Showing 63001 words to 66000 words out of 70697 words
Chapter 22 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf
mu da iyaye acan mu ne iyayen junan mu mu zamu taimaki kan mu, dole sai mun
zama masu irin wannan tinanin gudun shiga matsala kan dayan mu ya kai mana agaji" wani
kallon so da qaunar qanwar tasu ke yawo a zuqatan su, a haka suka samu abin hawa bayan an
masu niqan kayan qamshin, gida suka nifa a gajiye, wajen bayan azahar, alwala sukai sukai
sallah, sannan sukai wanka suka ci abinci, sai baccin gajiya.
Tin da sassafe angwaye suka jera mota uku Jabeer kuma ya dakko hanya shima amma bai iso
ba Adda Suwaiba da Innarmu sun zo suma, amare ana ta dan koke koken rabuwa da gida,
Saudat kuwa tsoro ne fal cikin ta na komawa Abuja, ji take kamar ta fasa auren, amma ta dake,
tana son tai wa mijin ta kyakkyawan zato, Adda Suwaiba anyi anyi tai rakiya tace ita da Abuja
ko a film ba ta so taga Alihu a can ba, haka aka hakura aka barta she will come around wataran
zata je ne, Jabeer ne ya iso, inda nan kai tsaye gidan su Juwairah ya sauka, ta sauke shi da
abinci da komai na motsa baki, Amare sun daga sun bari akan in sun je zasu nemi gidan su, tin
da Jabeer bai huta ba, haka suka tafi Goggo Sarai na ta zabga masu addua da Abba sannan
Mama Bilki, kwalla kawai Goggo Sarai ke sharewa , bata san wannaj karon me zai faru ba,"
Adduar fatan alkairi zaki bisu da ita, ki daina zurfafa tunani, ki masu kyakkyawan zato Yaya," "
To Bilki Allah ya kao su lfy, Allah ya zaunar da su da alkairai marasa yankewa" amsawa dukkan
si sukai da" Ameen" suka koma ciki, inda Jabeer na dauke da Abrar, Ammar na wajen Suwaiba
tana ta mai wasa, dan ya damu sosai da rashin Adda Calman shi, fitowa tai zata debo mai
dambun naman da ya ragu a kitchen wanda akaiwa amare, giftawar ta Abrar ta gani ta ko sa
kuka tana miqa hannu, komawa tai ta dauke ta, Yah Jabeer na mamakin soyayyar su, " haka
suke , in dai Adda Suwaiba na kusa to pa ni na huta,sai mu yini ko Nono bata nema, sai dai tai
ta bata kunun ta" " ikon Allah lallai akwai soyayya mai qarfi a tsakanin su", gama wa yai suka
shirya komawa gidana su,inda suka tafi da Suwaiba itama, a motama Abrar na hannun ta, tayi
bacci, sun isa gida Suwaiba da Innarmu suka tafi bangaren su , suma suka tafi nasu gidan, a
hankali ta dorawa Juwairah Abrar a cinya amma juyawa tai ta qanqame ta, sai Jabeer ne yai
dabara ya raba su, tafiya tai cike da qaunar yarinyar a ranta tana share hawayen baqin cikin
rashin haihuwa, shafa marar ta tai daidai lokacin da ta shiga bangaren su, hawaye na fita mata
masu dumi, Salihu ne dake gidan a zaune ya hangota ya tashi cikin hanzari ya isa gareta,
rungume ta yai dan ya fahimci halin da take xiki, kuka ta saki mai ban tausayin mai sauraro"
yanzu mine shikenan ba zan haihu ba, da ba zai taba samun mazauni a wannan marar ba? Ya
zanyi da son yara dake addabar zuciyata?" Kuka shima yake sosai sai da sukai ma'ishi sukai
shiru" kiyi hakuri ni na jawo maki wannan nakasar, ki gafarta min, nima ina cikin quncin rashin
haihuwa,musamman inna kalli yanda Abrar ke son ki, take matuqar qaunar ki, sannan na san
zaki haifamin yara kyawawa kamar ta, amma na mana mugunta, Allab wadaran rayuwata" rufe
mai baki tai da sauri" pls don't say that again, Allah ya albarkaci rayuwar ka zaka ce, kabci gaba
da gyara kurakuren ka na baya, ka duba ka ga ni fa yanda Allah ya maka albarka a kasuwancin
nan, har fili ka siya, nan gaba kadan gida zamui mu koma, mu ci gaba da jin dadin rayuwar mu,
to mene na daga hankali, Allah ke bada haihuwa ya ba wanda yaso,mu ba zamui kuka da Allah
akan bai bamu ba,saboda mu da kan mu mukai wa kanmu mugunta dan haka hakuri zamu ci
gaba da yi," Juwairah ce ta koma gidan ta da gudu tana kuka, garin Kayan qamshin da ta niqo
wa Addan nata ta sake ya fadi a qasa, kuka take sosai har tana shessheka, wani irin tausayin
su ne cike a zuciyar ta, Jabeer gaba daya ya rude" Babe me ya faru? Waya mutu, Ya Allah
Sanar dani ko na sama maki kwanciyar hankali, ki sanar dani kome kk so na miki , kukan ki na
daga hankalina" kwalla ce ta fito idon shi yai qoqarin mayarwa" Sweet one ka taimke ni ka
bawa su Adda Suwaiba Abrar" maganar ta doke shi, kuma yaga tsantsan rashin hankalin
ta,kyautar mutum sukutum, ya zai iya wannann kyauta? Amma duba da yanda take kuka sosai,
hankalin ta a tashe ne yasa ya kama ta ya zaunar, ya umarce ta da ta sanar da shi akan wane
dalilin zai ba da yarinyar shi guda daya tilo, bayanin komai ta mai cikin kuka bata rage komai
ba, shi kanshi sai da ya share hawayen, " Tabbas roqon ki ya amsu,nima Allah ne ya ban ita ai
ba ni naba wa kaina ba,dan haka na basu ita halak malak, ko bayan raina Abrar Hafsat Ta su
Suwaiba da Salihu ce"sai ya kashe murya just to cheer her up"kinga da mun koma sai na sake
wani zubin a nan wajen, na sama mana Abban ki ko" yana shafa marar ta" kai anan ma yau ba
sai mu fara ba, har Allah ya sa a dace, kinga daga gobe sai a koma kiran ki Maman Abba"
dariya ta saka ta kai mai dukan wasa ya goce ta bishi ta haye cinyar shi tana qoqarin sai ta
hargitsa mai sumar kanshi yana qocewa, a haka suka fada kujerar a kwance suka hau kissing
juna kamar su cinye kansu, nace toooooo abun na manya ne Hamma yace babyna baki girma
ba zo mu tafi kar su batan keí ½í¸‰
Da wajen qarfe goma sun gama shirin tafiya sun hada akwatin kayan Abrar da komai Sallama
suka je yi ma su Innar mu, Su suwaiba da Salihu suka shigo, cike da fara'a suka gaggaisa,
Abrar na ganin Suwaiba ta ko hau qoqarin zuwa wajen ta, cikin shauqi da kewar yau zata rabu
da Abrar din ta dauke ta ta rungume tana kissing din ta, ita kuma sai dariya take, irin na yara,
wata kwalla Juwairah ta share ta son yar ta ta amma tabbas haka zata bawa Addan nata ita,
miqa mata akwatin yarinyar tai tace" Addan daga yau kin zama Ummu Abrar, dan Yah Jabeer
ya miki kyautar ta gaba dayan ta, kin cancanci zama uwa a gareta, dan haka ga tanan, dama ita
ba wai ta damu da nono bane, kunun nan da kk bata shi yakamata ki ci gaba da bata, Allah ya
raya maku ita da imani," ta ja baya Suwaiba da Salihu tare da Innar mu Baba Balarabe ne ya
katse shirun" a gaskiya Juwairah ke alkairi ce ga rayuwar zuri'ar mu baki daya, tabbas Qanina
da Bilkisu sunyi matuqar qoqari na baki tarbiyya managarciya, wannan shine dalilin da ya sa kk
zama haka, Allah ya muku albarka, kai ma Jabeer naji dadin wannan kyauta da kai, duk da
nasan ita zata saka ka, amma da baka aminta ba da hakan bai samu ba," godiya sukai innar mu
tace" Suwaiba Allah ya taya ku riqo, ya sa ki qoqarta bata tarbiyya mai kyau, yanda zata tashi
abar so ga kowa" Suwaiba da Salihu kuwa kukan farin ciki ya hana su magana sai gyada kai,
wanda hawaye ke kwarara a idanun su, zuwa tai ta rungume qanwar tata, da durqisawa a
gaban Jabeer, dago ta yai ya na buga bayan ta, yana kada mata kai, Salihu ne ya je ya miqa
mai hannu daga baya ya rungume shi ya saki kukan murna" Na gode na gode baku kula da
rayuwata ta baya ba kuka mana wannan kyauta Allah ya faranta maku, ya baku yara masu
albarka kuma," Ameen kowa ya amsa sannan suka tafi, suna tafiya Juwairah ta saka kukan
rabuwa da yar ta, hannun ta ya kama shima yana jin wannan kewar, amma ba yanda zasui,
Allah ya basu ladan hakan, a haka har tai bacci.
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: í ½í²…í ¼í¿¼ 'YAN ABUJA í ½í²…í ¼í¿¼
BY HAERMEEBRAERH
Page 34:
Labarin kyautar Abrar zuwa ga Suwaiba ba inda bai shiga ba a dangin nasu baki daya, inda
kowa yake farin cikin irin wannan kyautar da ba kowa ke iya ta ba, ( mutane in baka haihu ba
sun iya maka tereren baka haihuwa ko kalmar juya ta shiha tsakanin ka da su, musamman
dangin miji daga sanda aka ce basu da cikakken ilimi, jahilci ya musu yawa to daga ranar ka
shiga uku in baka haihu ba, ba sa tinanin cewar ma ko laifin daga dan su me? Aa kawai ki haihu
kamar ke zaki bawa kan ki haihuwar, sun manta cewar komai nufin Allah ne, Allah shike bawa
duk wani wanda muka gani da da, shi bai isa qoqarin shi ya bashi ba, komai himmar shi a gado
kuwa, ko sune Ayu qarewar making love ba zai haihu ba sai da izinin Allah, to me zai hana mu
tane su zama irin Juwairah, da ka zo kana ma wanda bai da da gorin haihuwa, mai zai hana kai
tinda ka samu Allah ya baka kai ma ka dauka ka bawa wanda kk tinanin juya ne bazai taba
haihuwar ba? Ba zaka iya ba? To karka shiga hurumin Allah, matsalar nan ta fi faruwa a
tsakanin mu mata, yayyab miji , qannen miji, da surukai, to ki sani ke yar uwata mace, ko wacce
mace dangin miji ce wataran, in kikai a gidan ku kika je wani gidan wata ce zata shimfida maki
nata ikon, wataqila ma wanda yafi naki, dan haka ki mai kyau kiga mai kyau, kikai sabanin
hakakiga abinda ya fishi, ko daidai shi, in kina kyautata wa ana munana maki,ki hakuri jarabawa
ce daga Allah zai maki magani zai kuma baki lada mai yawa, Allah ya sa mufi qarfin zuciyar mu)
.
A sati biyun da suka koma Juwairah ta shiga kitchen da yamma, a lokacin ta gama komai na
girki, gyaran gida, wanka, da kuma tsaftace ko ina na jiki da muhallin ta tana jiran Haerbeebeen
ta ne, miqa hannu tai ta dakko wata roba da ta cika ta da niqaqqen garin ridi, a hankali take jin
jikin ta ba kwari tin kwana biyu da suka wuce, cup din da ke hannun ta ta matsar jikin robar
domin diba, tana budewa taji qamshin kantun da take so na neman ya zama mata wari, amma
ta daure a haka ta saka spoon ta diba, zuwa tai tukunyar da ta dafa madarar shanu, wadda
Jabeer ke nemo mata a cikin wani qauye anan Abujan, ta dibi yanda zai ishe ta, zumar ta asalin
mai kyau mara hadi ta diba ta saka, yanda take buqata, palo ta koma ta zauna, bayan tai
bismillah ta riqe cup din da hannun ta na dama ta kai bakin ta ne, wani irin amai ya yunquro
mata, da gudu ta miqe zatai hanyar dakin su taje toilet,karo taci da shi yana shigowa, wani
yunquri da tai sai anjikin shi, jikin ta har rawa yake yi, dan azabar da take ji a jikin nata, aje jakar
shi yai hankalin shi a tashe matuqa, ya kama ta tai ta kwarara amai, sai da ya zamana bata iya
fitar da komai sai yunqurin azaba, sannu kam ta shata har bata iya amsawa,idon Jabeer sunyi
jaa saboda tausayawa matar tashi,tabbas in hasashen shi gaskiya ne wannan karon da alama
mai wahalarwa ne, dan ya kula kwana biyu kenan tana fama da wannan wahalhalun, ga
zazzabi dake addabat ta, haka ya jata suka tafi toilet,kayan su ya cire masu,ya saka su a
bathtube,ruwa ya cika masu suka dauraye jikin su sannan ya tsiyaye ya saka wani, wanka ya
musu suka fito, bayan ya shirya ta ne ya kwantar da ita a agado yaje ya shirya shima,zuwa yai
kusa da ita ya kwanta ta bayan ta" Honey kaje kaci abinci everything is ready at the dinning
area" " I know,but i can't eat when u are like this, me ke maki ciwo, me kk so, dan daga ganin ki
da kuma aman da kikai,bakici komai ba in ba wainar flour din da kikai mai manja ba da safe,"
turo baki tai daga baya ta kwabe shi irin na shagwababbun nan, shi kuma yana jin yanayin
saukar nunfashin ta ya san na kuka ne, saurin juyar da ita yai, " What is wrong my love,pls tell
me ur problem,or what you want, i will provide you with anything i have inshaa Allah" kukan da
take son yi ne na shagwaba ta fara, rungume ta yai yana kissing wuyan ta a hankali yana shafa
bayan ta,sai da tai ya ishe ta tai shiru tana ajiyar zuciya, a hankali ta fara magana" Yah Jabeer
banda lfy, kwana biyu jikina ciwo yake sosai, ga zazzabi da amai, abubuwan danake so sai naji
vana son su," sai ta qara saka kuka, " Shhhhhhhh, yi shiru my bby, ki daina kuka, ko zaki gwajin
ciki a gida ne, tinda muna da abin yi" jimmmmm tai kafin ta wuntsila daga gadon cikin doki da
zumudi, binta yai a baya yana mata dariya, dan ya kula bata kawo hakan ba sam, sai yanzu,
zuwa tai tai gwajin ta fito, layukan na farko ya fito radau na biyun ga shi nan dai, amma tabbas
akwai shi, kwabe fuska tai tace" ni ban gane komai ba," " to ko asibiti zamu?" " ehhhh haka za
ai ina zuwa" fita tai da hanzari taje ta sake kayan jikin ta zuwa doguwar riga da babban mayafin
da zai rufe har mazaunan ta, bayan ta gama ne ta juyo taga shima shiryawar yake, a tare suka
fita, sun isa wani makeken asibiti, a unguwar tasu ta Jabi, suna zuwa sukai mata gwaje2 inda
suka dau wasu yan lokuta, likitan ya tabbatar masu da tana dauke da ciki ne na sati biyu, wata
irin murna ce ta kama su, Jabeer ba ko kunya ya daga ta sama ya hau juyi da ita, ita ko sai
dariya take, kissing din ta yai kadan sannan ya aje ta, godiya ya hau ma Doc da bakin shi ya qi
rufuwa shima, yana mamakin irin soyayya ta wadannan mutane, bayanan yanda zasu kula da
cikin ya musu, wanda sun riga sun sani,amma sai suka koma kamar ba su taba ma sanin ya ciki
yake ba tsabar murna, bayan sun gama ne suka fito Jabeer na wanilallaba ta kamar kwai, "
Babe me kk so ki ci kinga kar kina barin kan ku da abinda zaki haifa mana da yunwa" kada kai
tai a hankali tace"ni ba komai kawai ina son wainar flour ne irin ta dazu," aiko ba wata wata ya
saka ta a mota sukai gida, suna zuwa ya shiga kitchen, ya hau mata wainar, daukan, abinda ta
kasa sha yai shi kuma bayan ya gama mata, tana ci yana sha,"lallai babyn nan, da qoqarin
shi,da gaske so yake kar ana shan abubuwan da zasu qara mai kuzari" dariya suka saka dikkan
su" ko kuma abubuwan da zasu qara ma Abban shi kuzari ba" qara fashewa da dariya sukai(
hadin kantu da madara ko da nonon Raqumi hadine tested and trusted dake saukar da ni'ima
sannan yai maganin wasu cututtukan jiki in baka da nonon Raqumi sai kai da madarar shanu).
Saudat ce na hango ita da angon ta suna ta zagaye gidan suna guje2 cikin tsantsar so da
qauna tare da begen junan su, wani irin shaquwa ce ta musamman a tsakanin su,tare da
tausayawa juna, dan suna cikin gudun ne santsin tiles ya kusa kwasa Saudat a qasa, amma da
ikon Allah sai bata fadin ba, ta dai tsorata ne kawai, da hanzari ya isa gare ta,yana wani juya ta"
Sweet one baki ji ciwo ba,ta ina kk bige??" Kamo fuskar shi tai gaba daya a hannun ta, ta matso
lips din shi irin yanda mutum zai iyayi da hannu ko da bakin shi ya tsuke su sui tsini, haka ta mai
itama, sannan ta kai nata bakin tai kissing din shi, sai da taga suna neman faduwa ta tsaya" me
ma kk tambaya ta dazu?" Ta fada cikin qunshe dariya,da daga gira,cikin in-ina ya fara bata
amsa" Ammmmm..... immmm.... damaaa... cewa... nai.... imm.... can u pls kiss me again" dariya
suka saka sosai har tana riqe ciki,daga ta yai ta bayan ta cikin nata suka samu wajen zama a
kujerun nasu, bayan ya kwantar da ita a kujerar ne ya kwanta ta bayan ta,ya rungumo ta ta
ciki,suna ci gaba da dariya, a hankali sukai shiru yana mata wasa da gashin ta" Babe me yasa
baka damuwa da batun rashin haihuwar da kasan ba zan yi ba, saboda rashin mahaifa, bayan
kai baka taba aure ba, ar u planning to have another wife ne nan gaba?" " My dear ina so ki san
cewa da auren da haihuwar duk nufin Allah ne, tayu a baki da mahaifan mu haihu, ta yu ba za
mu haihun ba, to ina son ki sani, haihuwa is a blessing that everyone will love to have it, amma
ni bana daga cikin wadan da suke ganin in mace bata haihuwa bata da amfani,to ina soyayyar
da yake mata? Dama dan Yara kawai ya aure ta? Ita ce take ba kanta? Idan zan maki kishiya
saboda baki haihuwa tabbas na zama daga cikin azzalumai, na kuma zama daga cikin masu
butulci ga Allah, domin