Showing 54001 words to 57000 words out of 70697 words

Chapter 19 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf

27 Apr 2025

4565

dahu sosai sannan ta zuva

madarar shanun, tana tafasa daya biyu ta sauke ta kaima Juwairah guda dayar dan dama dayar
can ta batwa Innar mu ta dafa wa kowa a gidan a ci wannan ta mai jego ce, godiya ta mata
Jabeer na shigowa ya zauna zai saka hannu, Nafee ta riqe" A'a Yah ga tamu can wajen Innar
mu wannan nata ne, ita fa ta haihu ba kai ba, sannan na zuba mata maganin basir a wannan ka
jira tamu" dariya yai sosai har yana kama ciki," yarinya zaki bayani ne kice kawai Nafeesa na
hada maki kayan da zaki warke da wuri ki dawo na dora daga inda na tsaya ne kawai, banqi ba
in an hanani ci saboda ita ta haihu tai wahala ya kamata taci tai qat amma batub ace wani basir
in haka ne ai na fita bair nifa namiji ne" dariya sukai dika. Wajen jaririyar yaje ya dauke ta yana
kallon ta yana mata wasa, wanj farinciki yake ji, nan take ya hau mata hotuna, yana gamawa ya
danna kiran Abban su Suwaiba, lokacin duk suna tare har Goggo Sarai, duk da ba wani sake
mata kowa yai ba amma sun rage gudun ta, sallama yai ya sanar da shi haihuwar, cike da
murna kowa ke amsar wayar suna gaisawa, amma Juwairah sam taqi karbar wayar wai kunya
take ji, dariya suke ta maya Suwaiba tace sai gobe zasu zo, dik da mamakin dake zuwatan
Jabeer Juwairah Da Nafee bai hana su suma sakewa da ita aita hirarn ba, bayan sun gana ne
Juwairah ta dauki pilon da aka kawo mata dan ta zauna ta jefawa Jabeer, tana.buga qafa cike
da shagwaba" ni baka fadan zaka kira su ba kawai sai dai naji kana waya, kuma wai Abbana ka
fadawa na haihu, wayyo ni Allah da wanne idon zan kalle su?" " da idon da kk kallen a daki ki ka
kuren su kina lumshe su a daka lokacin inaa....." bata san sanda ta miqe da sauri ta damqe
bakin shi ba, tana kallon inda Nafeesa take cike da kunya , duka ta kai mai mai zafi a qirji,ya ko
yi qara, Nafeesa ce ta fita tana ta dariya" Yah Jabeer Allah mun bata" ta tashi daga jikin shi zata
tashi, saurin kamo ta yai tana tirjewa" A'a faaaa ba zan iya da shagwabar nan ba bayan kin san
ke ba lafiya gare ki ba, ki hakuri dan Allah ba zan sake ba kinji" kama kunnen shi yai alamun
ban hakuri,murguda baki yai ta tashi ta shige daki ta dau jaririyat dake kuka ta fiddo nono zata
bata, ga shi ya qura mata ido qurrrr, tura mai tai gaba "ni wannan kallon ya ishen, tinda ka gama
naka turn din this is hers pls let her enjoy ita" ta qarasa tana murguda dan bakin ta, sakama
bbyn nono tai a baki taji wata azabar zafi na tsotso, janyewa zatai amma jabeer ya hana ta ta
hanyat kai bakin shi nata, rasa wanne zata dauka tai, zafin bada Nonon ko kuma kiss din da
take karba????





Makaranta ku zaba mata daya...... lols���
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 💅🏼 'YAN ABUJA. 💅🏼





BY HAERMEEBRAERH

Page 29:





Alhj kallane ya kalli Alhj salihu yace, " kai nifa ba qungiyar da zan bari, haba me akai da maza
inji karuwa, har yanzu fa da quriciyar mu, ko hamsin bamu rufa ba, akwai sauran rayuwa gaba
na tuba" " hmmmm Kalla knan kai abokina ne mun taso tare dakai, iyayen mu da yan uwan mu
mun bada su ta wannan harka, kana ganin zunubin bai isa haka ba? Tin da ba yanda za ai mu
dawo da su? Ka duba fa in bamu tuba ba yanzu kowanne lokaci mutuwa na iya zuwa, ita bata
sallama bare qwanqwasa qofa in......" " malam dakata, yqu in da abin da kazo kenan, i am very
sorry to disappoint you, cos i am not ganna buy this shit, akan me ina tsaka da jin dadin rayuwa
ta kace na koma rayuwar talauci, bayan kasan sharadin fita daga qunyiya mai da duk abinda ka
mallaka ne daidai da allura ba a yarda ka aje ba, me na tanada wanda ba daga qungiya bane?
Haka sidda madalaqan kasa na koma almajirin qarfi da yaji, kan kuma ka fita karka manta sai
an yi asiran rufe maka tinanin ka na gidan Oga zaks da qungiya gaba daya wanda a kallah zai
kai nan da sati uku, kai ka san dan mun riga da an bamu daukaka a qungiya ne yasa akai mana
wannann alfarmar da qananan yan qungiya ne kashe ka za ai ko tinanin nan kai, ni dai ina nan
kai kuma Allah ya taimaka ka fita lfy, amma ka sani sisina ba zan taimaka maka da shi ba in ka
talauce, abotar mu na nan har yauma ta nade" baza babbar rigar shi yai.ya fice ya bar Alhj
Salihu da tinani, wata zuciyar na kwadaita mai ci gaba da rayuwar hutu, daya ban garen na
nuna mai illar hakan, in ya ci gaba da zama dan qungiya yakai soyayyar Suwaiba inaa? Kaiii
daya rasa abar son shi gwara ya hakura da qungiyar nan Allah zai kawo mai wata hanyar,
miqewa yai, yana miqewa wayar shi ta hau ringing, dubawa yai yaga kiran Alhj Kallah, tsaki yai
kamar ba zai dauka ba, dan abin da ya mai dazu ya sosai ran shi sosai, amma sai yandaga yaji
ko ya canja ra'yi ne zasu fita tare, yana dagawa yaji wata muryar daban da bai san ta waye ba"
waye kai ina mai wayar?" " ranka ya dade mai wayar Allah ya mai cikawa yanzunnan ya samu
hatsari wanda gaba daya kan shi ya fashe, sannann qafar shi ta dama ta karye" " innalillahi wa
inna ilaihirra ji'un" kalmar da yake maimaitawa kenan, ya kashe wayar ya zauna, qarar message
ne yashi, cikin tashin hanakali ya duba sai yaga address din inda Kalla yai hatsari aka turo mai,
kamqr wanda aka ma allura haka ya miqe yana fadin" Allah na tuba ka yafeni, Allah ka gafarta
min ni Salihu daga yau nai alqawarin tuba daga zunubaina na daina harkar nan ko zan rasa
raina ne" kuka hake matuqa haka ya kai ga motar shi ya tada yai inda aka kwatanta masa,
wayar shi ce ta qara ringing " Oga Zaks" shine abinda ya gani, tsaki yai ya daga" Salihu kaji
abinda wani ta fadan? Kana ina yanzu haka, da gaske ne Kalla ya mutu?" " nima ban sani ba
sai na isa wajen na gani, ka oashe na kusa isa ga mutane can dai an taru.a wajen sosai" kashe
wayar yai ya qarasa, yanda ya ga abokin nashi take ya yanke jiki ya fadi, wasu je a gefe suka
taimaka mai da ruwa ya farfado, yai wajen shi a guje yana kuka, riqe shi mutanen wajen sukai
suna bashi hakuri, umarni ya basu akan su taimaka mai su daga gawar akai masallaci mafi
kusa a mai wanka a binne, kawai dan basu da kowa, haka ko akai , waya ya zaro ya sanar da

Oga zaks, jikin Oga zaks yai sanyi amma dake zuciyar ta dake ko kuka bai ba, sai dai ma kawai
ya mai taaziyya ne kawai yace in an kai shi yaje yana son ganin shi, kashe wayat shi yai yace"
ba dole ma na fita ba, ai ko ba komai Kalla yai wa qungiya hidima, ya cancanci azo kan gawar
shi a mai addua amma wai in an kai shi na je, ko baka ce ba zaka ganni kuwa" share hawayen
shi yai shima yabi bayan yan tsiratun mutanen da suka gama rife Kalla a makwancin shi na
gaskiya,mota ya fada yai gidan shi, tattaro duk wata dukiya tashi yai, yaje ya dakko ATM cards
din shi, da makullan motar shi, da takaddun filaye da gidajen shi kamfani da komai ya zuba a
motar, ya sa kai, bai zame ko ina ba sai qofar gidan Oga Zaks, yana isa a ka ya tsaya ma Oga
Zaks , " ya haka Salihu, zaka zo ka tsayan akai kamar wani sanda" " miqa mai komai yao da
suke a wani akwati, ya ce" Oga ina son barin qungiya ba dan komai ba sai dan ina son na koma
tsaftatacciyar rayuwa, abinda ya faru da Kalla ya qaran son barin qungiya" take ya kwarorowa
Oga Zaks duk abinda ya faru da Kalla da shi kafin hatsarin da yai, nqn danan jikin Oga Zaks ya
dau rawa, qaton cikin nan kamar ana buga ganga haka yake qara, maganganun sun shige shi
sosai, " To salihu ba za ai haka ba ka fita kai daya, yau kuma a yanzu zan tara mutanen mu, na
sanar da su, wanda yaga zai fita ya biyo mu dan nima fita zan, wanda yaga zai zauna ga waje,
amma zan so yanda ni ne na assasa wannan qungiya na rusa ta, dan ko na tafi zunubin xai
bini" wani dadi ne ya lillibe Salihu dan bai zaci hakan ba, ya zaci zai sha wahala kafin ya amince
mai, waya yasa ya kira mutanen su,kusan awa biyu sika dauka kan kowa ya hallara, ganin
fuskar Salihu da ta sha kuka ya badu mamaki, nan take ko Oga Zaks ya fara zayyana masu
komai, cikin qanqanin lokaci wasu da dama suka aje makaman yaqin su, wasu kuwa suna
ganin ai su akwai sauran lokacin tuba,tsawar da Oga Zaks ya daka masu ce ta dawo dasu daga
cece kucen da suke ta yi" na yake hukunci wannan qungiya rushe ta zan, wanda ya sake kafata
shi ya sani, amma ni kam na gama , dan haka daga gobe zan rushe ta, tsakanina da dodo ko
kashe ni yai na kubuta da ikon Allah, fatana Allah ya gafarta min, ya ba wa wadan da na zalinta
ikon yafe man a filin qiyama" sai ga Oga Zaks na kukan nadama, basu rufe baki ba suka ji gidan
na wani irin qara, mai firgitarwa, haba mana xo kuga gudu, kowa na gudun ceton rai, Salihu ne
ya ke qoqarin taimaka wa Oga zaks su gudu, amma ya dakatar da shi" Salihu kai ta kan ka
kawai, ni nasan tawa ta qare, da wannan uban tumbin nawa kk tsammanin samun gudu a
gareni? Ka dube ni fa ka gani nayi ka bakwai, ka barni kawai, abin da na aikata zan girba, i am
willing to give my life for urs, coz i started everything, i think it has to end with me, just go, run
for ur lyf, and pls don't forget to pray for me, ask Allah to have mercy on me" tura Salihu yai da
qatfi a daidai lokacin da wani qaton baqin zaki ya fito daga wani baqin daki, yayo kansu, Salihu
diba yai da gudu ya bar wajen, Oga Zaks salati kawai yake, ya cika wando da fitsari shataf,
tsoro da tashin hankali ya ganshi qarara, tinawa yai ashe haka wadanda suke ba dodon suke ji
kan su mutu, take yaji qirjin shi na wani mugun bugu, cafka zakin nan ya kaiwa wuyan shi ya
hau cinye shi, Oga Zaks kam an tafu inda Kalla ya tafi, Salihu kuwa gudu yake kamar me , mota
ya gani da makulli jiki me ita wataqila tsabar tsorata ne ya hana shi ci gaba da tada ta, dan
harda takalmi qafa daya a ciki, da alamar danshi a sit din, maybe fitsarin shima ya sake🤔 take
Salihu ya tada motar ya debi hanyanyat kano.

Sin gama gyara gidan tsaf, sun ma iyayen nasu girki, wanka sukai, suka gyara jikin su, jikin
Suwaiba duk ba kwari haka take jin faduwar gaba, Saudat kam ita in banda sharar dakin su ba
abinda ta tsinana, komai kusan Salma da Suwaiba ne sukai, gaban ta sai tsananta bugawa
yake, amma sai tai ta maimaita addu'o'i a bakin ta, haka itama Suwaiba, bayan sun shirya ne
suka dauki hanyat gidan Juwairah me jego, sun isa daidai Jabeer ya fito riqe da towel din da
yake gasa mata jiki musamman cikin ta da bayan ta da shi, kallo suka bi shi da shi , saka
makon ganin Juwairah ta fito tana" Ni dai gaskiya a canja min me yin wanka, kai gaba daya
kamar ba wankan ne ke kai ka.......... " maganar ta maqale dan ganin yayun nata na shigowa,
niyyar ta ta koma bandakin dan juyawa tai tare da damqe bakin ta, zata shige, Saudat ce ta
ruqo ta da sauri tana dariya," Me Yah Jabeer din ke maki? In kina son a canja maki mai wanka
sai na dinga maki, amma ni sai ruwan ya tafasa sau uku sannan zan amfani da shi" zaro ido tai
waje tace" A'a Adda Saudat a barmin Yah Jabeer din mu lallaba a hakan" dariya suka kwashe
da shi, Jabeer yace" kuji yarinyar nan fa, wai zata lallaba a haka sai kace wani mugunyar nake
mata" Nafee ce ta amshe da" Hmmmm Yah ai shiru kawai da wannan maganar amma ko dazu
naji qarar ta" hararar ta yai yace " Suwaiba ku shiga ciki mana kuka tsaya a waje" shiga sukai
har me jegon, Nafee ce ta miqe sakamakon kiran ta da Innar mu ke yi, zuwa tai ta bata wani
kwanika biyuo ta kawo wa juwairah, amsa tai tai ta tafi bangaren juwairah, sallama tai ta shiga
suna ta hira kowa na yava kyaun jaririyar da sunan ta" wannan suna na yan gayu anya kowa zai
iya fada" cewar Salma, dariya Nafee tai da ta qarasa aje kwanon gaban Juwairah dake shafa
man kade a cikin ta," ai jiya sai kun sha dariya dan daga Innar mu har Abban mu basu itmya
fada ba" " ai ko wannan suna zan so jin shi a bakin Goggo" cewar suwaiba, dariya suka bushe
da ita dikkan si sun san a kwai case dib fadan Abrar a bakin Goggo sarai, Juwairah ce ta gama
shiryawa Suwaiba ta daure mata cikin ta, sannan Jabeer ya shigo dauke da plate da Spoon da
cup sai tea spoon, gaishe shi sukai dika ya amsa tare da yi masa barkar qaruwar da aka samu,
godiya yai ya isa gun kwanukan ya bude, farfesu ne na naman qaramar dabba, yasha kayan
qamshi irin na jiya harda ridi, gefe kuma kabewa ce innar mu ta dafe ta tai laushi ta dame ta tai
kamar kunu, sannan ta zuba maya madarar shanu mai matuqar yawa sai zuma, zuba mata yai
a cup din ya zuba mata naman a plate, " oya maza taso ki ci ki shanye, dan bana son kina
zama da yunwa" turo baki tai gaba, " ni fa na qoshi, dazu da asussuba na qarasa naman jiya
saboda yunwar dana tashi da ita, yarinyat nan ci gare ta kamar Innar ta Salma" dariya suka
dauka da dikkan su" ai ko baki isa qoshi ba da dan ragowar naman nan, in baki matso kin fara
ci ba zan maki dura gaban su, dan dora ki cinya zan na maki irin na kwanaki" zaro ido tai waje
sai gata a qasa ta saka pilo ta hade qafafun ta waje daya ta miqe su( haka ake so mai haihuwa
tana zama, kai ko ba haihuwa ba a son zaman nan na ware qafa, kabewa da madarar shanu da
xuma duk wadda ta hada ta zata bada labari bazan ce komai ba🙊) kaiwa baki tai ta fara ci
dadin da ya ziyatce ta bata san sanda ta cinye ba ta shanye kabewar dika, " just like a gud gurl"
kissing din gefen fuskar ta yai ya dauke kwanukan zai fitar Salma tai saurin karba, " haba yayah
muna nan ai sai ka bar mana aikin in mun tafi ka ci gaba" muemushi yai ya sakar mata yace" ni
bari naje.na shirya zan wuce Abuja yau zuwa qarasa shirye2n komawar mu bayan suna" anan

ya sanar da su komai game da aikin da ya samu, murna suka taya shi , da fatan alkairi, fita yai
yai wanka, ya dawo zai shirya Juwairah ce ta tashi taje, yna shiryawa suna.hira tana hada mai
kaya a jaka, duk da hana tan da yau.sai da ta hada masa, bayan ya gama ne ya dauki Abrar ya
mata addu'a yau kissing din ta ya hade bbyn da maman ya rungume, daidai ya sake ta yai gaba
ne ya dawo" Af nayi mantuwa" " me ka manta honey?" Matsawa yai kusa da ita ya janyo ta jikin
shi yana mata kallo qasa2," No no no u can't do this now pls, Adda Suwai ba is here, Adda
saudat is here, and Salma too, pls kai hakuri har ka dawo, kasan lips dina ja suke kuma zasu
gane, ni dai dan Allah ka daina bani kunya," ta fada tana yar kwalla dan ya kyale ta, lake mata
hanci yai yana" mun kusa komawa gidna mu mu uku, mu yi abinda muke so" dariya tai na
samun nasara, ta mai addua ta rako shi suna zuwa palo tai fuska ta zauna kamar ba tare suke
ba, kunya ce da ita kamar me, dariya suka mata Salma tace " kinji da shi ciwon ajali a dan
yatsa, mu zaki layancewa," dukan wasa ta kai mata tace" Adda Suwaiba kin ganta ko" dariya
sukai" ya kamata ki rage shagwaba yanzu kin haihu," cewar Nafee, murguda mata baki tai ta
kauda kai.



Ahj Salihu ya iso kano da kyar ya gane gidan su suwaiba....

.
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼





BY HAERMEEBRAERH








Page 30:

Alhj Salihu ya iso gidan su Suwaiba da wajen bayan la'asar kadan, dai dai su kuma suna
dawowa daga gidan Juwairah, daga nesa ta bayan da ya juya Suwaiba ta gane shi, ya rasa dan
aike, kuma yana matuqar jin nauyi, kunya, da tsoron wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login