Showing 48001 words to 51000 words out of 70697 words
Chapter 17 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf
wanke wajen sosai, wankewa ta je tai
ta gama ta fito, still fuskar ta ba walwala, " Haba Juwaireren Mama Juwaireren Yah Jabeer, me
kuma ya faru, me kk so gaba daya bana jin dadin rasa murmushin nan naki mai kwantar min da
hankali, da ki hana ni murmushin ki gwanda ki hana ni ruwa inna dawo daga kasuwa a gajiye"
bata san sanda murmushi ya kwace mata ba, dan tasan yanda yake matuqar son ruwan sanyi
in ya dawo daga kasuwa, qarasawa inda yake tai, ta zauna a jikin shi tana kukan shagwaba,
tana zamewa a jikin shi, gaba daya ta susuta shi, " Babe, ni agwaluma nake son sha" cike da
kasala yake kallon ta" kin tabbata ita kk so yanzu?"ya fada yana kashe mata ido daya, yana
shafa cikin ta, saurin kauda kai tai dan ta fuskanci effect din da take da shi a wajen shi
musamman in tana shagwaba a jikin shi tana murza ko ina na jikin ta a nashi, tashi tai tana son
gudu, dan she is not ready for him, saurin riqeta yai yace "tin dazu nake daurewa, yanzu ke da
kan ki kin san ke kk jawo dan haka muje na duba bbyna sai inna gama naje na siyo maki
agwaluma ya kk ce?" Biga qafa ta fara cike da shagwaba sannan tana qara narkewa a jikin shi,
" Ni dai Honey ban da lfy" "muje na baki.magani to" " ni dai Aa" kan tai wani yunquri tini ya
dauke ta sun yi bedroom din su. Jan qofar yau ma yai nace da qarfi, ka daina min irin wannan in
ba haka ba na fara maku leqe, ai ni bance zan biyo ku ba damaí ½í¹„í ½í¸™( yan uwana mata ina son
fadakar damu akan murmushi, macen da ta cika mace ta san wacece ita, murmushin ta kawai
ya wadatar da ita wajen bawa mijin ta farin ciki, komai bacin ran da mijin ta ke ciki, murmushin
ta zai iya calming din shi daga dikkan damuwar shi, murmushin ta zai zama abun da mijin ta zai
iya tinawa a ko ina yake ya jishi cikin nishadi yaji shima yana murmushin ba tare da ya sani ba,
abu na biyu shine, da damar mata ba su iya shagwaba ba, shagwaba kala2 ce, amma wadda ta
fi tasiri, ko da namiji na cikin fushi ki kwantar mai da hankali, ko da namiji bai da buqatar ki , ko
bai da sha'awar ki yaji nan da nan ba wani abu da yake so a jikin shi ko kusa da shi sai ke, ba
komai bane face shagwaba irin wadda yara suke yi dinnan suna hawa jikin mutum suna murza
shi ko ina na jikin ki ya zama yana manne dana oga kina murza jikin ki da nashi kina zamewa,
yanzu zakiji sauyin yanayií ½í¹Š)
Faduwar da sukaji anyi a bayan su ne yaja hankulan su sika juya gaba dayan su, Goggo Sarai
suka gani zube a qasa, idonta bude hawaye ya wanke fuskar ta, ta sa hannu ta toshe bakin ta,
da sauri Mama Bilki ta isa, dan ta kula gaba daya yaran nata kallo suka bita da shi, ba wacce ta
motsa, daga ta tai, ta kaita kan kujerar dake daf da bakin qofar ta zaunar da ita, ruwa ta debo
mata ta miqa mata a cup, kasa shan ruwan tai tana ta kallon Suwaiba da ta hade girar sama da
qasa, tai hanyat dakin Mama Bilki, kuka ne ya kwacewa Goggo da taga yaran ta duk sun bar
wajen sun yi dakin kishiyar ta da ta dasa musu tsanar ta a ransu, yau itace abin son su, wani
gululun baqin ciki ta hadiya, ta kalli Mama Bilki da ita daya ce a kanta ta kauda kai taci gaba da
zubda hawaye, Abban su ne yai sallama ya shigo, dakin Mama yake can ya nufa, kukan da yaji
ana yi a dakin je ya ja hankalin shi ya qarasa da sauri, " Suwaiba ke nake gani? Meke faruwa
ne, naga kuna kuka, ku sanar dani damuwar ku yarana, duk da banda arziqin da zan maku
maganij ta, Allah ya horen bakin yi maku addu'a akan komai" Suwaiba ce ta je gareshi da gudun
ta ta rungume shi, shima eungume ta yai kuka take mai ban tausayi, bai dago ta ba, sai da tai
kukan ta ya ishe ta, sannan ta zame ta zauna a qasan qafar shi" fadamin diyata, fadan
damuwar ku naji" " Abba.... Abba ka yafe min, Abba ka yi hakuri akan qin jin maganar ka da nai
abaya, Abba nadama ta samen alokaci qurarre" " Aaa Suwaiba karki ce haka, lokaci bai qure
maki ba yata" " Abba duba ka gani" daga mai rigat ta tai ta nuna mai qirjin ta da gefen cikin ta,
anan ta juya wajen Saudat tace" Saudat nuna mai cikin ki kema" nuna mai tai itama tana kuka,"
me ke faruwa haka" Abban ya fada cikin tashin hankali ganin da yai Suwaiba ta zama Nonoless,
" Abba mazajen da muka aura ta dalilin mugun son kudin mu, da influence na Goggo, Abba yan
qungiyat shan jini ne su" ta qarashe cikin qunar rai da dacin da take ji a wuyan ta, a zabure
Abban su yace " me kk ce? Shan jini fa Suwaiba, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Ya Allah,
wannan wace irin rayuwa ce haka? Ya salam" zama yai ya dafe kan shi," to sanar dani me ya
sami qirjin ki da kuma gefen cikin ki gaba dayan ku ke da yar uwar ki?" Kwashe komai tai ta
fada mai, cikin kidima da tashin hankali ya miqe ranshi ya gama baci da jin abinda ya samu
yaran shi, duk ta dalilin matar shi da ta kasa taimaka mai wajen ba yaran shi tarbiyya, ficewa yai
a dakin ya nufi dakin Goggo," hankalin ki ya kwanta, Saratu hankalin ku ya kwanta nace, an mai
damin Yara marasa haihuwa, ba zan taba ganin jikokina ba ta bangaren su, ke baki saki jiki kin
haifa min yaran ba,ga shi kin ja sanadin son kudi da abin duniyan ki ya sa jikokin nawa ma zasu
zama ragaggu, ban manta wa ke da kan ki ki kai kutunkutun ki ka tsaida haihuwa, wai yaran
sun ishe ki, wace irin mace ce ke? Ki duba kiga Suwaiba an yanke mata nono gaba daya,
banda jinin yaran nan da ake diba duk wata, tsahon wata takwas, ina zaki kai alhakin su?" A
wannan lokacin Abba kuka yake, Goggo kuka , yaran kuka, Mama Bilki hawayen tausayin
yanda rayuwar gidan na su cikin qanqanin lokaci ta koma take, wannan rayuwa ! Goggo ta kasa
cewa komai, bakin ta rawa kawai yake, sai zatai magana sai ta ji bazata iya cewa komai ba,
Suwaiba ce ta katse su da cewar" Abba ina neman izinin ka barni nai mana daki a ta can wajen,
dan ba zan iya ci gaba da zama da Goggo a daki daya ba" murmushin takaici Abban su yai
yace" kinji ? Kinji da kunnen ki, Yar ki ba zata iya zama dake ba? Kar ki damu Suwaiba, wannan
kudin bai kamata ki amfani da su ba, kamata yai a bada sadakar su, ina da qasa, da ciment,
dan dama ina da aniyat yin daki dan ku, koda kun zo ganin gida, dan haka da kaina zan yi"
juyawa yai ya fita, kamar abun wasa Abban su ya fata hada qasa da komai, nan da nan
Suwaiba da yan uwanta suka hadu suna taimakawa mahaifin su wajen yin ginin, harda mai ciki,
Ammar ne ya tako dugui2, ya isa wajen su ya debo qasar a hannun shi ya miqawa Abban su,
dariya sukai gaba dayan su, a haka Ammar ya zama shi ne ke saka su nishadi har yamma ta
gabato Mama Bilki ko tana can tana masu girki har ta kammala, Goggo ba wanda ya kula da yin
ta, ko kukan ta, sun maida hankali akan son yin dakin da zasu nesanta kan su da ita, ginin ya
masu nisa sosai, a haka suka bar wa gobe sukai wanka, suka zauna bangaren Mama Bilki,
suka zauna gaba dayan su, a babban faranti ta zuba masu, kowa ya saka hannu har Abban su
suka fara ci, Mama Bilki ce ta miqe Abba ya kalle ta" Ina zaki kuma Sarauniya ta?" " Abban su
zanje na kira Yaya ne, mu ci abincin dika" cikin zare hannayen su dika, tare da turo baki alamar
basu yarda ba suke kallon ta" kin samu amsar ki a wajen su dan haka zauna mu ci bincin mu"
komawq tai ta zauna, suka gama ci suka wanke hannaye suka sha ruwa, wanke kwanon
Saudat tai ta aje ta dawo suka zauna suna ta hira, suna wasa da Ammar" Mama Ammar ya
girma yai wayo sosai" " aiko dai kinga dik sa'annin shi ya fisu girma da wayo" " lallai kam" "
Suwaiba, Saudat, Salma" daga kai sukai suka kalle ta jin yanda ta ambaci sunan su alamar ba
wsa, amsawa sukai gaba dayan su suka zuba mata ido" ina son na baku shawara a matsayina
na uwa, sannan ina son ku duba abinda zan fada maku da da kyau, ku qoqarta amfani da shi,
kun ga da farko dai uwa ba kamar ta a rayuwar duniya, Allah ya ce abi shi sannan abi iyaye,
Annabin rahama ya jaddada bin uwa sau uku kan uba, dan haka ni ina son ku yafe ma
mahaifiyar ku abinda tai maku, tabbas bata kasance uwa ta gari ba, mai ba yaranta tarbiyyar da
musulunci ya tanadar, amma ta baku so, ta nuna maku qauna, na uwa da yaranta, in kun kula
ita a tinanin ta tayi abinda ya dace daku ne, amma koma dai menene ina son ku sani, wanda
bai yafe ma wani ba, shima ya ji tsoron kar Allah ya qi yafe mai nashi laifukan, dan haka nake
mai baku hakuri a madadin ta, ku taimaka ku yafe mata, kar kuja wani ciwon ya kama ta dan
Allah na roqe ku" cikin kuka suka matsa kusa da ita suka rungume ta, Suwaiba ce tai magana a
cikim su" Mama Bilki ke alkhairi ce a rayuwar mu, ki yafe mana abubuwan da mukai maki a
baya, tabbas mun cutar da ke sa kalaman mu, da ayyukan mu, bamu zama yara masu biyayya
ba, ki hakuri ki yafe mana" " indai nice na yafe maku baku ce man komai game da Yaya ba?"
Salma ce ta amsa masu dan Suwaiba da Saudat har yanzu akwai daci da wata irin qiyayya da
suke ji game da mahaifiyar tasu, amma sun sani dole su yafe mata, sui hakuri da abinda ta
musu" mun yafe mata Mama Bilki Allah ya yafe mana" " to ya kamata kuje ku sanar da ita kar ta
kwana cikin damuwa" Suwaiba ce tai saurin miqewa" ni dai Mama ba zan iya zuwa yau ba, dan
Allah kar ki tirsasa ni yin abinda ban jin zan iya yin shi a yanzu" ta qarasa cikin kuka,"Bilkisu
Allah ya miki albarka, amma ki bar su haka, zuqatan su cike yake da abinda ta musu, daga
baya a hankali komai zai warware masu" " to Allah ya kaimu, Allah kuma yansanyaya zuqatan
ku ku yafe mata gaba daya" amsawa sukai dika da " Ameen" hankalin Goggo kam ya kai
qololuwa wajen tashi, Wanj duhu take gani ya rufe mata ido......
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: í ½í²…í ¼í¿¼ 'YAN ABUJA í ½í²…í ¼í¿¼
BY HERMEEBRAERH
Page 27:
Kuka kawai talle yake ya kasa tsaida hawayen shi, wannan rayuwar ba wanda ya ja ma su ita
face shi, mugayen halayen shi ne da yi ma yaran mutane sakin wulaqanci, da zinace2n shi ne
ya kai su ga haka, gashi tsabar lalacewa Yayan shi ke neman matar shi ta sunna, Yaran yayan
shi na neman na shi yaran, kaiii jama'a wannan wace irin musiba ce ta sauko mana a wannan
zamani, Marka kam irin kukan qabilun nan take, tai girgiza tai girgiza tai kukan sai kuma tai dif
ta cigaba da gyada kai, abun ya shigeta sosai ba kadan ba, jummala ta mutu sakamakon
yunqurin zubda ciki, ga Hawaila tana kallo a gaban ta da ciki dan kuyat a gaba, itama ga nata
farkan a gefe, wace irin rayuwa suka jefa kansu a ciki? Maqota ba mai zama wai da sunan
makoki, ko sun shigo yada magana ne yake kawo su, wasu daga ciki zakuji suna cewa" Tohhhh
abinda ya faru kenan hmmmm Allah dai ya jiqan ta amma zunubu kam an kwasa" ire2n
kalaman mutane kenan ana yi ana kyabe baki, wasu kuma bayan sunyi gaisuwar sai sun dora
da" ikon Allah kamar ciki nake gani a jikin Huwaila, ni dai bani da labarin auren ta, sannan mun
san ba a shan ciki a ruwa, hmmmm Allah ya kyauta,gidan Talle kenan, gidan uwa ba kwaba ya
ba hantara" kowa da abinda yake furtawa, baqin ciki kamar ya kashe Haule, wai yanzu nan ne
gidan ubanta, gidan da ba tarbiyya ba kwaba, yanzu itama tambarin ya shafeta, ai kuwa da an
gama arba'in guduwa zatai qauyen da taji wata qawar Marka da tazo kwanaki ta fada da sunan
wata mata a matsayin mahaifiya gareta, mai suna Husai, qauyen yana nan kusa da su, in ta
zauna a gidannan ko mashinshini rasawa za tai, in ko ta koma can ko sunqi karbar ta ba zata
dawo nan ba, kwalla ta share ta ja hanci, tana kallon su cike da tsana, da tsanar halayen su,
tashi tai daha wajen kwata2 tai shigewar ta daki,addu'a take taima 'Yar uwar ta a ranta na Allah
ya yafe mata, Yayan Talle kuwa zaman daki ya kama shi, bai da damar fita waje dan abin
kunyar da suka aikata, by now kowa ya san meke faruwa a gidan Talle, ba kowa a qofar gidan
yan karbar gaisuwa ko yan gaisuwan, sai su Baban gida da Badamasin, Talle kallon su yake
kamar ya shaqe su, amma yasan a iskancin da sukai shi yayi ninkin nasu sau ba adadi, nade
tabarmar da yake kai yai ya shigo, fakam2 ya tsaya kan Huwaila, kwalama su Baban gida kira
yai, suma shigowa sukai da tabarmin su a hannu, kai a qasa kamar munafukai," a cikin ku waye
me cikin Huwaila?" Badamasi ne ya nuna Bangis, shi kuma ya qara duqar da kai qasa," Yanzu
yarannan wai har kunyi girman dirkama wata ciki? Ko dake maganar wai kun yi girma ma bata
taso ba tinda ga misali kun bayar, kun yi sanadin mutuwar daya, ga daya nan da tambarin abin
kunyar da zai bi zuri'ar mu har abada, dan haka sai ka bari ta haihu a maku aure kun renu dan
shegen cikin gidan da kuka samar tare," cikin tsananin qunan rai yake maganar, ita dai Marka
bata cewa umm bare Aa, tai dif sai hawayen nadamar rayuwar su ke fita mata, a cikin zuciyar ta
tana ayyana wannan lamari ba laifin kowa bane face nashi, daya tsaya ya tsare mata sha'awar
ta da buqatun ta da batai zina da auren ta ba,( dik d wannan ba hujja bace ga matan da suke
ganin dan mijin su baya sauke haqqin shi akan su bari su bazama neman mazan waje, ko su
fara aikata wani abun da ya kauce hanya, su sani Allah zai masu hukunci daidai da abinda suka
aikata ne shima mijin Allah zai mai hukuncin abinda ya aikata, so ni a ganina ba dabara banw
hakan, wadda ke da matsala haka maganij ta ya kamata su zauna suyi in ya gagara su tattauna
da mijim to ta nemi waliyyan su su shiga lamarin haka islam ya tsara,bai halatta ta fada halaka
ba da sunan rashin kulawar miji mu kiyaye)miqewa marka tai zata shiga dakin ta, ya dakatar da
ita, " Marka ina neman yafiyar ki akan dikkan abubuwan da suka faru tabbas laifi nane, da na
tsaya na zama namijin kirki da duk haka bata faru ba, ki yafe min mu dawo mu gyara rayuwar
mu,"kauda kan ta tai saboda kukan da yake neman cin qarfin ta ga wani haushin shi da take ji
na jefa su wahala da yai, Yayan shi ne ya fito daga dan qaramin dakin shi ya zube akan
guiwowin shi" Talle qanina ka yafeni na biye wa son zuciya, da rudin shedan na aikata
mummunan abun da ko mutuwa mukai sai yabi zuri'ar mu, ka taimaka ba dan ni ba domin Allah
da zumunci ka yafen" kuka ya kifa hannayen shi a fuskar yana yi, Talle daga shi yai kawai ya
dan daki kafadar shi dan shima kukan yake ji, kauda kai yai zai shige daki yaji maganar yayan
nashi," a gaskiya sai mun gyata rayuwar gidannan namu kan komai ya tafi daidai, na farko
yanayin yanda iyalin ka take yawo a tsakar gidannan ya jawo min matsananciyar sha'awar
kasancewa da ita, dan zakaga tana yawo ba isasshen kayan da ya rufe dikkan jikin ta, tana tafe
tana juya dikkan jikin ta, sannan ga maganganun ta danake jiyo wa yawancin su na batsa ne,
wajen kallon ta da maganar ta bata kiyayewa, wadannan abubuwan sun ja ra'ayina matuqa, dan
haka in muna son mu samu kwanciyar hankali da kiyaye war zinace2 a tsakanin mu sai mun
kiyaye, sakewa yarannan da mukai shima ya jawo wannan bala'i da muka shiga har yai sanadin
mutumar Jummai, ( sakacin iyayen yanzu da kusan nace kowanne gida hakan na faruwa,sai
ace cousen din tane ai, kaji tana yayana ne, ko yana qanwata ce, amma da sun samu sarari su
biyun su zai zauna ya lalube ta tsaf ya miqe, ita kuma tai dif da bakin ta, da wuya kaga cousens
din da a wannan zamanin suke gida daya ko suke yawan ziyartae juna wata barna ba ta
gilmawa, wanj sa'in gaba ga iyayen zakuga suna kallon yanda Yarinya ke mannewa namijin
amma sai su dau hakan a wayewa, kuga tana wasan banza da namiji sai ace ai yayan ta ne ba