Showing 24001 words to 27000 words out of 70697 words

Chapter 9 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf

27 Apr 2025

4556

a qasan ranta na ganin me yasa ba
su son su haihu, suna son su san me ya hana su haihuwa????









Cikin dare Salma taji kamar buga qofa ake, a hankali ta miqe ba tare da tai wanai kwakkwaran
motsi ba, dan tare suke kwana da Haule yanzu, leqawa tau ta qaramar qofa ta bular ta hango
wan mijin nasu na waige2 yana kwankwasa qofar Marka, mamaki ne fak cikin ra dan duk yan
kwanakin nan mark ke zuwa, yau fushi take da shi, daren jiya ya hana ta dari da hamsin da ta
roqa yace bai da su, shine tace yau ba za ta ba, shi kuma gashi a mugun matse yake, hannun
shi na kan wandon shi, haka yake kwankwasa qofar, budewa tai tana magana qasa2" Dalla can
sai ka tada yaran ma sun gan ka, ni shigo kayi ka gana ka tafi" jawo shi ciki tai ta wandon shi,
aiko akan idon salma, kame baki tai tana fadin " tab ashe wannan matar munafuka ce? Ba ta da
maqiyi da rana kuma bata da masoyi da dare da ya wuce Babam bangis, lallai ran da Su
Badamasin suka sani akwai case" tana cikin wannan tinani ta fara jiyo qarar dan qaramin gadon
na Marka irin na qarfen nan, sannan ga sambatun ta nan da bata iya shiru ita sai ta tona masu
asiri, yaran akwai nauyin baccin tsiya, to an wuni shiririta kuma anyi bacci late dole in sun
kwanta kamar gawwaku, Marka a wayon ta hade yaran take dika daki daya saboda irin haka,
kafin Salma ta zo ne dakin ta yake na Yammatan, amma kawo ta yasa aka hade su, motsin qofa
Salma ta ji zai fito sai da ya fito Marka ta biyo shi tana miqa tana gantsaro girji, shi kuma yana
qara shafawa" kamar na koma mui ta yi sai asuba na tafi" " lallai Yaya kaima a gaida ka, duk
wannan aikin da garar da ka diba bai ishe ka ba, in kana son ka koma ciki qaron nera daru
kacal" murmushi yai haqoran shi jajaye suka bayyana" Aaaa dari tab na gama baki dari ukun
yau, ni dai gaskiya ban da su" " to kuwa kama gaban ka ka wuce ya ishe ka haka a barwa
gobe" yana qarasa fitowa gaba daya Salma ta fito da buta a hannu ita ma , hankalin su ne ya
tashi, gaba daya da ganin ta" Salame dan Allah ki rufa mana asiri, kar kowa yaji labarin nan"
suna hada baki suka fada" a nawa zan shiru ko ko haka nan zan rufe bakin nawa kuke nufin"
kudi ya dakko dari biyar guda biyu ya miqa mata" sauran naki kema, da sauri ta shiga daki ta

dakko dari biyar ta hada dana hanun ta ta bata, " sannan ina son ki sani Talle ya kusa dawo wa
dan jiya baki nan kina yawon ta xubar Badamasi ya fada sun yi waya, in ya dawo kk kuskura na
ganku tare har kk hada jiki da shi warin ki ta mannu a jikin shi saina fada mai, dan ba zaki sa
yanda ni na tsare aure na ba ina juran ya dawo mu raya sunna ki ja min amai ba kuma ba biyan
buqata, kinji ni ko, wani yawu ta hadiya na yau ta shiga uku an raba ta da gwarxon maza, tace"
na gane kiyi wa Allah ki rufa mana asiri" " baku da matsala in ma komawa zakui sau asuba din
zan iya maku gadi" Aaaaa ni na ma ta fi yannan" fakam fakam Yayan Talle ya bar sashen nasu,
ita kuma ta koma daki ta bar Marka da cizon yatsa an amshe yan kudaden kuma ba wai itama
ta qoshi da abun bane, yau tayi biyu babu, tura qofar tai ta koma, Salma me zatai ba dariya ba
yanzu sun dawo hannun ta kenan da taji tana son kudi zata neme su kuma dole su bayar ko ta
tona su, wani muna tai ta dale gadon ta ta miqe.











Yau shamsiyya qawar su Juwairah da Nafee ta kawo ma Juwairah ziyara dan tana son ta qara
bata wasu shawarwarin game da yanda zata gyara nonon ta da suka lamushe kamar an yi
gobara ta ciki an yashe komai sai fata, sannan ga kanta dake yawan karyewa gashin ta na
zuba, abu mafi mahimmanci da zai kaita ta taya su murna dan Nafeesa ta bata labarin samun
cinkin da tai, murna take sosai itama da jin hakan. Shiryawa tai bayan ta gyara gidan ta tsaf
kamar ba ita ba ta fito ta hau abin hawa har gidn su Juwairah da Nafeesa bayan ta sauka ta
sallami mai adaidaita sahun ne ta shiga ciki, bangaren innar mu ta fara shiga, bayan sun gaisa
ta mata murna ne ta shiga ciki , wajen Juwairah, a can ta hango Nafeesa tana alwalar la'asar,
Juwairah na daka tana gabatar da sallah.........
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ' YAN ABUJA




BY HAERMEEBRAERH


This page is for u SWEETHEART, Sis Juwairiyyah, u ar d best sister that one could ever ask for,
i love u so so very much dear, u ar d best.❤❤❤❤❤❤❤❤

Page 14:









Itama sallah tai domin da alwala ta baro gidan ta, tasan lokaci zai mata hakan, bayan sun idar
ne suka hau gaishe gaishe, Juwairah na tsokanar Farha akan ta girma ta isa yaye," hmmm ke
dai bari sis abinda na ke son ki ban shawara akai sis, ya zan dan nan da sati uku nake son yaye
ta, nono gaba daya ya koma slipas b kyaun gani, ya barni da fata, duk nankarwa a jiki, ga cikina
ma nankarwa tun na haihuwa, dan ma Allah ya san Abban su mutum ne mai kawaici baya son
ya bata raina amma ba namijin da zai so hakan, dan kan ya koma hakan na kula yana matuqar
son wajen" " sister kin ko kawo kuka wajen maganin ki" dariya suka saka Juwairah tace" Nafee
kina ban matsayin da bai kai nawa ba Allah" " no ba haka bane dear a gaskiya kina burge ni
wajen hangen nesa wallahi na san ba komai bane ya jawo sai mai da hankali da kikai kk koya
wajen Mama Biliki da muna ganin kina 'yar ta amma tana baki wahala ke ke komai a gidan
gashi yana maki amfani" haka ne kam, dan ko ni a da watarab sai naji na gaji bana son
taimaka mata, data fahimci haka bata mun fada amsa take tayi takan ce jiki da jini, ti tanzu dai
kin san me zaki yar uwa na farko ki nemo wadannan garin maganin ki fake su waje daya ki
samu alkama ji qarin ta kina kunu kuna zubawa ko da madara ko ba madara, zaki iya sha, ke ko
a ruwa xaki iya sha amma yafi kyau a alkama da madarar musamman ta shanu, magungunan
sune kamar haka, NONON KURCIYA, GANYEN BAFULATANA, GADALIN NONO, su ne
abubuwan ana samu a wajen masu saida maganin mata, sai kuna na biyu mai sauqi kuma yana
yi sosai shima, wanda zaki samu farar shinkafa, ki wanke ki jiqa akai markade ta zama kamu,
sai ki daka bagaruwa da ake tsarki da ita, ki na dibar kadan ba mak yawa ba kina yin kunu kina
sha, zaki iya saka madarar shanu ko ta ruwa in babu zaki iya shan shi haka, banbancin su
wancan in ya karbi mace yana dadewa a jikin ta, sosai, sannan kuma ba a son qiwa kiyi yau kiqi
gobe sannann ana son ayi kamar na wata daya, zuwa yanda nonon ki ya lalace, bangaren
nankarwa kuma ki samu, man kade(wanda ake shafawa faso ko kaushi) sai kina shafawa a
cikin ki da kuma nonon da dai in da kk san akwai nankarwar(stretch marks) kinji wadannan a
sauqaqe kenan"" kaiiiii amma wallahi yar uwa na gode sosai, Allah ya saka miki da alkairi, Allah
ya sauke ki lfy, ya bamu bby mai albarka," sunkuyar da kai tai a ranta ta amsa, " Dalla in zaki
amsa ki amsa ba ma son gulma kikai cikin ma" " sannu Nafeesa sarkin rashin kunya na gode
dani kk wannan maganar tin da ni nayi" cikin kaduwa Nafee ta hau zare ido, tama kasa
magana, su kuma dariya da kunya ce ta kama su musamman ma Juwairah ashe Yayan ta duk
yana jin su, tashi tai ta ja labulen ta fita wajen shi kai a qasa" sannu da zuwa mine" " yawwa
princess, how ar u feeling,now?" " i am kind of k, amma fa kaina yanajuyawa kuma cikina na

motsawa sai nai ta jin tsoro kuma abin na min daban haka" " ki ta hakuri kinji princess u will be
fyn inshaa Allah, kawai hakurin nan naki dana san ki dashi zaki ci gaba zamu iya komai we can
get thiugh it all" murmushi tai, shima haka yai kissing bayan kunnen ta a hankali, sai da yasa
tsigar jikin ta tashi, " yanzu tinda shamsiyya ta zo bari na je wajen Innar mu na yi hirata nima"
gai da shi shamsiyya tai ya yi ma Farha wasa ya tafi, Nafeesa ta aika da abincin shi da komai,
da kyar ta karba dan kunya da tsoron Yayan nata, dariya suko sukai ta mata,bayan ta dawo ne
ta ce" laaa Matar Yayah na hada mana zogalen da ramar?" " kaiii amma Allah ya miki albarka,
pls do" ta shi tai suka je Nafee na hadawa suna hira ta saka komai zata yanka albasa kenan,
Juwairah ta dakatar da ita" Nafeesa kar ku sa mana albasa sai dai a naki dan mu muna da
masu shinshinar bakunan mu, ehe, baki san ba a son in yamma tai mace ta ci albasa ba? Dan
haka ki kiyaye ko ke zaki in miji na gida ki hakura da albasa,in ko kinci ki tabbatar kin wanke
bakin ki tass yanda ba yanda za ai ya ji warin ta" godiya suka sake mata dikkan su shamsiyya
tace" lallai zan yawai ta zuwa gidannan don na samu sirrin da yasa baki taba fada da mijin ki ba
kuma kk iya controlling din shi haka" " hhhh haba shamsiyya ai mace bata controlling miji sai
dai ya zamar mata bawa a lokacin da itama ta zamar mai baiwa, na miji ba ya sanin ya zama
maki bawa sai dai yaji mutane na cewa ya zama mijin hajiya, ko mijin kan tace, da sauran su,
babban abinda ke jawo ma mace hakan kuwa shine, neman soyayyar Allah makadaici, in mace
ta nemi soyayyar Allah, ta kuma samu ta gana da na miji, wanda hakan yai qaranci a cikin mu
mata, daga wajen boka sai dora rai akan, maganin mata, bayan ba su kadai ne ke riqe zaman
aure ba, wallahi in Allah ya so mace ta gama samun dacewar duniya da lahira, dan haka ni
sirrina na zaman gidan aure shine son Allah da neman Allah ya so ki, saka soyayyar namiji a
saman ta Allah shi ke saka mata fadawa halaka, daga zuwa wajen boka, zuwa zinace2, da
dikkan abin da ya kauce hanya dan haka ina horon ku da neman soyayyar Allah, wani irin dadi
ne ke ratsa su dikkan su, musamman Jabeer da ya kawo kwanuka da niyyar yin alwala yai tafi
masjid, wani irin dadi yaji yakuma godewa Allah a zuciyar shi sosai da samun mace kamar
Juwairah, suma sallah sukai, suka raka ta ta hau abin hawa ta tafi, tana cike da farin cikin
samun qawa kamar Juwairiyya.






Kui hakuri da wannan sisters dan nayi alqawarin typing ne yau ma da ba zan samu yi ba, tanx
alot. Me love u xoxo.❤
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA




BY HAERMEEBRAERH

page 15:





Yaune ranar da Suwaiba da Saudat suka hada akan zasu je asibiti su ga meke faruwa har
yanzu ba su samu ciki ba balle a kai ga sa ran haihuwa, sun shirya tsaf inda suka yi ma
mazajen qaryar zasu tafi shoping ne, Dunes Supermarket suka nufa cikin isa da qasaita, da
nuna su wasu je a Abujan ma, Alhj Salihu ne ya biyo su a boye ya tabbatar da ina zasu je,
ganin sun nifi nan ne ya sa hankalin shi kwanciya, ya kira Alhj Kalla ya sanar da shi cewar da
gaske shoping suka tafi, Suwaiba ta kula da bin ta da yake duk da qoqarin boyewar da yake
shine dalilin ce ma driver ya kai ta can tai ma Saudat message akan su tafi can din, bayan sun
isa ne sukai sauri suka fita ta baya suka je wani private hospital dake kusa, ta shin farko likitar
ta gane ai ba ma mahaifa a tattare da su an cire ta, hankalin su ba qaramin tashi yai ba, kuka
suka saka kamar wasu yara, jikin Saudat sai rawa yake dan ta fi Suwaiba son yara, dan
Suwaiba dama ita ba wai ta wani damu da su ba ne, amma kasantuwar yanzu taji bata da
mahaifa kwata2 hankalin ta ya dagu sosai, tashi sukai bayan sun gama biyan komai suka dawo
supermarket din suka debi wasu daga abubuwan da suke buqata musamman na gyaran jiki,
Suwai ba kuwa acici kayan kwalam fa maqulashe ta jida," da mu zauna ba mahaifa ba kayan
more rayuwa ai gwanda mu kwashi rabon mu muci tin da bamu da magada" fadan hakan ke da
wuya Saudat ta saka kuka," Malama kar ki taran jama'a, meye na kukan kuma a cikin mutane,
daga cewa mu more rayuwar mu, dan haka ni dai kinga, in ba zan haihu ba ba kuma zai hana
na more rayuwa ta ba,come to think of it, ba mahaifa ba haihuwa ba kudi, wahala ta kama mu fa
kenan, kuma mazajen mu suka san bama haihuwa mun shiga uku, in gaba suka so qara auren
su za sui, ba gwanda mu ware ba mu saki ran mu mu tatsi abinda muka tatsa, tin da mun taba
zaman Abujan munji abinda ke cikin ta, kinga sai mu canja sheqa" gyada kai tai kamar
qadangaruwa, amma wannan zancen rashin mahaifa kuma ita da yar uwar ta a tare akwai wani
abu a qasa wanda sai ta binciko ta san mene shi, bayan sun kammala kowa ta kama hanyar
gidan ta.

Yau gidan Talle shar da shi domin ta shi kawai sukai suka ga Salma na bada umar ni ko ta ina
kuma Marka bata ce komai ba, da farko sawa tai manyan sukai shara sosai, suka share ko ina,
suka wanke bayin su, aka fito da wanki narke da daki kowa ya duqa har yaran sukai ta wanki,
da kudin da ta karba a wajen su da shi aka siyo sabulun wanki, bayan sun gama ta sa su
wanka, gidan yai fes da shi, Marka ma sai da tai wanka ranar, Salma tai wanka ta tafi daki ta
kwanta, dan ta bada kudi a siyo kayan miya ai girki, kwanciyar ta ke da wuya, Huwaila da
Jummala suka shiga dakin mamar su da ya sha gyara suka hau tambayar ta wai me ke faruwa
ne" Um Um Um Um Um" shi take maimai ta wa kawai tana kama baki, alamar sui shiru
maganar babbace , kame bakin nasu ko sukai ba su qara tambaya ba,Marka ko cikin zuciyar ta
cewa take, "yarinya ni ce fa uwar shedanu, ki gama wannan mulkin naki na yan kwanaki, kiga
abinda zai.faru nan gaba, dani kk zancen" da yamma suka ji qarar mota fita sukai da gudu,
Huwaila na can Ita da Baban gida a wani lungu na gidan suna sana'ar tasu, sukaji qarar, ai a
firgice suka saki juna sukai hanyar fita daga lungun kowa na zare. Idon, Talle kenan mai gayya
mai aiki, shine ya iso, Salma da jin haka ta miqe tana rangwada ta je.ta taro shi, dawowa sukai
ciki yaran nata gaida shi, yana amsawa, dakin Marka ya leqa ta ganta tai wanka dakinnan fes,
wata uwar dariya ya saki" Shegiyar sama wato ganin amarya ta kyakkyawa ya nutsar dake, yo
ni dana san haka ne ai dana dawo da jimawa, da ban tsaya wajen qadangarun bariki suna
amshen kudina ba" leqawa zai ya shiga Salma ta tsaya a bayan shi tana kallon Marka, da sauri
Marka ta miqe ta ja baya," Aa Talle in ka zauna dakin nan ba ai wa yarinyar can adalci ba kuma,
wancan karon ai a wajena ka fara zama ina ganin wannan karon wajen ta zaka fara zuwa"
tsantsar mamaki ne ya kama shi ya sake baki, qarasa yai wajen ta ya taba wuyan ta yaji lafyr ta
qalaou kuwa? Ya jita daidai, amma abun nan akwai mamaki, kada kai yai ya juya yai dakin
Salma dan tana ma Marka kallon nan ta juya, hira ya dinga mata da ba wai ganewa ta ke ba,
dan gaba daya tsami yake yi, dabara ce ta fado mata, ruwa ta saka a bokiti babba, ta dakko
brush guda biyu ta saka toothpast jiki ta je kusa da shi zuciyar ta na tashi amma ta jure ta zauna
a cinyar shi tana shafa shi, " Babe taso muje mui wanka magariba na yi, kaga in munyi munyi
sallah sai muzo nai maka tausa dan da alama ka gaji ko" gyada kai ya dinga yi kamar
qadangare ya daga ta yana son ya dauke ta, da sauri ta sauka dan in ya sata a kafadar nan sai
tai amai dan tsamin zufar da yake, nuna mai tai akwai yara kawai yaje ya fara shiga zata biyo
shi ta mai wankan, tafiya yai yana washe baki, rabon da a mai haka tin tana amarya a cikin
garin Abuja, wanka ta mai sosai, ta bashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login