Showing 36001 words to 39000 words out of 70697 words

Chapter 13 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf

27 Apr 2025

4550

ta, ya bazata ji
gwarin guiwar fidda komai ba, kuka Abba ya barta tai har saida ta daina da kanta, yasan ta
fidda koma meke cin ta a rai, zaunar da ita yai, yace ina zuwa, Mama Bilki ya kira bayan ya fada
mata abinda ya faru, shigowa tai taje kusa da Salma, Salma na ganin ta taje da sauri ta
rungume ta, tana neman gafarar ta, Mama Bilki yafe mata tai, ta zaunar da ita, " fada mana me
ya faru" a cewar Mama Bilki, da gudu Goggo Sarai ta iso gaban Salma" yi shirun ki wannan
sirrin mu ne karki magana a gaban maqiya" wani kallo dukkan su suka watsa mata, kowa da irin
nashi, Salma magana ta fara, ta sanar da su komai da ya faru tin daga tafiyar ta har dawowar ta
yau din, kuka sosai Abba keyi duk jarumtar shi, ya tausayawa diyar tashi,Mama Bilki ma haka,
Goggo Sarai ga tausayi ga kunya itan ma kukan take, Salma ce ta juya ta kalle ta" Yanzu
Goggo a wanne hali su Adda Suwaiba suke? Baki sani ba, kawai suna aiko maki da kudi kina
ajewa, Goggo baki san ina ne Abuja ba, da tin tasowar mu kk kimsa mana son ta, yanda kk
saka mana son abun duniya da hutu, da haka kk sa mana son ku kadai da muku biyayya da
anyi yaran kirki,amma baki wannnan ba ba a kaiga dasa mana tsoron Allah da son Allah da ma
Annabin rahama biyayya akan saqon da ya zo mana da shi ba, Goggo kin ci amanar kiwon da
Allah ya baki, Abba na qoqari akan mu kina rusawa, ni yanzu ba zan zauna anan dakin ba,
Mama Bilki ina riqon arziqin komawa wajen ki na zauna, dan tabbas nima ina zargin ciki garen
yanzu watana kusan hudu bana ganin al'ada ga yawan ciwon kai da mara, sai zazzabi danake
yawan yi, ki koyan dukkan irin tarbiyyar data kamata nima inna haifi nawa na basu,ba irin
wannan tarbiyyat mara kyau da ma'ana ba" Goggo Sarai ce ta kwade mata baki," dan uban ki to
ki dauki haihuwar ki da nai ma kice ita ce tai maki mana? Ku tashi ku fice man a daki gaba
dayan ku bana buqatar kowa, yaran da suka san daraja ta da qimata za su zo su kula dani,
dama ke tinda akai auren me kk tsinanan, baki tsaya kin nemi kamar na yan uwan ki ba , me kk
samo banda wahala? Sai ku tattara ku je can, jikoki kuma yarannan biyu ba zan rasa su da ciki
ba yanzu haka, dan ba zaman banza na aika su ba" miqewa sukai Mama na mata addu'ar
shiriya a ranta, dakin ta ta kai Salma, abinci ta dakko ta bata, kamar mayya haka ta hau shi da
ci tana hawaye, tana gama ci ta sha ruwa sai bacci, Mama Bilki ce ta gyara ta, tana tsananin
tausayin ta, Abba sai godiya yake mata da sanya albarka.










Su kuwa yan Abuja ana can ana shanawa, hanakali kwance, suna zaune ana kasafin sassan
jikin su.........
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼

BY HAERMEEBRAERH





My Saerwwaermaerh
Ke ta daban ce Haermeen Hamma na son ki,

Billy shantali (Billisiou)
Hassana D
Ummul
And dikkan Surukaina na Tabital fullaku, har da surukar zamani🙄😙duk ina gaida ku ba adadi,
ur love is daban in my qalbi� ANA MUGUN TARE.ME LOVE U XOXOâ¤






Page 20:

















Alhj Kallah, Alhj Salihu, Oga Zaks, su ka dai na iya ganewa a qaton table din da yake kewaye
da manyan Alhjzawa, wanda a qalla zasu kai ashirin , gaba dayan su da shigar tasu ta red and
white, with a little black on it, kowa muzurai yake, irin nima wani shegen ne�, Oga Zaks ne yai

gyaran murya, ya ci gaba da magana" A a Salihu, wannan qorafin naku bai karbu ba, kun san
qa'idar qungiya, an baku dama, ku kadai na bawa damar da ban ba kowa ba, saboda koba
komai ana qaruwa da ku sosai, amma wannan karon, u guys disappointed me so much, that u
have to pay for what u did, dan haka , nake baku imarni ba shawara ba, u go back and bring ur
wives here, dole ne a yanki abinda ake buqata daga wajen su, ba dan komai ba kuwa sai dan
cika sharuddan Dodo, dan haka na baku nan da kwana uku, kuje ku gama sallama da su ku
kawo su" miqewa yai cikin izza yai hanyar waje, guards din shi na biye, Alhj Salihu ne ya kife
kan shin a table, dan a qashin gaskiya ya fara son Suwaiba duk da wautar ta da gabuntar
ta,Alhj Kalla na kula da shi, taba shi yai akan su tafi, miqewa yai da kyar, suka fice , ana ta yan
gulmace2 , ko ina ba a raba mutane da gulma🙄bayan sin isa gidan Saudat ne, suka shiga inda
suke tattauna matsala irin haka, suka zauna, Alhj Kalla ne ya fara magana, dan ya kula in bai
ba Alhj Salihu ba zai ce uppan ba, " Salihu ni ban ga abin daga hankali a maganar nan ba fa,
duk da ni kaina a yanzu haka na fara son yarinyar can,koba komai duk matan da muke hulda da
su yaran nan na kula suna da na su sirrin daban a jikin su, ga yarin ta ga kyau, amma kasan
bijirewa Oga Zaks na nufin qarewar arziqin mu, nikk dana talauce gwanda na aikata abinda
yake so, mu kaisu kawai, nono ne kawai za a yanke, to meye? Naga dai ana ciwon cancer ma a
yanke masu nan kuma su rayu" " bazaka gane ba abokina, in ba wajen a ina mutum zai na
hutawa? Kai ni fa bari kaji ba zan iya bane kawai, duk sokoncin yarinyar nan ina son ta, dan in
tare kk da ita ta bara maka wani haukan sai kaji kamar kaita zane ta shegiya, amma tayi akwai
zuma, banjin zan iya rabuwa da ita, yanzu ni dai shawarata shinr suje gida kawai su ga gida na
kwana daya ko biyu su dawo muga ya za ai, tinda kaga bai kamata har in ma mutuwa za sui
tsohon su bai gan su ba, dan ta uwar su ita tajiyo bamda case da ita ni" " haka ne kayi gaskiya,
to bari na fada masu kawai gobe su shirya zasu gida ko ya kace, dan da kaina zan hada mata
kayan ta, amma ka tashi ka tafi gaskiya dan saina dana sosai kan ta tafi, bamu san ya
abubuwam zasu kaya ba" dariya sukai suka tafa, " shegen sama nima ba ri na hanzarta" aiko
hakan akai washe gari da asussuba suka dau hanya kowa da drivern ta dan wadata, ga wata
mota nan shaqe da kayan arziqi na bin su, haka suka iso gida cike da doki da murna, suna
shiga gidan, Salma suka hango kanta akan cinyar Mama Bilki tana mata kitso, a kwance, kamar
wata jaririyar ta, " Kan ubancan, me nake gani haka ni Suwaiba? Yaushe gidan ya koma haka?
Da jin muryar ta Salma ta miqe da gudun ta tai kansu, tana ihun murna," Goggo fito ga su Adda
sun zo, Mama kinga su Adda sun zo, ina Abba? Abba fito ka ga ikon Allah su Addana ne a
gidan yau" suma basawa sukai aka ci gaba da murna amma cikin ransu akwai tambayoyi sosai,
dakin suka shige tana ta kwasar bacci, tashin ta sukai, ta miqe tana mittsika ido, aiki tana
wartsakewa ta gansu, sai kukan dadi ya kamata, ta ko hau kukan murna suma sunayi, Abba ne
ya lallashe su, nan fa aka hau gaishe gaishe" Ayyyuririri, kai shiyasa nake son Allah, akwai shi
da biyan buqatar bawa, dubi yarana , san kowa baqin cikin marashi, ga kudi ga kyau, ga hutu,
naji dadin zuwan ku yarannan, ya mazajen naku?" Cikin murmushi da dagun kai an gama
kumbura masu kan suke amsawa" suna lfy suna gaida ku, ga abubuwan kayan abinci nan da
kudade da suka aiko a baku ke da Abba" cikin murna kamar zata kifa ta dafe kudin dika har na
Abban nasu, shi ko ko wajen bai kalla ba, ya masu godiya, Mama Bilki ce ta shigo dauke da
ruwan Pure water a plate ta doro masu sanyi ta kawo masu, ajewa tai ta zauna a gaisa" wai ni
shin gaisuwar nan dole ce ne, a bar yara su huta, kuma in banda abin talaka, duba fa wa zai
sha wannan ruwan, dan Allah kije an yafe Allah ya bada lada" Goggo Sarai ke maganar nan,

cikin shewa suka hada baki" Hahaiiiiii Casssss sai Goggo, ashe ana nan ana ci gaba da gashi,
Allah sassaka to" dariya tai cikin isa tana wani daga hanci, Mama Bilki ce ta tashi ta ja hannun
Ammar da ke son shigowa sukai gaba, Salma ma tashi tai rai bace ta fita" wai Goggo me ke
faruwa ne me nake gan? Salma da waccan matar?" Abba ne ya basu labarin komai, nan da
nan suka hau kokawa yar uwar su wahalar da ta sha, sannan ya qara masu da hukuncin da ta
yanke, anan ne ransu ya baci sosai, suka kwala mata kira, bayan ta shigo ne suka balbale ta da
fada kowa da abinda yake fada, sai da ta tabbatar sum gama ta miqe tai waje ba ta tanka ma
kowa ba a cikin su, da bala'i Suwaiba zata bita ta daka Goggo ta hana ta, "aini yanzu na cire ta
a Yarana nima, taje can ta qarata, ina da ku kun ishen rayuwa, kuma yanda kukai jan nan da
alamar kuma kuna dauke da ciki, dan haka jika ne nake matuqar kwadayi yanzu a duniya fiye
da komai, taje tai ta fama, ita ta sani, naku sun ishen zaman duniya dai ba na qiyama ba" kallo
suka bi junan su da shi, take Saudat ta fada jikin Goggo tana kuka, Suwaiba ma idon ta ya cika
da kwalla sosai, "Adda Suwaiba akwai abinda na si fada maki tin da na qi dan nasan halin ki
tona mu zaki su kuma su kashe" cimin zaro ido Goggo tace" Suwa..... suwaye zasu kashen
ku?" 😨" mazajen mu Goggo yan qungiyar shan jini ne,na gano hakan da jimawa, yanzu haka
bamu da mahaifa da ni da Adda" wani mari taji guda biyu a fuskar ta, daya na suwaiba daya na
Goggo" dan ubanki sharri kuma zaki masu, mutanen da suke kasuwanci a qasashe ko ta ina,
arziqi ya wadata ya bunqasa shine zaki ce haka, so kk ki dawo kema ki xauna ki jamin asara,
na haifi ya kamar ki da zan samu dukiya ki dankwafe kanki? To ki bude kunnen ki kiji, ko ya ake.
Ciki gobe zaku koma va zan lamunci asara ba" cikin kuka ta rarrafa wajen Abban su," Abba ka
yarda da ni, wallahi gaskiya na fada, yan shan jini ne, naji da kunne na" " na yara dake yata,
dan baki taba fadan hakan ba kuma da dikkan alamu akwai gaskiya a zancen ki, wannan kudin
nasu yayi yawa" " Abba ya zaka yarda da wannan maqaryaciyar ? Qayra ne fa kawai dan sun
taba dukan mu sau biyu, shine fa ta qullaci abun take son ta gudu, to in ke bazaki koma ba ni
xan kma dakina" " yauwa yar albarka, ai nasan in kowa zai juyan baya ke kin haifu" tashi akai
inda kowa zuciya ba dadi, Saudat ta kafe bazata koma ba, inda Suwaiba tace ita zata koma,
Salma kuma suna jiyo komai,hankalin ta ya tashi amma tasan bata da say a wannan
kamarin,Mama Bilkince ta shawarce ta akan ta musu addua kawai, hakan akai kuwa ta kwantar
da hankalin ta suka hau yankan farce bayan sun gama kitson.





" Bbyna wai ni yaushe zaki gaida Mama ne kafin a zo ya zamana bazaki iya fita unguwa ba
kuma, tinda ita tana abunnan na mutan da taqi zuwa dakin ki har yau" " hmmmm kaidai bari
abunnan na min zafi ace wai uwa ba zata je dakin yar ta ta gani ba? Ba komai, xan je ko gobe
ne naji dazu Nafee tace su Adda sun zo, kuma Salma ta dade a gida" " Eh haka ne, rand naje
gaida su ma na ganta ai, Allah ya kaimu goben..........â¤

Na gode maku da nuna kulawar ku akaina masoyan YAN ABUJA naji dadi sosai da yanda novel
dinnan ya samu karbuwa a zuqatan jama'a masu tarin yawan da ban san iyakar su ba, ina
roqon ku da ku qoqarta ku sa na samu ladan abinnan, ta hanyar aiki da abinda kuka karanta na
amfani , in da kukaji nai kuskure ku yafen ku nemamin gafarar Allah, wanda yaji dadin novel
dina kuma ya mafana da abinda ke ciki ya min adduar samun biyan buqatuna na alkairi. Tanx
Love u allâ¤
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼





BY HAERMEEBRAERH





Dan Allah masu tambayar novel daga farko ina qara baku hakuri da cewar, na kusa kammalawa
inshaa Allah, so ina ganin it will be better and easy for me inna kammala nai document sai mai
so ya same shi. Na gode. Love u xoxoâ¤





Page 21:






To day is a busy day for Juwairah,amma dik da haka ta kafe yau take son ta je gida dan su
gaida da yan uwanta dika, da farko Jabeer yaso hana ta ta bari sai jibi tace sam zata iya ba
wani gajiyar da zatai, haka ya hakura, tana idar da sallar asuba azkar din ta dik a hanyar
kitchen take yin shi, fitowa tai dan yi ma Jabeer abinda zai samu ya tafi da shi Abuja wajen
interwie da aka kira su na wani aiki da ya nema a NNPC, dubawa tai taga basu da wasu kayan
abinci sosai as usual, ragowar Flour da ba zata wuce gwangwani hudu ba ta dakko da dan kifin
da ta siyo a jiyan, na dari, da kayan miya albasa ta yanka mai ganye sosai ta daka attaruhun ta
hada da dan kifin nan, ta soya sama2, nan take ta hada flour tai meatpie cikin mintina qalilan(
da ace akwai wadatar a cikin meatpie dinnan zata iya amfani da nama ko kifin ya fi wannan da
veges masu yawa a ciki in ta hada sai ta soya sama2 dika amma a yanzu tinda Juwairiyyar mu

na da dabara sai ta cika albasa dan ya tada kifin) bayan ta kammala me ta dakko kamun su tai
mai koko, ta hada mai shi ta kai mashi, daki kafin ta gama shima yana ta shirin tafiyar, jakar shi
da komai ta hada mai dama, komawa tai ta samu zobon ta da ta dafa da yamma jiya ya sha
kayan qamshi ta tace ta hada mai shi, ba qaramin dadi yai ba, ta samo wata yar robar ta cika
mai da ita ta daure yanda ba zai zuba ba, ta debar mashi meatpie ta rage ma surukan su da
zasu zo anjima wajen neman auren Nafeesa, sannan ta koma daki, qarasa tayashi hada komai
tai, dai dai da brush din shi bata manta da saka mai a jaka ba, bayan ya gama cin abincin ne ya
gama komai ya janyo ta jikin shi" My princess ba abinda zan ce maki sai dai nai maki fatan
shiga aljanna, tin da ance sai miji ya yarje wa matar shi shiga aljanna zata shiga My Juwairiyyah
na yarje maki shiga madaukakiyar aljanna da izinin Allah, ke macen kwarai ce, macen nunawa
kowa ba tare dana kunyata ba, Allah ya sauke ki lfy, ya shiryar min dake , Allah ya qara miki
imani, kinga ga wannan ba yawa kwama biyu zan kamar yanda na sanar dake, ki ta tayani
addua inna samu aikin nan xamu samu hutu sosai, zan jiyar da ke dadin da baki taba zato
mace zata iya samu wajen mijin ta ba, Juwaireren Mama ina son ki" ba abinda take zabgawa in
ba murmushi ba, amma yana cewa Juwaireren mama ta turo baki tana buga qafa," Ni dai Yah
Jabeer bana so, taso ka tafi kar ka makara, Allah ya karen kai mijina kaje lfy ka dawo lfy, Allah
ya bada sa'a a abinda aka tafi nema, inshaa Allahu kai me nasara ne akan komai na alkairi da
ka sa a gaba, dan haka don't feel nervours, u will do just fine, u can do it, saboda kai din na
daban ne a cikin mazaje,karka manta da karanta lahaula wala quwwata....... da hasbunallahu
wa ni'imal wakeel, Allah will be at ur aid, he will guid and protect u, ina son ka Jabeerun Baba"
ta fada tare da miqewa da sauri tana dariya bin ta yai ya cafko ta ya hade ta da gini, " maimaita
me kk ce" turo baki tai tace " yo ni me nace, dan dai kawai an ga yau mijina zai tafiya sai kuma
a ce za a min yar qure a ci zalina, dan irin wannan kallon da kk min ji nake kamar na dawwama
da kai a haka a tsaye ba tare da duniyar ta juya ba" ta fada cikin qasa da muryar ta, wani irin
farin ciki ke ziyartar zuqatan su, a cikin ran su kowa na yaba kyau irin na dan uwan shi, bakin
shi ya kai saman nata, ya shiga sarrafa lips din su, cikin salon da dikkan su zuciyoyin su sai da
ta narke, biye mai tai sosai suke jin dadin hakan, aka kace musu da sallama, Nafeesa ce tai
sallama ta taho dan Juwairah tace ta zo sui komai da wuri zata gida yau, janye jikin shi yai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login