Showing 75001 words to 78000 words out of 102125 words

Chapter 26 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

1851

buɗe gidan baya inda Baddon ke kwance sai washe haƙora yake gami da susa ƙeya,so yake kawai su karaso ya fasa kwan tunda ogan nashi ya kasa fasa musu,wannan karon Hafsa ce agaba Jamilar kuma biye da ita,Musa yace"kun san meh…?matar yallabai ciki ne da ita..."

"Whattt..?ciki..?dagaske kake..?toh inda gasken kake waya fada maka hakan..?" Hafsa ta fada cike da tsananin mamaki tare da ja da baya,Jamila kuwa wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta,dasauri ta karasa har gabanshi tana mai bayyana farin cikinta tace"Musa dagaske kake ko wasa...?dan Allah buɗe baki kayi mana bayani…"

baki awashe yace"wallahi da gaske nake don muna wajen aiki ne aka kira ake ce masa wai bata da lfy tunda taje makaranta take ta tila amai,toh shine aka kaita school clinic aka mata ƙarin ruwa,koda muka isa ma tuni an mata test ko,shine suke cewa ai ciki ne da ita,gata nan dai yallabai yace akular masa da ita kafin ya iso...."

Baddo dake kokarin saukowa ta sunnar dakai kasa don sosai take kunyar haɗa idanu da Anty Jamila,dasauri Jamilar ta karasa gareta tana kokarin taimaka mata don ta fito daga cikin motar,sai ji sukai Hafsa ta rushe da kuka tana fadin"Na rantse da girman Allah bazai yiwu ba!wallahi bazai taɓa yuwuwa ba!...ashe dama wayau ne abun..?ko kuma dai ince shiri ne..?wato basu son ɓare ya samu haihuwa da ɗansu shiyasa suka aura mishi ƴar"uwarsa ita tazo ta zuba mishi ya"ya,toh asirinku ya tonu kuma wallahi bazamu yadda ba dole ne ah warware duk wani abunda aka mana har yasa muka kasa daukar ciki........." afusace Jamila ta juyo ta doka mata tsawa"Ke!! Hafsaaaaa meye haka ne...?why do you always behave lyk a hell dog huh...?Hafsa tambayarki nake meyasa ke baki da hakuri da kuma fahimta ne arayuwarki sai dai neman tashin hankali akodayaushe...?yanzu fisabilillah anan ne ya dace ki amayar da irin wa"ennan maganganun agaban yaransa...?azatona kin canza ne ashe dai tuban ɗan muzuru kikai……"

Hafsa na kokarin sake magana Jamila tayi saurin taran numfashinta"Karki cikani da hayaniya if not zan nuna miki ɗayar kalata don karki manta na taɓa fada miki cewa ni ɗin hawainiyace mai canzawa aduk sanda naso,ki ɓace mun daga gani kafin ranki yayi mugun ɓaci yanzu……" sosai Jamila ta fusata ainun,ɓacin rai ya bayyana karara akan fuskata,zan iya cewa bata taɓa nuna ɓacin ranta sosai akan wani abu ba kamar na yau…ita kanta Hafsan ta tsorata kwarai da yanayin Jamilar hakan yasa ta kasa tsayawa cece kuce da ita,sai kawai ta juya ta koma cikin gida da gudu tana cizgar kuka,Jamila ta bita da"Banza kawai mara hali...." su Musa sai hakuri suketa bata,bata kulasu ba ta riko hannun Baddo tana jera mata sannu da murmushi akan fuskarta,ita kuwa Baddon tamƙar zata nitse akasa don kunya,

Sannu ahankali suke takawa zuwa ciki ayayin da Musa ke biye dasu da jakar makarantar ita Baddon......

    *****

Tun daya sako kai cikin falon yaketa jiyo hayaniya wanda ke fitowa daga master bedroom,bai kai ga tantance muryoyinsu ba idanunsa suka sauka kan kayan maza dake yashe akasa,gabansa ne yaji kawai yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske,zare baƙin shade ɗinsa yayi ya maƙaleshi agaban aljihun kakinsa sannan ya taka ahankali har zuwa inda kayan suke ya tsugunna agabansu,hannun hagu yayi amfani dashi ya daga wandon da yatsunsa biyu gabansa na cigaba da bugawa,dasauri ya jefar da wandon sannan ya daga rigar itama ya shiga jujjuyata ahannunsa yana mai ambaton sunan Allah aransa,can ya jefar da rigar ya nufi wayar daya gani asaman centre table ƙirar samsung,babu ɓata lokaci ya dauki wayar ya kunnata,idanunsa suka sauka akan hoton Kasim wanda yayi amfani dashi as lock wallpaper ɗinsa,gabansa ne ya tsananta faduwa yace with a shaking voice"Ka....Kasiiim kuma...?" Tunaninsa ne ya yanke sanda yaji Kasim ɗin na yiwa Azeema magana muryarsa asama,with a very broad and clear voice yake fadin"Azeema ki zageni,call me what ever name you feel like calling me with don nafi ganin nawa laifin da har na aminta nake kwanciya da matar dan"uwana da sunan in bata ciki,abun kazanta abun tirrrrr dani,wallahi ban taɓa nadamar zuwan wannan ranar ba kamar yau………kuma ki sani kamar yadda na fada muddin kika koma tarayya da wani awaje tofa zan fasa kwai……"

Kuka ya rushe dashi wiwi tamƙar karamin yaro,sai taji jikinta yayi mugun sanyi,dasauri ta rungumeshi tana lallashinsa"Am so sorry my kani wallahi nadau maka alkawari bazan taɓa gigin neman wani awaje ba,dakai na fara kuma insha Allahu sai mun cimma nasara kan abunda mukasa gaba,don Allah kar kace zaka gujeni kaji my dear Kasim...?"

Ai rikicewa yayi jin ta kirashi my dear kasim,bai san cewa duk nan salon kissarta bace,so take kawai ta sake jawo ra"ayinsa zuwa gareta,sumba yashiga zuba mata kota ina ajikinta yana fadi jikinsa na mugun rawa"Ai duk barazana ce nakeyi ammh wallahi koda wasa bazan iya barinki ba my Zeema,ina mugun sonki wallahiiii....inaama ace ke ɗin matata ce……………"

Gidado dake laɓe akofa yana sauraransu yaji kawai zuciyarsa na neman yin bindiga,bai san sanda wasu zafafan hawaye suka shiga wanke masa fuska ba,wai Ƙasim ne dai ke cin amanar dan"uwansa Mustapha,ashe sunma kwan biyu suna wannan aika aikar kuma babu wanda yasani,yau ne dai Allah yashirya tona asirinsu shiyaasa tayi wa mijinta ƙaryar rashin lfy har kuma ya nemi alfarman yazo ya dubata,ashe asirinsu ne zai tonu,dunƙule hannu yayi daƙyau,zuciyarsa na ingizashi kan ya afka musu kawai ayayin da wata zuciyar ke ce masa kar ya shiga yanzu ya bari yabi komi asannu,don yanzu idan yakai magana gaba ba lallai ne ayadda dashi kai tsaye ba ammh labarin zaifi armashi idan har suka gani da idanuwansu,har ya juya zai koma yaji Azeema tace"pls Kasim kazo jibi mana don inason daga yanzu mu dunga tsallake kwana daddaya ne kawai,sati guda ɗinnan na mugun min nisa……"

"Naji gimbiya yadda kikace hakan ai za"ayi...bari na hanzarta na tafi gida kar wani ya shigo yaga kayana ayashe afalo...."acewarsa,gwalalo idanu waje tayi tana fadin"wayyo Allah niba nama manta wai mun manta bamu kulle wurare ba.....muje don Allah mu duba Allah yasa dai babu wanda yashigo......"

Jin tattaunawarsu yasa babu shiri Gidado yabar inda yake,cikin sauri yake tafiya cikin sanda gudun kar cover shoes ɗinsa su bada sauti,fitarsa cikin apartment ɗin yayi daidai da fitowarsu,ajiyar zuciya duk suka sauke ganin basu cimma kowa ba,an canzawa wayar Kasim wajen ajiya ammh sam bai dago komi ba tunda shi kansa yama manta inda ya barshi kan su shige dakin,kafin Gidado ya fice ya wurgashi ne saman wani two seater,acan waje bayan yafito ya zaro shade ɗinsa ya mayar don bayason mutane su gano cewa yana cikin damuwa,saidai duk da hakan hawaye bai bar ziraro mishi ba,sai kirarsa Mustapha yake tayi don yaji yadda yanayin jikin matar tasa yake,cikin rawar murya Gidado yace"Mustapha mai zan gaya maka yanzu...?am so confused.......wallahi kona fada maka ba yadda zakayi bama...."

shigewa wani lungu dake kusa da gidan yyi sannan ya daga ƙiransa,ajiyar zuciya Mustaphan yasauke yana fadin"Haba dan"uwa wai meke faruwa ne duk kunsa hankalina ya daga....ko jikin Azeemar ne ba dadi..?don girman Allah na rokeka karka ɓoyemun ka gayamun gaskiya…" runtse idanu yayi ayayin da wasu sabbin hawayen suka bulle masa na tsananin tausayin dan"uwan nasa,cikin rauni yace"Mustapha ka kwantar da hankalinka jikinta da sauki sosai ammh inason ka daure kamun wata ƴar alfarma ne…"

Gaban Mustapha ne ya fadi ammh bai kawo komi aransa ba yace"Dan"uwa what ar you hiding away from me...?ka gayamun ko mutuwa ne matata tayi...?" ya furta so confused,Gidado yace aransa"Ina ganin da"ace mutuwa tayi da zaifi maka abun bakin cikin data aikata wanda zai iya zamo sanadin mutuwar zuciyarka……" cikin kwantar da murya yace"Wallahi tallahi Azeema is very very fyn nidai kawai so nake karka kuskura ka kirata harka dawo....."

Wuta ne ya daukewa Mustapha yace"ban gane kar in kirata ba....wai what d heck is going on…?brother you are getting me confused don Allah kamun bayani..." ya ida magana zuciyarsa na azalzala,ajiyar zuciya Gidado ya sauke yana mai firda huci kan yace"Lil pls calm down ka saurareni mubi komi asannu,idan ka daukeni amatsayin dan"uwanka wanda kuka fito ciki ɗaya dashi wanda kuma ke agaba dakai toh juz obey me,idan har zuciyarka ta yadda cewa bazan iya cutar dakai ba toh kayi duk abunda nace...."

Ajiyar zuciya yasauke kan yace"fine naji kuma na yadda zanyi duk abunda kace don na aminta dakai fiye da tunaninka dan"uwanka..." ya fada ayayin da wani guntun hawaye ya ziraro mishi,bayan hannu yasa ya daukeshi,shi kansa Gidadon dauriya kawai yakeyi inba haka ba kukan neman kufce masa yake,yace cikin jarumta"Yaushe zaka dawo...?" Mustapha yace"Da sai next week ammh mahaifiyar mr.Governor ba lafiya sosai don haka adaran gobe zamu taso,sai mu wayi garin jibi ah Nigeria...."

Da sauri Gidado ya tari numfashinsa"Azeema tasan da hakan...?" Mustapha yace"No bamu kai gayin wannan zancen ba ta kashemun waya..." Gidado ya saki murmushin ƙarfin hali yana fadin"Thats very good dama banson ta sanin...kana iya kiran nata and be very careful karka sake kace mata kana nan tafe goben and most importantly karka kuskura ka tambayeta ko nazo dubata...?don ban bari ta ganni ba nafito....nasan you are very confused ammh karka damu zan maka bayanin komi idan ka dawo,saidai kuma idan ka kiyaye sharuddan dana gindaya maka kenan,be very very careful and do juz as i said if not zaka ɓata rawarka da tsallanka…" yana gama maganarsa ya yanke call ɗin yana kokarin danne kukan dake neman cin mugun ƙarfinsa,ahaka yaji ƙarar buɗewar kofa,ahankali ya leƙa yaga kasim ne ya fito yana ɗan dube dube,dasauri ya dauke kansa gudun karya gansa,saida ya tabbatar da cewa ya ɗan jima da tafiya sannan ya fito daga cikin lungun ya soma tafiya jiki duk babu kwari,wayarsa yaji yana ringing kuma,yana dubawa yaga call ne ke shiga wayar Hafsa kuma andrew ne,murmushi mai ciwo ya sakar yana fadin"sum people are trying to push me to the wall ammh bakomi zanyi maganinku ne...."

daga call ɗin yayi,muryar Hafsa ne ya soma dakar dodon kunnuwansa"hello pls wake magana...?" daga ɗaya ɓangaren Andrew ya sauke ajiyar zuciya yana fadin"Gimbiya ranki shi dade masoyinki ne wanda ya jima yana crushing akanki...." cike da mamaki tayi saurin taran numfashinsa"spare me the drama plss...wani masoyi kuma...?i think wrong number ka kira don wannan matar aurece...."

Kasaitacciyar dariya ya saki kan yace"No i guessed i called the right person....ko bada Hafsa nake magana ba...? Kafin tayi wani magana taji an katse call ɗin,dukansu biyun na tunanin ko ɗayan ne ya kashewa dan"uwansa wayar,basu san cewa gogan ne ba sannan kuma yayi blocking duka lambobinsu,acikinsu babu wanda zai iya kiran ɗayansa kuma,cikin hanzari ya aika da lambar Andrew ga wani abokinsa dake aiki ah MTN office,yana gama turawa sai ya kirashi bayan sun gaisa yace"Adam pls kamun tracking lambar dana aiko maka,you have the whole day to do dat...saina ji daga gareka..."

Ya yanke call ɗin zuciyarsa na zafi,yau daya kaamata ace yana cikin farin ciki ammh gashi an maye masa gurbin wannan rana da tarin bakin ciki,cab ya tare yace akaishi Garki,yau abun mamaki wai the whole DCP SAG ne acikn motar haya………

****

Har dakinta Jamila ta kaita ta hada mata ruwan wanka sannan ta fito ta bata wuri don ta watsa,komawa main falo tayi inda ta baro Hafsa na cizgar kuka,amaimakon taga tana kuka sai ta cimmata kuma ta gama waya har tana jan tsaki (alokacin da Gidado ya katse mata call da Andrew ne..) Jamila bata damu ba tace"Hafsa kina bani mamaki wallahi,wasu lokutan kita abubuwa tamkar mai hankali ayayin da wasu lokutan kuma kita abubuwa tamkar mai bakaken iskokai....yanzu ke ba abun farin ciki bane awajenki ace mijinki ya kusa samun karuwa...?ai karuwarsa duk karuwarmu ce gabaki ɗaya,sannan kuma ɗan Mubeenah muma ɗanmu ne......."

Afusace Hafsa tace"In ɗanta ɗanki ne toh ni ba ɗana bane,nima inason na haihu,Jamila inason naji radadin haihuwa ajikina,inason ganin gudan jinina aduniya,ki sani ɗan daka haifa da cikinka shine naka………kibar tunkaho da ɗan wasu don baki haifa ba,ba naki bane....." ta rushe da kuka,nan da nan hankalin Jamila ya tashi,cikin kankanin lokaci ta fita cikin hayyacinta,ciwon rashin samun haihuwa ya dawo mata sabuwa dal,rushewa tayi da wani irin gigitacciyar kuka tana fadin"Hafsa kinyi gaskiya....ɗanta ɗanta ne ammh ba nawa ba,wanda na haifa da cikina shine nawa…but try to get it into ur skull Hafsa,dani dake _*WE ARE BARREN*_ …we cant bear children............✍

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

_*KISHIN MATA...!*_

_Na marubuciya Hafnancy..._

_akan naira 200kacal👌_

   _ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

   _*💫BABI NA TALATIN DA DAYA...💥*_

  ………Ah babban katafaran falon Tsoho Gidado ya sami iyayensa maza zaune dashi Tsohon ana tattaunawa kuma duk akan karuwar da aka samu ne,suna ganinsa kowa ya hau washe haƙora,Baba munniru yace"Ga ɗan halak ɗinnan ma ya iso…" Baba Alseny kuma yace"Baban ƴan biyu ba…" saurin taran numfashinsa Tsoho yayi yace yana murmushi"kai kuma waya fada maka ƴan biyu ne da har kasawa ranka hakan…?

Kasaitaccen dariya Baba Alseny ya saki kan yace"Tunda ubansa ƴan biyu ne insha Allahu sai shima ya haifa ƴan biyun……" gabaki ɗaya aka saka dariya,shidai Gidadon binsu yake da kallo yana murmushin ƙarfin hali,duk akokarinsa nason ganin ya danne damuwarsa ne,ɗaya bayan ɗaya ya gaidasu suka tayashi murna da karuwar da aka samu,daga ƙarshe ya nufi Tsoho ya rungumeshi gami da sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya wanda hakan ya ƙaryar da zukatan kowa awajen,tsoho hadda ƙwallarsa shima,Gidado yace cikin ƙaryayyen murya"Kaka bansan da wasu kalmomi ne yadace nagode maka da wannan hadin da kayi ba wanda ada naso turjewa sai gashi auran Mubeenah ya zamomun alheri,ta sanadiyyarta zanga guɗan jinina adoran ƙasa……kaka nagode kwarai da gaske sannan kuma ina neman afuwarka da yafiyarka kan rashin mutuncin dana shuka maka adalilin wannan aure,dama ka fada kace wataran zan tako da kafafuna inzo har gabanka in duƙa ina maka godiya da wannan hadin dakayi……"

Dasauri ya cikashi tare da ƙarya gwiwowinsa akasa ina nufin kneels down yace yana jan majina"Kaka ga ranar ta iso...gani agabanka Kaka ina mai nuna godiyata da kuma jindadina agareka.....Kaka na kusa zama uba kai kuma ka kusa samun ɗa……" ya ida magana yana washe haƙora gami da dora kansa akan cinyar Tsoho,dariyar farin ciki Tsoho ya saki,yana yi su Baba Alseny na tayashi,can yasa hannu yana shafa kansa yake fadin"shaƙiyyin yaro kawai ai dama na fada maka cewa watarana zakazo kana godemun da wannan hadin danayi ammh ka musa mun,toh yau waye agabana...?"

    saurin bashi amsa yayi da"Wallahi nine kaka..." gabaki daya aka saka dariya har shi ɗin,Tsoho ya tayashi murna sosai tare da fada mishi cewa tabbas kuma sai an dage da du"a"i akan wannan cikin don neman kariya da kuma tsari daga masu mugun nufi akai....har ya tashi zai bar falon zuwa ɓangaran iyayensa matan sai mahaifinsa yayi saurin dakatar dashi,Baba Tsoho ne da kansa yashiga yi mishi bayanin sakin da akayiwa ƙanwarsa Surayya da kuma dawowarta gida tun kwana biyu da suka shuɗe,da fari ya dauki zafi ne da abun ammh sai aka shiga tausarsa da kuma kwantar masa da hankali akan yayi hakuri ah rungumi kaddara duka dama haka Allah ya tsara tun fil"azal,ya riga da ya diba iya lokacin da zasu zauna tare amatsayin mata da miji,akarshe ya mike yana share hawaye yake fadin"Allah sarki Surayya Allah yasa ki cinye jarabawarki..." cike da tausayinsu aka amsa da ameen,ya mike yabar falon aka bishi da kallon tausayi,bayan fitarsa Baba Haruna mai raunin zuciya uwa mace ne ya fashe da kuka yana fadin"Allah sarki yaran nan suna bani tausayi wallahi....Allah ya tona asirin duk wanda yake da hannu acikin lamarinsu...."

Gaba daya aka amsa mishi da ameen………

  ******

"Hafsa abunda nakeso ki sani shine ita haihuwa nufin Allah ce ba wai wayan mutum ba ne, iko ne na Allah.  Idan Allah bai nufeka da haihuwa ba toh duk hanyar da zaka bi ba zaka samu biyan bukata ba.Abu mafi muhimmanci a gareka shi ne kayi dangana ga Allah, ka koma gare Shi wajen yin addu’a har Allah Ya biya maka bukata,ammh bawai ka nemi ƙauce hanya ba don hakan nasa wasu matan fadawa cikin bin wadansu hanyoyi marasa kyau duk da niyyar neman samun haihuwa,Kai wasu matan kan ziyarci bokaye ko malaman tsibbu da niyyar su samar masu mafita...kuna ire-iren waɗannan bokaye kan yi amfani da irin wannan dama wajen yaudarar irin waɗannan mata,wasu lokuta har su rika yin lalata da su wai ta haka ne za su samar musu maganin da zai sa su rika haihuwa.

Na taba samun wani labari makamancin haka na wata mata da ta daɗe ba ta haihuwa kuma dangin mijinta suka tsane ta kamar yadda nima ada wasu dangin mijina suka tsaneni.Hankalinta ya tashi ne bayan sun shafe shekara 15 da aure ba tare da sun haihu ba,Wannan mata sai ta kasa mayar da al’amarinta ga Allah, sai ta rika yin shigar burtu tana ziyartar bokaye da malaman tsibbu da niyyar ta samu haihuwa.Nan fa irin waɗannan bokaye suka yaudari wannan mata suka rika kwanciya da ita ba adadi wai da niyyar su yi mata ciki don ta yi wa mijin kazafi cewa na mijinta ne.  Abu ya ki ci, ya kuma ki cinyewa daga baya asirinta ya tonu mijin ya sake ta.  Takaici ya ishe ta, tilas ta sa ta canza gari ta koma wani wuri don ta samu sauki saboda irin tsangwa da kuma tsanar da ake nuna mata daga wajen danginta da kuma sauran al’ummar da suka santa.

Ashe matsalar rashin haihuwar daga wajen tsohon mijinta ne, tun da ba su yi tunanin zuwa asibiti don a duba lafiyarsu su biyun ba.  Bayan mijinta ya rabu da ita ne sai ya sake yin aure, nan ma ya shafe kimanin shekara 10 ba tare da ya samu haihuwa ba.  Ita ma matar ta biyu da ta gaji da rashin haihuwa sai ta nemi mijin ya sake ta, don ita ba za ta iya ci gaba da zama da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login