Showing 30001 words to 33000 words out of 70697 words

Chapter 11 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf

27 Apr 2025

4566

ta shiga uku, ta hada sharri kuma
ya zame mata tsiya......
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ' YAN ABUJA



BY HAERMEEBRAERH



Masoya novel din 'YAN ABUJA dan Allah ku min hakurin jina da bakuyi akai2 yanda na saba,
inshaa Allahu in komai yai normal zan ci gaba ba da tsaya ba har sai na gama dika. Na gode.
Love u all❤





Page 17:

" wa'alaikumussalam shigo shigo yar uwa kiga me yayana ya saimin" Juwairah ke fadin hakan
cikin murna da kuma zumudi, Nafeesah ce ta qara sa shiga itama cike da dokin ganin me za a
nuna mata, sanda ta gani itama yar qarar murna tai ta haye kujerar da Juwairah take" kaiiiii
amma Allah ya saka ma Yah Jabeer da alkairi, ya sai mana waya mun daina leqen ta qawaye" "
to malama ba wai an sai mana waya ba na dinga neman ta ina rasawa" " hhhhhh Allah baki
hakuri ai wannan wayar inna dauke ta yanda kk san jariri sai kin nema na miqo maki, ko in tana
buqatar a sa mata kudi" dariya suke sosai, " yauwa wai ni ruwan meye wancan a butar qarfe na
ga kin saka a garwashi?" " Oh ban cire ba dama je ki sauken dan Allah ki dawo na fada maki
hajiya tambaya" " ah to dan kin san in baki fadan ba baki da zaman lfy yau" fita tai ta sauke
mata butar ta dora ruwan wankan ta , ta koma dakin, xama tai tare da tanqwashe qafa agaban
Juwairah tace " To malama a bamu darasi, dan zama dake akwai diban ilimi" " ke ko, ke ko,
hmmm kina raina sanin da Allah ya baki ne amma kin fini ilimi ai, kefa duba ki gani yanzu ci
gaba da karatun ki kike ni fa ina zaune a gida kullum" " kema zaki ci gaba ne komai lokaci ne sis
oya ina jin ki meye wancan a butar qarfe?" Dariya Juwairah tai sosai sannan tace" ke dai ba ki
mantuwa to magani ne, maganin infection musamman na masu ciki, Mama Bilki naga ta yi
lokacin cikin Ammar shine nayi, Oh har naji ina son ganin yaron nan wallah" " to naji magani ne
amma ai baki fadan ya ake hada shi ba ko" haka ne, kinga dai da fari zaki samu ganyen
garahuni, da 'ya'yan hulba ki tafasa su sosai sai ki bari ya sha iska sai kina tsarki da shi, da
yawan masu ciki suna fama da infection sosai, mai fidda ruwa kala2, amma da zasuna amfani
da wannan zai masu magani duk da ba wai yana dauke shi dika bane kwata2 amma yana
ragewa sosai, in aka hada da wasu magungunan na sanyin" " yauwa ko ke fa ba ga shi kin qara
min ilimi ba ni ina ma san wannan abun,in ba yanzu ba, yauwa rannan naji kina fadama
shamsiyya wani abu lokacin na fita ban ji me kuke cewa ba game da warin gaba" " Oh k
wannan, dama muna magana ne akan macen da take fama da warin gaba na farko dai akwai
na lalura, akwai wanda mace da kanta take jawo wa kanta" "hhhhhh kaji Matar yaya wai mace
ta jawo wa kanta kamar yaya? Kana sane kabar jiki yaita tsami" dariya sukai sosai suka tafa, "
Allah da gaske nake, yanzu misali Nafee, ke ce kin tashi a rana kin wuni da pant daya a jikin ki,
kin je fitsari kin yi fitsari baki wanke wajen sosai ba kin maka pant kin mayar, kin yi bayan gida
kin maka kin mayar, sannan da jiqar da komai kk mayar wa, ki fadan pant din dan uwan ku ne
da zai qi wari?" " hhhhhhh wallahi dole yayi amma dai misalin nan dama ba dani aka buga shi
ba a canja gaskiya a saka Salma" " wulaqanci yayar tawa, Allah sarki mutan Abuja ana can ana
shan dadi an manta da dangi" " hmmm ke dai bari buri ya cika, Allah muma ya sada mu da mafi
alkairi" " Ameen dai" " to yanzu fadan ya za ai ai maganin wannan warin dan Allah dan akwai
yar makarantar mu, kin zauna kusa da ita sai kinji wannan warin, dan ba zanji kunyar fada mata
ba, da azo ana ta gulmar ta tana jin haushi" " Allah sarki, aiko gwanda ki sanar da ita, dan aboki
na gari ke wayar da kan abokin shi, kina ji ba, a rana a baki canja pant a ki canja sau uku, ya
zama na kina da tsimma ko towel qarami a toilet din ki wanda in kikai fitsari ko bayan gida zaki
tsane wannan ruwan, sannan in kin zo tsarki ki fara da gaba ko da baki komai ba, sannan baya,
karki hade wajen wajen wankewa, in kk gama kk goge wajen sai ki maida pant din ki, in rana
tayi kikai wanka sai ki canja, da dare ma haka, ba yanda za a same ki da wari ko da baki shafa
misk, balle a same ki kina wanke wajen da ruwa mai dumi da kk zuba zuma asalin me kyau,
wannan wanke gaba da ruwan zuma ya samo asali ne daga Annabin rahama yana daga taskar

magungunan daya bayar muna amfani da shi, bake ba warin gaba in dai kina wanke wa da
ruwan zuma kina saka misk, kina tsanewa in kinyi bayan gida, ina fatan na amsa tambayoyin ki
Hajiya tambai" " hhhhh wallahi kin biya ni kin amsa har da wanda ban ma zata ba ke dai Allah
ya barki da yaya, ya sauke ki lfy" cikin jin dadi tana shafa cikin ta ta amsa, tashi tai ta tafi bayi
da butar ta a hannu, bayan ta fito ne take ce ma nafee" Nafee gobe ne kin san ranar gyaran
jikina ina zan samu dankalin turawa pls na wa ya qare" karki damu zan samo maki kan gobe, ji
cikin ki ya fa girma amma kk maganar gyaran jiki, ki bari ki haihu mana" " Tab aa ni dai ki samo
min, in babu ma ina da zuma da sugar kawai ki samon lemon zaqi ko daya ne ko biyu" " to Allah
ya kaimu, bari nai wanka na fita makaranta" "to Allah ya bada sa'a, bari na dan huta nima".







" Alhj wannan itace mata ta da kuka karba min auren ta a garin kano, dama na dawo da ita nan
ne dan na dinga samun kulawa, zama ni dayan ba dadi" Talle kenan ya fada yana sosa qeya,
murmushi uban gidan na shi yai yace" Allah sarki ai ba damuwa, hakan da kai kayi tinani, kuma
ka kyauta, ina maku fatan alkairi, Allah ya bada zuri'a dayyiba" " Ameen" gaida shi salma tai
kanta a qasa tana wasa da gyalen ta, ya amsa ba tare da ya kalli in da take ba, kudi ya qirgo
dubu goma ya bata, yace gashi ta sai wasu abubuwan da take buqata, amsa tai hannu na rawa,
rabon data riqe kudi haka ai ta manta, tashi sukai suka fito, suna isa daki ya miqa mata hannu,
fuskar nan ba walwala," me zan maka kuma" ta fada cikin tsiwa, " dan uban ki ni kk tambaya me
zaki min, to in baki san me zaki min ba bari na fada maki, kawo su nan" alamun da ta gani na
ba wasa yasa ta miqa mai tana hawayen baqin cikin ga samu ga rashi, murmushi ya fara yi jin
dumus da yai," Ko ke fa salameme na, yanzu ai kin ga ko dari biyar na baki ai yafi na qattin
qauye masu baki dari da hamsin ko" juyo wa tai cike da bala'i tana kallon shi kuma sai ta fasa
dan wani tsoron shi daya kamata, gani tai yana cire kayan shi, ita ko bata shirya ba, ga ciwon
jiki da take fama da shi, gashi shi in ya fara abu bai san ya bari a huta ba, sai ya gajiyar da
mutum, kuka ta fara tana" ni na barma dari biyar din dan Allah ka bari sai nan da kwana uku, na
gaji banda lfy" dariya yai sosai ya maida kayan shi" da kyau matar manya matar Dan Abuja
kenan, ku baku da buqatar kudi ai, ni na fita to ga wannan ki leqa waje akwai shago ki siyo
kwaki da sugar ki sha, ina jin har canjin gyada zaki samu ma" nera dari ya wurga mata ya fice
yana wata tafiyar yan duniya a shagide, kuka ta durqusa tana yi, " wai ni ina yan uwana ne,
suna can suna jin dadin su sun manya da rayuwa ta, basu san a halin danake ciki ba,Oh Allah
ka kawon dauki, na tuba, Juwairah kin huta, dabaki zabin aure ina zaki ba, gani ina cin ubana a
garin da na taso da kwadayin yin aure cikin shi" kuka take mai ban tausayi, yunwar dake cin ta
ce ta dawo da ita daga tinanin da take, tashi tai ta wanke fuskar ta, ta saka mayafi ta je ta siyo
garin ta da sugar da gyada, hadawa tai tana sha tana kuka,ganin duk talaucin su ba su shan
gari a gidan su amma yau gata da gari, share hawayen ta tai, ta jingina da katifar su, a haka
baccin wuya ya dauke ta.

" Adda Suwaiba ya kamata fa mu je ganin gida yanzu haka, haba tinda muka zo yau watan mu
na takwas kenan fa, muna cikin na tara, bamu taba zuwa gida ba, ba a taba zuwa mana ba, ga
labarin Salma shiru, har yanzu" " hakane kam ya kamata muje muga ya su Goggo suke, batun
Salma ki daina damun kanki tana can suna cin amarcin su, kin san mijin ta ma ba laifi akwai
kudi, wataqila ma basa qasar nan" " haka ne Allah ya jiyar da mu alkairi, amma nikam na
tambaye ki?" Ina jin ki" " dan Allah baki zargin komai game da mazan nan namu kuwa?" Kamar
ya fa?" Tina wa da tai in ta sake Suwaiba ta san me ake ciki kashin su ya bushe ya sa tai saurin
kauda zancen ta basar tace" ba komai yanzu dai mu tambaye su, yaishe zamu gida" " Ba rana
balle wata" amsar da suka ji kenan ana basu bayan an bude qofa an shigo, " ke tashi mu tafi
gida, ai an sada zumuncin haka, ku da kuke son Abuja kamar ran ku, in ban manta ba, Saudat
kan mui aure cewa kikai, in Allah ya baki miji kuka tare a Abuja sai kin shekara biyar baki je
ganin gida ba, ko ba ai haka ba?" Cikin qunar rai da kwallar da ta maqale mata tace" anyi haka,
amma a da ai ban da isasshen sanin ya Abujan take kuma gani nake zan iya amma ni yanzu
gaskiya gidan mu nake son zuwa naga uwata" wani hatsabibin kallo ya watsa mata, ba ta san
sanda ta durgusa ta dau jakar ta ba tai hanyar fita, sallama yai wa abokin shi wanda daga jin
warin da suke sai da suka biya sukai tatul, nikam nace Saude Allah shi kyauta karki daku
yauma.......�
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA




BY HAERMEEBRAERH



MAMAN YOUSUP
Mutan Gwambe ina godiya sosai da nuna so da qauna, kuma saqo daga Salamemen Talle tace
a sanar dake bata da qawa sama dake tana son ki sai kin isa ABUJA adama da ke�� ME
LOVE U XOXO❤




Page 18:

Goggo Sarai ce ta qame kan kujera tsabar ba a iya samun wajen ba ma, da nuna ita bata gaji
arziqi ba, iyakar wajen ta aka shata aka gyara, baqin cikin da kanta da kanta take, dan ko ba
wanda ya kula da ita, ita amma gani take all eyes on her, ita a dole ga uwar masu kudi, mijin
Salma kawai take jira su dawo daga waje a yo mata kabakin arziqi na waje, Ammar na hango
yana tafiya dugui2, dan ba wai ta gama kwari bane, ya zo wajen randar ruwan Mama Bilki, da
dikkan alamu qishirwa yake ji, Mama Bilki na daka tana baccin tsakanin azahar da la'asar( bacci
ne da in bawa yayi shi yake samun lada daga wajen Allah) ita ko hakimae ana zane ana kora
jus da meatpie, ga mafici a hannu irin wanda ake kamar zuge shi dinnan ta kwama uban baqin
glass a ido na ba mutunci dinnan, Abban su shi ke da bangaren ta yau amma gudun wulaqanci
sai dare yake shigowa, kan tace ita ke ci da gidan, ko makamancin haka, dan haka yana qofar
gida, Ammar ne ya dakko cup yai ta buqawa a jikin randar," Yauwa yaro fasa wa uwar ka dan
arziqin da ya rage mata ka huta gadon mugun abu kawai" bata gama rufe baki ba ya saki fitsari,
gangarowa yai qofar ta, habaaa ai kamar an watsa mata ruwan zafi, ta miqe kafin ta isa ya fara
qoqarin tafiya yana kuka, da alama ba iya fitsarin zai ba, daidai fitowar Mama Bilki da shigowar
Abban su, hannu ta sa ta wanke Ammar da wani lafiyayyen marin da ko Maman akai wa sai
jikin ta ya gaya mata," ganin wannan kini babbun iyayen naka masu son abin duniya da har
suke ganin Da namiji ya fi Ya mace daraja ba zai hani cin uban ka ba, in banda baqin ciki da
aka koyawa yaro qarami tin yana ciki, duba fa ku ga yanda ya tsanyaran fitsari a qofata yai
gaba, to ba zan lamunta ba" Ammar tsabar kuka ya gigice sai ga kashin ya biyo baya, zuciyar
Mama Bilki tafasa kawai take ba iyaka, tin da Abban su yake da ita bai taba ganin bacin ranta
haka ba, ita kanta Goggo Sarai ta tsorata , wandon Ammar Mama Bilki ta cire ta wurga a jikin
qofar da aka canja wa Goggo Sarai, qofa ce irin ta qarfen nan mai kauri milk color, ta aje
Ammar din ta isa jikin qofar ta samu wandon ta goga sosai har labulayen, sannan ta dawo ta
daga hannu zata wanka mata mari, amma sai naga ta tsaya,( nace kash dama kin qarasa mun
sha kallo) me ya tsaida ta oho, daukar Ammar tai da yake ta kuka yaqi shiru ta je ta fara
gyara shi sai da ta gama taje ta dauke wandon nashi ta wanke ta shanya, sannan ta qara
wanke mai jiki dika, ta bashi ruwa da abinci ta goya shi sai bacci, yana yi yana ajiyat zuciya,
wata irin wuta aka dauke a gidan gaba daya , ba mai iya cewa komai, Goggo Sarai na tsoron
tace kanzil yanda Mama Bilki ta bata rai bata san me zai je ya zo ba, ita kuma Mama Bilki ta
fasa marin ta ne ganin datajar Abban su dake bayan ta, shi kuma ya fuskanci hakan, sannan ya
yi shiru ne saboda kar ya bata damar magana ya san kuka zatai dan zuciyar ta cike take da
baqin ciki, sai da ya tabbatar ta fara sauka tinda ta ci gaba da yan aikace2n tsakar gida sannan
yace" kin ban mamaki Sarai ba kadan ba, ki duba kiga abinda kk aikata, yanzu marin da kk wa
yaron nan ko ni ki kaiwa ai sai naji a jikina ba shi ba ma, dubi yanda yatsunki suka kwanta a kan
fuskar shi, kamar quna, haba dan Allah, kin kyauta kenan, baki taba ganin fushin Bilkisu haka
ba , to ina mai tabbatar maki ki kiyayi sakata a irin fushin nan bana kusa, dan duk abinda ta
aiwatar akan ki ke kk jawo, kinga misalin hakan ai dazu ko?" A sannan ne ta samu bakin
magana, " eh tinda kun haifi dan gwal, dole mana ku fifita shi akan komai, to da dan da uwar na
san meye matsalar ku, baqin ciki, kuma nan gani nan bari dumamen mayya in dai nice ni da
Yayana yan albarka" juyawa tai fuuuu ta hau cire labulayen dika aka watso su tsakar gida ta

dau daya ta goge qofar dakin da shi, ta saka ruwa ta wanke, ta qara gogewa da labulen masu
kyau din, da su ta gyara wajen, duk kyau da tsadar labulayen haka ta saka hijab din ta ta fita
waje ta watsar ta dawo, tana wani isa da taqama taje ta canja wasu," a hayyyeeeeee
ayyuuuuririiiiii, to bari kuji sau goma wannan shegen tsinanne yana bata qofa sau go........bata
ida fadin me take so ba ji tai qummmmmm a bakin ta, ludayin hannun Mama Bilki ne ta saita shi
a bakin Goggo Sarai, ihu ta saka, ita kuwa ta je ta durqusa ta dau abin ta ta juya ta ci gaba da
aikin ta, Abban su mai zai in ba dariya ba, " Kai amma Gimbiya yau kam sai dai ace na zama
munafukin mata, amma kin burgeni, ke kuma da dai da kk kira shege, duniya ta san ni ne uban
shi, sannan, tsinanne da kk kira min da ba zakiga tsinewa a 'ya'yana ba inshaa Allah ina mai
musu addu'a ko keme abin qi Allah zai karen su, sai dai kiga tsinewar a kan kan ki dan ba yau
na fara jin kin kira min Da da wannann sunan ba, ke yanzu ba abin kunya bane ace yar haka ta
fara shiga tsakanin ku? To ina qara gargadin ki ki kiyayi randa bana gida ki taba wannann
baiwar Allah ina tausaya maki" ya qarasa maganar cikin dariya ya fita qofar gida, duk abinnan
da ake Mama bata ce uppan ba aikin ta take kawai, Goggo baki ya haye sama, abinka da farar
mace fatar tai jawur, daki ta shiga ta dau waya ta danna Number n su Suwaiba, dannawa tai
tayi ana turanci, gashi yau harda Malam din akai fadan ba mai duba mata yaji me ake fada,
kama kan ta tai da taji yana ciwo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login