Showing 18001 words to 21000 words out of 70697 words
Chapter 7 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf
nata, su kuma suci nasu, hakan da tai yada Abban sun ya samu ragi daga
dawainiya, shiyasa ma wataran suke samun abinda suke aikawa Juwairah dan Mama ta kula da
rayuwar da take ciki a zuwan da tai sau daya, amma da ta tambaye ta, qeqasa qasa tai tace ita
lfy lau komai yake tafiya masu, addua tai mata kawai amma tasan akwai wata a qasa, cikin
firgici ta daga kai daga tinanin ta sakamakon......
...............
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA
BY HAERMEEBRAERH
Hey guys i am sorry yesterday i fogot to number the page, it suppose to be page 10 and this is
page 11. Thanx me love u XoXo.
Page 11:
Wata qara da Goggo Sarai ta sake da sunan dariya, dan kawai ta ja hankulan
su,"Hahhhhaaaaa kaiiii amma naji dadin haduwar ku gaba daya tare, ikon Allah ana can ana cin
amarci sai yau aka samu haduwa kenan, to ya masu gidan? Ya rayuwar hutu da jin dadi?"
"Lfy qalaou Goggo, ina Abba?"
" Hmmmm ga shi can wajen waccan sallamammiyar matar tashi da ta shanye shi"
" Bashi mu gaisa kar yace bamu neme shi ba"
" Aiko bada wayata ba ehe ku kira shi a yar rakani kashin shi kawai"
Tana fada tana hura hanci tana turo dankwali gaba irin na fitsararrun matan nan? Kada kai
Abban nasu yai yace" Allah ya kyauta" murguda baki tai kamar wata qaramar yarinya, irin na
rashin kunyar nan,( dan kunsan murguda bakin ma kala2 ne, akwai sexy murguda baki mai
daukan hankalin oga, yaji dole sai ya kai nashi bakin a naki sabida yanayin yanda kikai yi shi da
salon jan hankali, sannan akwai na rashin kunya kamar na Goggo sarai dai) miqewa yai da
niyyar fita sai wayar shi ta hau ringing, dagawa yai da sallama, su Suwaiba ne, gaida shi sukai
kamar ba sa so ya amsa tare da tambayar su gidajen su," hhhhhh Abba do u really have to ask
? We ar fyn, komai normal kamar dai yanda ka sani Abba mazajen mu masu kudi ne, so ina
ganin ai bamu da wata matsala mu"
" Suwaiba ni mahaifin ku ne ba zan gaji da maku nasiha akan ku bi duniya a sannu ba, yau in
kaine gibe ba kai bane, dukiya da abinda ke cikin duniyar nan ba komai bake face rudin shaidan
ga wanda ya mai da su abin bauta, kuji tsoron Allah a lamarin ku, Hello ! Hello..... shiru yaji
ashe sun dade ma da kashe wayar tin da ya fara wa'azi suna ta surutan yanzu zai takura masu,
mamaki je cike da zuciyar shi, " yarannan ni suka kashewa waya?" " Abban su kai hakuri komai
zai daidai ta da qarfin addu'ar da zaka dinga wa iyalan ka, Allah zai shirya maka su inshaa
Allahu, adduar iyaye amsasshiya ce a wajen Allah, Allah ya shirya mana zuria" " hmmmmm
Ameen Gimbiya ta Allah ya albarkace ki da zuriar mu duka" dadi ne ya kamata mara musaltuwa
a duk sanda ya mata wannan adduar" Ameen a bin sona" murmushi sukai, nan da nan yaji
baqin cikin shi ya tafi, ruwan wankan da ta saka mai yaje ya shiga yai wankan shi, ita kuma ta
fara qoqarin dora madu abinci.( magidan ta ku na qoqarin yi wa matan ku godiya da addua
musamman ta nema masu albarka a wajen Allah, in albarkar nan ta wanzu a garesu ta shafe
ku, da xuriar ku kenan, mata ku dinga dukkan abinda kk san zai faranta masu rai sui maku
adduar, soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa).
Nafeesa ce ta shirya tsaf cikin riga da skirt na atampa, tayi kyau sosai ta taho bangaren su
Juwairah" matar Yayah ya naga baki shirya ba kin saka dan guntun wando da vest an faka
gashi gefe?" " Nafeesa kenan ina ga alama kin manta yau Yaya da wuri zai dawo sannan yau
ranar dana ware domin gyaran lambu na ne ko? Ga girki da zan da wasu aikace2n, kuma sanin
kan ki ne ni fa yawon shiga nan shiga can dinnan ba son shi nake ba, shike kawo mace ta daina
kula da iyalan ta da gida tana qarewa a titi" " hakane kam gaskiya, ni dai zan tafi gidan
Shamsiyya na gaida ta, dan na mata alkawarin zani yau din, na zaci zamu tare ne tinda naga ke
kin dade baki je ba, sai na dawo to" " to ki dawo lfy, ina gaida ta da yaran" fita tai ta tafi, ta je
gidan Shamsiyya inda ita shamsiyyar yaran ta biyu mace da namiji, Farha da farhan, goyo take
tana goyon macen , gaba daya gidannan sai a hankali, komai da kan shi yake zama, bai da
muhalli, shiga tai palo ta zauna da sauri ta miqe tana duba skirt din ta daya jiqe, hannu ta kai
hancin ta taji wani mugun xarnin fitsari, da sauri ta kauda kanta ta fita tsakar gidan,ruea ta sa ta
wanke hannnun ta saka a skirt dinta tana masifa" ni gaskiya shiyasa bana son zuwa wajen ku
shamsiyya, ga gida har gida Allah ya hore maki amma sai uwar qazanta, duba dan Allah daga
zuwa na xauna akan fitsari , ko da Juwaira bata haihu ba na san.abin da ba za a taba samun ta
da shi ba kenan, yanzu haka saboda gyaran gidan ta da kula da haqqin mijin ta yasa taqi biyo
ni, Juwairah nada lokutan yin komai, tinda ba za a hadu ace kullum zaka hada kowanne aiki
kayi ba zaka gajiya, sai wanda suka zama aikin yau da gobe, dan Allah ki gyara, dan yana daya
daga abinda yasa Baban Farhan yake neman aure duk.da ya fada maki amma kinqi gyarawa"
kaiiii hajiya bala'i daga zuwa.sai wannan dogon karatu? To dan Allah ya kuke so nayi? Ga aikin
gida gana miji gana 'ya'ya" sai ta fara hawaye wai ita a dole komai ya mata yawa, kama hannun
ta Nafeesa tai suka koma palon ta zaunar da ita a kujera, sai da ta laluba wata taji ba jiqa ta
zauna ta fiskance ta, " qawata ni ba wai ina maki fada dan ranki ya baci bane" " to dan meye?
Saboda kowa ya tsane ni sai a dinga ce min qazama ? Kalmar qazama fa na da ciwo tsakani da
Allah" majina ta sharba tana gige hancin da zanin ta, " to yanzu kingq hakan da kikai ni ba zan
yi shi ba, da na goge majina da zani gwara na je na wanke hancin, ai in kk ji ance qazama
akwai kalmar tsafta kuma ko? To ni so nake ki cire kalmar da kowa ke kiran ki da shi na qazan
ta ki mai da shi mai tsafta, yanzu ki fa duba kiga Mama Bilki, kullum kk dhiga wajen ta kinga dai
ta tsufa ko, amma tsabar qamshi da tsafta bazaki so barin wajen ba, come to think of it ba fa ta
da kudi da wadata kamar ki? Dan Allah ki gyara ki rage son jiki,son kallo da karancr2n nan na
zamani har sai kin gama komai sannan ki dauka ki fara,ina fatan wannan ya zama na qarshe da
wani zai baki shawara ko za a zage ki akan tsafta, in baki gyara ba Abban Farhan yace maki zai
qara aure kuma ya fara nema in kk gyara nasan bari zai dan matsalar shi dake kenan ba wani
abu ba" " Na gode qawata, ba wanda ya taba zaunar da ni ya min bayanin ya shige ni" " ba
godiya a tsakanin mu" murmushi sukaiwa juna shamsiyya ta miqe ta fara tattara kayan wajen
data loda a kujera, nan da nan Nafeesa ta taya ta suka gyara gidan ya dau hake da qamshi,
girki sukai mai rai da lfy kala2, wajejen la'asar Nafeesa ta bar gidan cike da tsaraba daga wajen
shamsiyya, a ranar ta sha wanka da gaye, Abban Farhan daya dawo ya sha mamaki amma bai
nuna ba, sai ya nuna mata matuqar jin dadin shi, dakuma yabawar shi tashi yai yaje dakin shi
yace " ina xuwa" wata sarqace ta gold mai kyau ya zagaya ta bayan ta ya daura mata suna
kallon madubi, dan harda koyawa yaranta baccin wuri sai da Nafeesa ta koya mata, godiya tai
ta masa shima yana godiya, ba a jima ba taji zancen aure ya rushe, sai dai ya sanar da ita
cewar" Baby ki kwantar da hankalin ki dan ni ba mai ra a yin mata biyu bane ko sama, tsaftar ki
da rashin tsaftar ki in ni me ra ayi ne ba zata hana min yin aure ba, na fada maki ne dama dan
ki gyara mu more ratuwar auren mu yan da ya kamata" taji dadi sosai inda ta qudurta ma ranta
xama mace mai tsafta ta bugawa a jarida, yan dakowa ya mata tambarin qazan ta sai an buga
mata na tsafta in Allah ya yarda. Ni ko na ce to Allah ya yarda ya shiryemu mu gane tsafta na
da kaso mafi tsoka a rayuwar aure.
Bayan Juwairah ta gama komai ta yi wanka ta kwanta tana hutawa, tasbihi take ta yi ga Allah
bacci ya dauke ta, tafiyar tsutsa yake mata a qafar ta ta farka idon ta na qara lumshewa, juyi tai
ta cusa kanta a cinyar shi ta ci gaba da baccin ta, a hankali ya janye ta dan ya kula a gajiyae
take, yaje ya cire kayan shi ya aje inda take aje masu kayan wanki bayan ya ninke, ya tafi
wanka dan har da ruwan wanka ta aje mai, bayan yai wanka ne yaga kamar bata ci abinci ba ya
shirya ya zo ya qara tashin ta sai magagi take bacci ne sosai a idon ta a haka ya daga ta ya
zubo abincin yana bata yana ci duk abinnan da ake idon ta rufe yake, " Yah Jabeer ka dawo?" "
Eh na dawo princess" " Sannu da xuwa" "yawwa, meke damun ki ne yau?" " bacci nake ji na
gaji ne sosai, ga jiri danake ji, tin shekaran jiya kuma sai naji cikina na ciwo, kamar ana min
motsi a ciki" har yanzu ta qi bude idon," Subhanallahi, gobe zamu asiniti mu ga likita dan
shiyasa kk ji kwanaki ina ce maki sai naga kamar baki da lfy, abinda ke kwantar min da hankaki
kawai ganin yanda jikin ki ba wani damuwa sai kyau da kk qarawa ma, nan din ki har wani kyalli
suke" hannun shi ya kai saman rigar ta yana shafawa, a hankali ta janye hannun shi ta juya
baya ta ci gaba da baccin ta, wani yawu ya hadiya, ganin yanda hips din ta suma suka ciko
sosai kamar sui magana, tashi yai ya maida plate din ya wanke bakin shi da hannu ya rufe ko
ina ya dawo" princess ko dai fushi kk ban dawo da wuri ba yanda na saba? Shi ne kk share ni
kk son yin bacci?" Shiru yaji, matsawa yai jikin ya ya janyo ta, bacci yaga tana yi sosai, bai so
haka ba, gaba daya ta rikita shi, amma haka ya hakura dan yasan ba halin ta bane kyale shi
koda tana cikin fushi ne, ja masu abin rufa yai yai masu addua ya shafa masu, suka
kwanta........
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA
BY HAERMEEBRAERH
Alhamdu lilLAAH ala kulli halin, naji sauqi sisters na gode da kulawa, Allah ya barmu tare da
alkhairi mara yankewa. ME LOVE U XOXO❤
Page 12:
Da asuba ta tashi ta duba taga har ya fita masjid, addu'ar tashi daga bacci tai " "Alhamdu
lilLAAHi alladhi ahyani ba'ada maa amatani wa ilaikannushour" sannan ta sakko daga gadon ta
je tai alwala ta dawo ta gabatar da raka'atanil fajr tai sallar subh,tai azkar din safiya, tana idarwa
tai azkar din ta, tana gama wa wanka taje tayi ta sake yin brush, gaban madubi ta zo ta
warware kitson da tai da yamma, guda biyu akan ta sakamakon ba ta son kitso sosai kuma
shima Yah Jabeer din nata yafi son tana mai adon gashin haka ba tare da ta kitse ba( yana da
kyau mace ta iya yin kitso biyu irin na indiawan nan da muke gani ana raba kai biyu a kwantar
gefe da gefe a dame shi a kitse sai yai matuqar kyau in ke mai santsin gashi ce ma zakiga har
sheqi yake da dare ake wannan kitson bayan kin gama wa oga kwalliya, ma'anar yin wannan
kitson na farko dai zaki bacci ba tare da kanki yai buyaya ba, kinyi muni, da safe zaki tashi kan
ki tsaf da shi, bai barbaje ba, sannan kuma in ma kun samu kusantar juna da me gida kin yi
wanka kanki ba zai na lalacewa ba nan da nan kiji mata suna kai yasha ruwa gashi na.zubewa,
akwai fa'ida sosai akan yin hakan da sai kin fara zaki gano su da kan ki) da sauri take yin komai
ba son jiki, dan ba ta son sai ya dawo ne zatai wadannan abubuwan, ya na dawo wa daga
masjid ya tsaya wajen Innar mu su gaisa, kamar kullum, riqe shi tai d surutai na ba gaira ba
dalili, daga baya ne ta fara tura mai saqon dake ranta a wayon ce" Allah sarki Juwairah yarin
yar nan akwai hakuri, kaga fa yanzu wata na wajen.shida kenan.da auren ku, qawayen ta sun
haihu amma ita ko batan wata bata taba yi ba, amma bata damu ba, ko dake dama yaran
zamani.ai ku ba ruwan ku, mu ne dake son yan jikoki mu za mu damu, waya sani ma ko
maganin hana haihuwa take sha" wani irin faduwar gaba ne ya samu Jabeer ido ya zaro waje
yace" Haba Innar mu Juwairan nawa take d zatai wannan tinanin? Kuma har ta aikata hakan?
Inaaaa sam ba zatai haka.ba kima daina wannan tinanin dan Allah, kuma da kk zancen sa'o'in
ta Innar mu Nafeesa ma fa sa'ar ta ce ita kinga ai har yanzu ma batai aure ba, in da zaki gane
komai nufi ne na Allah ko" habaaa kamar ya watsa mata wuta, bala'i ta fara kamar ta ari baki"
iyeeeee lallai e Jabeeru ka nuna min mata tafi 'yar uwa ko? Har qanwar ka zaka duba kaiwa
gorin aure? To bari na fada maka abin da nake boye maka, nifa na fara gajiya da wannan
yarinyar, tin da ka aureta ka daina bamu lokacin ka, ka daina zama ai hira kamar ta da da kai,
sannan gaba daya soyayyar ka da kulawar ka ta koma wajen ta, akqn me?" " akan shi ne mijin
ta, kuma hakan da yake shine yake nuna ya haifu dan sunna ne, yanzu dan Allah bakiji kunya
ba? Kk hada kan ki da surukar ki? 'Yar ki kuma ta wani bangaren? Habaaaa Hansai, wace irin
rayuwa kk daukar wa kan ki yanzu, abinda ba halayyar ki ba kina neman shaidan ya maki
huduba ki fara, to bari na fada maki abinda mata kan ku yake toshewa akai, kowacce mace
dangin miji ce, kuna uwar miji ce wataran in ranta ya kai, dan haka in kikai wa matar dan ki
adalci, kema sai wata taiwa taki yar, in kk kyautata wa matar wanki ko matat qanin ki, kema naki
qannen mijin da matan yayun sa zasu tausaya maki su miki adalci, in kuma duk kin kiyaye
amma ana maki abinda bai dace ba, to ki sani kowanne dan Adam akwai jarabawar shi,
wataqila taki anan take, sai ku hakuri ki qoqari kuma ki cinye jarabawar taki, dan haka in kk
kula, tin da Jabeeru yai aure kulawar da na ke ba ki ta qaru, ba dan komai ba sai dan kula da
nai kin kai idon ki gidan matar dan ki, ki gyara hali ko kun samu rabauta a lahira, baki tafi da
haqqin kowa ba, haihuwa ta Allah ce, ko bata haihuwa haka yaga zai zauna da ita ke baki isa ki
ce dan me ba" Baba Balarabe kenan da ya dade a tsaye yana jin maganganun Innar mu, wata
irin nadama da kunya ce ta kama ta," Malam ka yi hakuri, Jabeeru ka yafe min sharrin zuciya da
shaidan ne, ina ganin tin da ta zo komai namu yaja baya, ga shi kana nuna mata tsantsar so,
idona ya rufe akan hakan na manta nima nawa mijin yana iya qoqarin shi akaina, ku yafen ba
zan qara ba" nan ta zayyano yan sace2n da tai tayi wa Juwairah dan ta hada su fada amma sai
taji shiru, saka makon iya zaman duniya da Juwairah ke da shi da ta kula hakan ta faru zata san
dabarar da tai ta bashi hakuri, da jikin ta da kalaman tq, " Ba komai Innar mu ya wuce ke uwa
ce a wajen ta, da bata dauke ki uwa ba uwar miji ta dauke ku da ita kanta zaman sai ya mata
wuya amma tasan ko da uwa da uba ana sabawa fiye da haka ma a kuma ci gaba da zama,
dan haka na san ba ta qullace ki ba, jiya kwana tai ba lfy, asibiti xamu ma" Subhanallahi" suka
hada baki dika ukun har da Nafeesa, " meke damun ta?" Inji Innarm mu, " Da ciwon jiki ta
kwana ga zazzabi da ciwon kai, ciwon mara, da kasala, dan jiya wani irin bacci ta dinga yi"
murmushi Innar mu tai tana" ikon Allah ai ya kamata a kaita ta ga likita bokan turai a fada mana
wata nawa ne, na fara tanadin kayan kwalliya dan da alama bana zan yi ango nima, in kishiya
ce na samu na gyaran daki,kar ta zo