Showing 60001 words to 63000 words out of 70697 words
Chapter 21 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf
zauna, tana ta wasa da hanun ta, dayan ne yace
ma Salma," Angel, da farko ni suna na Salmanu,kuma aboki ga ango, wannan yaya na ne,
farouq, tin da kuka zauna anan muka sa idon mu ana ku mukaji ba zamu iya barin ku tafi ba
tare da mun isar da manufar mu ba, dan da dikkan alamu ku yan uwan amarya ne ko," cikin
nuna kulawa Salma ta kalle shi dan itama sai taji ya mata," Eh mu yayun ta ne, amma bayin
Allah ba ku sammu ba baku san ya muke ko rayuwae mu take ba kawa sai ku fara isar da
manufar ku, to da farko dai ku duba kuga wadan can yaran na hannun yayata"duban su suka
kai wajen suka ga kyawawan yaran, sannan suka dawo da kallon su suka fada mata sun gani,
ci gaba tai da magana dan bata son abinda zai karya masu zuciya gaba dayan su gwanda ai
maganar gaskiya,dan ta kula dikkan au samari ne basu taba aure ba," to yam biyun nawa ne ni
na haife su, amma aure na ya mutu, ita kuma wannan yayar tawa, mijin ta Allah yai mai rasuwa
ne,a yau ta fita takaba," cikin mamaki da tausaya wa suke kallon su,dan duk yanda akai mijin
daya saki Salma na da tabin hankali ko shafar aljanu, hauka ne kawai zai sa kana da mace
kamar wannan ka sake ta, nan take sukai wa Saudat ta'aziyya sannan farouq yace" a gaskiya ni
har yanzu ina ciki kaifa dan uwa? Dan ba zan taba barin wannan tsaleliyar ta wuce ni ba zan a
sara mai yawa, domin da dikkan alamu akwai tarbiyya awajen ku" a sannan Saudat tai magana"
yanzu dai kui hakuri zuwa a gama biki da komai sai kuje gida ku samu mahaifin mu akan komai,
dan as for me kam wanda na san haka yar uwata ma, sai abinda mahaifin mu ya zaba mana"
godiya sukai sosai kuma suka qara tabbatar da taebiyyar su, karbar No wayar su sukai, sukai
sallama suka tafi, Adda Suwaiba ce ta dawo ita da Juwairah, suna zama Salma ta labarta masu
komai, suna cikin addu'ar neman zabin Allah ne Muhammad din Salma ya hau kuka, kuka yake
sosai har Salma ta rude kamar za tai kukan itama,miqo masu hannu suka ga anyi"hey little
buddy come here" Salmanu ne ya karbe shi kamar yaron da aka bawa chocolate nan da nan
yai shiru, jijjiga shi yai ya tafi wajen yayan su suna ta hira da sauran abokai, wannan ya karbe
shi wannan ya karbe shi, a haka daga baya Salmanu ya karbe shi, har yai bacci a kafadar
shi,cike da so Salma da yan uwan ta ke kallon shi,an gama komai za a tafi gida ne ya iso, ya
miqa mata shi, godiya tai ta mai, yace" ya kk man godiya ne dan uba ya kula da yar shi ai ba
wani abu bane" murmushin jin dadi tai idon ta cike da kwalla ta gyada kai tai gaba, bayan sun
fita ne suka fuskanci basu da abin hawa zuwa sukai kowa da motar shi, ya zo ya faka, Yaha
Jabeer ya iso dan daukar matar shi da su ne ya samu labarin komai wajen Juwairah, murmushi
yai yai fatan alkairi yace mata shige to mu mu tafi dan kinga sun isa gare su nasan kuma gida
zasu kai su, nima a gajiye nake, wanka nake so mai dumi,ko na murmure" murmushi tai tace
"Hmmm Abu Abrar kenan na gane in da ka dosa, to yau kam a very big N-O to u saboda i am
so exchausted" dariya yai yace "we shall see then, i know u can't resist my charm"yana wani
kashe mata ido daya, kauda kai tai tana muemushi, dan tabbas ta bakin nashi ne, ya san
abubuwan da yake ya kwace mata dikkan lissafan da take da shi.......
*Nafee tace a fada maku tana godiya da zuwa biki, amma 'yan maermue group da suka je sukai
ta dibar kaji suna boyewa, su raba da sauran wanda basu je ba, musamman Mum Sultan Bizzy
Aisha, da Roumio, a canja hali malamai*
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA
BY HAERMEEBRAERH
*I dedicated this page to all my Kebbi state people, i heart u guys, u are wonderful, and kind,
wish to came back soon inshaa Allah, Missing you bahut bahut*❤❤❤❤
Page 32:
'Yan kai amarya basu tafi ba sai wajen qarfe 12 na rana, Innar mu ta sha kuka, Nafee mai son
gida kamar me, ranar tun tana kukan sai da yakai ta gaji ajiyar zuciya kawai take lodawa, sai
kace wacce za ai wa auren dole, kowa sai da ta bashi tausayi, Salma ba ta samu zuwa ba haka
ma Suwaiba, Saudat ita aka wakilta a madadin su, sai Mama Bilki, wadda cancanta ce ta sa
aka zabe ta a masu zuwan, tinda ita Goggo Sarai har yanzu bata da tinani masu kyau a kanta
banda wauta tai mata yawa, sai girman shekaru da jiki kawai ta aje, tana jin zafin rashin tafiya
da ba ai da ita ba amma haka ta jure, Juwairah ta so matuqa ta je amma Abrar ta sha gajiyar
biki bata da lafiya dan haka Jabeer yace ba inda zata, tayi kuka kamar me, amma haka ta
hakura ba yanda zatai, wasu mata suka dauka biyu daga bangaren su Abban Suwaiban wato
Goggo Karima da Goggo mero, sai ta bangaren Innar mu, suma biyu, Innar Fateema, da Inna
Aishe, sai wata aminiyar Innar mu wato Baba Maryam, ba su isa kebbi ba sai takwas na dare,
gaba dayan su jikin ta qaura yai la'asar, tun Nafee na irin abun amaren nan a mota tini ta janye
mayafin a fuska ta sake, tambaya ko tafi nawa tana ma, abokin angon dake tuqi, dan motar
daga ita sai abokin angon dake tuqa su sai wani a gefe sannan ita da angon, mota uku sukai,
janyo ta mijin ta yai jikin shi ta kwace a kunyace tin suna Gusau, da wahala tai wahala da kanta
ta dora kanta jikin shi ta sha baccin ta, ko da ta farka ta zaci zataga sun kusa isa amma taji
shiru, kai na taqaice maku sai da Nafee ta matse kwalla, tinanin ta daga Kebbi Nigeria ta
qare,lokacin da suka isa ana ta kiraye2n sallar isha'i ne, suna zuwa gidan dake unguwar Alieru
Quaters, a bangaren Three bed rooms a nan aka aje ta, fasalin nasu gidan daban ne dana
sauran, ya tsaru iya tsarin zamani, kana kallo zaka san gidan masu hali ne, yan uwan ta kam
sai san barka suke, da mata addu'ar Allah ya zaunar, kwanan su biyu aka tashi juyowa da su,
Saudat kuka tasa data tuno hanyar da suka kwaso, sai lallashin ta ake abokin angon daya tuqo
su yana ta mata dariya" a gaskiya zan fada ma Umar farouq ya shirya matat shi raguwa ce" ai
tana jin haka ta miqe ta goge hawayen ta tare da zabga mai harara" inji wa? Ni kar ka wani fada
mai mu tafi" dariya aka saka dukka wajen banda Nafee da take rabe a gefen mijin ta tai kalar
tausayi, ai ko suna sa kai ta fashe da nata kuka, bayan sun fita ne suma suna cike da tausayin
ta angon ta ya dauke ta cak yai ciki da ita yana lallashi, su Saudat sun kama hanya sun baro
nafi, wajen mijin ta mai matuqar so da kulawa, tare da tausayin matar shi, dake tashin qarfe
bakwai da rabi sukai sun iso kano qarfe wajen uku na rana ne kowa sai da aka aje ta gidan su,
drivern daya kawi su Mama Bilki ne ya tsaida Saudat, " ba daban Farouq ya rigani ba kuma
yana matuqar son ki, tabbas dana kawo kaina nima, amma ba zan iya tafiya bam sanar dake
sirrin dake raina ba, na kamu da son ki a kwanakin nan da mukai kusan wuni a tare daku, ina
maki fatan alkairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuria mumina saliha" taji dadin fahimtar shi da
kuma yabawa da hankalin shi sosai dan haka ne ma yasa tace mai," na gode sosai da siyayyar
ka a gare ni, ina ma ka fatan alkairi, Allah ya baka wadda ta fini, tabbas abotar ku akwai amana
kuna da halin manya," murmushi sukai sannan daga baya ya mata sallama ya ja ya tafi.
Kwana biyar tsakani, bayan waya da musayar saqwanni dake tsakanin masoyan hudu, sai
gashi wata lahadi da yamma, wasu dattijai suka zo gidan Abba Baballe, da nemawa Farouq da
Salmanu auren su Saudat din, a wasu maka2n motocu suka zo, wanda yasa Abba jin tsoron kar
a maimaita yar gidan jiya fa, amma saka makon bayani da suka samu shi da Baba Balarabe, da
kuma shaidu sun tabbatar da cewar tabbas mutanen kirki ne, a nan take suka roqi arziqin a
daura auren in ba damuwa, saboda ba a kusa suke ba, kowa da garin da yake aiki, shi Abban
su Farouq mazaunin Abuja ne, sai qanin shi dake lagos, dayan kuma a kebbi yake, Abba
Baballe sawa yai a kira wani kawun su daya rage masu da abokin shi babba, nan take aka
daura auren su Saudat da Farouq, Salma da Salmanu, akan sadaki dubu hamsin hamsin, tare
da alqawarin Salmanu zai riqe yaran Salma kamar nashi in sun masu izini, su Abban Suwaiba
sun yarda amma sun qara da cewa in ba takura, suka jaddada masu, cewa shi Salmanu ba
Salma kawai yake so ba, har da Yaran ta ya gani ya kamu da qaunar su dika, Abban Suwaiba
yaji dadin hakan sosai, a haka taron ya tashi cikin farin ciki da yarjeje niyar sanda Amaren da
angwayen suka shirya a tsakanin su ayi tarewa.
Bayan wannan daddadan labarin ya iske su Juwairah ne ta roqi Jabeer akan ya barta har
tagama batun tarewar Yan uwan ta kan ta koma, ya amince amma shi da yamma zai koma
Abuja sabida aiki, sun bari akan in ta kammala ta sanar da shi sai su koma tare, kudi ya bar
mata mai yawa a hannun ta kan ya tafi, tin kan tafiyar kuma sai tai tajin ba dadi zai tafi ya barta,
bata son abin da zai raba ta da mijin ta , musamman wannan bata san kwana nawa ba zai
dauka, shima gaba daya bai som rabuwar tasu amma dole ya qarfafa mata guiwa , haka suka
rabu kowa na kewar dan uwan shi. Ta dawo daga raka shi ne taji wayar ta na ringing dake kan
fridge din ta, dauka tai taga Nafee ce, bayan sallama da gaisuwa ne tare da tambayar bayan
rabuwa Nafee tace" matar yaya kunyi min mntuwa fa, kun manta tsimi na ba a sako da shi ba" "
Subhanaka ya raheem, ai ko kinga har yanzu ba wanda ya kula, ba damuwa ai kinga yanda na
hada maki wancan, ki hada wani wannan na ba su Adda Saudat, keee an daura auren su ma
jiya, tarewa kuma ance ba yanzu ba sai sun shirya magana da mazajen su, iyayen sunce basu
buqatar komai sai matan yaran su za a kai masu" cikin murna Nafee ke addu'a, bayan gama
murnar ne tace" nifa matar Yaya na manta wasu abubuwan dan sake fadan mana pls" " kai
Nafee ko angon ya kwashi romo har da basirar ki ne?" Dariya sukai Nafee tace cikin shauqin
son mijin nata" matat yaya wato My love daya ne tamkar da ba iyaka acikin maza" " Oh ni
Juwarah yarinya ta fitsare bari nayi na gama fada maki na kashe wayata, ina nan ina tausayin ki
ashe ke kin gama.zama yar hannu ma abin ki, " dariya sukai tayi kafin Juwairah ta lissafa mata
kayan hadawar da suka qunshi" kanin fari kadan zaki saka ba mai yawa ba saboda masu
magungunan gargajiya sun tabbatar da shan shi da yawa na kawo ciwon hanta, dan haka ki
saka kadan sai citta mai dan yawa, minannas, sai ki matse ruwan rake mai yawa, ba a qara
wani ruwan fa da wannan ruwn raken iya adadin yawan dakk so da shi zaki amfani, sai ki samo
zuma mai kyau sosai ki saka sai ki dake kayan qamshin nan ki saka a ciki, sai kin ga yai kauri
kadan ma'ana bai irin ruwa tsululu ba, zumar ce zata saka yai kaurin, ki dinga sha da
yamma,amma pls wajen nemo zumar ku tabbatar me kyau ce kin san yanzu an bata zuma, na
ba su Adda saudat wannan nakin nima na dan sha" " na gode matar yaya sai an jima ki shan
fan bbyna, ina gaida yaya" nima ina gaida angon ki" .
Wahse gari sallama taiwa Innar mu ta tafi gidan su ba zata dawo ba sai an gama tarewar yayun
ta, ta kaiwa Yayun nata wannan tsumin, sannan tun da suka fada mata mazan su sunce ai nan
da kwana biyar za a kaisu su tare, nan da nan ta hau taya su gyaran jiki kala2, sai ga su sun fito
amare sak, itama sai da ta gyara dan a cewar ta itan ma amarya ce, tin da taje, take ma su
kwadon zogalen daya sha timatir dahuwar ruwa2 haka take kwashewa, timatir mai yawan gaske
take saka masu gulin yaji kayan qamshi,(wannan hadin ga masu son hips din su ya fito zasu na
ci sosai har su samu biyan buqata ko su saka zogalen a danyen shi bayan sun wanke shi sai su
mai hadin, sannan ana iya yin hadin da alayyahu ma) sannan ta samu kabewa tai ta hada masu
da madara da zuma suna sha,( wannan kuma yana gyara masu skin din su ba kadan ba)lokaci
ne na mangwaro ta dake da siyo masu mangwaro suna sha ba qaqqautawa( mangwaro na
qarawa mace ni'ima sosai da dumin jiki) ga tsarki da hadin ta na musamma da baya wuce ta,
isu isu suke abin su, Goggo Sarai gaba daya jikin ta yai sanyai,bata taba nadamar rayuwa irin
ta yan kwanakin nan, ganin cewa tabbas Allah shine mai yi ba mutum ba, duba da cewar gashi
dai duk bala'in son kudin ta, ta kai yaran Abujar kuma sun wahala, babbar ma har da nakasa,
finally gashi yanzu Allah ya basu ' YAN ABUJA na kwarai, hawayen da take qoqarin mayar wa
ne wani ya gangaro," Yaya ki daina kuka, in yaran nan suka gani zaki daga masu hankali" "
Hmmm Bilki dole abun ya damen, bam zamo uwa ta gari ba, na tsani rayuwa da turbar dana
dora yarana akai a baya" " haka ne Yaya kinyi kuskure babba, amma yanzu ai ya wuce, ya
zama tatihi,kuma in shaa Allah hutun da kk nema masu su ji shi," cikin gyada kai da yarda da
maganar ta ta dauki kwanon abincin ta isa dakin su ta miqa masu ta fice..........
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA
BY HAERMEEBRAERH
Page 33:
Washe gari angwaye zasu zo tafiya da amaren su, su Goggo Karima dai ana nan sune yan
rakiya Abuja, yau shiga kasuwa, su kai har Juwairah,kudin da angwayen suka basu na siyan
kayan lefen su da basu samu damar hada masu ba shi suka je suka hado, bayan sun gama ne
sika fara siyan kayayyakin da in sunje zasu buqata wajen gyaran jiki ko ni'imar su, wadan da
suke ganin ba samu zasui da sauqi ba a can, musamman hadin kayan qamshin da Juwairah ta
basu shawarar niqa mai yawa su tafi da shi, dan ko shan shi da madara da zuma, zasu buqata,
a gefe daya Juwairah ta lodarwa mijin ta kayayyaki kamar dangin qanan kaya, vest, boxers, da
turaruka, sai takalma, da huluna biyu, masi kyau sosai, mamaki ne ya kama su suka kasa
jurewa sai da Saudat tace" ke kuma ya naga kina ta siyan kayan maza ne, baki saiwa kanki
komai ba sai tirare da kayan bacci," " Adda Saudat Yah Jabeer na debarwa, ba dan komai ba
sai dan yanda shima yake man dukkan hidima da qarfi da iyawar shi, na sani komai zan mai ba
kamar ya shi ba ne, sannan wannan abun da na siya already yana da su, amma kyautata wa
juna na qara soyayya, kyauta tsakanin miji da mata musamman irin wannan ta tiraren da miji ya
fi so, tana da matuqar tasiri a zuciyar namiji, shiyasa naga ya dace tinda ya wadata ni da kudi
shima na sai mashi" " lallai Juwairere ke kin ma fi Mama Bilki iya tattalin miji, na rasa waya koya
maki, ko kayan baccin ki da tiraren ki is for his on benefit" dariya sukayi" Salma ai gaba kin ga in
ya tashi bani zai ban wanda yafi wannan tinda yasan ko me zan duk inda aka je aka dawo zai
amfana shima in one way or another" tafiya suke suna jinjina wayo irin na qanwar tasu, a sama
sukaji muryar ta"Adda Saudat ku daina mamaki na, kowacce mace tana da kaifin hankali da
basirar zaman gidan miji, bambancin mu shine wata tana shiga kwakwalwa da zuciyar ta tai
tinani, ta mafana da baiwar ta wasu su amfana, wata kuma dunkufe kanta take, bata son yin
dogon tinani sam, bama ta son tana zurfafa tinanin ta akan komai, da matsala ta same ta sai
tace sai ta nemi shawarar qawa, wani lokacin ai sa'a ta samu shawar qwarai wani lokacin
sabanin haka, amma in da zamuna bude zuqatan mu da maza su ji dadin zama damu, aure
daya rage mutuwa, da hakuri da sanin ya kamata ya wanzu gidan auren mu, Adda muna a
garin da ba