Showing 3001 words to 6000 words out of 102125 words

Chapter 2 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

1846

aranka cewa muddin itama wannan din ta shigo bata haihu dakai ba,,tou insha Allahu ni tsoho zansa ka jaraba auran gida gida,,don acikinku dukah hatta iyayenku bbu wanda ya ta6a shaawar yin auren dangi,,don haka ni dakaina zan za6o maka macen kirki acikin zuriar nan don ka aura,,watakila idan akayi 'yar gida gida sai kaga an dace....''

Kallon kwayar idonsa Gidad'o yake cike da mmkinsa don tabbas iya gaskiyarsa yake fad'a,be gama tsinkewa da lamarin ba kawai yaga tsoho ya fashe da kuka,da sauri Gidado ya isa gareshi zuciyarsa na kuna yake fadin''wai shin kaka ni kadai ne jikanka namiji acikin zuri'ar nan?gasu mansur,Gambari,Saikou,Yaro,Ibrahima Mustapha dadai sauransu,shin su din ba mutane bane sai nine zaka takurawa?ga kuma ya'yansu nan duk sun haihaifa inajin mustapha ne kawai muke jirgi daya dashi,tou meyasa bazaka takurashi ba sai ni?sannan kuma ai inajin ya'yan sauran sun isheka basai lallai dole mu mun haifa ba musamman ni daka fi takurawa,ni don Allah tsoho ka fita daga harkar rayuwata banison matsi da takura,kuma insha Allahu daga Hafsa dinnan bbu kari,,shin ina kke son nakai mata fiye da biyu ne?kai ne zaka ciyar mun dasu?ni wlh arayuwata bani da raayin ajje mace fiye da daya ammh gashi ka sani dole sannan kuma hakan be isheka ba tun baa kawo ta biyun ba kana sake bani umarnin karo wata idan har itama wannan din bata haihu ba,shin wannan wacce irin jarabace haka?ka sani koda kuwa zan aura mata sama da dubu ne idan har Allah yace bazan haihu dasu ba tou bbu wanda ya isa ya canza hakan.......''

Ji kake tatassss! an daukeshi da wani irin mahaukacin marin da har sai daya ga walkiya sun gifta idanunsa,azabar bata gama sakeshi ba yaji an kara mai wani,,muryar Baba munniru ne yaji ya daki dodon kunnensa,magana yake cikin tsananin fushi da kuma dacin rai''Uban namu ne ka tsaya kke jefawa magana haka tamkar wani sa'anka?ai idan tsoho bai haifeka ba ya haifi ubanka Alassana,,ko kuwa don kaga yafi kaunarka akan sauran jikokinsa ne shiyasa kke takashi yadda kaga dama...?ai ina ji ma adadinka ne don ya nuna damuwa akan rashin ganin gudan jininka ah doron kasa,,ammh dake kai din butulu ne......''

   Da sauri tsoho ya tari numfashinsa ta hanyar daka masa tsawa yace''Kai munniru banison iskancin banza,shin waya sako bakinka cikin zancen nan ne?ka tafi ka bamu wuri bbu ruwanka dani da jikana....'' kafin ya gama rufe baki yaga Gidado yasa kai ya fice zuciyarsa na azalzala,murmushin takaici ne ya su6ucewa Baba munniru yace''Tou dubi wanda kafi fifitashi akan kowa dubi yadda yake watsa maka kasa ah ido,,ko kadan baya darajaka da kuma ganin girmanka sai in an tursasashi dole,gaskia tsoho yakamata ace kayi karatun ta natsu,,lokaci yayi dayakamata ace ka fita daga rayuwar Gidado da kuma dena fifitashi akan sauran don hakan ba karamin haifar da kiyayya yayi atsakanin mutan zuri'ar nan ba,,kai ni kaina haushi nakeji yadda baka wani damuwa da nawa 'ya'yan sai tsatson Bobbo Alassana (Yaya Alassana),komi dansa Gidado Gidado haba yakamata ka kwatanta adalci mana yabba (Baba).....''

Shiru tsoho yayi don yama rasa ta cewa kuma baya jin zai iya rage son da yake ma Gidado don sauran su samu,ayau daace wani ne acikin jikokinsa yay masa wannan rashin ta idon tou da wlh daga shi har iyayensa sai sun fuskanci hukuncinsa,,ammh sbd qaunar da yakewa Gidado haka yana ji kuma yana gani yake takashi son ransa ya tafi kuma bazai dauki mataki akai ba kuma duk wanda yay yunkurin dauka sai kaga ya takama wannan din burki,,duk umarninsa da Gidado kebi tursasawar iyayensa ne in ba donsu ba bbu umarnin tsoho ko daya da zai cike.....

   ____________★★★★

 

Ciwon kan daya saukarwa Gidado akan rikicin Tsoho be gama sakeshi ba sai ga wani babbar rikicin ya kunno masa,,wai matarsa Jameelah ita da kanta ta bud'e masa wuta alan dole da ita za'a je dakko amaryarta kuma acikin tata motar amaryan zata zauna,arikice Gidado yace''Yanzu ke Swthrt ina kika ta6a jin anyi hakan ne?ki gayamun ina kika karanto inda akace uwargida na zuwa dakko amaryarta kuma ma wai acikin taki motar zata zauna?uhmmmm ina sauraronki??

    ''Nidai kawai ka banni inje if you really trust me bana son dogon surutu bani keys na motata...'' ta mika masa hannu ba tare data kalleshi ba,,shi ko shiru yay mata yana binta da kallon mmki,ganin shirun yay yawa ne yasa ta dubeshi tace''Yallabai kaifa nake jira lokaci na tafiya gashi har an soma wucewa....''

Samun kansa yay da mik'a mata makullan,tace thank you Sir sannan tayi gaba ya bita da''Jameelah pls dnt do anthing stupid kinga na yadda dake if not idan komai ya faru abakin aurenki nadai gaya miki...'' murmushi kawai tayi sannan taje ta jawo matar dan'uwansa wanda suke ciki daya dashi wato matar mustapha Anti Azeema,dama bakinsu daya,,mutane sai cece kuce akeyi akan wannan bak'on al'amari ammh bbu wanda ya iya daga murya ya fadi agaban Gidado tunda ana shakkarsa sannan kuma Tsoho da Hajju sun bada goyon baya don ayi zaman lfy duk da cewa su kansu bawai sun aminta da ita bane,,Tsoho da Hajju wato matar babansa sune masu fada aji awannan zur'ia,,daga tsoho sai Hajju don ko mijinta Alassanar shakkarta yake,bawai muguwa bace ammh kawai shakkarta ake,haka ya samo asaline da kasancewarta babbar 'ya awajen abokin Tsoho,Tsoho ne ya nemawa dansa aurenta,Alh.Manu abokin Tsoho ne na kut da kut ammh ya dade da rasuwa hakan yasa Tsoho ke nan da nan da 'yarsa Dije wacce akafi sani da Hajju,tou shiyasa ta samu mulki,iko da isa akan kowa na gidan tare da daurin gindin Tsoho,sai dai kuma tana da mutunci sosai shiyasa kowa ke qaunarta,

Jameelah da kuma anti Azeema kadai ne acikin motar,,agaban motar kuma wani katon banner ne wanda aka rubuta ajikinsa _*'WELCOME HOME MY BRIDE'*_ ,,abun dai gwanin ban sha'awa,,Atsiyace ta figi motar tasha gaban jerin kwanon motoci 10 dake gabanta,kallo ya koma kan wannan motar,mutane sai lek'owa ake ana kallon yadda take wasan mota asaman titi abun dai gwanin ban shaawa kuma kamar ba mace ke tukin ba..........

_*Tofa! my fiful shin meke faruwa ne acikin wannan zuri'a?ayadda ake nuna mana kamar wa'enda suke ciki daya ma da Gidadon su kansu bbu wanda ya ta6a haihuwar wato matar mustapha da kuma kanwarsu Surayya,,bbu asibitin da basu je ba dukkaninsu ammh magana daya ce har yau wato lafiyarsu qalau haka ma matayensu,ita ma kanwarsu Surayya ance lafiyarta qalau,,tou duk da cewa ansan iko na Allah ne ammh ga dukkan alamu ya nuna kamar akwai wani kitumurmura acikin wannan babban Zuria'r?mudai je zuwa don yanzu wasar zata soma armashi*_

_*Da kuma alamun Jameelah na kokarin tafiyar da rayuwarta ne akan *'KISHIN ILIMI'* da kuma *'KISHIN JAHILCI'*😳,,,dnt hesitate much kudai ku cigaba da kasancewa da alkalamin hazikar marubuciyar taku✍*_

_*Inason ku bani hadin kai sosai acikin wannan tafiyar da zamuyi tare da fahimtar characters din dakyau,kuyi kokari ku gane matar wani da matar wance,haka ma d'an wani da d'an wace,jikar wani da jikan wance☺,,dnt allow urself to be confused don komi is well explained👎*_

_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

_*#HAFNANCY_LURF💓*_

_*#KISHIN_MATA*_

_*#2020_NOVEL*_

_*#SALO_NA_DABAN*_

_*IWA🖊*_

*🍃KISHIN MATA🍃*

               🍃🍃🍃

         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT



WɾƖTҼɾ

ى

 

ASSɷ

*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_

           _*[Hafseesee]*_

_*💫Dedicated to:-Anti Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   

*#An_Intense_Jealousy_Story*

*#Love#fiction*

_•Copy cats ar advised not to transform diz publication by any means_

_#In this article, we will investigate what is going on in the minds of men who seek to marry more than one wife. What are their views on the matter? We also want to know what their wives think about their husbands’ looking to marry again_

         _*💫BABI NA BIYU…✌*_

___________★Akan idon Gidado motoci suka tashi kuma duk yana kallon irin gudun gangancin da Jameelah takeyi da mota asaman kwalta,ahankali ya furta''ke kuwa Jameelah salon naki kishin kenan?tou Allah ya kyauta...!'' komawa yayi inda yabar wasu abokan aikinsa wa'enda basu samu zuwa daurin aure ba shine sukazo tayashi murna da yammacin nan,wasu acikinsu sai cewa suke matarsa ta burgesu ayayin da wasu ke cewa suna tsoro kar tayi fuckup cuz mayb she's upto something freakish,murmushin yake kawai Gidado yayi tare da cije kakkauran lips dinsa yace''I trust my wife bazata ta6a bani kunya ba...!'' daga kafadu sukai suna fadin''Tou Allah yasa,fatanmu dai Allah ya baku zaman lfy dukah..''

Ameen shine abunda ya amsa da kana suka sallameshi shi kuma yayi musu rakiya wajen motocinsu,bayan wucewarsu ne ya koma ciki sai part din mahaifiyarsa *'Yumma'*

Ya cimma jama'a sun dan ragu ah part dinta,tsirarun mutane ne kawai ke zaune ah katafaran falon mai alfarma,bayan ya gaishesu ya wuce dakin Yumma direct,da sallama abakinsa ya shiga cikin dakin,Yumma ce kawai ta iya amsawa don ita da Ramlah kanwarsa ne kadai adakin,fad'a take mata sosai akan cin zarafin Jameelah da tayi acikin jama'a,ita kuwa Ramlar sai kuka take kaman zata hadiye zuciya ta mutu,Yummah na ganinsa ta yanke fadarta bayan ta amsa mishi sallamar,itama Ramlar shiru tayi da kukanta kamar anyi ruwa an dauke,tsit kakeji don mugun tsoronsa take kamar wani mala'ikan mutuwa,

Idonsa k'yam akan Ramlah wacce sai faman ajiyar zuciya take ta saukewa ajere,tun kafin ya karasa wajensu ya doka mata wani irin gigitacciyar tsawa''K…! maza knees down tun kafin na karaso wajen na tattakaki awajen stupid gal kawai...!'' ya fadi da jajayen ido,ai tuni ta zamo daga kan gado jiki na rawa takai gwiwowinta kasa kamar yadda ya umarta,yana isa gareta beyi wata wata ba ya daga hannu zai sharara mata mari,da sauri Yumma ta daga hannu ta tareshi,cike da dacin rai tace''Haba Gidado meye haka ne wai kke kokarin yi?wai kai meyasa idan ranka ya 6aci sai ka nemi ka fita cikin hayyacinka ka koma tamk'ar mahaukaci ne?ni nasan abunda kake wa zafin ran ammh ai yakamata ka dakata tunda ka cimma ina mata fad'a ne,,mutumin banza kawai mtssss...!''

Cike da mmki yake nuna Ramlah yace''Ya rabbi…! Yumma yanzu agaban mara kunyar yarinyar nan ne kike zagina salon ta kara rainani...?'' saurin taran numfashinsa tayi''Kai kana da kunyar ne?ba agabana kke kokarin jibgarta ba?dake kai baka da ta ido dukan d'a agaban idon iyayensa,tou wlh kar inji kuma kar in gani ka sake dukan Ramlah agidan nan,karshe ma daga daketa sai data kwanta jinya dake kai baka da imani ko kadan.....!''

Maganarta ta karshe ya kara fusatashi yace''Ai wlhy bata ma kwanta jinya dakyau ba har sai naga na fasa jikinta da belt tukun idan har bata fita aharkar matata ba,ga matar dan'uwanta nan Azeema da kuma yar'uwarta Surayyah cikinsu duk bbu wanda ya haihu ammh dake tawa matar ta raina shiyasa take takata son ranta kuma ana gani ayi shiru,tou wlh Yumma ki gargadeta bazan sake daukan wannan rainin da wulaqanci ba,ni kowa ya fita daga harkan matata,tunda dai kunsa na qaro wani auran zamu gani ai ko ita din zata haihun ammh adai cin zarafin Jameelah banaso.....!''

Ji kke tatatasssss Yumma ta kwasheshi da wani irin mahaukacin mari,,muryarta na rawa tace''wallahi suleiman ka fita daga cikin idona in rufe,lallai ashe rashin kunyar taka ba'a kan Tsoho kawai ya tsaya ba har yana neman shafarmu mu iyayenka?ai kuwa da sakel ya zama dole na dau kwakkwaran mataki akai,,maza fitar mun ah daki kafin raina ya karasa jagulewa...!''

Cike da tsantsar mmki yake kallonta hannunsa rike da kumatunsa inda yasha wawan marin,,

   ''Ko bakaji abunda na fada bane?I said getttt outttt...'' ta sake fadi cikin hargowa tare da nuna masa hanyar kofa,da sauri yayi waje gudun kar ta tara musu jama'a....

Shidai yau yaga rayuwa,ayau ya karbi zafafan marin mutane biyu na Baba Munniru da kuma na mahaifiyarsa abunda wani acikin zuri'ar bai ta6a gigin masa ba kenan kuma duk akan yana fad'ar gaskiyarsa?shi bama wai don tursasashi da sukayi kan ya qaro aure bane ke soya ransa ba kamar yadda aka matsawa matarsa Jameelah,anbi an tsangwameta da rashin haihuwa bayan ga matar dan'uwansa mustapha yana nufin Azeema ko 6atan wata itama bata ta6a yi ba,haka ma k'anwarsa Surayya dake aure ah kaduna duk ba'a saka musu ido ba sai shi??tou meyasa?amanta da batun Surayya tunda gidan wani take,shi mustaphan meyasa baa takurashi da tasa matar ba sai shi?Tsoho bai ta6a bada shawarar wai mustapha ya karo aure ba sai shi harma yana ikrarin har ta uku sai yyi idan wannan da zata shigo itama tazo bata haihu ba,wai kuma Tsoho ya kira hakan da So?wani irin so kenan ana takura rayuwar mutum shiba karamin yaro ba?at 37 yakamata ace an fita daga harkarsa ai ya tsara rayuwarsa yadda yakeso,,shi abinda yafi daure masa kai ma be wuce yadda su ukun nan wa'enda ke ciki daya suka kasa haihuwa ba,shi,Mustapha da Surayya,ita Ramlar ce auta kuma batayi auran ba,ansan iko sai Allah ammh gsky abun da mmki ace duk matayensu ko 6atan wata bata ta6a yi ba haka ma kanwarsu Surayya,ita kanta tana fuskantar tsangwama da kyara acan dangin mijinta,duk wani jikan Tsoho  ah zuri'ar nan wanda yayi aure,matan ne da mazan duk kowa ya haihu ammh tsatson mahaifinsa Alassana bbu wanda yaga gudan jininsa,sai yake zargin kamar akwai wani lauje cikin nadi ammh bayason ya daura zargin akan kowa,don zato zunubi koda ya kasance gaskia,,zai dai cigaba da kaiwa rabbi kukansu don yasan abun na damun iyayensa ba kadan ba shiyasa Yumma wasu lokutan takan huce haushin akan ko wanene idan an 6ata mata rai,tai ta fad'a akan abun da bai taka kara ya karya ba,kuma duk yasan abu na cinta ne arai ammh ta kasa bayyanawa,ajiyar zuciya ya saukar sannan ya nufi part din Hajju don ita kadaice kurum zata iya saukar masa hankali ahalin yanzu,,shaquwa na musamman ne ke tsakaninsu,ko kadan bata mashi kallon d'an kishiya,ji take tamk'ar ita ta haifeshi da cikinta,gashi kuma Allah bai ta6a bata haihuwan ba itama...!

   Bayan fitarshi Yumma ta zauna agefen gado tare da dafe kanta dake barazanar fashewa tsabar ciwon kai,dkyar ta iya duban Ramlah dake shesshek'a ta doka mata tsawa tace''Kema tashi ki fitar mun adaki kafin na huce haushin akanki..!'' da sauri ta mik'e jiki na rawa ammh taki motsawa sai kokarin 6ata hakuri take,

''Ramlatu...! nace ki bace mun daga gani ko?wlh idan baku dena 6atamun rai keda wanki ba tou na rantse da Allah bazaku sake ganin sakin fuska awajena ba tunda ku din ba 'ya'yan mutunci bane...! ta furta cikin tsananin fushi...

''Yumma don Allah kiyi hakuri bazan sake ba...!'' ta fad'a with a breaking voice,wani wawan kallo Yummar ta watsa mata,da sauri ta fice tabar mata dakin,,,fitarta keda wuya Yumma ta rushe da kuka tare da zu6ewa saman gado,hakika tana jin zafin rashin haihuwan 'ya'yanta uku,Gidado,Mustapha da kuma Surayyah,tasan tabbas ba hakanan kawai aka barsu ba,akwai lauje cikin nadi,ammh kuma yadda zuri'ar nan take da yawa tou waye zata dora ayar tambaya akansa?zata dai cigaba da kaiwa Allah kukanta don shine kadai yasan gaskia kuma da karfin mulkinsa zai magance matsalar insha Allah....!

Cikin karyayyen murya wanda ya cakud'e da kuka tace''Zuri'ar Tsoho why??ni Ummerherny meh na muku ne wanda har yasa kuka huce haushin akan 'ya'yana?how can three of my children unable to conceive?such isnt possible....!'' ta furta tana share hawaye gami da jan majina kan ta cigaba''Akwai sa hannun wani acikin wannan al'amarin ammh ni Ummerherny na barwa Allah komi don shine zai mana maganinsa,,Allah ya saka muku Suleiman...!'' ta sake rushewa da kuka,ji tayi Goggo Boddiya na tunkaro dakin tana kwala mata kira,da sauri ta mike ta shige bandaki ta wanke fuska gudun karta gano taci kuka........

     ★__________★

      _*★THREE ARMS ZONE,ABUJA*_

Sagir best frnd na Gidado shine yayi kokarin shan gaban motar Jameelah yana mata magana''Haba..! Haj.Jami kibi ahankali mana,menene amfanin tseren motar?''

     Tsoki tajah ba tare data tankashi ba ta kara gudun motar,na gefensa Suraj yace''Ammh lallai na yadda da maganar mutane da suke cewa wai rikicin duniya da mai rai ake,nifa ban ta6a ganin mace irin wannan bafa?wai da ita zaaje dakko kishiyarta shi kuma Gidadon ya daure mata gindi bbu jan ido,anya Sagir baka ganin cewa diz woman is upto something stupid?

    ''Ni kaina abun ya dad'e yana bani mmki abokina ammh ai zamu gani,,ni bbu abunda ma yake bani haushi kamar gudun da take da mota sai kace ma tasan gdnsu amaryar ne,,aff! nafa manta cewa Allah ya kawomu zamani,karka sha mmki ma tafi shi gogan sanin kan gidan,,kasan wasu matan da zarar sunji za'a musu kishiya sai kaga sun soma shige da fice suna binciken gidan dayake neman auran,,gashi dai mun shigo 3 arms zone and she's the one leading us sai mu cigaba da bibiyarta....'' Sagir ya ida maganarsa yana shafa gashin bakinsa,hannunsa daya kan sitiyari,Suraj dai ya kurawa bayan motarta ido ne yana kallon abun al'ajabi...!

     

     __________★

   ''Jameelah don girman Allah ki rage gudun motar nan pls kar ki jawo mana accident,shin wannan wani irin zafin kishi ne haka?donna tabbata duk haukan nan acikin salon naki *'KISHIN'* ne....'' Azeema ta ida maganarta cike da zafin rai,,Jameelah bata saurareta ba har sai data isa ga gate din wani madaidaicin gida,,ji kke kiiiiiiiiii taja wani wawan burkin daya tada kura wanda hakan ya janyo hankulan yara dake wasa ah kofar gidan,ihun murna suka fasa ah sa'ilin da suka tabbatarwa kansu da cewa yan daukan amarya ne suka iso sbd jerin kwanon motocin da suka hango can nesa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login