Showing 87001 words to 90000 words out of 102125 words
Chapter 30 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx
banza dani...?nace maka tsareni yayi yana tambayata wanda ya mareni har yatsunsa suka fito akan fuskata......" da tsananin ɓacin rai ya katseta"shine har kika bashi damar taɓa miki fuska don bakisan darajar auren dake kanki bako…?idan shi bashi da hankaline ai ke kina dashi amma dake baki damu da halin dazan shiga ba,baki ki ko in haɗiyi zuciya in mutu ba……lallai Azeema kinci amanar aure da kuma soyayyar dana baki, kin juyani son ranki tamƙar masa ah tanda, kin maidani makahon ƙarfi da yaji tare da ingizani cikin duhu…" dauke kai yayi daga gareta ya maida kan hanya yana tuki, murmushi mai ciwo ya saki kan ya cigaba"hakika muna rayuwa ne a cikin duniya mai cike da mutane marasa-aminci da masu cin amana, Azeema cin amanar wani a ko wacce hanya mugunta ce, Cin amana mafi sa baƙin ciki ita ce zina,kodayake cin amana hali ne dake nuna cewa muna kwanaki na ƙarshe……"
Aƙidime ta dubeshi gabanta na harbawa da sauri da sauri tana fadin"Zina kace fa...?toh ni na aikata zinar ce da har zakace naci amanarka...?" murmushin takaicinta ne ya saki gami da satar kallonta yana fadin"kin manta ance zinar idanu itace gani…?zinar kunnuwa itace ji…?zinar harshe kuma itace magana…?zinar hannu kuwa itace damƙa wanda shine abunda na kama Ƙasim yana aikatawa akanki…?shin kin manta zinar kafa itace taku…?zuciya kuwa tana ƙwadayi haka kuma tana fata,farji kuma shi yake gasgata hakan koya ƙaryata…" ya ida maganarsa tare da sakar mata wani killer smile,tuni taji numfashinta na barazanar daukewa tsabar tashin hankali,hawaye ne kawai taji yana rushing daga idanunta babu gaggautawa, ko kafin ta farga sai gani tayi ya haura titin dazai kaika 5-star hotel amaimakon titin da zai fiddasu cikin unguwarsu, al"amarin dayasa hankalinta kara kololuwar tashiwa har taji zarginta na neman tabbatuwa wato asirinta ne ya tonu,cike da tashin hankalin da bata taɓa mafarkin shiga irinsa ba tace"Musty ina zamu kuma...?inace gida zamu...?"
Satar kallonta yayi yaga yadda ta rikice wanda hakan zai tabbatar maka da cewa lallai bata da gaskiya koda na kwayar zarra ne, ba tare daya sake kallonta ba yace"Wani wuri zaki rakani daga nan sai mu koma asibiti…" miyau mai ɗacin gaske ta haɗiye kan tace muryarta na mugun shaking"Ina....ina...ke...kenan...?" sosai ya haɗe rai tamƙar bai taɓa sanin dariya ba yace"Malama karki cikani da tambayoyi idan mun isa kya gani da idonki...." daga haka babu wanda ya sake cewa ɗan"uwansa ci kanka, kowanne da bikin da yake da zuciyarsa, tashin hankali da damuwa suka cika mata zuciya, lokaci zuwa lokaci take zazzaro idanu tana dube dube, basai an gaya maka ba don kai kanka akallo ɗaya da zaka mata zaka karanto rashin gaskiya atattare da ita, tuni Mustapha ya daɗa sarewa da wannan al"amarin don babu tantama matar tasa ta aikata abunda yake zarginta akai ne wato bin mazan waje…babu zato kawai yaji wasu zazzafar hawaye sun wanke mishi fuska,
" *MATATA* ya zakimun haka bayan na aminta dake...?azatona kina kaunata kamar yadda nima nake kaunarki! azatona kin rikemun amana tamƙar yadda ni na riƙe miki………ashe ashe duk mafarki nake sai ayanzu na farka……kinci amanata *AZEEMA* …" ya ida magana tare dasa hannu yana goge hawayensa, bata ma san yana yi ba don ita kanta tayi nisa ne acikin tunani,
Tun sanda kasim yaga sun haura titin 5-star hotel sai yaji kawai hankalinsa ya tashi ainun,amma sai yayi kokarin kwantarwa kansa da hankali har yake fadin cewa watakila ba nan zasu ba, cigaba yayi da binsu abaya ba tare da saninsu ba,kadan ne kawai ya rage zuciyar Azeema batayi bindiga ba tsabar tashin hankalin daya daɗun mata na ganin yana zuɓa horn ah daidai gate ɗin 5-star hotel,kafin takai ga magana taga an wangale musu kofar,babu ɓata lokaci ya danna hancin motar zuwa ciki,ah parking lot ya paka motar sannan ya dubeta yace"Sakko muje...." sai kallonsa take ta kasa magana sabida tsananin mamaki, cike da fargaba tace"Hotel..?musty mai zamuyi ah hotel kuma...?inma haƙƙinka kakeson karba ai muna da gida da can ɗinne muka tafi ammh bawai muzu nan mu zubarwa kanmu da mutunci ba, yanzu mai kake tunanin mutane zasu fassara akaina…?kallon karuwa fa za"ai mun........"
Danne takaicinta yayi sannan yace"In banda shirmenki karuwai ne kadai ke ziyartar hotel...?ke inama ruwanki dasa idon mutane tunda kinsan cewa ke ɗin ba karuwar bace, da auranki dadin daɗawar ma tare da mijinki kike…?" cike da karin tashin hankali ta sake cewa"Hmmm Mustyna bazaka gane abunda nake nufi bane, kasan bamu taɓa zuwa hotel ɗin bane shiyasa ammh muje idan har hakan shine zai faranta maka…" ta fada tana dubansa don masifar ƙaunarsa take,sam bata jindadin sabon attitude ɗin da yake gwada mata, tana son ganin sun koma kamar da yadda suke mutuwar son junansu, babu fada balle zagi, atsakaninsu mutunta juna ne da kuma soyayyar da sukewa junanmu,
Ƙala bai sake ce mata ba yafita itama ta buɗe kofa ta fito, suka dumfari entrance door ɗin kowanne da abunda yake sakawa yake kuma warwarewa,kasim kuwa tunda yaga sun shige wannan hotel ɗin yaja wani wawan burki yana fadin"innalillahi wa"inna ilaihi raji"un shikenan ta faru ta kare, ruwa ya karewa dan kada, asirinmu yau ya tonu....?" ya furta cike da tashin hankali tamkar zai saki ɗan marayan kuka, dakyar ya iya jan machine ɗin zuwa gaban wani ƙatoton pharmacy wanda yake kallon hotel ɗin ya paka, sauka yayi daga machine ɗin yana dube duben hotel ɗin amma sai dai baya iya hango activities dake gudana aciki kasancewar the gate is locked, daka ganshi kaga mara gaskiya anan, shigewa cikin pharmacy yayi don muddin ya tsaya awaje tofa idan suka fito zasu ganshi, hakan kuma zai taimaka wajen karasa jagula al"amarin, lokaci zuwa lokaci yake kai duba ɓangaren hotel ɗin daga inda yake tsaye,
shigarsu ciki yayi daidai da bayyanuwar wannan receptionist ɗin wanda akwanakin baya ya taimaki Ƙasim ya tayashi siyo kaya ah boutique, yana ganin mustapha ya washe hakora don bazai taɓa manta da fuskarsa ba kasancewar yaɗan mori wani abu daga gareshi, wato daya bashi wasu ƴan canji sanda ya aikeshin,karku manta kamaninn mustapha da kasim har ya ɓaci toh shiyasa receptionist ɗin ke mistaking nasu,
dasauri ya nufo mustapha yana washe hakora al"amarin daya jefa shi mustaphan cikin tsananin mamaki, koda ya bashi hannu don musabaha dakyar ya iya bashi nasa hannun, jansa gefe receptionist John yayi yace in a low pitch"Sir na aza ko bazaka sake waiwayar hotel ɗinnan bane, wallahi jiya na gama yanke shawarar kona kayan girlfriend ɗinka don na rasa yadda za"ai na sameka na baka su……" cike da rashin fahimta mustapha yace"Ban fahimceka ba...wata girlfriend ɗin sannan wasu kayan kake magana kenan…?"
Dauke fara"arsa John yayi,cike da tsantsar mamaki yake fadin"Haba sir ya kake abu kamar ka manta dani...?koba kaine *KASIM MUNNIR* ba…?bcuz the very last time i checked the record book sunan dake kai kenan, kuma i could still remember ur face kaine dai ka kama daki mai lamba 105 har kuma ka aikeni siyan wasu kaya anan nearby boutique, bayan wucewarka dana koma don kimtsa dakin shine naga wasu kaya ayashe akasa wanda babu tantama na budurwar da kukazo tare ne......"
dafe kai mustapha yayi yana mai ambaton kalmar innalillahi wa"inna ilaihi raji"un,babu tantama wannan mutumin na mistaking ɗinsa da kasim ne, tunano abunda ya faru some minutes ago yayi, wato sanda ya kama kasim na taɓa fuskar matarsa, ya ilahi...! doz dat mean kasim na having affair da Azeema kenan...?da sauri kuma ya kawar da wannan kazamin tunanin daga ransa don aganinsa matarsa bata taɓa cin amanarsa ba, ko abunda ya faru adazu tsakaninta dashi kasim ɗin tsautsayi ne, sai dai kuma menene tazo yi ah hotel akwanakin baya...?he really have to find out kuma mafita dayace kawai shine ya yadda kawai shine kasim munnir ɗin don sosai yake son ganin wa"ennan kayan budurwar, inma na Azeema ne duk zai sani.....amma ko kadan baya fatan hakan ya faru.....
Cike da dauriya yace da John"Yes yes i could still remember, nagode da addana dama shi nazo karba jeka kawomun...." da sauri John ya juya ya shige wani store inda suke ajiya, wucewarsa yasa Azeema matsowa kusa dashi atsorace tana fadin"Mustyna wai kus kus ɗin mai yake maka ne…?" ba tare daya dubeta ba ya sauke ajiyar zuciya yana fadin"Shi ɗin abokina ne kuma nazo ƙarban wani sako ne awajenshi…"
Ba don ta yadda ba taja baki tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido…
***
Akalla an samu kusan 30mins kenan da discharging ɗin Gidado don matsawa yayi yace alan dole sai an sallameshi ayau, babu yadda ba"ayi dashi ba akan ya hakura zuwa koda gobe da safe ne ammh yace fafur shifa sai an sallameshi, haka babu yadda suka iya suka mishi abunda yakeson tunda jikin nashi akwai kyau sosai,family house direct aka nufa dashi wanda umarni ne daga tsoho, tun ah asibitin aka gaya mishi cewa Baba Munniru shi ya rasu don ya matsa ne sai an fada masa inda yake kasancewar yaga shi Baba Harunar amma bai Baba munniru ba shiyasa ya matsa yace"meyasa kuke ɓoyemun ne…?in mutuwa ne yayi afadamun man...?atunaninku bazan yi tawakkali ga Allah bane ko yaya...?ai mutuwa tana kan kowa kuma koba jima koba daɗe tana nan zuwa agaremu duka…"
Sai kuma duk jikinsu yayi sanyi toh shine suka gaya mishi, Haƙiƙa kusan zan iya cewa yafi kowa jin zafin wannan mutuwar don hauka ne kawai bai yi ba, tuni yaji wani irin muguwar tsanar kasim da Azeema ya sake samun gurbi acikin zuciyarsa,sai fadi yake yana daɗa nanatawa"kasim mahaifinka yabar duniyar cike da tsananin son jin abun tirr ɗin daka aikata, gashi Allah yadau ransa ,ya tafi da tsananin jin kishirwar wannan al"amarin....cewa yake yana dada nanatawa _Suleiman ka gayamun abunda ɗana ya aikata,inaso in sani koda kuwa hakan na nufin zan sadaukar da rayuwata ne akai😭_ abunda yayi ta fada kenan ga Baba Haruna atambayeshi....."
Ya fada yana cizgar kuka sai dora laifin akansa yake tayi don aganinsa ɓacin ransa ne ya haifar da hakan har ya zamo sanadin da ƙanin babansa ya rasa rayuwarsa, ammh sai aka zaburar dashi aka nuna masa cewa dama can lokacinsa ne yayi, matsa masa sukai akan dole sai ya fadi musu abunda ke faruwa, kuma ya zamar masa dole ya fallasa asiri koda kuwa baza"a yadda dashi ba, akaro na uku daya sake tambayar inda mustapha ya tafi...."
Tsoho ya dubi su Baba Alseny yace"Wai har yanzu layin mustaphan bai shiga bane...?" Baba Alseny yace"wallahi fa shiru kake ji tsoho har yanzu dai....in banda ɗan banzan yaro ma zai fita tare da matarsa ai sai yace mana ga inda zasu ammh sunyi fitarsu kai tsaye ba tare da sanin kowa ba……"
"shi kasim din fa ina dan iskan ya shige ne...?don yana dakyau ace yana nan wajen kasancewar shine tushen faruwar komi...."acewar Goggo Boddiya cike da zafi....
"Hadda Azeema matar mustapha....kuma Inda hali zanso ace itama ɗin tana nan don al"amari ne wanda ya shafeta......" haka suka ji Gidadon ya furta with full seriousness.....cike da tsantsar mamaki suke binsa da kallo zuciyoyinsu cike fal da tambayoyi kala kala akan taya Azeemar take da alaka da wannan case ɗin…………?
_*insha Allahu zaku samu karin update zuwa yamma……true fans ku cigaba da bibiyata muje sannu sannu dont rush...ILYSM❤*_
_*HAFFY MOUSTY🌷*_
_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_
_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_
_*KISHIN MATA...!*_
_Na marubuciya Hafnancy..._
_akan naira 200kacal👌_
_ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_
_*💫BABI NA TALATIN DA SHIDDA...💥*_
…………Tunda Mustapha ya fito daga cikin hotel ɗin ya nemi wuri ya paka mota gami da kifa kansa asaman sitiyari yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa kuma ba komi bane ya haifar masa da hakan ba illa black nylon ɗin da John ya bashi, duba ɗaya ne yayiwa kayan ciki idanunsa suka gano favourite threequarter da kuma ficiciyar rigar matarsa wanda tafiso aduk cikin kayan shan iskanta, yawanci ma tafi saka masa su idan yana gari kasancewar shima ɗin sosai yake son ganinta acikinsu tsabar ƙyan da yake mata, innalillahi wa"inna ilaihi raji"un ashe dama kasim yana iya cin amanarsa har haka...?mai yayi mishi ne arayuwa da har ya zabi kuntata masa ne har haka...?idan har ita zata iya cin amanarsa baya tsammanin hakan daga gareshi kasancewarsa na dan"uwansa,meyasa...?wacce irin bakar rana ce haka mai munin gaske tazo agareshi ne haka...?wasu hawaye masu radaɗin gaske ne suka ziraro mishi,
Azeemar duk hankalinta atashe yake don ya hana mata kallon abunda ke acikin nylon ɗin,saka ledar yayi atsakanin cinyoyinsa sannan ya haɗe kafafunsa hakan yasa ta kasa samun damar daukarta don ganin abunda ke ciki……cike da rawar murya mai nuna tsantsar ɓacin rai mabayyani tace"Haba mustyna wai mai yake faruwa ne...?menene bakason na gani acikin ledar ne ehhhh!?" dago dakai yayi yana mai kokarin son yaga ya daidaita bugawar zuciyarsa don gab take da bugawa idan har bai yi hankali ba,kwakulo murmushin dole yayi kana yasa bayan hannu yana share hawayensa,kafin yakai ga magana sai ga kiran Baba Alseny na shigowa hakan yasa hankulansu komawa ga wayar, kwata kwata tashin hankali ma yasa ya manta da batun dan"uwansa dake cikin yanayin rayuwa ko mutuwa, dasauri ya daga wayar ko kafin yakai ga magana yaji saukar amon maganar baba Alsenyn cikin dodon kunnuwansa"wai kai ina ka shige ne anata nemanka ba"a ganga ba...?layinka ma duk bata shiga mai ke faruwa ne...?"
Tabbas alokacin da suka isa hotel ɗin shida kansa ne ya sanya wayar ah flight mode don bayason akatse mishi abunda zaiyi kasancewar ya kunna audio recorder sabida ta kwasar masa duk wata tattaunawar da zaiyi aciki ba tare da sanin kowa ba, sai da suka fito bayan yayi saving recording ɗin asannan ne ya cire wayar ah flight mode hakan ya baiwa ƙiran Baba Alseny damar shigowa awannan karon, sosa ƙeya yayi yace cike da dauriya don bayason ya fahimci cewa yana cikin damuwa"Yabba kayi hakuri ina jin sharrin network ce...yanzu haka ma ina kan hanyar komowa asibitin ne wani sako naje karbowa..." katseshi baba yayi"Wani asibitin kuma..?Tsohon magana kenan ai mun kusa awa guda kenan da komawarmu gida,dan"uwanka ya samu lfy yanzu haka ma shi yace anemo masa kai don haka maza ka hanzarta zuwa..."
Ai tuni wani bakin cikin da yake ciki ya gushe ayayin da farin ciki ya mamaye gurbinsa, yace yana fadada fara"arsa"Alhamdulillahir rabbil alamin, Yabba yanzu kana nufin Hamma Gidado ya farfado kuma ya samu lfy...?toh ka bani shi inji muryarsa don in gasgata zance..." bai ci masa musu ba ya ya mikawa Gidadon waya, Gidado na kange waya akunne yace"Dan"uwa kazo ina jiranka.....Allah ya sake aramun wani ran da kuma dama akaro na biyu..." hannu mustapha yasa abaki yana kokarin danne kukan dake neman cin ƙarfinsa,cike da farin ciki yace da rawar murya"Alhamdulillah dan"uwa Allah abun godiya, ka yafemun duk nine silar shigarku cikin wannan halin, sila kuma ga mutuwar Baba munniru...."
Saurin katseshi yayi yana mai girgiza kai"kul mustapha kar in kara jin zance makamancin wannan ya sake fitowa daga bakinka...menene haka sai kace baka karanta ka sani ba...?inason kasan cewa dama can tun fil"azal Allah ya rubuta cewa hakan zata faru damu sannan kuma shi Baba Munniru lokacinsa ne yayi shiyasa ko sakwan bai ƙara ba yakoma ga mahaliccinsa, takaici dai ayanzu bai wuce yadda ya tafi da tsananin kishirwar son sanin abunda dansa Kasim ya aikata ba....." wuta ne kawai ya daukewa Mustapha gabaki daya sai yake jin tamkar na"urorin jikinsa sun bar aiki ne, Kasim kuma...?akaro na biyu...?doz dat mean ba"a hotel kadai ma suke haduwa ba hadda cikin gidansa yakan je..?kenan dama can yana da dangantaka da abunda dan"uwan nasa keson nuna mishi agidansa...?ko shiyasa Azeema ta kora maigadinsu..?kuma koda ya nemi jin ba"asi bata wani bashi gamsasshiyar dalilin korar tasa ba hakanan kuma ta dauke masa hankali ga kokarin bin kafarsa,
Koda wasa kuma bata bari ya ajje wani maigadin ba, toh dake yana masifar sonta shiyasa yake mata abunda takeso duk da cewa shi karan kansa abun ya dade yana bashi mamakin ta yadda za"ayi mace kamarta tayi ta zama ita daya acikin makeken gida haka don har zuby kanwarta ma bata nuna masa kamar iyayenta sun hanata zuwa bane kuma,lallai kam ga abu nan ya fito baro baro ba shakka Kasim da Azeema amanarsa ne suke taci ah ɓoye....amma for how long…?
tambayar da yayiwa zuciyarsa kenan amma bashi da wanda zai bashi amsa ayanzu har sai yaje yaji ta bakin shi Gidadon tukunnah, harga Allah yama manta cewa waya yake sai ji yayi yace"Mustapha bakya jina ne...?toh sai ka karaso dai muna family house..." kafin yace wani abun ya datse call ɗin,cike da tashin hankali Azeema tace da rawar murya"Hamma ne ya farfado...?"
"Ai kinji da kunnuwanki..." ya bata amsa atakaice yana danne dannen wayarsa, bata sake cewa wani abun ba taja bakinta tayi shiru ammh damuwace fal ranta, haka kuma kallo daya ne zaka mata ka tabbatar da cewa babu gaskiya atattare da ita duba da irin yadda ta fige ta kuma lalalace ayinin yau zirr,yadau tsawon mintuna biyar yana danne dannensa kafin daga bisani ya yaja motar sukayi gaba, ba"a wani jima ba sai ga kiran Abbanta na shigowa, gabanta ya tsananta faduwa ta dubi Mustapha ammh sai ya dauke fuska yacigaba da tukunsa, yayi kamar bai san ma ana kiran nata ba,
"Abba ne..." ta fada tana kallonsa,cikin halin ko in kula yace"Toh ina ruwana...?" sosai ta shaƙa da wannan cin fuskar da yayi mata ammh sai ta batsar tayi picking, bayan sun gaisa yake cewa"Yanzu naga sakon mijinki wai yayansa ya farfado kuma yana family house, wallahi Azeema don dai dakwai sauran mutunci ne atsakani in ba haka ba kinji na sake cewa wallahi da babu inda zamu je, yanzu zamu shirya mu taho tare da maminku don asakonsa yace zaiso ganinmu akwai tattaunawar da zamuyi mai matukar muhimmanci...don