Showing 90001 words to 93000 words out of 102125 words

Chapter 31 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

1850

rainin hankali in ba dan iska ba mune ma zamu biyoshi bashi ba...?dake kin bashi damar ya rainamu ko...?ba damuwa Allah yasa sakinki ne zaiyi don dama har yanzu bawai na hakura bane da haɗaki da wanda raina keso ba……"

Baki ta rike tana fadi da rawar murya"A"uzubillahi Abba wai meyasa kake fadin wannan maganar ne haka...?sa....." sai kuma taja bakinta tayi shiru don batason Mustapha yasan abunda suke tattaunawa da mahaifin nata, bata san cewa nan ya riga da yaji komi ba kawai karfin hali yakeyi ammh kam sosai ya shaƙa da zagin da yayi masa, zancen saki kuma daya ji ya furta abun har yaso bashi dariya yace aransa"wayyo Allah kai rikicin duniya dai da mai rai akeyinsa...mai kake ci na baka na zuba ne...?badai saki shine matsalarka ba...?toka kwantar da hankalinka don da dukkan alamu ƴar taka ta siyesa da farashi mai tsoka…ka jira nan da wasu mintoci ko awanni zata zamo free woman...."

Ya ida maganar zuci gami da sakin murmushi wanda ke nuni da cewa ta karfin hali ce, daya bangaran zuciyarsa kuma yace"Dama ashe Azeemar tana cikin halin tsangwama da matsi daga wajen iyayenta shine bata taɓa gigin fada masa ba…?azatonsa damuwarta shima damuwarsa...?azatonsa suna iya sharing problems ɗinsu sa"annan su magance matsalar atsakaninsu...?ashe shi ɗin ba kowan kowa bane awajenta…?kenan bata taɓa sonsa ba…?dama iyayenta so suke ta rabu dashi su aura mata wanda suke so…?ammh sabida meh..?zaiso yasan dalilinsu na kokarin hakan,

 

sosai ya addabi zuciyarsa da tambayoyi barkatai dai masu bukatar gamsassun amsoshi wanda har bai san sanda ta gama waya ba sai ji yayi tana fadin"Yaushe ka aikawa Abba da sako..?sannan kuma wacce tattaunawarce kakeson kuyi da har yasa kace kana son ganinsu...?aganina ko menene bai dace kace kai kanason ganinsu ba domin kuwa yin hakan raini ne yafi kai kaje ka samesu…" ajiyar zuciya mai zafi ya saki kan yace"permit my bad manners ammh yana da matukar muhimmanci yaji wannan tattaunawar……"

Daga haka bai sake cewa da ita komai ba, sai damunsa da tambayar abunda ke faruwa kawai take tayi ammh ko kara bin takanta bai yi ba har suka iso gida, isarsu bada jimawa ba sai ga Iyayen Azeemar suma sun iso wanda saida kowa ya sake cika da tsananin mamaki, atake akasan cewa wani babban al"amari ne yau yake shirin kunno kai, da yawa sun danganta hakan da cewa watakila Mustaphan da Azeema sun dan samu matsala ne ammh shi kuma Kasim menene nashi dasu...?wannan shine tambayoyin da kowa keta yiwa kansa,babu jimawa shima Kasim din ya shigo don daga baya anzo an kirashi ance ya taho family house an sallami Gidado, da rashin kuzari ya shigo makeken falon, ganin kowa yayi cirko cirko an zuba uban tagumi ana jimami sai hankalinsa ya dada tashiwa, bama kamar sanda ya hada idanu da Azeema wacce kana ganinta kasan nata ya riga daya kare, tuni zuciyarsa ta soma tsalle tsalle don ba shakka asirinsun ne ya tonu...sai barka da zuwa kowa keta mishi kasancewar shi kadai ne ake jira, don tsabar iskanci irinna Aliyu hadda dakko masa kujera ya ajje yana fadin"Mr.Chairman sir you are welcome...pls have a sit..."

Ya fada yana nuna masa kujerar da ƴar yatsa hakan yasa ya daɗa sarewa da lamarin don da gani wannan honouring ɗin da ake masa bata lafiya bace, babu ɓata lokaci Gidado ya zayyane musu komi na zancensu daya awannan ranar agidan shi Mustaphan, babu abunda kake ji sai kalmar innalillahi wa"inna ilaihi raji"un, masu karyayyen zuciya hadda kukansu, mustapha kam ba"a maganarsa don da"ace za"a iya dubashi ahalin yanzu toh kuwa babu abunda zai hana ace yana shirin kamuwa da ciwon zuciya, su mutanen naku kowannensu su bibbiyu bazan iya misalta muku kalar tashin hankalin da suka shiga ba, Azeema tayi ɗan karfin halin miƙewa tsaye tana kokarin haɗiyar kukanta tace"wallahi ƙarya yake karku kuskura ku yadda da zancensa Allah sharri yake mana………"

Kafin ta karashe maganarta taji kawai an dauketa da wani irin mahaukacin mari,Mustapha yace yana mai binta da kallon tsana"Dan"uwan nawa ne yake karya..?don baki da kunya ki dubi tsabar idanunsa kice yana karya...?keda kanki ma ai kin riga kin nuna mun rashin gaskiya atattare dake ayau ɗinnan kawai, harda taɓa fuskarki dana kamashi yana yi shima ɗin karya ne ko…?toh idan kince karya yake yanzu za"aji gaskiyar zancen ai dakyau...."

Ya ida magana tare da zaro wayarsa kowa yabi hannunsa da kallo, voice record ɗin daya yi ne ya kunna, kuma clearly kowa ke jin tattaunawarsa da John………  _"Sir na aza ko bazaka sake waiwayar hotel ɗinnan bane, wallahi jiya na gama yanke shawarar kona kayan girlfriend ɗinka don na rasa yadda za"ai na sameka na baka su……"_ muryar mustapha suka ji yace _"Ban fahimceka ba...wata girlfriend ɗin sannan wasu kayan kake magana kenan…?"_

John ya sake cewa _"Sir koba kaine *KASIM MUNNIR* ba…?bcuz the very last time i checked the record book sunan dake kai kenan, kuma i could still remember ur face kaine dai ka kama daki mai lamba 105 har kuma ka aikeni siyan wasu kaya anan nearby boutique, bayan wucewarka dana koma don kimtsa dakin shine naga wasu kaya ayashe akasa wanda babu tantama na budurwar da kukazo tare ne......"_

Kai gabaki ɗaya saida suka ji tattaunawar tasu, kadan ne kawai ya rage fitsari bai bulle musu ba, sai salati kowa ke tayi ana tafa hannaye, masu la"antar dasu da kuma tirr dasu nayi, haka ma masu jimami nayi, hawaye masu radadi ne suka wankewa Mustapha fuska yace yana binta da kallon tsana voice ɗinsa na mugun shaking"ko shima zaki karyata hakan ne..?ko bayan na nuna hujja ta karshe shima ɗin zaki sake karyatawa ne…?

Ya ida magana tare da firdo kayanta dake cikin black nylon, waro idanu kowa yayi har ita kanta don ruwa ya riga daya karewa ɗan kada, daga ita har Kasim basu da wata kalma ko dabarar kare kansu don dubu ya cika, kwana cassa"in da tara na barawo, kwana ɗaya rak kuma na mai kaya……



"Azeema!kasim! Kunci amana....innalillahi wa"inna ilaihi raji"un..." shine abunda mutane keta fadi suna kuma nanatawa,kuka sosai mustapha keyi mutane na tayashi,Tsoho wanda wuta ta dauke masa nadan wucin gadi ne ya mike afusace yana fadin"Kai mustapha menene kake yi ne haka...?ka rasa wani naka balle wannan...?bance ba al"amari bane babba ammh maza taso, yaka nan kaji......"



_*HAFFY MOUSTY🌷*_

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

_*KISHIN MATA...!*_

_Na marubuciya Hafnancy..._

_akan naira 200kacal👌_

   _ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

   _*💫BABI NA TALATIN DA BAƘWAI...💥*_

 

……miƙewa yayi daga tsugunnon da yayi, sannu ahankali ya nufi inda kakan nasa yake tsaye cike da rashin kuzari, kowa awurin sai daya tausaya mishi, mamin Azeema ita kanta kuka ne take ta sharbawa tana zagin Azeemar, Abbanta kuwa shiru yayi cike da jimamin wannan abun kunyar da ƴar tasu ta ɗebo masu (bayan kuma kuna da hannu aciki,ina jin mantuwa yayi komu tuna masa ne?)Goggo Binta tace tana cizgar kuka"Mustapha Allah ya saka maka..!"  hakan ne ya kara rura wutar baƙin cikinsa, dakyar ya isa ga Tsoho ya rungumeshi gami da fashewa da wani sabon kukan mai taɓa zuciya yana fadin"kaka meyasa Azeema da kasim zasu mun haka...?mai nayi musu ne...?"

Shi karan kansa Tsoho dauriya ce kawai yake yi ammh ji yake tamƙar ya wangale baki ya rafka uban kuka son ranshi don kakaf zuri"arsa babu wanda ya taɓa kafa kazamin tarihi na abun kunya kamar su Ƙasim,hannu yasa ya shiga bugun bayansa yana lallashinsa, sai daya samu yadan natsu sannan ya soma jawabinsa"Haƙiƙa *CIN AMANA* hali ne dake nuna cewa muna acikin kwanakin ƙarshe aduniya, *CIN AMANA* yana daga cikin halayen munafurci, *CIN AMANA* yana daga cikin abubuwan dake tauye imani da kuma tauhidin mutane, matuƙar mutum zai riƙa cin amanar mutane, toh tabbas imaninsa raguwa yakeyi awajen Allah mahaliccinsa, *CIN AMANA* na daga cikin halayen dake qasqantar da darajar mutum awajen Allah SWT, matuƙar mutum ya riƙa cin amanar bayin Allah, toh Allah ne zai zamo abokin rigimarsa agobe ƙiyama, haka kuma *CIN AMANA* yana sanya mutum yayi baqin jini acikin al"ummah, darajarsa, Qimarsa, mutuncinsa da komai ma zasu zuɓe ne ah idon duniya, sannan kuma al"ummah zasu ta gudunsa tamƙar mahaukaci ko wani dodon, abunda zaifi girgizaku shine ita *CIN AMANA* tana zama sanadiyyar dulmeyewar mutum acikin wutar jahannama kamar yadda yazo acikin hadisi ingantacce 'Allah zai sanya amana acikin qarqashin wutar jahannama sa"annan amurci maciyin amanar da cewa ya shiga ciki ya dakkota, sai ya dakko ya hauro wani babban tudu wanda acikin wutar take sannan sai kuma ita amanar ta kuɓuce ta koma can kasar wutar jahannama, sai mala"iku su daka masa tsawa suce yakoma ya dakkota, haka zai tayi har ila masha Allah……"

Dakatawa yayi yana sauraron koke koken mutane don sosai jawabinsa ya ratsa zukatan kowa awurin, Azeemar da kasim sai sharba kukan nadama sukeyi wanda dama can ai ita dana sani ƙeya ce,Tsoho yacigaba da jawabinsa cike da raunin zuciya"Ƙasim tabbas ka kafa kazamin tarihin da wani acikin zuri"ata bai taɓa gigin yi ba, ashe duk akuyancinka da nake ji ana fada ya wuce girman tunanina...?har zaka iya haɗa shimfida da matar aure…?matar auran ma ta dan"uwanka...?Ya ilahi wannan cin amanar da mai yayi kama don Allah...?har tsawon yaushe ne ma kuka dauka kuna cin amanar…?"

Shiru suka masa suna cizgar kuka, kowanne hawaye da majina ya ɓata mishi fuska, Baba Alseny ne ya taso masa yana mai daga mishi tsawa"Ba daku ake ba kunyi shiru...?" dasauri Yabban Gidado yakamoshi ya zaunar dashi yana fadin"Haba ƴan biyuna mu bi komai asannu muji ta bakunansu don bamu san dalilinsu na aikata hakan ba, daukar zafi bazaiyi maganin komai ba illa kara assasa wutar al"amarin domin kuwa aikin gama ya riga ya gama, Alseny mu lallashi zuciyoyinmu, nasan da ciwo sosai ammh mu dauki hakan amatsayin tasu kaddarar kenan...." ya ida magana cike da raunin zuciya uwa zai saki ɗan marayan kuka, sosai kalamansa suka taimaka wajen sanyaya zukatan yawancinsu anan, sai da Ƙasim ya tabbatar da kowa ya shiga taitayinsa, ya zamana shessheƙa kawai ake ji daga masu raunin zukatu, sa"annan ya budi baki dakyar yace"Akalla mun kwashi kusan watanni biyar kenan muna cin amanar Mustapha, sau ɗaya ne muka taɓa haduwa ah 5-star hotel inda shi Mustaphan yaje aka bashi wa"ennan kayayyakin nata da muka manta dasu,toh ina ganin sabida tsananin kamar da nake dashi ne yasa receptionist ɗin tunanin ko nine Mustaphan, sauran affairs namu kuma ah gidansa ne mukayi.......don Allah ka yafemun banso biye mata ba sharrin shaiɗan ne wallahi"



Afusace Mustapha ya dubeshi yake fadi da zafi"Komai idan mutum ya aikata wanda ba daidai bane sai kaji ya budi kazamin bakin nan nasa yace wai sharrin shaiɗan ne, in baka bashi dama ba da kuma nuna masa cewa kaima ɗin irinsa ne ba zaiyi gigin zuwa inda kake nema balle ya jefaka cikin masifa…?ka sani shaidan zai hau munbari agobe ƙiyama alokacin da ƴan wuta suka shiga wuta, ƴan aljannah kuma suka shiga aljannah, sai yace bayan an gama gudanar da duk wani al"amari na hisabi da sauransu _*'Lallai Allah yayi muku alƙawari, alƙawari na gaskiya ni kuma nayi muku alƙawari na ƙarya, sai kuma nazo na saɓa muku, bani da wata hujja agareku sai dai na kirayeku kuka kuma amsa mun, kada ku zargeni ku zargi kanku, ayanzu haka ni bazan iya tsinana muku komai ba haka kuma ɗin bazaku iya tsinana mun komai ba, komai nina kafurce da shirkan da kuke yi mun tun can, kuma Allah yana fadi cewa lallai azzalumai suna da azaba mai radadi kuma sai na kasance acikinsu, toh ni kuma bazan dandani wannan azabar ni ɗaya ba shiyasa na nemo abokan tafiya, kune kuma wa"enda na kiraku kuka amsa mun da cewa lallai zaku bini....'*_ toh ka gani ka sani cewa babu wani sharri da shaiɗan ya nufeka dashi illa kai da kanka ka amsa mishi kuka aikata barna……"

Juyawa yayi ga Azeema wacce take duƙe sai faman kuka take sharɓawa, ji take tamƙar kasa ya buɗe ta afka ciki tsabar wannan abun kunyar,cike da tsana Mustapha yace"ke kuma tsakanina dake babu yafiya tunda har kika iya kai wani ƙaton gardin kuka sheƙe aya akan gadon auranki, gadon da muke kwanciya akai muke raya sunnar ma"aiki shine kuka kazantashi, kikamun ƙarya wai awannan ranar daga saloon kike ashe daga wajen aikata alfasha kika fito, wallahi da"ace awannan lokacin nasan kin kwaso kafirin kazanta ne da bazanyi gigin kara haɗa jiki dake ba, ko alokacin bawai na yadda da abunda kika fada bane kawai nadai share ne, toh dayake shi Allah ba azzalumin kowa bane, sa"annan bani da hakkinku shiyasa ya tona asirinku ya bayyana gaskiya, kai Azeema! Kasim kunci amanata kuma Allah ne kawai zai kwatar mun hakkina gobe ƙiyama……"

Ya ida magana gami da rushewa da wani salon kukan mai taɓa zuciya,har Tsoho na kokarin magana sai suka ji tace"Meyasa kowa sai haushi yake akanmu ba tare daya tambayeni dalilina nayin hakan ba...?ku sani akomi na rayuwa baka taɓa yinsa saida dalili, meyasa wasu mutanen ke neman ilimi har kuma suyi amfani dashi...?ba don su tsira agobe ƙiyama bane…?meyasa wasu ke taimako..?ba don suma Allah ya saka musu da abunda yafi taimakon da su sukayi bane...?haka zalika ta ɗayan ɓangaren munanan ayyukan ana yinsa ne tare da dalili, ko zaku cemun shi ɗan fashi bashi da dalilinsa na fadawa harkan fashi…?mashayin fa...?shin shima baida dalilinsa...?ita kuwa karuwar fa..?atunaninku bata da dalilinta da kwakkwarar hujjarta ta fadawa aharkan karuwanci ne...?toh meyasa nima ba"a nemi jin nawa dalilin ba kowa sai cewa yake munci amana munci amana, tawa kaddarar kenan shin ku kunsan naku...?kun san ta yadda zaizo muku...?wallahi nayi imani da Allah da yawanku anan sai tawa kaddarar tafi ƙyau akan naku, nobody knows my reason for sleeping with my husband's brother and none of you cares to know, abunda kawai kuka sani shine naci amana…"

Mustapha wanda shine yafi kowa fusata da zancenta yace"And nobody still wants to know, abunda kowa anan yasani shine kedin fasiƙa ce ƴar gidan fasikai wa"enda suka fita daga yin biyayya ga Allah……"

"Haba dan"uwana kar ɓacin rai yasa ka nemi fita daga cikin hankalinka man, ka sani Fushi ko bacin rai na daya daga cikin wasu dabi’u da Allah subhanahu wata’ala ya halicci dan Adam da su. Shakka babu muddin dan Adam yana raye a wannan duniya da muke  ciki toh ba zai iya guje wa abubuwan da suke sanya bacin rai ko fushi ba, sai kuma akace idan haka ne, me ya dace mu yi a duk lokacin da muka ji ranmu ya ɓaci?muyi kokarin shawo kanta ta hanyar danne zuciyoyinmu don ɓacin rai na janyo musifu kala kala ciki kuwa hadda sanya mutum aikata abunda zaiyi dana sani nan gaba, kamar yadda Yabbanmu yace mu lallashi zuciyoyinmu, tabbas al"amarin da ciwo sosai ammh mu dauki hakan amatsayin tasu kaddarar kenan....don haka Hamma Mustapha cool down ur temper, atleast abata dama itama ta fadi dalilinta nayin hakan kamar yadda tace kowani ɗan adam baya taɓa aikata abu kai tsaye ba tare da kwakkwaran dalili ba…sannan kuma inason na zaburar dakai ko kuma ince in tunasar dakai cewa har yanzu amatsayin mata ake agunka, iyayenta wato surukanka suna cikinmu, ka sani duk yadda ɗanka yakai ga aikata abunda ba daidai ba still wannan soyayyar ta ɗa da mahaifi nanan maƙale aransu, don haka babu wanda zaiso awulaƙanta masa ɗa agaban idanunsa koda kuwa ɗan ya kasance shine bashi da gaskiya, sabida haka na haɗaka da girman Allah da kuma darajar naka iyayen daka ɗan sassauta mata kodon darajar idanun iyayenta……"

Ta ida magana tare da hada hannaye tana roƙonsa, sosai jikin kowa anan wurin yayi la"asar da maganganunta mai cike da hikima da kuma ma"ana, gata nan dai karama ah fuska ammh zuciyarta da girma yake, ko shakka babu wannan ɗiya tayiwa yawancin mutane fintikau, ƙyawawan halayenta suna da kamanceceniya dana _*SAURAUNIYA MEELAT GIDADO*_ kasancewar ita ɗin rainonta ce, _*MUBEENAH SULEIMAN SHAGARI*_ kenan ,shi kansa gogan nata wato Gidado sosai ta burgeshi har yake jin kamar yaje ya rungumeta tsam ajikinsa yata shi mata albarka, kuma daya tuna cewa tana dauke da gudan jininsa sai yaji wata sabuwar soyayyarta ta sake samun wani promotion azuciyarsa, idanun mustapha akanta wanda yadan shiga taitayinsa yace" MUBEENAH! cin amanata tayi fa shine har kike cewa in sassauta mata..?don mai zan sassauta matan...?ni tamun adalci ne alokacin da shaiɗan yake ingizata…?ba rufe idanu tayi tabi son zuciyarta ba...?"

Sauke ajiyar zuciya tayi sa"annan tace"Abunda nakeson ka sani Hamma Musty shine, sam mumini kamarka wanda yayi imani da Allah, ya kuma yarda da kaddara mai ƙyau ko mara ƙyau baya maida sharri da sharri, sai dai ya maida khairan ga sharran, haka zalika kuma yakan maida farar aniya ga duk wanda ke nufinsa da baƙar aniya, Hamma Mustapha nasan fa ka fini sani don haka karka ɓatar da sanin naka ka daure, ka kuma danne zuciyarka kayi aiki da ilimin da Allah ya sawwaka maka daidai gwargwado...karka kuskura ka yanke hukunci cikin fushi ka tsaya kaji ta bakinta....."

Sosai ta sake burgewa tamƙar ah sunkuceta sama ata yawo da ita ah iska, sai jinjinawa kaifin hankali da kuma tunaninta kowa yakeyi, Gidado kuma aransa yace"Ya Allah nagode maka daka azurtani da mataye na gari ma"abotan addini da kuma dabi"u, Mubeenah ina mai cike da farin ciki da kika kasance kece zaki zamo *UWAR YA"YANA* ... *JAMILA* DA *HAFSAT* kuma Allah dai yasa kuna da rabo...." duk azuciyarsa ne yake wannan zancen,

Fashewa tayi da matsanancin kuka tana fadin"ba kowa ne ya jawomun kauce hanya ba illa iyayena........" cike da kaduwa iyayenta suka ce"What....??meye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login