Showing 42001 words to 45000 words out of 70697 words
Chapter 15 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf
kwallah, ji take kamar an yake naman wajen dan azaba, ni ko nace ba kama bane Suwai matar
manya
Baki ta bude tace.....
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA
Ina qara bada hakuri dai dan Allah masu son Novel din nan ta PC ba zai yu nai ta sending
from d begining ba, i am so sorry, kui man hakuri zuwa dan kwanaki kadan zan kammala dika
na mayar Document, inshaa Allahu, Na gode sosai,Love u from qarqashin heart, u guys ar
awsome ❤
Page 23:
Gobe ne ranar da Jabeer zai dawo, waya suke da Juwaireren shi, gaba daya ta shagwabe ta
susuta mai lissafi, ji yake kamar ya dawo a daren, ko da fuskar ta ne ya kalla, ya san zai ji
nishadi, kwantar mai da hankali tai akan gobe suna tare, kar ya damu, tina mai tai akan yai
addu'ar bacci kafin ya kwanta, sukai adduar tare suka kashe waya, bayan cika juna da "I love
u", da sukai bacci ne a bangaren Juwairiyya da Jabeer mara dadi, don tin da ya tafi hakan ne ,
baccin baya masu dadi ba junan su a kusa, a haka bacci barawo ya dauke ta bayan juye2 da ta
sha, da sassafe ba yan tayi sallah, tayi abubuwan da suka zama na al'adar ta da safe kamar
yanda kuka san Juwaireren Mama, tashi tai yau ranat gyaran lambun ta ne, taso ta bar shi tai
gyaran gida tai ma Yah Jabeer din ta girke2, amma ta saka diguwar riga gajera, mai hannun
vest, ta dau kayan gyara lambun ta taje, ta tattaba abubuwan da suke da buqatar gyaran,
Juwairah akwai saurin aiki akwai kuma biyan buqata( ba a son mace ta kama aiki daya taita
fama da an xo aga ba wani abun kirki da ta qulla bayan kuma ita a qasan ranta aikin nan take
bil haqqi, gani take tana ta faman aiki amma an kushe ta, to yar uwa kin kama aiki daya kina ta
yi kuma wataqila ba ma wanda ya fi zama dole ba, kin bata lokacin ki ya tafi baki qulla komai
mai amfani ba, kinga in kina da miji mai mita akan komai dole zai magana, dan haka ana son
mace mai zafin nama, mai saurin aiki, kuma tai aikin da kyau) tama gamawa ta wanke qafa da
hannu ta shiga daki, ta hau gyaran ko ina, ta canja bedshit, ta dakko wancan ta fito da shi ta
gyara palon ta, ta canja mazaunin kujerun ta, sallamar Nafee ne ya sa ta dan tsagaita da aikin
ta, shigowa tai" haba matar Yayah ai sai ki kirani, da wannan tsohon cikin kk aiki irin haka, wata
bakwai fa, kun shiga na takwas, ki ja mana aiki, habaa gaskiya banji dadi ba" ta fada tana turo
dan bakin ta wai ita ba a kyauta mata ba, murmushi Juwairah tai ta kama kafadun ta" kar ki yi
fushi da ni 'Yar qanwata, taho ki taya ni, na dauka kina taya Innarmu aiki ne, shiyasa ban kira ki
ba, tayata aiki ai yafi nawa" murmushi sukai tare suka ci gaba da aikin, bayan sun gama canja
fasalin wajen ne, suka debo ruwa da tsumma nan ma suka goge ko ina, kitchen ta tafi ta barma
Nafee ta qarasa nan din,taje ta mai na shi kyaran sosai kamar Jabeer din zai leqa in ya fara
shigowa, bayan ta kammala da nan ne ta wuce toilet, Nafee ce ta bita ta amshe wankin toilet
din , bayan sun gama ne aka fara gyara tsakar gidan, in da yake anyi siminti, nan wanke wa
Juwairah tai qasan kuma suka share" wai nikam me zaki dafa mai ne naga baki fara batun girki
ba" His favorite u know, da kudin da ya ban jiya nai aike kasuwa an siyo man kwai, nama
dankalin turawa, da cabage sai carrot da green beans kindan bak da su a lambu, sai flour ina
da mai, an siyon yan kayan qamshi da maggi, dan wake zan mishi, kin san shi a duniya na kula
yana son abunnan" " wai sosai ma kuwa, bakigan shi bane yana satar danwake a tukunyar
Innar mu da dai kin sha dariya, Innar mu in ta kama shi sadaf2 take tafiya ta damqe hannun shi
da ludayin tsamar danwaken, yai ta ihu ta qi saki" dariya sukai tayi sosai tinawa da wannan
kabarin, miqewa sukai suka fara gyara dankalin, suka yanka veges harda na lambun nata, ta
debi dan alayyahu kadan, da albasa mai ganye, suka gama yankawa sai ta soya dankalin nan
ta dakko dafaffen naman ta da suka yanka qanana ta soya sama2 ta aje gefe, sannan ta rage
man suyar ta dakko jajjagaggen kayan miyar ta, da ba timatir sosai guda biyu kawai tasa ba
manya ba suma sosai, ta saka da tafarnuwa da kayan qamshi ta soya ta saka maggi da dan
gishiri, sannan ta dakko wannan veges din ta zuba akai bayan ya fara soyuwa, ta juya suka
tirara, sai ta juye akan wannan dankalin da daman, ta juya su, suka hade, dakko dafaffen
kwanta tai shima bayan ta bare ta hada da shi ba tare da ta yanka ba, ta juya su tare,flask din ta
ta dakko ta zuba wannan hadin ta rufe ta rage masu nasu, dakko flour tai naga ta dakko wani
gari" Matar yayah wannan garin meye?" " to tambaya an fara ne, garin wake ne na markada da
yar dawa kadan, sai alabo, na niqo su shine zan hada da flour din yafi dadi sosai" "
Auuuuhooooo, to ai sai ana yi ana tambaya ko kinga laifina?" " Aa aa matambayi baya bata ai"
murmushi sukai ta debo kuka, mai dan yawa yanda zai santsi, ta dakko ruwan kanwar ta, ta
zuba ta hada da wani ruwan dan bata son ta cika kanwa da yawa, ta kwaba yai laushi kwabin,
ba tauri sosai ba ruwa, haka ta kwaba ruwan na tafara ta fara jefawa qanana, dan yafi dad,
bayan ta gama ta tsame a ruwa mai kyau ta hada mai nashi a flask, ta miqe ta barma Nafee ta
qarasa ita timatir daya ta dakko nunanne, ta fada mai sugar a tsakiya bayan ta yanka, ta hau
goge fuskar ta da shi, sai da ga baya kuma ta dau rabin ta saka xuma ta goge fuskar shima,
nan da nan wani duhun murhu da rana ya bace fuska ta dau kyalli da kyau, bayan ta gama
kuma ta dakko lallen ta, ta saka mai man kwakwa kadan ta kwaba shi, ta hau murge jikin ta duk
inda hannun ta ya kai musamman fuskar ta, kafin kace me Juwairere tai kamar ba ita ba," tab
lallai Yayah na shan dadi aradu, yau fa ba ranar gyaran jikin ki bane, bama ki dade da yi ba
amma ji yanda kk koma kamar wata tauraruwa" " Nafee kenan, ai ita mace ana son in mijin ta
yai tafiya ko na kwana daya ne ya dawo yaga ta canja kawai ko ta ina, balle wannan da kk gane
we ar talking about Yah Jabeer, My love, everything" dariya sukai, Nafee nata tsokanar ta ta
gama ta shiga wanka, shigar da yake matuqar so tayi ta dakko kayan ta fara sakawa, doguwar
rigar material ne aka mata irin na masi ciki, an daure sama kamar bra akai mata sai hannun ya
zamana a wuya aka daure shi, cikin nan ya sha mai da gyara, sai kyalli yake gwanin sha'awa,
sai dogon wando da akai mai fadi sosai ta zura, ta dakko kayan gyaran gashin ta, ta tsaga daga
gefe, ta kwantar da shi, ta daure in a ponytail style, qamshi kam ranar kamar an barin turare,
fuskar ta daga powder sai lipstick, ta gyara girar ta, ta saka kwalli,( kwalli na da matuqar tasiri
ga mace, macen da ta saka kwalli ta iya kallo ta yi a rayuwa, in baki iya ba koyi ki fara)dogon
hijab ta saka, tai sallar magrib ta zauna, tai azkar din ta, ta fara karanta qur'ani, ana kiran sallar
isha'i ta tashi ta fara, Sallama yai ya shigo, yana ganin tana salla ya aje kayan shi yai alwala
shima ya tafi masjid, tana idarwa qara gyara jikin ta tai duk da ba abin da yai, ta qara turare, ta
gama, dauke kayan da ya shigo da su tai, na ajewa a kitchen ta kai ta fito da kayan nashi,masu
datti ta fitar wamda bai amfani da su ba ta mayar wajen kayan su, sai wata leda da bata taba ba
ta aje a gefe,daga alamu tsaraba ne, ruwan wanka ta je ta hada mai mai dumi, ta dawo kenan
zata zauna taji shi, bayan qofa taje ta maqale tana ta dariya qasa2, shigowa yai yana ta dube2
bai ganta ba, sai da ya kama qugu sannan yace" Juwaireren Mama ko ki fito ko na zauna a
qasa naita kukan rashin ganin ki, in an shigo nace baki son gani na ne" kan ya rufe baki yaji ta
mai wata iriyar runguma ta baya wadda tasa shi fidda sautin da bai san ta ya akai yayi shi ba,(
rungume mutum ta baya akwai yanayin da mace ko miji zasui ya zama ba wata runguma da ta
fita dadi, ana yin ta ne ta hanyar zuro hannu a hankali ka zagaye mutum sai ka ja shi baya cikin
shauqi ka manna shi da jikin ka) juyawa yai gaba daya ya daga ta sama, suna ta dariya, kisses
kam kun san ranar an yi bari da ruwan su, zaunar da ita yai a cinyar shi, yana shafa cikin ta,
yana ma cikin surutu kamar wanda yake hira damutum babba, dariya kawai take yi ita kam, "
sannu da zuwa hasken cikin gidana, tin da ja tafi kaga daya gidannan duhu ya mamaye shi,
yau haske da ya bayyana daban ne, na gode Allah da ya ban kai a matsayin miji, Yah Jabeer ba
zan iya rayuwa ba kai ba, i missed u so very much" ta qarasa tare da qanqame shi tana
hawaye, dagota yai yana jin wani sabon qaunar ta na ratsa shi, dan yasan she meant every
word, " Hushhh Husshhhh my princess, ki daina kuka, Yah Jabeer na Juwaireren Mama ne ita
kadai, bana fatan na wayi gari baki kusa dani, u ar my happiness, i cant do without u, u ar
everything that i ever wanted in my life, so don't be scared of loosing me, nine ya kamata naji
wannan tsoron, amma ba zan damu ba dan nasan zuciyar ki, da ruhin ki , da gangar jikin ki
nawa ne" wata runguma ta qara mashi da ta saka shi jin dadi sosai, daga shi tai ta ja hannun
shi zuwa wanka ta taya shi yai wankan yai brush suka fito ta shirya shi bayan sun gama ne kan
shimfidar da suke cin abinci ta jawo hannun shi ta zaunar da shi, shikk binta kawai yake kamar
raqumi da akala, dan waken ta fara zubawa a gefe, wanda har wani kyalli yake dan santsi
sannan ta zuba mai wannann hadin da tai na dankali, zobon da ta dafa da abarba, da cittta
kaninfari, kai da kayan qamshi dai da suka dace dika, ta saka harda cocumber, ta sa sugar, ci
yake yana lumshe ido kawai, yana wani gurnanin magana amma ba a ganewa me yake fada,
daukan zobon da aka saka a randar sanyi yai dan basu da fridge yai ya kurba, saurin bude idon
shi yai sannaj ya mayar ya kulle, " Yah menene, yayi daci ne jo wani bu?" Ta fada tana zaro ido
waje dan a tinanin ta ko bai mai bane, " matso kiji me yai" yana dan yatsina fuska, ita kuma sai
ta danji zuciyar ta ba dadi, saboda gani take ta bata xobon garin iyayin mai hade2, dan ba ta
san dama ana saka cocumber ba qirqira tai, matsawa tai kanta a qasa, " sai kin rufe ido zaki iya
shan wannan abun, matso sosai na baki da kaina kiji ya yai" matsawa ta sake yi, ta rufe idon,
jitai ya kama lips din ta yana masu wani salon da ya sa ta magana a qasan maqoshi, saida ya
dade kan ya sake ta, ta kasa bude ido, dan wasu taurari ke mata yawo a kai" bude idon mana
Princess, ni ba mai kudi bane bare na maki kyautar wannan kayan dadin da kk ban yau, amma
na san i will make u feel something special, with every part of me" daukr ta yai sukai daki, zan
bisu aka bugon qofa,nace ba sai an karya ma Hammana hanci na ba, zan tafi
malamai
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ' YAN ABUJA
BY HAERMEEBRAERH
Page 24:
" Adda Saudat dan Allah ki ban dubu daya mana ina son in dan ja jari ne ko ba yawa, xaman
haka baya min dadi,ke ma kuma ya kamata kafin kudin hannun ki su qare ki kama wata sana'ar
saboda kin saba yanzu da kudi, randa kk da buqatar su kk rasa ba qaramin damuwa zaki shiga
ba" tinani Saudat take mai zurfi, can ta nisa tace" gaskiya kin ce wani abu kema, zan baki dubu
biyar ki ja jarin, ni kuma zan fara kasuwanci ta waya da naga qawaye na da nai a whatsapp da
facebook sunayi, ana samu in ka riqe amanar mutane, sai kaga ka samu riba mai yawa kana
daga zaune" " yauwa Adda, sannan ina son nuna maki kinga Mama Bilki mace ce mai kirki, tana
matuqar son mu, sai dai tabbas tana kishi da Goggo, wanda wannan dole ne a zaman kishiyoyi
dama,mu sai mu kau da kai akan wannan, tinda iyayen mu ne, ba ruwan mu da hurumin su ta
wannan bangaren, ya zama wajibi mu masu biyayya dikkan su, su a matsayin iyayen mu, itq a
matsayin matar Abban mu" shiru Saudat tai domin maganar qanwar ta ta yau tana shigar ta,
amma akwai nau'i na girman kai, da kishi a zuciyar ta, " hmmmm zan duba na gani" ta miqe ta
dakko mata kudin ta bata, akan idon Goggo kuwa, " habaaaa Salma ai innice ke yanda na canja
uwa, yan uwan ma canja su zan, auhoooo ba zaki iya canja yan uwa ba saboda kin same su su
masu arziqi ne ko? Zaki roqa za a baki ko" " ni fa Gogga ba haka bane, ya kamata ki bude idon
ki ki gane inda gaskiya ta dosa, ki daina rufe idon ki akan abinda bai kamata ba" " rufen baki
sallamammiya kawai, an yi asiri da tuggu kala2 an rabani dake, to kije nima na huta da
dawainiya, da dan wani da zanyi" juyawa tai tabar wajen Salma kuwa cikin qunan rai da baqin
cikin halayya ta uwar ta ra shige dakin Mama Bilki, wadda taji komai, fadawa kan cinyar ta tai
tana kukan takaicin hali irin na uwar tasu, shafa kanta kawai Mama Bilki take, bata furta mata
komai ba," Mama ni fa ba kwadayi ne ya sa na tambayi Adda Saudat kudi ba, na tambaye ta ne
naga ko tirare bani da shi, ga shi yanzu sai da Alimun ko lemon tsami nake amfani a madadin
tirare, ba dan komai ba sai babu da take neman ta min yawa,amma in ina sana'a kudin zasu
taimakan wajen kula da abinda ke cikina, shine Goggo take fadan maganganu marasa dadi
akaina" " hakuri zaki Salma uwa ba abin wasa bane, dole mui mata biyayya in ba inda za a
sabawa Allah bane, dan haka ki hakuri tin da kin samu jarin yanzu me zaki na yi na siyarwa?" "
Mama Bilki ni da ina son na fara saida Meatpie ne, naga kina da injin yin taliya, kuma na kula
kayan flour ana cinikin su, in ba su ba ban san me zan iya yin sana'a akai ba" " hakan ma
shawara ce mai kyau, Allah ya sanya albarka" " Ameen mamana" kwantar da kanta ta sake yi a
jikin ta ita kuma tana shafa gashin ta.
Yau kusan sati daya da kwana uku kenan Suwaiba na kwance tana jinya, Alhj Salihu dayaga
zata farka ya danna mata allurar bacci ta koma, ko ya shaqa mata wata powder ta koma baccin,
a haka tai wadannan kwanakin, zai mata wanka, zai canja mata kaya,sannan ya saka mata drip
dan tana samun abinci ta jikin shi, ya zama babban likita kawai a cikin gifan shi, a haka sai da
ya kula wajen ya warke tas sannan ya kyale ta da allurai na bacci da yake mata, yau ne ranar
data bude idon ta tana kallo. Wajen kamar sabon waje aka kaita, a hankali ta bude idon gaba
daya, akan na Alhaj Salihu ta bude su, kanta ne taji ya mata nauyi,kwantar da kan ta sake yi a
pillow, jikin ta a mace ta bude baki tai magana da kyar" Me ya samen Sweet? Me yasa nake jin
zafi sama2 a qirjina kamar naji ciwo?" " Shiiiiiiii karkina nagana sosai, hatsari muka samu a
gidan, yan fashi ne suka suka shigo, kina bacci suka yanke maki Nono, ni kuma dana dawo na
ganki kin suma shine nake ta kula da ke" a firgice ta miqe daga kwanciyar," an cire man nono?"
Ta fada tare da zaro ido waje wanda suka cika da kwalla mai dumi, " na shiga uku ni
Suwaiba,ya zan rayu ba mahaifa ba nono, gaba me zan rasa kenan, Alhj na fa san kai ne
sanadin rasa nono na Saudat ta fadan ban ji ba ban yarda ba, saboda ina son ka, ko da ina son
kudin ka, ya zan rayu yanzu ba nono ba mahaifa" rushewa tai da wani kuka mai ban tausayi,
cikin tausaya mata Alhj ya fara