Showing 66001 words to 69000 words out of 70697 words

Chapter 23 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf

27 Apr 2025

4553

ya min kyauta countless, to me zai sa dan akan abu daya danaoe so
ban samu ba na mai butulci? Ba zai yu ba, daga ranar da kk ji na qara aure Saudat ban qara shi
dan baki haihuwa ba ne, sai dan itama ina son ta,kuma Allah ne ya halatta mana qara auren,
dan haka ki kwantar da hankalin ki ni ba mai ra'ayin tara mata bane, bana.son hayaniya, bqn
son takura, mata da yawa na saka ni damuwa dan bana son raba fada kullum," ya qarasa ta
yanda tabbas yasan hankalin ta ya kwanta da maganganun shi, amma hawayen dadi sun kasa
tsaya mata, tabbas Allah ya azurta ta da namijin gaske, Allah ya qara mai hakuri da juriya akan
hakan ta ayyana a ranta, ci gaba da shafa wuyan ta zuwa bayan ta yai ita kuma tana wani
miqewa tana juya jikin ta anashi, tini ta burgita shi,ni kuma na ja sayyarar qafata na waje a
100�



"Ki taho da fidar yarannan, da tissue love" amsawa tai shi kuma ya zauna yana masu wasa,
bayan ta iso ne ta zauna kusa da su," ni dai gaskiya ban yarda ba nima sai an min wajen zama
a nan, dan wayo kullum ni a qasa ko gefe su a cinya"ta fada tana turo baki,dariya ce ta kama
shi, sai ya dauki Muhammad ya dora a wuya, sannan ya dago ta ya saka a cinyar shi,murna ta
saka tana mai kiss a kumatun shi, " Na gode na zaci ai ce min za ai nai hakuri yaran su zauna
da ba zan yarda ba sai dai a maida su daki ni na hau" ta fada tana sauka, dariya yake sosai,
dan Salma ba dai kishi ba, kishi take da yaran nan sosai , dan gani take gaba daya ya kwashe
soyayyar ta ya basu, lokacin shi gaba daya nasu ne in yana gida, amma a qasan ranta ba
qaramin dadi take ji ba, hankalin ta a kwance yake dan bata tsammaci hakan a wajen saurayi
da bai san ya zai gama kula da kan shi ba bare wasu yaran har biyu, kujerar basu abinci ya
saka su,ya dorawa kowa a gaban shi, ya basu cokula a hannun su na dama,sa kyar suke
riqewa saboda rashin iya hakan, amma yana tsaye in zasu karkace ya gyra masu, ta baya ta
ziro hannun ta ta tsugunna itama ta kwantar da kanta a bayan shi ta furta"I love u" shima
waiwayar da kan shi yai suka hada ido yace mata" i love u more" kiss ya mata a goshi ya juya
ga yaran su( da na kowa ne, baka san wa zai more shi ba, dan haka bahaushe yace, da da
dukiya ba a masu mugunta, in ka lalata wataqila kai zaka amfana a gaba,ka bata to da me zakai
amfani, in ka gyara kuwa ka amfana, wani ma sai ya gama gyarawar ya zamana ba shi zai mora
ba ya gyarawa al'umma ne, ladan shi na a wajen Allah, wani kuma sai ya bata ya mutu ya
barwa al'umma annoba, yana qasa ana rubuta mai zunubin mummunan upbringing da ya ba
wani,mu gyra duniyat mu lahirar mu ta amfane mi)



Talle ne ya shirya tsaf da yar jaka a hannun shi, wadda ta qunshi kayan yara mace da namiji
dan bai san me Salma ta haifa ba, incase ko wace gender ta haifa za a samu na ta kayan,
sallama suke da Marka inda qasan ranta kishi ne danqare, amma yanzu halin ta mai kyau data

koya ya danne kishin, miqamai leda tai da ta daka kuka daddawa, sa kubewa, tace ya kai masu,
godiya yai mata,Huwaila ce ta leqo da gyada soyayya itama dan sana'ar ta kenan yanzu, tq
bashi tace ya gaida su ya nema masu gafar ta, amsa yai ya sa kai......




*To masu karatu Talle fa yai shiri, wa zai bishi ya fada mai bata gidan kar yai wahalar banza*�
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA





BY HAERMEEBRAERH







Page 35:



Talle ne ke ta kwada Sallamah a qofar gidan su Salma, da ga can Ammar ne ya fara leqowa,
like a big bo he is, da tsamin bakin shi yake tambayar wa ake nema, yaro yana da kaifin
hankali, shekara biyu da watanni amma akwai qoqari ga karatun qur'ani a bakin shi tar, na
bokon iyakar shi A B C D, sai counting da Mama Biliki ke dan koya mai, komai akai yana sane
da shi kuma yana ganewa, murmushi talle yai, aranshi yace wannan yaro da ya dan da Salame
zata haifan ya kai shekarun shi ai sai nace dana ne suna kama, " Yaro ina malam," " faya nan" (
Baya nan), Talle ne yaga yaron ya kalli gaban.shi yana dariya ya fita da gudu yana " Abbana
Oyoyo" shima wajen ya kalla sai yaga ashe Abbam su Salame ne ya dawo, saurin isa yai wajen
shi, inda gaba daya Abbam ya sauya fuska, daga fara'a zuwa bacin rai, " me ya kawo ka?"
Tambayar da ya wulla mai kenan" Abba dan Allah dan son Annabin rahama kai hakuri, ka
yafeni, tabbas na kasance daga cikin jahilai, marasa sanin Allah a baya, sakamakon jahilcin da
ya mamayi zuciyata, kuma naqi na nemi sanin Allah da dokokin shi, ina jin girman kai, da ganin
na wuce wajen ai, hakan tasa na aikata munanan abubuwa a rayuwata, kala2 wadan da naga
isharar su Abba, babbar isharar shine mutuwar 'ya ta, kama dan uwana yaya na da mata ta
suna zina, daya 'yar tawa ga ta can da dan gaba da fatiha, ga abinda ke dagan hankali rabuwa
da Salame d nai, ta tafi da cikina na rabunda ita rabuwa cikin rashin tausayi da imani, a yanzu
nayi nadama, na koma islamiyya ni da iyalina dika, ka yafe min ba dan halaye na ba sai domin

Allah" kalaman shi sun saka jikin Abba yai sanyi amma ya wuce cikin gida kamar bai ji shi ba,
yana shiga Mama Bilki ta sauke shi da ruwa da abinci, ga kuma ruwan wanka ta kai mashi,tana
goge masa zufa ne tare da jera mishi sannu da zuwa cikin rattausan lafazi, umartar ta yai ta kira
yayar tata,miqewa tai ta tafi, ta kira Goggo Sarai da tai zurfin a cikin tinanin baya, yanzu da
hankali ke qara shigar ta, ba qaramin kunyar Mama Bilki take ba, tasowa tai kamar wadda kwai
ya fashe ma a cik, ta biyo ta, " Gamu Abban su" dagowa yai ya kalle su cikin sha'awar yanda
suka koma a nitse ba hayaniya ko mummunan kishinnan, Ammar ne yaje wajen Goggo Sarai ya
zauna a cinyar ta, shafa kanshi tai tana mai murmushi, Abba labar ta masu komai yai sannaj ya
sanar da su Tallen na qofar gida ma yanzu, haquri ya ba Goggo Sarai da yaga ranta ya baci,
yama juyawa yaga fuskar Mama Bilki ma a bace, domin shi mijin Salma shima ba qaramin
azzalumi bane kwantar masi hankali tai da dadadan kalamai sannan suka hakura, aika Ammar
yai yace yaje ya shigo da baqon nan, tafiya yai ya sanar da shi, Talle ya shigo qafa duk ta sage
mai saboda tsaiwa, waje Abba ya matsa mai kan tabarma, tayin abincin ya mai Goggo Sarai ce
ta qaro ruwan sha da wani abincin, ci sukai suka qoshi, sannan Abba ya kira su again, " da
farko dai ina son sanar da kai dukkan mu nan iyayen Salma mun yafe maka, kuma muna saka
ran itama ta yafe maka, tabbas ka cutar mana da yarinya, ka zalumce ta, amma duba da cewar
muma masu zunubi ne a wajen Allah kuma mu roqe shi ya yafe mana, banga dalilin qin yafe
maka da zamui ba, daga qarshe ina mai sanar maka yanzu haka Salma na Abuja gidan kudi
gidan hutu ita da yaran ka dan biyu ta haifa, kuma ta samu miji saurayi ya dauki yaran kamar
mallakin shi, ni ba zan sanar da kai ina Salma take ba a yanzu dan ta fara samun farin......." "
ban katsi nunfashin ka ba Abba, amma tabbas nima ba zan so abinda zai hana ta farin ciki ba a
daidai wannan lokacin, tabbas, na amince su ci gaba da rainon yara na, lokaci zuwa lokaci zan
dinga zuwa nan din, ana gaisawa,ga address dina saboda wataran ko za a buqaci hakan,"
takardardaya rubuto tun a gida ya zaro ya miqa ma Abba, idon shi ya kada yai jawurr, tabbas
har yanzu akwai son Salma a ran shi, wanda tin da ya dauka sha'awa ce kawai, miqawa Abba
ledar Hannun shi yai ya mai sallama dan komai dare gida yai, ya ma yaran shi addua, an nuna
mai hotunan su, inda Mama Bilki ta dakko mai wasu ajiyayyu tin na jarirantar su,har randa zasu
tafi, hawaye kawai yake sharewa, duk yaran shi ba mai kyaun wadannan da ya koro, dan duk
macen da ya aura in zata tafi sai ta dire mai da ko yar shi, ko in taje gida ta haihu zata dawo
mai da shi, Haule ce kawai take itama kyakkyawa saboda uwar ta, yana tina ta sai zuciyar shi ta
qara tsinkewa,ya kula yara uku ya bari yanzu, amma wannan na daga cikin horon da Allah zai
masa ya raba shi da yaran da yafi qauna, tashi yai bayan ya sake masu sallama ya isar da
saqon su Huwaila,godiya suma sukai masa, ya kama hanya sai qauyen su.






*BAYAN SHEKARA BIYU*


Salma ce ke zaune da jaririya a hannu da suke kira da suna Faiha, gefe Juwairah ce tana riqe

da hannun yaron ta qaqqarfa mai kuma barna, Salim, Sai Suwaiba da ke ma Abrar kitso a
lallausan gashin ta mai tsaho, gefe kuma a kwance a kujera Saudat ce ke latsa waya tana ta
doka murmushi, Maganar Juwairah ce ta katse shirun nasu" In baka tsaya ba Salim zan kira
Daddyn ka ya dauke ka ku tafi kona huta," da sauri yaron ya zauna a cinyr ta ya nutsu, dan a
cewar shi Daddy is no fun to be with, amma Mummy, yana son zama da Mummyn shi ko da
duka zatai mai in yai halin nashi na barna, ' Yan biyu ne sika shigo da gudu, suna haki" Mummy
Daddyna yace wai ki bada Faiha, Salim da Abrar mu je park" kowa a cikin su daidai lokacin da
kowa yace Daddyna sun kalli juna da harara,ba su fada a tsakanin su sai akan abu biyu,
chocolate da kuma Daddyn su, sai kace kaya haka ake rabon shi a tsakanin su, wannan yace
nashi ne wannan yace nashi ne, fatima ce tace" kaiii wannan Muhammad din sai son yi min
kwace kk kullum for how long zaka gane cewa Mummy ce taka ni kuma Daddy nawa" "
Fateema ke ce baki san komai ba hat yanzu" ya fada yana mata kallo wai shi harara, dan
kwata2 bai kaita wayo ba, ga shi fadan ma bai iya ba" kai ni ku karbe ta sarakan rabon
iyaye,kada Allah yasa ku zaben din ga Faiha in ta girma zata zaben ai" miqa masu ita tai suka
karbe ta,dariya saudat tai sosai tace" Mummy ar u jelouse ?" Dariya dika suka dauka, Juwaira
ta sauke Salim ya bisu,daidai an gamawa Abrar kiston ta, miqewa tai tace" Tanx Mum" tai
kissing kuncin Suwaiba ta fita a guje, murmushi tai mai nuna alamun jin dadi ta bita da"ku dawo
lfy kui adduar fita daga gida kan ku fita, kar a manta da yin addua in zaku dawo," daga nesa ta
amsa mata da" inshaa Allah mum, i love u," " i love u too baby" nan ma Saudat ce dake ta
Chatting da mijin ta ta sake dagawa tace" lovers kenan" nan ma dariya sukai, juwairah ce ke
kallon ta da Yan uwan ta cikin farin ciki da nishadin da Allah ne kadai yasan iyakar shi," to ya
kamata mu ma muje Shopping, akwai wasu abubuwan danake so mu siyo yau" ta fada tana
kashe masu ido, Saudat ce ta diro da sauri ta dage hannaye sama tana murna" Yeeeeehhhhh
shopping" " u always act like a kid Saudat," inji Salma, pilon kusa da ita ta wurga mata, " eh din
anyi,my husband always treat me like one," ta qarasa tana murguda baki, dariya suka saka,
Juwairah tace" yeh u ar always his baby" " and u ar more like baby to me than she is always my
love" juyawa tai taga Jabeer ya shigo cikin qananan kaya, tare da mijin Saudat, tsallen murna
Juwairah ta daka taje ta rungume shi,wanda dama yana fada hannun shi is open, rungume ta
yai kamar su kadai ne a wajen,gyaran murya mijin Saudat yau yace,babban Yaya muje ki, tinda
shi wancan Baban yaran ya debe su muma mu kai su shopping din kawai, kallin juna sukai
matan, ba haka suka so ba, akwai dan abubuwan su na mata da suka so kwasa, amma ba
damuwa sun taya su zaba ma, dakko hijaban su sukai,Juwairah har da Niqab Yah Jabeer yake
sata sakawa, haka suka fita, gwanin sha'awa, waya sukai ma mijin Salma ya same su a Sahad
dake can ABJ din, aiko Salma da tana jin ta out of place sai murn,sa riya sukai mata, a can
suka hadu da yaran da mijin Salma siyayya sukai sosai kafin kowa ya nufi gidan shi, Suwaiba
gidan Jabeer zata kwana kafin wase gari mijin ta yazo su tafi.






Arziqi ya wadata a zuri'ar gidan Abba Baballiya, gidan kuma 'YAN ABUJA, albarkar Allah ta

sauka masu, ko ta ina,inda a tsakanin Jabeer da yake dan su da surukan su, kowa qoqarin yi
ma iyayen abun da zasuji dadi suke, an canja fasalin gidajen iyayen daga na qasa zuwa na
cement, da kayan alatu kala2, ga shaguna da suka bude masu, na saida kayan masarufi suka
saka amintattun yara suke kula da wajen, shiko Yah Jabeer kasuwancin shi yana nan da
kamfanin jakunkuna na AF2 dake malaysia, abun ba a cewa. Komai sai godiyar
Allah,makaranta mazajen dika ke tinanin maida iyalan nasu nan kusa su ci gaba da neman ilimi
har sai sun ce ya ishe su, Suwaiba nonoless tin bata son saka bra din acuci maza irin ta Cutie
har ta fara, mijin ta ya masu gini a unguwar Kabuga, qaton gida, yanzu harkar gwanjo ta bude
sosai, Talle arziqi ba laifi, ana nan an zama manyan ustazai masu ma wasu wa'azi musamman
da basu misali da rayuwar su, Saudat da mijin ta, sun fawwala ma Allah dukkan lamuran su, na
rashin haihuwa, ba sa damuwa a ransu ko adan, tin ana zuga mijin ta yai aure har an gaji,
domin soyayyar su suke sha, da shaquwa ga fahimtat juna dake tsakanin su.



Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya.


*Masoya novel na 'YAN ABUJA ku dakace ni gobe domin jin wasu bayanai da sharhi da zan
akan wannan novel da inshaa Allah nake saka ran zai amfanar kuma zakuji dadin shi da yardae
Allah, ina roqon ku da kuma fatan duk abinda na fada daidai kuma kuka san abin koyi ne da ku
qoqarta saka wa a ayyukan ku, sannan wanda nai kuskure ku yafe ni akai, ina jiran gyaran ku
akai daga yau zuwa gobe inshaa Allah na gode. Me love u XoXo❤*
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA



BY HAERMEEBRAERH


*Assalamu alaikum Jama aree bandi raabe am, yidibee novel 'YAN ABUJA, mido yetta on
masin,beyeddi on holli am haa dow defteream, mido yeela ko end jangi pat end habdai end
naftira bemai koo na pat ba end habda ko sedda on, mido usa mido yetta on walama bana fulbe
haa on woni fu ha duniya do miyetti, walama bana yare IBRA, end doo woondi inshaa Allah,
mido yidimon*❤


*Ina kuma riqon duk wanda Allah yasa ta fara bin wannan novel daga farko ko ta riski wannan
page din koda bata bi daga farko ba ta daure ta karanta wataqila ta samu koda abu daya ne mai
amfani a ciki*


Page 36:

Zan yi sharhi ne akan wannan novel namu na yan abuja, inna gama nawa wataqila ba zai yu
na fidda komai ba ina son kuma makaranta ku fiddo man da naku hakan zai sa naji dadi maybe
gaba na sake mana wani novel din


1- da farko dai gaba daya a kuma dungule nai magana akan iyaye da tarbiyya ne, yanda iyaye
in Allah ya basu yara ya zasu saka su akan hanya mai kyau wace tarbiyya zasu basu, me yaka
mata su saka masu a zuqatan sh saboda gudun kar su tashi ba akan tarbiyya mai kyau ba.

2- sannan nai magana akan kwadayi, mahaifiyar su Suwai nonoless ta taso da su akan
kwadaryi sa burin zuwa inda ba lallai ne arziqin su na can ba, unlike Juwairah da suka raina ta
akan auren Yah Jabeer.


3- Ana son mace ta zama mai tarbiyya mai kyau, wadda ko ina ta shiga za ai sha'awar ta da
halayen ta in bata nan ai kewar ta, ki iya zama da kowa da kyakkyawar mu'amalat, ki kasance
wadda ko minti daya miji yai baku tare zaiji damuwa da tashin hankali, da duk wanda kk tare da
shi ma.
4- Ana son mace ta zama mai tattali mai dabara in ba wannan a gida ta san ya zata hada
wancan ya bada outcome mai kyau mai dadi, yanda ba mai gane ma rashi ne ya jawo hakan,
sannan ta zama tana qoqarin dasa kowacce hanyar da zata kawo masu sauqi a gidan ta, kamar
yanda Juwairah tai lambu a cikin gidan ta.
5- Mace mai rufawa mijin ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login