Showing 69001 words to 70697 words out of 70697 words
Chapter 24 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf
asiri a kowanne lokaci abar so ce ga kowa, ba namiji ma kadai ba
ga kowa.
6- Mace ki zamo mai tsari, ya zamana kina da lokutan yin abubuwa, in kina haka za a same ki
mai tsafta, baki kwaba wannan da wancan, misali, kina girki wannan bangaren zaki iya ci gaba
da gyaran daki, sannan ko ya za ai mace in zaki wanki ki fara gyara dakin ki da gidan ki sai ki
zuba wankin ki tayi, akwai wasu dana kula ko nace da dama, taqamar zasui wanki sai kiga
gidan kamar bola da kin magana ace wanki zan shiyasa, yana daga cikin tsari ki ware ranar da
zaki na ma gidan ki gyaran tsaf misali muce a qarshen sati ko sati biyu ko wata daya ki fitar da
komai daga mahallin shi ki share ki wanke ko ki goge, sannan yana daga tsari ki ware ranar
zuwa kitso da qunshi, sannan ranar yin gyaran jiki irin dai na Juwairah, in Allah yasa gidan ki
kina da halin yin lambu kin yi to ki ware mai lokacin duba shi, in baki da lambu a sameki dai da
wata shuka da kk kula da ita ga lada ga huce takaici ga amfani,musamman ZOGALE.
7- kar ki zama mai kwadayin abun hannun namiji, komai qanqantar shi komai yawan shi, in kk
kasance mai kwadayi tabbas zaki wahala, wataqila ma a kwadayin qima da darajar ku ta zube
son ki a hankali ya fita daga zuciyar shi, sannan qataqila in bakinda rabon zama da wani sassa
na jikin ki ki rasa shi in d process of kwadayi, da roqo, kamar dai irin na Saudat mahaifaless.
8- A rayuwa kullum Namiji shine jagora shine uba shine yaya ko da kuwa qani je yana zama
shugaba, ko abokin shawara, dan haka in baka kasance mai tausayi da tallafawa mace ba ka
aje sunan ka a namiji ka daura dankwali ka bi layin matan aita buga cinya da kai, ku duba
rayuwar Yah Jabeer da Abban su Salma , Yah Jabeer ba abinda bai taya matat shi, har da
gyaran jikin, shaving, gyaran gashi, wanka, wanki, wajen haihuwa ma tare sukai komai, da ace
mazan mu na zuwa dakin haihuwa suga azabar da mata ke sha, wataqila da sun rage ma mata
rashin mutuncin da suke masu, sun tabbatar matan suna ta mata, suna matuqar qoqari, suna
jarumta, da tausayi da sadaukarwa ya shiga zuqatan maza, da sun tarairayi abinda aka haifa
masu da kyau da mutunci. Ta wani bangaren kunga yanda Abban su Salma ya dabbaqa sunnar
Rasulullah yake kiran matan shi da suna masu dadi, kamar Gimbiya Da kuma Sarauta, wannan
sunna ne ko mai tsufan ku soyayyar ku karta gushe,SO baya tsufa sai dai masoyan su tsufa ju
jeme, amma soyayyar su na nan.
9- mace kar ta zama mai zazzafan kishi, zai lalata mata rayuwa da tarbiyyar yaran ta, zai sa miji
duk son daya ke maki ya fara raguwa, sanan mutane ma masu hankali zasu fara tsanar ki,
kuma daga baya kizo kina dana sani, lakin kar ki bari kishiya ta zama tana cin kashi akan ki,dan
ko islam bai yarda ka zama mai sako2 yanda mutane zasu raina ka ba,kamar Mama Bilki, ta
riqe zaman auren ta da amana ba mummunan kishi, tana da sanyin hali da hakuri,amma me
bata yarda a taba yaran ta ba, ta tsaya masu, sannan kuma bata tsayawa ai hayaniya da ita in
abu yai yawa action ta dauka, amma ban ce mace ki zama sarkin fada ba fa in dai tabbas
zaki dau halin Mama Bilki sak to ratuwar ki da kishiya zaki samu sassaucin zama.
10- Qofofin Allah a bude suke ga bayin shi da suka yarda akwai shi kuma shi mai rahama ne, to
duk zunubin da suka aikata ko da shirka ne, har dai in basu mutu akai ba suka tuba to Allah zai
yafe masu,kamar yanda misali ya tabbata akan Kallah ya ce akwai lokacin tuba a gaba amma
me yana fita mota ta mai lalata, ta dauke shi a duniyar, ai kunga ba lokaci kenan, mutuwa tana
jikin skin din ku, at anytime zata iya cika mana aiki da izinin Allah dabularnin mala'ikan mutuwar,
take za a zare ran mu, sannan shi Salihu daya tuban ga shi kudin dai yaoe dasu a bayan na
haram daya tuba ya gyara ya sha wuya na dan lokaci na sana'a wan da a da bai san ya zai ba,
daga baya kuma yai kudi ta hanyar halal.
11- Matan da basu taba haihuwa ba sui hakuri, Allah na sane da mu baki daya, ki zama kina wa
kanki wannan adduar yar uwa" Ya Allah Ya rabbi ya khaliqu kulli shai'in Allah ina riqon ka, indan
haihuwa alkairi ce a rayuwata da ta mijina da al'ummar musulmi da musulunci Allah ka bani,
idan sabanin haka ne Allah ka samin hakuri da juriya tare da dangana, Allah kar ka bani, ka
shiryar mana da sauran yaran musulmi su zama masu albarka" wallahi damuwar eashin
haihuwa na maki alqawai in dai kinyi adduar nan da ikhlasi Allah ba zai barki haka ba sai ya
maki zabij da kk nema.
12- Ta bangaren maza kuma in matar ka bata haihu ba ba shi zai sa ka juya mata baya ba, dan
mace bata bawa kanta haihuwa, wataqila matsalar daga wajen ka ne, to misali ace ma daga
wajen ka ne mace zata iya hakuri ta zauna da kai a haka, ka duva ka gani ba ta da wani namijin
bayan kai amma zata zauna da kai, kuma ba shi zai hana kai ta maya rashin mutunci ba, amma
kuma in ita ce mai matsalae wataqila ka sake ta, in ka barta kuma ka ce aure zakai ba zaka
zauna da juya ba ita daya, ka gani mata ko yaushe su ake tauyewa duk inda aka je aka zo, me
zai hana mazaje ku dage ku dabbaga sunna, ku kuma qoqar ta ku tabbatar ma duniya ba
addinin da yaiwa mace martaba da qima sama da ISLAM?
13 - ko wanne stuation dayan ma'aurata ya shiga dayan ya nuna mai i am by ur side no matter
what, duk daci duk zaqi ba zan barka ba tare muke a ciki.
14- soyayyar yan uwantaka abu ne mai matuqar mahimmanci sai da hadin kai bawa ke zama
sarki, sai d hadin kai mayaqa kan samu nasara, in kanku a hade yake zuriar ku zata zama abin
tsoro da kwarjini ga kowa, za ai tsoron taba dayan ku, za a na ganin ku as ka tabo daya goma
ta shafe ka wa zai so?
15- mace ana son ku zamo mai iya tarairayar miji, mai bashi haqqin shi na auratayya a koda
yaushe, mai iya salo kala daban daban, ba tare da kauce hanya irin na matan yanzu da suka
maida kallon turawa suna zina ya zama wai suna koyon style na auratayya wa'iyadhubillah, me
ya kai ki ko me ya kai ka? Me suke da shi da mu bamu da shi, zuciya ce da kwakwalwa, muma
muna da ita,a rana in kin so zakui style kala biyar ko fi, ku gamsar da juna,ba tare da kowa ya
koya maki ba, to ku sani ni a nawa duk namijin da zai saka mana wani shirme mu kalla kafin
sex ba namiji bane, rako su yazo in sun gama sabgar su ya bisu su koma, dan ba rashin zama
na mijin da ya wuce ka kasa dagawa mace sha'awa sai kun ga wasu awaki na yi sannan ka
samu ka take matar ka da ya fi wannan, ga illoli dake tattare da hakan, fushin Allah da tsinuwar
shi akan ku dika, haihuwae yaran da ake cewa yanzu sun kashe iyayen su, sannan kuma ciwon
makanta, sai mai wannan hali ya shirya masu in bai daina ba. Sannan illar kallon nan yanzu ta
shine aka yawaita mata yan lessbians da maza gay dan musiba da qazanta Allah ya kare mu
da zuriar mu.
16- Sadaukarwa, ka sadaukar da farin cikin ka dan wani musulmi ko dan uwan ka ya samu
farin ciki shima, ga lada ga qarin arziqi da zai same ka, zaka samu da yardar Allah Allah ya
mayar maka abunnan da ka sadaukar har da fin shi ma, kamar yanda Juwairah ta sadaukar da
Abrar ma Suwaiba nonoless.
17- kowacce mace dangin miji ce ki kula da yanda zaki tafi da dangin mijin ki kema naki dangin
mijin su kula dake in kika qi yin da kyau zaki ga ba kyau kema.
18- kula da tarbiyyar yara a tsakanin dangi, musamman cousens a wannan zamani, cousens
sun ja an aurar da zawarwan yammata da yawa, ba tare da an sani ba, zaki ga suna wasan
banza ba za a hana ba ace wai ai yayan ta ne, ba aure tsakanin su? Ke ko da aure yanda
zamanin nan ya baci akwai limit na komai, ko kiga ya damu da ita da yawa,ko yaushe suna tare
mamat2 ace ai suna matuqar shiri,kin tintibi dalilin shirin? Sannan kuma wajen bacci a bar yara
sakaka ta nam wallahi cousens ke dada bata mana yara da qanne, dan haka mu kula dan kin
tsaya akan yar ki baki laifin komai ba a duniya da lahira.
18- ina ma mata nasiha da qamshi, da kwalliya,tsafta girki iya magana musamman da yawan
mu bamu iya kalamai ba da magana komai yabawa muke, ki iya kwanciya, kirsa, kwarkwasa,
iya saka qananan kaya,da daura zani, iya kallo,shagwaba, wayyo da mata sun san me ke cikin
ta da wataqila har makarantar koyar da ita an fara bude masu, ki iya girki, macen da ta iya girki
mai aji ce ki ba ta da aure, ba raini tsakanin ta da kowa, ki zama mai sassauqan halin da kowa
zai so mu'amala dake.
*ina riqon mu dab Allah ko daya mu qoqarta mu saka a aikin mu za a samu gyara da canji,
wadda take da abinda na manta ban saka anan ba qofa a bude take da ta rubuto mana da
sunan ta da komai dan mu qaru*