Showing 36001 words to 39000 words out of 102125 words
Chapter 13 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx
''Swthrt wai lafiyarki kuwa.?ʼ ya fada cike da mamakinta,dasauri ta bashi peck ah kumatu tana fadin''goodnyt baby sai munyi waya...!ʼʼ bata jira amsawarshi ba ta fice ayayin daya bita da kallo,can kuma ya maida hankalinsa kan Hafsa dake tsaye da yayansu Muktar wanda yazo shigewa cikin gida yaci karo da ita anan,
Yah Muktar yace''Hafsa tambayarki fa nake nace meya faru kikazo gida ah irin wannan lokacin har kuma shi mijin naki ya kyaleki kika.fito..?
Da rawar murya tace''Sa...sakina yayi...ʼʼ ta fada hawaye na kwaranyo mata,adaidai lokacin Nabeelah ta karaso wajen,cike da mamaki da alʼajabi yace''whatttt...!?saki fa kikace meh kika masa dahar yaga bazai iya hakʼuri ba ya sakeki..?dududu yaushe ma akayi auran..?anya Hafsa kina da gaskiya kuwa...?kar dai ince wani rashin mutuncin ne kika shuka masa don nasan halinki sarai baki da kirki...!ʼʼ
Juyawa yayi ga Nabeelah wacce murna fal ranta yace''Ke! Nabeelah meya faru aka sako yarʼuwarki..?
Kai tsaye tace tana taunar cingam''Rashin kunya ce take yawan mishi,kwata kwata bata darajashi ga kuma yawan neman rigima awajen uwargidansa toh shiyasa yace ya gaji ta tafi gida....ʼʼ
Kallon mamaki Hafsa tabita dashi don bata tabʼa tunanin cewa magana irin haka zai fito daga bakinta ba,ji yadda ma tayi maganar kai kace ko agabanta akayi komi,afusace Yah Muktar ya daga hannu da nufin yanka mata mari,juyawa tayi ta shige cikin gida da gudu tana kuka,yayi hanzarin bin bayanta haka itama Nabeelar wacce bazaʼa iya misalta irin tsananin farin cikin da take ciki ba,duk abunda yake faruwa akan idon Andrew ne dake zaune cikin mota,duk da cewa besan meh suke tattaunawa akai ba ammh yasan bezai wuce akan zancen sakin bane,sosai ya tausaya mata ganin danʼuwan nata ya dauki zafi da lamarin,girgiza kai yayi sannan yaja mota yayi gaba,
Kuka take tamkʼar ranta zai fita ta nufi entrance door aguje tana waigen Yah Muktar daya dauki wani cable akasa yana biyota abaya,Alh.Bilyaminu da matarsa Haj.Amina wacce ake kira da mami suna zazzaune suna cin abinci bayan sun idar da sallar ishaʼi,sai gani sukayi yʼar tasu ta fado falon tana rusar kuka,cike da tashin hankali duk suka mimmikʼe tsaye,Daddy ne yayi kʼarfin halin cewa''ke Hafsah lafiya kuwa..?meya faru kika shigo mana gida ah hargitse ne..?
Kafin ta bashi amsa saiga Yah Muktar ya shigo tamkʼar mayunwacin zaki,nufarta yayi ita kuma ganin hakan yasa ta buya abayan mami,
Mami ta doka mishi tsawa''Dakata muktar banson haukan banza ku natsu ku mana bayani,meke faruwa ne...?
Azuciye yace''Sakinta fa akayi,gata nan dai da ranta ku tambayeta ba kʼarya nake mata ba...ʼʼya fada yana nunata da yatsa,jin zancen sukai tamkʼar saukar aradu,afusace Daddy ya dubeta yace''Ke fito fili in ganki dakyau wai da gaske ne abunda nake ji ko kʼarya ne...?ʼʼ
Fashewa tayi da kukan bakin ciki tace''Hakane daddy Suleiman ya sakeni saki har biyu...ʼʼ
Salati suka sanya su dukah,mami ta tureta tace''Hafsa meh kika masa yayi miki irin wannan wulakantaccen sakin ne..?yaushe akayi auren da har ake neman maidaki bazawaran kʼarfi da yaji..?Ni Amina wannan wani irin abun kunya ne ya sameni haka...?ʼʼ zaman 'yan bori tayi akasa gami da dora hannu aka ta fashe da kuka mai cin rai,daddy da Yah Muktar su kansu hawaye ne ya tarun musu acikin kwarmin ido,alokaci dʼaya suka samu gu suka zauna jiki duk babu kwari,Daddy yace ba tare daya dubeta ba''Meh kika mishi Hafsa..?don komi baya faruwa saida kwakkwaran dalili,hakanan kawai bazai sakeki ba,meh kika mishi?wannan shine tambayar karshe dazan miki...ʼʼ ya ida magana cike da zafi,
Nabeelah ce ta bashi amsa,ta musu bayani kamar yadda tayiwa Muktar awaje,afusace Hafsa tace''you ar very stupid rufemun baki awajen sai kace kina nan abun ya faru,ki gayamun yinin yau zir kin yishi ne agidana..?ba kina can kin tafi yawon dadironcinki bane..?daddy gata nan ba kʼarya nake mata ba dazun dana nemeta da abun ya faru nayi imani da Allah saurayi na kanta ne...ʼʼ
Wani irin wawan mari Mami ta kwasheta dashi tace tana huci''Don kutumar ubanki abunda aka tambayeki kenan..!? duk wanda yayi meh kyau dan kansa,haka zalika duk wanda yayi sabaninsa kanshi yayiwa,yanzu fisabillahi Hafsa irin abun kunyar da kika jawo mana kenan..?kwana goma sha hudu da aure sai saki ya biyo baya..?muga takaddar donmu gasgata zancen...ʼʼ
Yah Muktar ne ya nufi Nabeelah ya shigeta da bugu yana fadin''Shegiya yʼar iska wato baki bar yawace yawacen banza bako..?ai dama wajen yarʼuwar taki kika koya,ina kikaje gayamun?'' Ya cigaba da bugunta tana ihu da kururuwa,Daddy ne yayi kʼarfin halin zuwa ya ceceta,yace da Muktar''kai Muktar ka kyaleta muji da babban matsalar dake gabanmu,taje tatayi rayuwace ai kuma ta ishi kowa riga da wando...ʼʼjuyawa yayi yakoma wajensu Hafsa da aketa fama da ita kan ta bada takadda amma tace da baki ya fada mata be rubuta ba,
Dadai suka tabbatar da cewa da gasken take be rubuta akan takadda ba,sai daddy ya latso Alh.Alassana awaya,adaidai wannan lokacin kuma yabba dasu Gidado ana falon tsoho da sauran yabbanin nashi ana hira har Aliyu da wasu acikin matasan gidan,can Gidado yace zai wuce gida don sam hankalinsa baʼa kwance yake ba,atare suka mike shida Yabba wanda kiran sirikin nashi ne yasa ya mike don girmamawa,bayan sun gaisa Alh.Bilya yace''Ashe abunda ya faru kuma kenan..?Banji dadi da irin wannan bakʼar kaddarar ta ratsa tsakanin yaʼyanmu ba,agaskiya abun bemun dadi ba ko kadan...!ʼʼ
Gaban Yabba ne ya yanke ya fadi yace cikin tsantsar tashin hankali''Subhanallah meh kuka ya faru halan Alhaji...?
Cike damamaki Daddy yace''kana nufin baku masan abunda ke faruwa ba..?toh ga Hafsa nan dai ta dawo tana kuka wai ya saketa saki har biyu ammh mudai bamu ganta da takadda ba shiyasa nace bari in kira ayi sulhu yarinya takoma dakinta da wurwuri kafin mutane su ankara da batun don zai zamo mana abun kunya ne,haba yaushe akayi aure da saki zai biyo baya nan da nan..?sannan kuma don girman Allah karku tursasashi idan yace bazai maida ita ba,kawai ya kawo mata takaddar shaidar sakin shikenan....ʼʼ
yana gama fadar hakan ya yanke call dʼin,afusace daddy ya waigo ya kwashi Gidado da mahaukacin mari yace cikin high degree of annoyance''Ashe dama kai din mutumin banza ne ban sani ba sai yau..?ai danasani dazu na bari mahaifiyarka ta kunyata dakyau ashe kamar ta hango abun assha dʼin daka aikata ne shiyasa tayi treating dʼinka kamar dabba agaban kannenka...ʼʼ
Baba Haruna ne yayi saurin shiga tsakaninsu ganin yabba na shirin sake kwasheshi da wani marin,yace''Haba Hamma idan rai ya bace toh ai shi hankali baya gushewa,ka natsu ka mana bayanin abunda ya faru don Allah...ʼʼ
Sauran ma suka shiga tausarshi har Tsoho,can yace''Sakin amaryarsa yayi fa wacce ayau take cika kwanaki goma sha hudu agidanshi,yanzu mahaifinta ne ya kira yake gayamun cewa ai taje gida,ku duba fa saki har biyu don bashi da tausayi da imani...ʼʼ
Gabaki daya mutanen falon suka dauki salati,Tsoho dayafi kowa kaduwa da zancen yace yana duban Gidado''Kai meh sunana wai haka ne...?shin meyayi zafi ne haka da zaka aikata irin wannan dʼanyen aikin ba tare da neman shawara ba..?idan laifi ta maka meyasa baka kawo kararta ba ,ko nan ko gidansu,a'ah sai kawai ka yanke hukunci mai tsauri kai tsaye...?
Hawaye duk ya cika mishi idanu yana mai takaicin wannan bakar ranar da tazo gareshi,kwashe labarin komi yayi ya fada musu irin rashin daʼa ta Hafsa da kuma gorin daya ji tana yiwa Jameelah da sauran yanʼuwansa,duk da cewa kowa beji dadin abunda tayi ba ammah still anfi dora laifin akansa ne da irin dʼanyen hukuncin daya yanke,kafin kace meye wannan kowa agidan labarin sakin ya iskeshi har inda yake,kai hatta dawanda baya zaune cikin gidan an kira an sanar dashi bad news din,Zancen na isan kunnen Baddo ta taso arikice tana kuka don azatonta Anti Jameelah ce akace ya saka,ta nufi falon Tsoho da gudunta ayayin dasu Ramlah suka take mata baya,Yumma tsabar bakin ciki ma ko iya motsa yʼar yatsarta ta kasa sanda taji zancen,tana can zubʼe akan gado tana kukan zuci,can wani irin kuka ya kufce mata tace cike da dacin rai''Suleiman why..?meyasa zaka saketa...?kodayake nasan wannan zafin ran ba naka bane saka ake ammh bazan bar ganin laifinka ba,duk wanda keda hannu acikin lamarin rayuwarka data sauran yanʼuwanka nabarshi da Allah...ʼʼ kuka yaci mugun kʼarfinka.can kuma kamar wacce aka tsikara da allura sai gani nayi ta mikʼe fuska babu annuri ta dauki belt dʼin Gidado da tayi ceasing ta fice daga dakin,
Gidado nacan iyayensa maza sun sakaci agaba da fada hadda matayensu,anata jimamin wannan babban alʼamarin daya kunno kai,masu murna da faruwan hakan nayi ayayin da yawancinsu abun be musu dadi ba musamman Hajju wacce har yʼar kwalla saida ta zubda,can saiga Baddo ta fado dakin aguje tana kuka tamkʼar ranta zai fita,gabaki daya sai hankulansu ya koma gareta,kai tsaye wajen da Gidado yake durkushe ta nufa ta shiga kai masa bugu akʼirji tana kuka tace''Kaje ka dawomun da antina meyasa ka saketa..?ashe da gaske kake kana iya sakin nata ko bayan ta gaya maka gaskiya...?na tsaneka hamma..!na tsaneka...!ʼʼ kuka yaci mugun kʼarfinta,gabaki daya sai kan kowa ya daure da wannan sabon alʼamarin,Ramlah da tasan dawan garin itace taje ta kamo hannunta take fadin''ke lafiyarki kuwa ba anti Jameelah ya saka bafa Anti Hafsa ce..ʼʼ
Cak! ta tsaida kukanta tana bin Ramlatun da kallo,Ramlan ta daga mata kai alamun tabbatarwa,bata yadda da ita ba hakan yasa ta waiga tana duban Aliyu wanda idanunsa dama akanta ne tun sanda ta shigo,yanata kallon yadda take ta zuba kukan shagwabʼa abun dai gwanin ban shaʼawa,tace dashi''Hamma Aliyu wai da gaske ba antina ya saka ba..?
Shima din gyadʼa mata kai yayi alamun eh don bashi da sauran kuzarin amsa mata in words,dagudu tabar falon tana dariyar murna ayayin da kowa ya bita da kallo,Tsoho ya girgiza kai yace''Kai Mubeenah akwai shiririta wato ita dai Jameelah ta sani wancan kuwa ko oho...ʼʼ aka dan murmusa,Tsoho yayi gyaran murya ya soma jawabi''wato kamata yayi ace mu hadu dukah mu tayashi rungumar wannan kaddara tasa bawai mu kalli abun ta baibai ba da kuma dora laifin kacokam akanshi ba,itama da nata laifin ammh bata cancanci irin wannan hukunci ba,haba meh sunan manya baʼa fa sanmu da haka ba,an sanmu ne da aiki da komi cikin ilimi,dan Allah ka rage zafin ran nan sannan ka dunga natsuwa idan ranka ya baci,karka biyewa bacin rai ka dunga tafka kuskuren da zakazo kayi danasani nan gaba,so nake yanzu ba anjima ba haka kuma ba gobe ba Aliyu da daya acikin yabbaninka su maka rakiya ka dakko matarka ka maidata dakinta,ka duba darajar igiya dayan daya sauran muku ka tseratar da mutuncinta karka maidata bazawaran kʼarfi da yaji....ʼʼ
''Tsoho kuyi hakʼuri ammh agaskia bazan iya maida Hafsa ba harsai ta hankalta kamar yadda na fada afarko...ʼʼ
Su yabba da yanʼuwansa suka taso mishi tamkʼar zasu cinyeshi dʼanye,yabba yace azuciye''Tsoho aina gaya maka taurin kai ne da wannan yaron,sam baya kʼarban maganar manya shiyasa yake yawan samun matsala da mahaifiyarsa,shi komi sai yace abunda ransa yakeso zaiyi toh ina kuwa rayuwa zai tafi haka baka da mai kwabonka da kuma nuna maka hanya madaidaiciya....!?ʼʼ
Hajju ta mikʼe tare da kamo hannun Gidado tace''Dana Taso muje muyi magana atsanake karsu cinyemun kai danye sai kace kowa baya kuskure...ʼʼ tashiwa yayi yabi bayanta sukabar falon,yabba ya bita da''Ai dama kece kika bʼatashi shiyasa baya ganin idanun kowa da gashi...ʼʼ
Direct part dʼinta ta kaishi ya zubʼe saman doguwar zuciye tare da dafe kansa dake barazanar fashewa,Hajju ta mikʼe ta shiga kichin ta dauki kofi tadan dibi ruwa kadan aciki ta zauna ta shiga zuba addu'o'i tana tofawa aciki har dai ta kammallah sannan ta dawo ta bashi yasha,nan da nan yaji wani irin dadadar sanyi ya mamaye masa zuciya,idan zaku tuna haka take mishi aduk sanda ransa ya bace,harta bude baki zata soma magana sai ganin Yumma sukayi ta fado dakin fuska tamau babu ko digon faraʼa,hannunta kuma rike da belt dʼinsa hakan yasa gabanshi faduwa,dataje can falon tsoho akace mata yana wajen Hajju,hakan yasa ta nufo nan ba tare data bari sun ankara da belt dʼin hannunta ba,kan Hajju tayi wani yunkuri tuni Yumma ta shammaceta ta zuba mishi belt iya kʼarfinta gami da fashewa da kuka take fadin''Suleiman insha Allahu bazaka kasheni ba sai lokacina yayi kana jina ko..?maza fita kaje ka dawo da matarka kafin yau nasa kayi danasanin fitowa daga tsatsona...ʼʼ
''Yumma wai meyasa kike mun hakane sai kace ba mahaifiyata ba..?why kikayi hating dina ne mena mikiiiiiiii ne arayuwa...? Ya fada yana mai rushewa da kukan takaicinta jikinsa na mugun shaking,azuciye tace''Ni kake gayawa wannan maganar...?toh Suleiman dakeni asannan zansan kana jin haushina,ko bakaji abunda nace bane..?nace ka dakenii..ʼʼ ta fada tana kokarin sake zuba mishi belt din,dasauri Hajju ta karbe ta jefar acan kasa ta rufeta da fada''Ummerheny nifa kina bani mamaki wasu lokutan meye haka kikeyi ne sai kace wacce ko alif bata karanta ba...?ʼʼ
Saurin fita yayi daga part din zuciyarsa na azalzala,hawaye duk ya gama wanke mishi fuska,agefe guda kuma yana jin wani irin mugun tsanar Baddo na dada lullube mishi zuciya don ya daura laifin ne kacokam akanta,acewarsa daʼace bata fusatashi ya dawo ba ai da komi be faru ba,
Yumma tace tana kuka''Hajju ki kyaleni in koyawa Suleiman hankali,duk acikin yaʼyana yafi bani ciwon kai,shine dan dake sakani zubar da ruwan hawaye wallahi na tsani yaron nan....ʼʼ ta fada tana mai rushewa da kuka......
'''''Tunda labarin rabuwar Hafsa da Gidado ya isa kunnen Azeema take ta kuka don ji tayi kamar itace ta rabu da mustaphanta,abincin kirki be wani shiga cikinta ba sai kuka take tayi wanda Zuby ta kasa gane dalilin kukan nata.....
_*2 extra free pages remaining purchased by Nanarh Ayeesha buh mind you registration is still goin on😜*_
_ku nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._
*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...
07065481260..Ko kuma 09069067488
_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_
*🍃KISHIN MATA🍃*
🍃🍃🍃
_mai dauke da salo na daban🤙..!_
*♟
ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT
WɾƖTҼɾ
ى
ASSɷ
*✍
*NA*
_*HAFNANCY LURF💕*_
_*[Hafseesee]*_
_*💍NANARH AYEESHAʼS PAGE..!😘*_
_*💫BABI NA SHA SHIDDA..💥*_
!.......Acikin wannan daran aka tasa kʼeyar Gidado gaba zuwa gidansu Hafsa tamkʼar karamin yaro,dashi da Baba Munniru,Baba Haruna sai kuma Aliyu da abokinsa Sagir wanda aka nemoshi awaya babu shiri,abunda abokin nashi ya aikata sam be mishi dadi ba,suka hada kai shida Aliyu sunata zaginsa acikin mota,Aliyu yace''wallahi malam ka bʼata wayonka,gaka nan dai ana ganinka anga mai wayau ashe abun ba haka yake ba da sauranka..ʼʼ
Baya cikin mood dʼin cece kuce shiyasa kawai yayi ignoring dʼinsa,Baba Haruna ne ya masa jan ido ganin yafi kowa zakewa yace''wai kai Aliyu bazaka rufewa mutane baki bane..?ai gara dashi har mata biyu gareshi kaifa dayan ma ta gagareka ajjewa ka tsaya kana ruwan ido,karka bari in sake jin muryarka acikin motan nan idan ba haka ba zan mugun sassabʼa maka,kaima Sagir ka kama kanka banison shirmen banza da wofi...!ʼʼ
Ba shiri kowannensu ya kama kansa,Gidado kuwa tunda suka kamo hanya uffan bece ba har kawo lokacin nan,lumshe idanu yayi yana tunanin sabbin halayen Yumminsa da take gwada mishi wanda ada can ba haka take ba,akwai soyayya da mugun shakʼuwa atsakaninsu don kusan zai iya cewa tafi kʼaunarshi akan sauran yaʼyanta ammh tunda ya auri Jamila komi ya sauya zani,abu kadan saita rufeshi da fada tamkʼar dama jiransa take ya aikata ba daidai ba,tunda ya auri Jamila zai iya kirga iya adadin daya zauna gashi ga mahaifiyarsa suna fira cikin so da kuma kʼaunar juna wanda ada can kafin yayi auran bazai iya misalta iya adadin zama na aminci da sukayi ba da kuma kʼaunar juna dake tsakaninsu ba,ammh ayanzu why diz sudden changes..?kodai haushinsa takeji akan rashin haihuwa..?ammh idan hakan ne toh meyasa bata dauki zafi da sauran ba sai shi..?
Wani zafafan hawayen dayake ta kafewa ne suka samu damar zubowa,adaidai lokacin suka iso kʼofar gidansu Hafsa,agogo ya nuna 10:15pm,bayan hannu yasa yana share hawayen gudun kar wani ya ankara dashi yana kuka,kowa ya fito sai ya rage shi kadai aciki yana tunanin ya fito ne ko kuwa aʼah,be gama yanke shawara da zuciyarsa ba yaji Baba munniru na fadin''zaka fito ne ko kuwa mu koma..?don bazamu shiga ciki babu kai ba...ʼʼ
Dasauri ya fito yana gyara zaman rigarsa wanda kananan kaya ne ajikinsa ko bari ya canzasu baʼa bari yayi ba aka taho gidan surukai dashi ahakan,bubbuga gate dʼin gidan suka soma yi,baʼa wani jima ba mai gadi ya budʼe musu,suka mishi bayanin kansu yace bari ya nemo musu iso awajen masu gidan,su Daddy na falo duk an zuba uban tagumi ana jimamin wannan alʼamarin har ita Hafsan,sai kuka take rerawa ahankali,Daddy ya dubeta afusace yace''Zaki rufewa mutane baki ko kuwa saina tashi na tattakaki anan..!?tunda zaman gidan kikeso ai gashi nan saiki zauna da tushi banza mara albarka wacce tayo gadon uwarta...ʼʼ
Dasauri mami ta tari numfashinta''A'ah ban gane tayo gadon uwarta ba..?ka tabʼa ganin nayi yaji ne balle naje gida da sunan ka sakeni..?ʼʼ wani irin wawan kallo ya kwasheta dashi yace''Ai don ina hakʼuri dake ne da kuma shanye abubuwan da kikemun inba haka ba daʼace wani ne bani ba inajin da tuni kun rabu Amina,ki sani darajan yaʼyanki kike ci har kika kai tsawon lokacin nan agidan nan,ga yʼarki nan ta kwashi halayenki kaf ta dorawa kanta kuma.....ʼʼ
''Daddy don girman Allah ku bari wai meyasa kuke haka ne..?ʼʼ Mukhtar ya katsesu cikin tsananin bʼacin rai,mami tayi shewa ta mikʼe tana kokarin magana sai ga Ayuba mai gadi yayi sallama hakan yasa tadan natsu ta koma ta zauna,aka bashi izinin shigowa,dukʼawa yayi yake sanar dasu bakin da akayi,daddy ya washe hakʼora