Showing 12001 words to 15000 words out of 70697 words
Chapter 5 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf
tafi da sauri zatai daki, binta
yai a baya yana" ai baki isa ba, ki tsokanen ki gudu, haba yarinya, tsayawa zaki ki qarasa ladan
ki kawai" dariya take tana bashi hakuri " dan Allah Babe ka bari kaci abinci kai wanka, sai
namaka tausa kamar kullum, in yaso in ka samu qarfin jiki yau till down zamui" tana kaiwa nan
ta rufe fuska tana dariya ta zagaye shi ta fita da sauri, zuwa tai ta hada mai ruwan wankan, ta
dawo shi kuma ya shirya wanka, shiga sukai bandakin a tare bayan ta je ta rufe qofar bangaren
su, wanka ta mai da kyau ta sa mai toothpast a brush din shi( mata da yawa suna cewa wai
mijin su yana warin baki baya son yin brush da sauran su, shawara gare ki sister mai wannan
matsala shine, ba a ce ma na miji je kai brush ko wani abu makamancin haka, dik da akwai
mijin da in shaquwar ku ta kai qololuwa kina iya sanar da shi kuma ba zai damu ba dan yasan
duk amfanjn ku ne ke da shi, so in ba irin mijin nan gare ki ba dabara zaki, ki hada maku ruwan
wanka tare kafin wankan ki tabbatar kin gama gigita shi yanda ba zai maki musu a komai ba,
daga nan sai kui wankan tare, in ba kui tare ba saboda maybe yanayin gidan naku, sai saka
mai ruwan ki kai masa da kayan wanka, sannan ki saka mai toothpast a brush ki aje mai a kusa,
ba yanda za ai ya qi musammab yaga kin saka maku tare, kinga ba zai zargi kina jin wari bane
daga wajen shi, har yai feeling bad kuzo kuna samun sabani) bayan ta mai wankan yayi brush
daki suka koma, ta gyara mai jiki tare sa feshe shi da tirare, palo ta dawo da shi yana biye da ita
kamar raqumu da akala, abinci ta zaunar da shi ta bashi, yana ta santi" kaiiiii amma ba qaramin
birge ni kkai ba, kin san rabona da faten wake har na manta kuwa?" " naji dadi da yabawar ka
Hubby" " kusa da ita ya matso" ke din ta daban ce, komai naki daban ne,Allah ya barmu tare"
murmushi sukai dika, kiran sallar magrib ne ya katse su suka tsaya suka saurara sannan suka
bi suma, bayan an idar ne sukai adduar da ake yi ba yan idar da kiran sallah, Allahumma rabba
hadhihidda'awatittammah, wassalatil qa'ima, a ti muhammadal wasilata wal fadeela
waddarajatirrafee'a wab'athhu maqamam mahmudan lladhi wa adtah, innaka la tukhliful mi'ad,
sannan suka dora da salatin annabi ingantacce, addua suka daga hannayen su sama sukai a
tare ita da shi, suna idarwa suka tashi sukai alwala, shi ya tafi masjid ita tai a gida, bayan ta idar
ne tayi azkar din bayan kowacce sallah ne, sai ta samu tai kuma azkar din yamma, tana idar wa
ta miqe ta je tai wanka ta dawo dan ragowar abincin nasu ta juyo masu ta kawo ta hado da
ruwa da komai ta aje a gefe, daki taje ta saka rigar baccin ta mai matuqar kyau da daukan
hankali, sai ta dora zani akai, da hijab tana jiran sallar isha'i bayan tayi sallar ne da minti 15 ya
shigo, sai da ya biya wajen Innar mu ya gaida su, baban shi na ta sa mai albarka, ita ko ta
cinkishe fuska tana hura hanci, daya tambaye ta sai tai qaryar kanta ke ciwo, dan yau wuni tai
da yunwa, can sai ta saki fuska " kasan da yake bana son faten wake, kuma bana son bawa yar
albarkar nan aiki shiyasa, amma da shinkafa zan bata ko gwangwani dayar nan ne ta dafa min,
tinda Nafee ita har yau bata iya tsantseni irin na Juwairah ba" ba komai Inmar mu kawo na kai
mata za tai maki ai, ba zai yu ku kwan da yunwa ba" da sallama ya isa daidai Juwairah ta fito
daga daki ta cire zanin ta da hijab din ta, tana qarasa shafa mai a cinyar ta, ko da ya higo tini ta
sauya salon shafawar, sake baki yai kamar dolo yana kallon ta, qarasa shigowa yai ya aje ledar
still idon shi a kanta, juyawa tai ta koma daki tana tafe tana juya bayan ta tana waigowa tana
mai wani kallo da murmushi, ni dai tin da ya shiga suka ja qofar bam qara ganin me suke
aikatawa ba sai dai kunnuwa na sun jiyo man Jabeer na sambatu da bana gane yaren da yake,
sayyarar qafa ta na ja nai waje♀♀
Qarfe hudu na asuba suka fito sukai wanka tare da alwala mai kyau suka koma, bayan sun
shirya ne suka fara habatar da nawafeel, kowa ya fara addu'ar shi, Jabeer ne ke hango baqi, a
gefen shi dan ba wuta sai ta wayar shi suka kunna, miqa hannu yai yaga meye, dagawar nan
da zai yaga shinkafar da Innarmu ta bashi ce jiya a dafa mata, " Ya salam ! Tab lallai da safe na
shiga magana wajen innarmu, aiko ni tai na kawo ki dafa mata wai yunwa take ji, tin safe bata ci
komai ba, bata cin faten wake, shine gaba daya na manta" " haba Yah Jabeer bai kamata ka
manta da wannan mahimmin abu ba kuwa, domin yunwa ba ta da mahadi" a qasan ranta kuwa
jinjina wa Innar mu take wajen iya hada makirci, matar da taci ta tande kwano, har ta aiko wai a
dada mata in akwai, tace babu shine take cewa ba ta ci, ikon Allah, lallai Allah mai jin qan
bawan sa mai tinawa da shi a kiwanne hali yake, da bata zama mai neman taimakon Allah a
kimai ba da bai taimaka mata jiya ba da bama ta san me ake shirin kulla mata ba, kiran sallar
asuba ne ya katse su ya fita masjid an yi sallah, ya dawo, ita kuma tayi tata a gida tai azkar tai
karatun asuba da take yi kullum ba fashi komai aikin da ke gaban ta sai tayi ko rabin shafi ne
kan ta tashi, tana rufe qur'ani ya shigo, lokacin gari ya dan waye, miqewa sukai akan zasu
maida bacci, dan Nafeesa ke abin karyawa a gidan, in ba arziqin abin karyawan ma da dama
koko kawai zasu dama su sha, sallama sukaji anyi..........
............
....
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA.
BY HAERMEEBRAERH
Page 8:
Nafeesa ce ta shigo," Yah Jabeer Innarmu tace ka bada shinkafar tin da tayi wuyar dahuwa"
" inna lillahi, ni gaba daya mantawa nai shaf dana shigo, dan Allah ki bata hakuri kice yanzu za
a dafa" tace in ka fadi haka na amso ka bata ta fasa wataran an dafa" "My goodness, yau ya
zan na je gaida Innar mu, yq kk ga fuskar ta tai fushi ko?" " hmmmm ba kadan ba kuwa Yah,
amma tace kar na fada maka tai fushi" Juwairah a ranta tace" ina fa zata so ya sani tinda tana
son nakasani ta qarqashin qasa" dauka yai ya miqa mata, yace ta bata hakuri sosai kan ya
shigo, fita tai da ita tana mai dariyar zaka amsa ne in ka shigo.
Bayan sun taba baccin su ne sun tashi wanka sukai sukai brush su ka shirya, hijab ta dora akan
kayan ta matsattsu da tai ma mijin ta kwalliya da su kan ya fita, sun shiga bangaren na su Innar
mu lokacin ta gama.raba abin karyawa, tace akai masu sai ga su sun shigo, duqawa Juwairah
tai har qasa suka gaisa," Ya jikin Nafeesa tace bakiji dadi bane yasa ya aje bai baki ba" zare ido
tai cikin duqar da kai," da sauqi Innarmu na ji dama sosai" to Allah ya qara lfy, yasa amarya za
ai min ko ango, danni na gaji da lfy sa banga qaho ba aure wata na biyar kenan shiru ba
magana" ta fada in a form of wasa take, amma duk wanda ya kula ya san magana take fada
mata, murmushi tai sosai tace" Innar mu karki damu komai lokaci ne amare za a samo maki
masu yawa da masu kawo cefane har sai kince sun isa haka" tana fada ta miqe tai wajen Baba
Balarabe ta gaida shi, sake baki Innar mu tai, shiko gogan be gane magana suka sakar wa juna
ba, dadi yake ji wai Innar shi da matar shi akwai shaquwa, har suna magana irin wannan a
gaban shi, matsawa yai yana" akwai abinda zan taya ki ne Innata?" Murmushin qarfin hali tai ta
ce eh ba a rasa ba, dan dai kawai kar ya koma wajen da matar shi take, " Baba ina kwana?" Lfy
qalaou diyar albarka, kina lf" " lfy qalaou babana" " to madallah, Juwairah ina son ki ta hakuri da
wannan Innar taku, wani hali ta dakko d ni kaina ta canja min kwata2 ba kamar yanda na santa
ba, dan haka kema sai kinyi hakuri, abotakar ta da Goggon ku ba abu ne mai kyau ba, na yi
nayi na raba su amma abun yaqi" " Ba komai Baba , ai uwa ce a wajena Innar mu ko da ba
matar ka bace, mahaifiyar Yah Jabeer uwa ce a wajena, tinda ita ta haife shi, kuma shi din
mijina ne, in ban so mahaifiyar shi a tawa ba ni kaina ba zan samu kwanciyar hankalin gidan
aure ba, rikicin yawa zai min, da mahaifiya ma ana samun sabani dan haka ita ma a hakan na
dauke ta, watarana ba zatai ba" " Allah ya miki albarka , halayyar mahaifin ki da mahaifiyar ki ba
wanda kk bari" murmushi sukai dik, bayan sun gama gaishe2n su suka koma suka karya ," to ni
zan wuce sai na dawo, ki kular min da kanki, kar ki wahal da kanki " tasowa tai ta zagaye
hannayen ta a wuyan shi shi kuma ya zagaye qugun ta sukai ma juna kiss sosai, da kyar ta
kwace kanta, sai wani shinshina ta yake " Yah zaka makara fa, ka tafi cikin amincin Allah,
Allah ya bada kasuwa mai yawa mai albarka, ya kare ka daga haramun komai qanqantar ta,
Allah ya hada ka da halal komai qanqantar ta, ka kular min da kan ka, ka tsaida sallah akan
lokaci, in kaji yunwa ka taimakeni kaci abinci, kaga yanzu ba da bane ba abubuwan da sai na ci
gaba da dafa maka kana tafiya da shi, karka barmin kan ka da yunwa kaji?" " Karki damu an
gama ur higness" ya dan duqa alamar gaisuwa, dariya sukai ta raka shi har waje, ta dawo daki
ta hau gyara wajen da suka ci abinci.
" kai jama'a wai dan tsabar baqin ciki na aje flask din nan anan an kai min shi can, ko uban wa
ya ce a tavan kaya oho, shikenan mutum in yana haushin talaucin da yai mai katutu sai ya
dinga taba kayan da ba nashi ba yana canja masu waje? Oh ni sarai na ga abin da ya ishen
yau" kamar ba zata amsa ta ba amma taga dacewar bata amsar" Hmmmm Allah nawa inji
bamaguje, to ai dai har yau wata kusan biyar ban ga daya daga YAN ABUJAN sun yi koda waya
bane balle nace ko an yi maki wani aike na azo a gani, ana nan dai yanda ake, ba wani hura
hanci da za ai mana kuma " haba kamar ta ari baki dan masifat da ta taso mata lokaci daya ta
yunquro,sai bala'i take tana gore2n ai abinci ma wataran ita ke taimakawa, Mama tace daga
yau in ta haifu karta qara taimakawar taga in bazata rayu ba ita da danta? Ammar ne ya kama
hannun maman shi yana kuka, dan baya son hayaniya shi sam, daukar shi tai sukai daki sika
bar Goggo na kumfar baki.
Oga Zaks na gani sun fito daga wani daki mai duhu sosai, Alh Kalla dauke da Saudat
Alh Salihu dauke da Suwaiba, suna fitiwa, " to ku maida masu sabbin kayan da kuka zo da su
kuyi gida,nan da awa uku zasu farka, kuma ku kwanta gefen su a matsayin bacci kukai, domin
wannan magungunan da sukai ta sha zasu sa masu kasala da ciwon jiki, na kammala duk wani
aiki da za ai akan su, kudi kuma sai kun ce sun ishe ku, dan mahaifar su na da kyau sosai,
Dodo yayi farincikin samun ta, ba a taba kawo mata irin wannan ba, nima kuma shaida ne,
hahhahaahhha" godiya sukai suka canja masu kaya sukai mota da su sai cikin.garin.Abuja,
kowa ya dau hanyar gidan shi, fadar kyau da tsaruwar gidajen nasu bata baki ne kawai, readers
ku hango kowanne gida mai kyau kawai a idon ku, a gado suka aje su suka kwanta gefen su
sukai ta baccin asara, basu suka farka ba sai wajen lq'asar, miqa Suwaiba tai, tana hamma,
tana kallon dakin nata, ko ta ina dakin ya ruda ta, ko tunanin komai ba tai ba sai na bari taga
wannan gidan na ta mai dimbin kyau, tashi tazo yi taji wani.ciwo a cikin ta komawa tai.ta zauna,
tana "wasssshhhhhh Allahna, me ya samen a ciki kum? Duk jikina ciwo yake" kamar a tare suke
wannan maganar da Saudat domin tafi Suwaiba raki harda kuka, a rude mazan suka tashi
kamar ba abinda ya faru" me ya same ki Sweetheart?" Cikina" dagawa yai ya gani," Ayya kiyi
hakuri zai warke a hankali hatsari muka samu a hanya, ke da yar uwar ki kwalbar cup din da
kuke shan drinks ta cake ku a ciki, amma mun kaiku babban asibiti an dinke wajen, so a hankali
zamu jira ya warke mu ci gaba da shan amarcin mu ko" ya fada tare sa jawo ta jikin shi yana
shafa ta, kwantar da kanta tai a jikin shi kamar ba ita ba, tashi yai ya je ya hado mata abinci
tana daga gadon ya aje mata, ya zauna yana bata a baki, wani dadi ne ya lillibe Suwaiba yau
mafarkin su ya zama gaske, tana gama wa ta dau waya ta kira Goggon ta, wayar a kashe take
ta kunna ta tanakiran ta ko bugu daya ta dauka kamar jira take, " haba yar nan yau wata biyar
da kwana uku, kun tafi shiru ba magana ba aike" wata biyar da kwana uku??????............
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA
BY HAERMEEBRAERH
Page 9:
Tinani ta ke son tayi, amma kanta ya kulle sai pounding yake, nan da nan ciwon kan da take
ya qaru sosai, komawa tai ta kwanta, tai qoqarin daina tinanin" Babe what us wrong?" " kana ke
ciwo sosai, so nake na tina abubuwan da suka faru a tsakanin wannan watannin da akai auren
mu gaba daya ban sani ba" " ki dena yawan tinani likita ya hana, saboda zai jawo maki ciwon
kai mai tsanani, ki kwantar da hankalin ki kinji, aikin da akai maku ne yasa kuka kai wadannan
watannin ba tare da sanin inda kan ku yake ba, nj dinnan da kk ganni sai da nai sati uku a
asibiti, abokina kuma wata daya da sati biyu, kafin mukaji sauqi" tausayin kansu ne ya kamata,
lallai ashe hatsarin babba ne? A haka bacci ya dauke ta shi kuma yai palo yana murmushin
samun nasara, waya sukai da Alh Kalla, " aboki ya ka qare da wannan 'yan rigimar?" Komai ya
tafi as planed, ban samu matsala ba, wannan shegiyar uwar tasu ce taso sawa mata ta tinani,
na kawar da shi, yanzu haka bacci take" dariya suka.saka, " ai ni tashi tai tana min shagwaba
naji kamar na manta da ciwon na dan more ta kadan, dan sai ta min kyau sosai" " shegen
sama, ana halin neman yanda za ai a rufawa kai asiri kana neman kayan dadi" dariya sukai
tayi" anyway na mata dabaru irin namu na manya ta bar zance fatan ta Allah ya bata lfy, kasan
har yanzu maganin bai gama.sakin su ba, bacci take tayi" " haka ne, to sai dare in mun hade a
gidan Oga, yau akwai meeting" k to ba damuwa sai daren" kashe wayar sukai kowa na
jinndadin samun nasarar da sukai, yanzu tinanin su bai wuce yanda zasuna samun jini da aka
ce suna kawo wa duk wata ba daga matan nasu, dan su ba sa son suna satar yayan mutane,
ana tsafi da su, aikin zai basu wahala, kuma kar wataran a kama su, dabara ce ta fado mai na
yanda zasu na samun jinin daga wajen su, murmushi yai sosai, " dan ta rashin haihuwa me
sauqi ne, tunda ba ni aka cirewa mahaifa ba bare na damu, 'ya'ya dama takura ne, sanda na so
haihuwa na nemo matar da zan haihu da ita, dariya.ya dingayi kamar mahaukaci sabon kamu.
Ni ko nace hmmmmm kwadayi mabudin wahala. " Ni dai marka na gani da yin abinci kullum nai
na talla nai na gida ?" " nima haka gaskiya, wannan yar rainin kullum sai dai mu dafa mu bata,
ga Baban ma ya tafi har yau bai dawo ba " tab ai ko yau ita zatai tuwon dare ko taji a jikin ta, ni
hutu ya samen, dan ba zai yu.na nemo na tuqa kuma na bata ba inaaaa" "sai Markaaaa, uwar
gidan Talle, an buga an barki" yaran suka fada cikin hada baki da dariya da shewa, ita kuma ta
wani dage qafa tana zaune a qasa ta turo dankwali gaba, tana kada qafarta da tai fururu, " je ki
kiran ita Huwaila" da hanzari ta miqe tana gyara daurin qirjin ta, tana tafe tana banqaro qirji,
qugun kamar an daurawa tabarya zani, " Amarya ki zo Marka na son magana da ke" kamar ba
zata amsa ba da dan duk.tana