Showing 48001 words to 51000 words out of 102125 words

Chapter 17 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

1836

kaiwa Gidado,mai hali dai baya fasa halinsa sai kara cusa mata mugun hali takeyi wanda zata shuka idan ta koma sannan kuma wai karta manta dasu idan ta koma su kudi sukeso ta dunga amso musu awajen mijinta,ammh fa wannan ra"ayi ne na ita mamin banda Daddy don besan abunda take kullawa ba kenan,idanun mami Amina ah kudi yake shiyasa idan yara suka fita muddin zasu dawo mata da kudi tofa babu ruwanta da tambayar inda suka je nata kawai ayagar mata mikkakku,Alh Bilya yana kuka da ita da wannan baƙin halin kuma babu abunda ya iyayi akai don kusan tafi ƙarfinshi ne ammh yana binta da addu"ar shiriya.

**

Tuni su Sagir suka bugo kati aka soma rabawa mutane,dayawa sai mamakin wannan karo auren da Gidado zaiyi sukeyi don yawanci basu da labarin fitar Hafsa,wannan karon babban abokinsa zai samu halarta bikinsa don be samu zuwa alokacin na Hafsa ba sabida ayyuka da suka sha gabansa, ina nufin _*'ACP SALEEM FREAKING KABIR KUMO'*_ megida ran gida agidan Malika angon Zahra'u,shida Saleem tare sukayi training sanda za"a daukesu aikin ƴan sanda,dama ance sai hali yazo ɗaya ne ake abota toh hakan ne ya faru dasu don sun kasance ne masu tsananin ganin kansu da jijji dakai shiyasa suka shaƙu har suka kulla abota,

Shirin biki ake gadan gadan wanda ba"a taɓa yiwa wani irinsa ba acikin zuri"ar kasancewar wannan ɗin yazo ne da wani sabon salo sannan kuma ya banbanta da sauran bukukuwan,wannan auran dangi ne wanda ake kokarin son aga an kafa dadadar tarihi akansa kasancewar shine farko da za"a soma yi shiyasa kowa ya baje bajintarsa don asan ya birge,aka sake furnishing gidan Gidado dakyau komi sabbi aka zuba ammh banda part ɗin Hafsa dake arufe,dama akwai wani extra part dake nan arufe kamar Gidado yasan irin wannan ranar nanan zuwa agareshi na ajje mace fiye da biyu ma toh shiyasa daya tashi tsara gidan sai yasa akayi 3 parts,agaskiya an nunawa Baddo gata don part ɗinta kai kace ko gidan wata sarauniyar sarkin makkah ce,sosai Jamila ke rawar jiki da kuma dokin wannan biki kai kace ko ba kishiya ake shirin kawo mata ma,itace hadda gayyato wato kawarta mai gyaran jiki daga maiduguri tazo yiwa Baddo gyaran jiki,ana gobe walima taje ta haɗo set daya na lefe datayi alkawari ta shakesu da kaya takai,gida ya ruɗe da guɗa anata shi mata albarka aka haɗa marun akwatinan data kawo da wanda su baba munniru sukayi nasu ruwan kwai ne sai abun ya bada citta,agaskiya Baddo tayi goshi wasu cousins ɗin nata ma da iyayensu mata har kishinta suke tamƙar su haɗiyi zuciya su mutu,Gidado komi be kada ba awannan biki yabar musu suyi komi tunda sune suka kirkiro abun wanda shi ba"a san ranshi bane za"ayi ammh sai yake pretending yana nunawa jama"a tamƙar yanaso,abun fa be tsayawa Jamila anan bafa saida ta shiga boutique ɗinta ta zabowa Baddo crazy night gowns da kananun kaya wanda zaiyi wuya ace Baddon ta kallesu balle takai ga sawa ajikinta,bayan ta gama zaba tasa yaran aikinta kai mata su mota suka jibge,har ta buɗe driver's side zata shige ta hango Nabeelah da Andrew suna fitowa daga cikin mota,kuma da alamu boutique ɗin zasu shige mai take _*'MEELAT GIDADO BLOSSOM BOUTIQUE'*_ sam Nabeelah bata masan da cewa Jamila nada boutique na kanta ba hasalima Andrew ne yakawota siyan kaya don yana shirin bankwana ne da ita,da azama Jamila ta jawo jakarta ta zaro katina uku donta tabbata su Sagir basu katin bikinsu Gidado ba kamar yadda Tsoho ya umarta,dasauri sauri tasha gabansu ayangance tana jifar Nabeelah da wani irin kallo na kaskanci,Nabeelar taja da baya itama tana watsa mata wawan kallo,suka saka Andrew aduhu kansa duk ya daure,Jamila ta nunata da ƴar yatsarta dayasha shan lalli tace"Nabeelah right..?" taɓe baki Nabeelar tayi gami da jan tsoki tace"A"ah ƙanwar uwarki ce dai,mtsww dallah malama bamu hanya mu wuce makira kawai you must pay for all kuma ki sani yar"uwata nanan dawowa gidan Gidado..." sosai maganganunta suka fusata Jamila ammh dake macece wacce tasan kan duniya saita batsar tare da mirmusawa tace"Ko meh zakice mun kice i dnt care or do i luk as if am scared..?lemme kindly rush into what brought me here,ga kati nan muna gayyatarku bikin jikokin Tsoho....."

Ta cilla mata katin farko ajikinta tana fadin"Gana Hafsa..." katin ya fadi akasa ta sake cilla mata wani shima ya tabi jikinta ya fadi tace"Gana maminku sannan ga naki..." ta karashe cilla mata ɗayan daya saura…afusace Nabeelah tabi katunan da kallo kan ta dago kai ta maida kallonta ga Jamila wacce take kyalkyalar dariyar mugunta tace"Mu ina ruwanmu da bikin wasu jikokin Tsoho..?meh muka haɗa dasu kuma meye namu aciki dahar zaki bawa kowacce acikinmu kati daya daya…?

Dariya sosai Jamila take ƙyaƙyatawa hadda ƴar kwallarta Andrew dai yana ta kallonsu don ba gane abunda suke tattaunawa akai yayi ba,ya kalli wannan ya kalli waccan,Jamila tace"Miss Nabeelah da ruwanku aciki fa hadda tsakinku kuwa don haka kedai dauka kiga sunayen ma"auratan tukunna ma dai.." ta faɗa tare da kashe mata idanu,dasauri Nabeelar ta duƙa ta dauki kati daya ta buɗe tana dubawa,arikice ta dago kai tana duban Jamilah wacce take jifarta da wani irin shu"umin murmushi tace"Gidado da Baddo zasuyi aure...?ar you kidding me...?"

Jamila ta fashe da dariya tace"Find out about it diz coming saturday,kinga na cika miki mafarkinki tasa Baddo zama matar Gidado,ayanzu tana shirin sake samun wani sabon matsayi,isa da kuma iko acikin gidansa,watarana kina ji kuma kina gani sai Mubeenah tasa anyi waje dake...."

Afusace tace"Ita asuwa..?wallahi duka kunyi kadan..." ta faɗa tana rushewa da kukan bakin ciki don ita ta nata take bata yar"uwarta Hafsa ba,Jameelah tace"Ita ah matar _*DCP SULEIMAN ALASSANA GIDADO*_ ..." ta ida magana tare da makala shade ɗinta tana mai haɗe rai wannan karon,daga murya tayi ta kirawo wani yaron aikinta yazo dasaurinsa tace dashi tana nuna Nabeelah"Meelat Gidado's blossom boutique tazo don haka abari ta dauki duk abunda takeso iya son ranta kar'a sake ah karbi ko kwandala daga hannunsu,ki saki jiki ki kwashi kaya ki haɗa hadda dana yar"uwarmu Hafsa,enjoy shopping in _*meelat Gidado's coastal loft*_ and have a nice day...." tana ida magana tasa kai tabar wajen ayayin da yaranta suka bita da kirari,wani irin kukan bakin ciki ne ya kufcewa Nabeelah,tana kallo Jamila ta bawa motarta key tana sake daga mata hannu alamun bye bye hadda kashe mata one eyes hakan ya daɗa fusatata tayi mota aguje da kati ɗaya ahannunta,Andrew yabi bayanta hankali tashe,yaran Jamila nata musu magana ammh ko sauraransu basuyi ba,shopping ɗin da ba'a yi ba kenan suka tafi gida,lallashin duniyar nan Andrew yayiwa Nabeelah ammh taki shiru balle ta masa bayanin abunda ke faruwa.....................✍



~ku shirya muje bikinsu Gidado nayiwa kowacce member anko,anjima da yamma zaku sama second update insha Allah as promised~

_*HAFNANCY😘*_

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

   

_*KISHIN MATA…!*_

     _Na marubuciya Hafnancy…_

         _akan naira 200kacal👌_

_ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

   _*💫BABI NA ASHIRIN…💥*_

……Jamila ce ta shigo falon tana tafiyarta mai jan hankali ayayin da wani security ke biye da ita da wasu uban ubansun paper designer shopping bags guda biyu kowanne kuma shaƙe yake da kaya,ta iske Gidado,Sagir da kuma Aliyu ah falon,Gidado zaune akasa bayansa kuma ah jingine da jikin kujera,daga shi sai farar singleti da wando na shadda,su Sagir kuma suna zaune saman lumtsuma lumtsuman kujerun katafaran falon,sun tasa Gidado ne agaba akan adole saiya basu haɗin kai wajen zaban atleast program ɗaya da za"ayi,shi kuma ya kafe ya kuma tsaya akan tsayin daka yace babu bidirin bikin da za"ayi tunda dai ba auran soyayya zaiyi ba,toh ana cikin hakan ne sai ga Jamila ta fado falon,idanuwansu duk akanta har ta karaso ciki,kowanne da tunanin dayake akanta don sosai tayiwa yawancin mata fintikau,Ta dubi Security ɗin dake binta abaya tamƙar raƙumi da akala tace dashi"Ajje kayan anan nagode..." ta fada tana nuna masa wurin da zai ajjen,bayan ya ajje ya gaidasu Aliyu suka amsa sannan ya fice,Jamila ta dubesu tana ɗan murmushi tace"Best men sannunku ya shirye-shirye..?Allah yasa ayi damu.." Suka amsa da ameen shi kuwa gogan wani uban harara ya watsa mata don shi yanzu tama daina burgeshi sai kayan haushin da take cusa mishi ganin rawan kanta yayi yawa sam bata ma kishinsa,sai yake ganin kamar tama daina sonsa ne,Sagir yace"Uwargida kece dai za"a cewa ya shirye-shirye don ga dukkan alamu ya nuna kina dokin zuwan wannan amarya taki,Allah dai ya baku zaman lafiya..." aka amsa da "ameen..." shi kanshi saida ya samu nasa rabon hararar daga wajen Gidado,Aliyu yadan ja tsokin takaici ya miƙe yana gyara ƙwalar rigarsa yace"Kai man tashi mu tafi donni na tsani rainin wayau haba ata bin mutum ana lallaɓashi tamƙar ƙaramin yaro,ba dole aciki saimu rabu dashi tunda yace bayason ayi kowani shagali dashi tunda auran ƙiyayya zaiyi…" afusace Gidado ya dauki filon kujera ya wurgeshi dashi afuska yana fadin"Haka kaji nace maka..?toh wallahi ka kiyayeni karka kuskure ka kaini gaba nadai gaya maka,na faɗa kuma zan sake faɗa bidirin ne dai baza"ayi shi ba,in kuma mutum zaisa mun kaca ne akafa yakaini wajen toh bismillah..."

kala Aliyu bece masa ba yasa kai ya fice yana jin zuciyarsa na masa wani irin tuƙuƙi,wallahi ko kadan baya ƙaunar halayen Gidado kuma sosai yake tausayawa Baddo idan ta shigo gidan don yasan tabbas zata cutu tunda ma shi Gidadon ya nuna baya sonta,dadinta ɗaya zata samu ɗan sarari awajen Jamila tunda ita tana ƙaunarta ammh shi ko kadan be gama yadda da ita ba,gani yake kamar akwai abunda take shiryawa,bazai taɓa so wani abu ya samu yar"uwarsa ba don dashi da Baddon iyayensu ne suka fito daga ciki ɗaya,saɓanin mahaifin Gidado da nasu iyayen ƴan uba suke,Sagir ya dubi Gidado yace"Daɗina dakai iya wulakanta mutum,yanzu fisabilillahi abunda kayiwa Aliyu ka ƙyauta kenan…?daga gyara kayanka ya zamo sauke mu raba..?toh Allah ya shiryeka,sauran idan abokin cin mushenka yazo ina nufin Kumo ka bari ya hure maka kunne ya doraka akan ɓatacciyar hanya kace zaka dunga wulakanta ƴar"uwarka,oho wannan ya rage naka kuma kaida Allahnka…" yana gama fadar hakan shima yasa kai yafice,yasamu Aliyu awaje wanda ya kumbura sumtun tamƙar zai fashe,haƙuri yayi ta bashi,Aliyu yace"Sagir wallahi ba dadun hannunka be ruɓewa ka cire kayar ba Allah da tuni na yanke yan"uwan takar dake tsakanina da Gidado,sam guy ɗin nan bashi da mutunci ko kadan wallahi ni har tausayin Mubeenah nake don nasan sosai zata cutu…"

Sagir yadan bubbuga kafadarsa yace cikin kwantar da hankali"Kabar damuwa abokina,kamata yayi mu bisu da addu"a sannan kuma ni inaji ajikina cewa Mubeenah zata canza mana aboki kuma na tabbata nan gaba zai sota don ance tsakanin mata da miji sai Allah,yau,gobe,jibi ana banaso banaso zakazo ne nan gaba kaji ana cewa idan bake ba wallahi sai rijiya…kaidai kawai mu zuba musu idanu..." suka bushe da dariya dukansu kana suka fada cikin motar sukayi gaba,

    "Sahibu wai meyasa kake haka ne…?meyasa idan ka kafe akan abu baka jin haƙuri ne…?pls ka bari ayi programme mana ko ɗaya ne… afusace yace"Na rantse da Allah Jamila ki fita acikin idona in rufe,bansan meyasa kema kika cikamun shisshigi ba,ana shirin auramun ƴar cikina ammh you are here trying to throw a celebration,wannan ba abun ƙunya bane azo aga the whole deputy commissioner of police yana auran ɗiyar cikinsa…?"

Itama azuciye tace dashi tana ɗan daga murya abunda bata taɓa gigin masa ba kenan tace"Is that a crime...?prophet muhammad SAW married his  second wife Nana Aisha at the age of 7,bata tare ba saida ta cika shekaru 9 aduniya shi kuma alokacin yana da 53,ka duba shi beyi jika da ita bama...?ammh shi aure babu ruwansa da wannan,agame da al"amarin aure mace bata yiwa namiji tsufa haka zalika shima ɗin baya yiwa mace tsufa,so my dear husband wise up…" tana gama faɗar hakan ta kwashi shopping bags tayi part ɗin Baddo dasu,cije laɓuna ya shigayi tamƙar zaya hudashi ya dunƙule hannu yana kaiwa tafin ɗayan hannunsa naushi,can kamar wanda aka tsikara da allura yabi bayanta afusace,tana gaban expensive wadrope ɗin Baddo mai central mirror doors tana shirya mata kayan data kawo,ta cikin mirror ɗinne ta hango shigowarsa tamƙar wanda aka jefo,sai tayi kamar bata ga shigowar tashi ba ta cigaba da abunda takeyi,bata ji isowarsa kusa da ita ba sai ji tayi kawai ya fuzgo hannunta ya jefata ta fada saman gado,cike da dacin rai yake fadin"wai in tambayeki man Jamila...shin yaushe kika daina sona ne...?ans me now..! when did you stop loving me...?"

Cike da rashin fahimta tace"what sort of question is this..?ban gane yaushe na daina sonka ba..?meh ka gani dayasa ka faɗi hakan...?" jawo karamin stool ɗin dake gaban dressing mirror yayi ya zauna akai sannan ya dubeta yace"Dole ne ince kin daina sona mana sabida duk wata mai son mijinta zata nuna haukan kishinta ne alokacin da mijin ke niyyar ƙaro aure ammh ke da alamun abun ma daɗi yake miki,sai ya zamana ma nine nake ji tamƙar ni ɗinne kike shirin yiwa kishiya tunda na lura kaman son da kikewa yarinyan nan yafi nawa,Allah Jamila karkiso kiga yadda nake baƙin ciki da wannan auran,am not juz ready to accept dat small gal as a wife...." miƙewa tayi ta cigaba da shirya kayan ta bawa banza ajiyarsa tunda ta lura shi yafison ata wasan yara,aiko ya shaƙa ba kadan ba ya miƙe afusace ya fuzge wani yalolon rigar bacci dake hannunta ya jefar akasa yace"Jamila wai meke damunki ne…?anya kuwa bakaken aljanu basu shafar mun ke ba kuwa da har suke neman hanamu zaman lfy…?donni gaskiya abun naki ya daina bani mamaki sai tsoro..." ita abunma har yaso bata dariya ammh sai ta cije taki kuma magana,hakan da tayi kuma ya daɗa fusatashi ainun,yarasa meh zaiyi wanda zai ɓata ranta sai kawai ya isa ga wadrope ɗin yasa hannu ya shiga watso kayan data shirya yana fadi cike da zafin rai"Bata isa tasamun wa"ennan shegunan kayan acikin gidan nan ba donni ba sa"anta bane kuma babu abunda zata nuna mun wanda ban gani ba ajikinki,don haka maza ki kwashe ki mayar dasu naki dakin ko kuma ki ƙyautar,koki maida boutique ko kuma ki kona,whatever..! I dont fucking care,the choice is urx ammh nidai kawai banason na gansu acikin wannan dakin..." girgiza kai ta shigayi tana mai takaicin yadda ya maida mata da aiki baya,aranta tace"Allah sarki Mubeenah Allah dai yasa kici hakurin zama da wannan dan"uwan naki mai murdadɗen hali…"

Tasata yayi agaba yasa ta kwashesu kakaf ta maida nata dakin,aranta tace"Ai in kasan wata ai bakasan wata ba muje zuwa..."

  ***

Andrew na ajje Nabeelah ko sallamarshi bata tsaya yi ba ta shige gida hankali tashe,tsaki yaja ya figi motar yayi gaba abinsa yana ta dura mata ashar don sosai yake jin haushin yadda taki ɗiga masa wani abun,ƙofar  gida ma abuɗe ta barshi tayi shigewarta,mai gadi wanda yadan zaga ne ya fito yana daure tomazagi yaga kofa abuɗe yaja tsoki sannan yaje ya rufe yana fadin"ko wani mahaukacin ne yabar kofa abuɗe oho bayan arufe ya gansa fa..."

Afalo taga mami zaune ta rafka uban tagumi,Daddy da Ya Mukhtar suma zaune saman kujera idanuwansu akan Hafsa dake zuɓe dirshan akasa da katin bikinsu Gidado ahannunta wanda su Sagir suka kawo bada daɗewa ba suka bawa mai gadi wai ya miƙawa mutanen gidan,Hafsa na ganin Nabeelah ta sake rushewa da kukan baƙin ciki tana fadin"Nabeelah kiji irin cin amanar da za"amun wai Gidado da Baddo ne zasuyi aure jibin nan…" fuskar tausayi ta shimfiɗa mata tace"Na sani ammh waya kawo muku katin..?" Hafsa tace cike da zafi"wazai kawo mana in banda wannan munafukin abokin nasa Sagir..?miƙawa mai gadi yayi abun tarin takaicin ma wai kiji wai mami za"a bawa,don kisan dama can sun shirya kuntata mana ne,ke kuma ina kika samo katin donna ga kamar shine ahannunki ko kuwa idanuwana ne suke mun gezau.?" su Daddy abun har yaso ya basu dariya ammh suka cije kuma su dadi sukaji da faruwar hakan donko bakomi Hafsa da maminta zasu gane kuransu,Nabeelah tace"Nima waye ne zai bani in banda maƙirar matan nan tasa…?ni wallahi banma san tana da boutique agarin Abujan nan ba sai dana raƙa ƙawata Habiba shopping shine na ganta tana fitowa,tana ganina don tsabar wulakanci irin nata ta shiga jifana da katinan bikin wai ga nawa,gana mami,sannan gana Hafsa wai suna gayyatarmu bikin jikokin Tsoho...hadda wani cewa yaran boutique ɗinta wai su bari na kwashi duk abunda nakeso iya son raina ina iya kuma haɗawa dana Hafsa karsu kuskura su karbi kwandala daga hannuna,Allah na tuba ma ko yawo muke tsirara zamu karbi sutura ne daga hannunta...?"

Ya mukhtar ne yadan saki murmushin yaƙe yana kallonta yace"waima Habiba...ƴar iska ko an faɗa miki banga lokacin da wani ƙato ya daukeki amota kuka fita bane…?ai bakisan ina laɓe ina kallonku ba ke azatonki nayi nisan kiwo ko…?Toh Nabeelah kisake fita bada sanina agidan nan ba kiga abunda zai faru dake..." mami ce ta doka masa tsawa"Dallah rufemun baki anan mutumin banza wanda sam bayason ganin farin cikin ƴan"uwansa sai baƙar hassadar tsiya,kabari muji da abunda ke damunmu kana jina ko tunda kai bakada tausayi arayuwarka..." kallonta yake cike da mamaki ammh Daddy bai bari yayi magana ba yakamo hannunsa yana fadin"Mukhtar tashi muje kamun rakiya unguwa,ka rabu da mutum duk wanda yayi mai ƙyau don kansa haka zalika duk wanda ya aikata akasinta kansa yayiwa…"

Su mami na kallo suka fice ta bisu da tsaki tana fadin"like father like son,Allah ya wadaran naka ya lalace..." taja dogon tsaki sannan ta juyo tana kallon Hafsa wacce take rera kukan tausayin kanta,tace"ke dallah malama ba kuka ne yakamaceki ba yanzu tashiwa zakiyi ki kammallah duk wani shiri daya kamata kiyi kafin jibin don so nake ki riga ita amaryar tasa isa gidan tafe da wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login