyu, miqawa Abban shi yai kashi daya, sai kuma ya dauki
dubu goma ya ba Nafeesa sauran dubu arba'in ya bawa Innar mu, yace gashi su sa mai
albarka," lallai wannan yarinya ta zama mabudin alkairi a gidannan, muna ma Allah godiya, nayi
murna da farin ciki sosai najin wannan abun alkairi daya same mu, Allah ya taya ka ruqo da
gaskiya da amana, Allah ya qaro maka arziqi mai yawa mai albarka," amsawa sukai gaba daya
da " Ameen" Innar mu kukan dadi take tin da aka fara maganar, dan bata taba tunanin riqe kudi
rabin wannan bama dan tasan ba ta dasu bata kowa ba ajiya, yau gata da su kuma nata, ai sai
murna, ta kasa magana sai kukan dadi take na daukakar da Allah yai wa danta a lokaci daya"
Innar mu ki bar kuka addu'a da albarkae ki Yah Jabeer ya roqa" Juwairah ce ta fadi haka a
lokacin da ta ke kurbar shayin da Nafee ta hada mata mai kauri da dumi, share hawayen ta tai
tace" Jabeeru ba abinda zance sai dai nace Allah ya qara maka albarka ninkin ba ninkin akan
wadda ya maka, ina alfahari da kai a matsayin ka na dana, Allah ya karen kai daga sharrin
maqiya" amsawa sukai dikka, Nafeema ba a barta a baya ba wajen taya murna da godiya balle
mai jego kuma, kiran sallah je ya karade wajen tare da duhun da ya bayyana hakan ya nuna
masu cewar magrib ta yi, miqewa sukai bayan sun gabatar da addua, sukai alwala mazan suka
tafi sallah matan sukai a gida, bayan ya dawo ne ya dakko kaza a akurkin su, ya yanka biyu, ya
kaiwa Innar mu, Nafeesa ce tace ni zanyi dan nasan yanda take son ta, dauka tai ta koma
bangaren Juwairah ta dakko ridin da suka daka tare , sa madarar shanun dake aje a randar
sanyi, dakko kayan qamshin da suka niqo harda minannas a ciki ta gyara kayan miya ta zuba
wannan kayayyakin amma banda madarar, sai da farfesun ya