Showing 72001 words to 75000 words out of 102125 words
Chapter 25 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx
lafiya sosai harma an kaita school clinic sakamakon aman da take ta tilawa,ga wani irin zazzaɓin daya rufeta,ah rikice yasa aka kawoshi makarantar,tun fitowarsa ah mota dalibai keta binsa da kallo cike da sha"awarsa don yazo ne alokacin break period,direct aka kaishi school clinic har dakin da aka kwantar da ita don an mata karin ruwa,Maryam da Halima friends ɗinta ne kawai ke zaune kusa da ita,sai kuka take ta musu tana fadin"ku kiramun dan"uwana kar in mutu ba muyi sallama ba!...Maryam!Halima! don sonku da annabin rahma ku dauki permission kuje ku sameshi awajen aikinsa ku fada masa halin da nake ciki......"
wata nurse ce take ta tausarta kan tayi hakuri tayi shiru ba"asan ta dunga sanya damuwa aranta sabida irin halin da take ciki,sunyi mata test ammh koda wasa basu fada mata abunda ya haddasa rashin lafiyar tata ba,sun dai ajje sakamakon ne har sai mijinta ya iso...ana cikin hakan ne sai gashi ya faɗo dakin,yaransa biye dashi abaya,cikin tashin hankali yakarasa gaban gadon da take kwance akai,su Maryam kuwa duk sun rikice da ganinsaa don basu taɓa ganinsa ba,
Tana haɗa idanu dashi ta fashe da kuka tana fadin"Dan"uwa ka taimakeni kar in mutu,jikina duk ciwo yakemun wallahi..." zama yayi agefenta tare da kamo hannunta ya sarke da nashi,cike da tausayinta yace"Babyna insha Allahu bazaki mutu yanzu ba kinji ko...?zamu rayu da juna har mu haihaifa insha Allahu..." juyawa yayi ga wata nurse yace da rinannun idanu"Meh akace yake damunta ne…?" Nurse ɗin wacce take riƙe da farar takadda ahannunta ta miƙa masa takaddar tana murmushi kan tace _*"I'm so happy to be the first person to break out the good news to you...congratulations sir! ur wife is 3weeks pregnant....."*_
Wani irin miƙewa yayi face full of amazement,tsawon minti biyu ya kasa iya futar koda kalma ɗaya sabida bakinsa daya cika da tsantsar farin ciki,dakyar ya iya cewa"You mean my wife is pregnant...?" cike da farin cikin itama tace"Yes she is sir,duba ka gani..." ta fada tare da miƙa masa takaddar,hannu na rawa yasa ya karba ya warware,ai kuwa haka ɗinne Mubeenah is pregnant for him,bai san sanda ya daka wasu tsallen murna ba,straight ya nufi kasa yayi sujjudur shukur yana mai nuna godiyarsa ga ubangiji da ayau ya share masa hawaye,babu wanda bai bawa tausayi awajen ba hatta Baddon kuka take rerawa na tsananin tausayinsa da kuma farin ciki,dagowa yayi yana zubda ruwan hawaye alokaci guda kuma yana mai farinciki ya nufeta,ranta fari kal tace azuciyarta"Hamma dama na fada maka cewa tabbas wannan ranar tana nan zuwa agareka wataran wanda zakayi kuka kuma farinciki alokaci guɗa,ah iya zamana dakai kafi kuntatamun ne,dadinka kadan na mora ammh sai gashi ayau ni _*MUBEENAH*_ na jefaka cikin jindadin da baka taɓa tsintar kanka aciki ba……………*PEN'S DOWN*✍
_*HAFFY MOUSTY🌹*_
_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_
_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_
_*KISHIN MATA...!*_
_Na marubuciya Hafnancy..._
_akan naira 200kacal👌_
_ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_
_*💫BABI NA ASHIRIN DA TARA...💥*_
…………Sannu ahankali ya nufi inda take idanunsa ƙyam akanta yana jin wani irin mugun sonta da kuma ƙaunarta na sake samun matsugunni acikin zuciyarsa,bakinsa ya kasa rufuwa don murnar har masa yawa tayi,agaskiya suna da bukatar privacy hakan yasa daga yaransa,su Maryam,ma"aikatan asibitin,da kuma wasu acikin malaman makarantar suka fice waje don basu wuri su gana,agefenta yasake zama tare da kamo yatsun hannayenta ya shiga murzasu ahankali,kallon juna suke ido cikin ido basa ko ƙyaftawa,sun kwashi kusan sakonni hamsi ahakan kafin can hawaye ya shiga zirarowa Gidado,ruwan hawaye yake fitarwa sosai na tsananin murnar ganin wai shine ayau Allah ya share mishi hawaye,ashe dai Baddo zata zo ta zama blessing ga rayuwarsa shine kuma yaketa wulaƙantata tun da can…?meyasa yayi hakan..?gashi wacce ya raina yake ganin abun kunya ne ache ya haɗa shimfiɗa da ita har ma kallon ƴar cikinsa yake mata,sai gashi ayau itace ke dauke da ɗan cikinsa,
Atake kawai yaji wani irin kunyarta da kuma tsantsar nadama ya lulluɓeshi,daɗinshi ɗaya bai yiwa Tsoho gaddama ba asanda ya yanke hukuncin aura masa Baddon,ashe dai alherinsa ce,wacce zata zamo sanadin ganin gudan jininsa aduniya wanda shine cikar burinsa arayuwa yaga ɗan cikinsa,lallai Tsoho abun girmamawarsa ne da kuma darajawa,ya zama dole yaje yayi mishi godiya don dama ya taɓa fada yace insha Allah zaka tako da kafafunka wataran kazo har gabana ka tsugunna kana mun godiyar wannan haɗin da nayi,sai gashi acikin biyar kacal da aurensu zancen tsoho ya tabbata,wani irin soyayyar kakan nasa ne kawai yaji ya kanainaye masa zuciya,hakan ne ya kara gudun zubar ruwan hawayensa,Baddo da itama hawayen take zirarwa tace tana ɗan matsa hannunsa"Haba dan"uwa..!Haba Ubana..!Haba Mijina..!......aganina ba koke koke da kuma tunane tunane zaka ɓatar da lokaci kana yi ba,a"ah kamata yayi ace ka nuna godiyarka ga ubangiji da irin wannan babbar ƙyautar da yayi mana wanda ka daɗe kana nema idanu rufe,sai gashi ayau ya share maka hawaye,ammh wallahi Dee naso ache wannan cikin ajikin Anti Jamila yake ba nawa ba don wallahi nasan tana samun labarin cewa ina dauke da cikinka zata shiga cikin wani hali mara misaltuwa sai dai ko kadan bazata taɓa nunawa ba zatayi kokarin barin ma cikinta ne…………"
Dasauri yakai hannu ya rufe mata baki gami da girgiza mata kai still yana hawaye yace cikin dakusasshiyar murya"No baby karkice hakanan,kar kiyi kokarin butulcewa mahaliccinki da ni"imar da yayi miki wanda ba kowa ke iya samun irinsa ba,inason kisa aranki cewa ke ɗin ƴar baiwa ce,kibar cewa kinso ache kaza da kaza sam yin hakan kamar baki godewa Allah da ƙyautar daya baki bane,yafiki sanin dalilin dayasa ke ya nufeki da samun rabon sannan ita kuma ya hanata,don haka kul kar in kara jin zance makamanciyar wannan ya sake fitowa daga bakinki,yanzu gatan da kawai take bukata awajenmu daga ita har sauran wa"enda ke neman haihuwar ido arufe shine mu tayasu da addu"ar suma ɗin Allah ya azurtasu da samun rabo na alheri…………" ahankali ta amsa masa da ameen,tasa dayan hannunta tana share mishi hawaye,ahaka Doctor yashigo yanata fada wai yakamata aƙyaleta ta ɗan huta sosai,ahalin yanzu babu abunda take bukata kamar bacci,hakan yasa yayi mata allurar bacci,ba"a wani jima ba wani nannauyar bacci yayi awon gaba da ita,waje ya fita ya shiga kiran yan"uwa da abokan arziki babu kunya yake fada musu cewa ai Baddo na dauke da jikinsa,acan gida ko"ina ya ruɗe da murna ammh wasu aciki yaƙe kawai suke tayi na ciki na ciki,Tsoho har ƙwallar farin ciki ya zubar,Yumma kuwa rufe kanta adaki tayi tana cizgar kukan murna da kuma nuna godiyarta ga ubangiji daya azurtata da ɗanta da samun rabo,Allah yayi kuma da rabon itama zata ga jikanta,hannu tasa tana share hawaye bayan ta tuno da Mustapha da Surayya,gashi yau kusan kwanakin Surayya biyu kenan agidan wai mijinta ya saketa sabida hakurinsa ya ƙare bazai iya cigaba da zama da ita ba,anki gayawa Gidado ne don ansan abun bazaiyi ƙyau ba muddin yasan an sako ƙanwar tasa,babu rokon da ba"a yiwa mijinta Awwal ba kan yayi hakuri ya maidata ya rufa mata asiri,ba"a hanashi ƙaro wani auran ba ammh yadai rufa mata asiri,Awwal ya rufe idanu yaci mutuncinsu na ƙarshe adan dole suma ɗin sukayi zuciya sukace idan anyi duniya don manzo Allah SAW itama bazata koman ba koda kuwa ya nemi yin sulhu ne daga baya,yanzu maganar da ake ciki ma zancen zuwa akwaso kayayyakinta ake duk ba tare da sanin Gidada ba don ya kwan biyu rabonsa da gidan,
Surayya ce ta buɗo kofar dakin ta shigo dauke da tsantsar farin ciki akan fuskarta,dasauri Yumma tasa bayan hannu tana share hawayenta gudun karta kamata tana kuka,karasawa tayi wajenta ta durkushe gabanta gami da kamo hannayenta tana mai kokarin son taga ta haɗiye kukan dake neman cin ƙarfinta tace"Yumma barkanmu da Hamma Gidado,yau Allah ya nufeshi da samun rabo da ƴar"uwarsa,lallai Mubeenah alherice agaremu duka,su Hamma an kusa zamowa Uba,ke da yabba kuma kun kusa samun jika,ni kuma nakusa zamowa goggo…ammh yumma banso Hamma ya gayawa duniya cewa matarsa tana da ciki ba don ba"a san zuciyar wani ba,da kawai yabar abun har sai cikin yafito sosai kowa ya gani,ammh yanzu wallahi ni tsoro ma nakeji kar wani mummunar abu ya samu babynmu don wallahi nayi imani da Allah da walakin goro amiya da wankan ruwan ƙwaryar da Hajju take mana…………"
Saurin katseta tayi ta hanyar saukar mata da wawan mari tana fadi cike da ɓacin rai"Meya faru da wankan ruwan ƙwaryar…?eyyy tambayarki nake nace meya faru dashi...?" dafe kuncinta dake azabar yi mata zogi tayi kan tace"Ina tunanin shi yake hana mana haihuwa,kowacce mace acikin zuriar nan da kuma wa"enda ke shigowa cikinta an musu wannan wankan kuma duk sun haihu,toh meyasa mu ƴa"ƴanki ne bama haihuwa…?baki tunanin watakila don kina kishiyarta ne kuma don taga ita bata haihu ba ammh ke kin haihaifa shiyasa take hana naki ƴa"yan haihuwa....?"
wani mahaukacin marin ne ta sake dauketa dashi tana fadin"Don ubanki meh kike nufi da hakan...?zarginta kike akan dasa hannunta agame da rashin haihuwar taku ko menene gayamun...?" Surayya tace tana kuka"Eh Yumma zargin nata nake wallahi don ki duba fa saida aka sauke wannan banzar al"adar nata ne fa shine har Allah yasa Mubeenar ta samu ciki......." duk da cewa tabbas ita kanta Yummar ta daɗe tana zargin Hajju ammh sam bata son ƴa"ƴan nata su suyi zarginta,hakan yasa takai mata shuri aciki tana fadi rai amatukar ɓace"Toh Surayya ni bbu ruwana kije kita zarginta ammh ki sani ni ban dora ayar tambaya akan kowa ba,na yadda cewa shi haihuwar nufin Allah ne,in yaso ya bada haka zalika in yaso ya hana,ammh babu uban wanda yake da iko da komi sai mahaliccin sammai da kassai.....idan kika kuskura naji wannan zancen awaje toh na rantse da Allah saina tsine miki kinbi gari...maza tashi ki bani guri....."
_Iyaye ku dunga kai zuciyoyinku da nesa don tabbas wasu na tafka babban kuskure wajen yiwa ƴa"ƴansu baki wanda daga baya sai kaga sunzo suna nadama,musamman ke uwa bakinki na saurin kama yaro don haka hattara,naki kawai ki bishi da addu"ar shiriya,wani abu sai ah littafina na gaba *'ABUL-HASSAN'* (BAWAN ALLAH)…anan ne zaku ga yadda uwa ta taimaka wajen ruguza rayuwar gudan jininta wanda bakin alƙalami ya riga ya bushe babu zancen maida hannun agogo baya😭🙏_
Acan cikin gida ma kus kus ake da zancen wai Hajjun ne ke hana ƴa"yan Yumma haihuwa har dai maganar ta fito fili,rikici ta kaure,Hajju nata cizgar kuka tamƙar zatayi hauka jin sharrin da aka liƙa mata,saida Tsoho ya tsawatar sannan kowa yakama kansa,ya kuma yi gargadi akan cewa kar kowa ya sake tada wannan zancen in ba haka ba zaiyi mugun sassaɓa masa,
Karo na uku kenan da Gidado ke dialing lambar Jamila yana yankewa,yama rasa ta yaya zaiyi breaking news ɗinne kawai agareta,yasan baza tayi fushi ba ammh kuma ai dole zata ji wani iri,aƙarshe Mustapha kawai ya iya ƙira ashe yama riga yaji,kokarin kira yake ma shine Gidadon ya rigashi,ya taya dan"uwan nasa murna sosai ayayin da shima Gidadon yayi mishi addu"ar samun nashi rabon very soon,bayan sun kare wayar kai tsaye Mustapha ya latso Azeema awaya alokacin Ƙasim na samanta yana kwasar zumarta,sai kukan dadi yake ta zubawa,abun nasu ma yanzu yayi kamari,zuciyoyinsu ya riga daya bushe sam basa tsoro,don yau akan gadon auransu ta sunnah ta jawoshi suke aikata alfasha (wa"iyazubillah)
Rikicewa tayi bayan taga mai kiran,dasauri ta ture Kasim gefe sannan ta sakko daga saman gadon tsirara tayi picking call ɗin bakinta na mugun shaking,Mustapha bai dago komai ba don yakosa ne kawai ya shafa mata dadadar labari,wuta ne ya dauke mata bayan taji abunda ya fada,cikin tashin hankali hawaye ya shiga ziraro mata tace"Mubeenah keda ciki...?toh nifa Mustapha yaushe ne zaka bani nawa cikin...." wani irin haushinta ne ya rufeshi yace"kinga karki tayarmun da hankali yanzun nan kina jina ko...?tunda ke ɗin bakisan kiyi tawakkali kibarwa Allah komi ba,nidai kiyi kokari zuwa anjima kije gida ki tayasu murna sannan kuma kiga jikinta don yace har gado an bata amakaranta....."
Azuciye tace"Babu inda zani don nima ɗin gani akwance ba lafiya…" nan da nan hankalinsa ya tashi yace arikice"Zeettyna meh yake damunki...?" bata tankashi ba kawai ta yanke call ɗin tana kuka,juyawa tayi ga Kasim wanda ke wasa da joystick ɗinshi yana kokarin son ya kwantar dashi don yasan tunda har hankalinta ya tashi tofa bazasu cigaba ba sai wataran kuma,jikinsa ta fada tana fadin"My kani wai sai yaushe ne zaka bani babynka..?meyasa kake mun rowa ne.....?Mubeenah is pregnant yanzu Musty ke fadamun...." ta sake rushewa da wani sabon kukan,tabbas ya taya Gidado murna kuma shima zaiso ace ya cikawa Azeema burinta ammh tsoronshi ɗaya muddin rabo ya ratsa atsakaninsu tofa daga ranar yabar moranta,shiyasa kawai rashin samun cikin nata bai dameshi ba, hannu yasa yana shafa sumar kanta sannan yace"Am so sorry my Zeema naki nanan zuwa very soon acikin kwanakin nan insha Allah..."
cakumar fatarsa tayi tana mai sakin wani sabon kukan tace"Thats all what you keep saying,zan dauka acikin kwanakin nan ammh shiru akeji.....ka gayamun tun wuri idan ma ɓata lokacina nakeyi abanza kaima ɗin baka haihuwan toh in sani inbar wasting zumata…"
cikin wani irin voice mai cike da kauna da sha"awarta yace"Taya za"ayi insan bana haihuwa tunda ba mata ne gareni ba...?kece kawai zaki iya amsa wannan tambayar tunda da kece nake harka da ita fata da fata,sauran matan kuwa danayi harka dasu ban ta6a gangancin yi fata da fata ba sai da condom......so i dnt think matsalar daga wajena take am sorry to say watakila the problem is from you…nidai kawai abunda nasani shine am madly inlove with you to the extent that har ina ji inama ace ke matata ce,dana cigaba da lasar zumarki mai dadin gasken nan hankali kwance......"
Ji kake tasssss! ta daukeshi da mahaukacin mari tana kuka tace"Wallahi kasim kaci amanata,you deceived me bayan na yadda dakai....i did everything for you...na mallaka maka komi,jikina ne da kuma gida duk na siya maka asirrance,na ɓataka da makuɗen kudaɗen da wani naka bai taɓa ɓatarwa akanka ba ammh irin sakayyar da zakamun kenan…?kace kana sona harma kana ji da"ace ni matarka ce....?dubar ni nan daƙyau Allah na tuba ba don lalura ba harkai ka isa ka kwanta da mace kamata…?balle ka buɗe kazamin bakin nan naka kace kana sona…?toh daga yau sai yau bani bakai,ina ganin kawai zan sauyaka da wani awaje wanda nasan zai biyamun bukatata ba tare daya ci amanata ba.....banza butulu kawai"
Rike kumatunsa yayi yana sakin wani shu"umin murmushi,saida yabari ta ajje aya kan ya dauka"Azeema wallahi wallahi na rantse da wanda raina ke hannunsa sa"arki ɗaya nayi nisa acikin ƙaunarki ba don haka ba da wallahi yau sai kinyi mugun raina kanki don ba"a haifi wata ƴa mace wacce zata takani ta kuma wuce lafiya lau ba,ammh ke zan kyaleki ne don kauna if not da zaki ga yadda Kasim yayi wa sauran maza tsere awajen iya kwanciya da kowacce iriyar mace,da ayau keda kanki saikin saramun da irin dagargazar dazan miki ta rashin imani,hakan shine maganin duk wata banza marasa kunya.......sannan kuma idan kin isa tantiriyar ƴar iska jeki nemi wani awaje wallahi saina tona mana asiri dukah……………ki sani shege sai shegiya......"
Akiɗime ta kamo hannunsa hawaye na bulbulo mata,da azama ya fincike hannun ya dauki rigarsa yana kokarin sawa......
Akalla an samu awanni uku kafin drip ɗin da aka sawa Baddo ya ƙare,kuma alokacin ta farka,aka sallamesu bayan an haɗa mata magungunan da zasu bata ƙwarin jiki da kuma rage mata ciwon jikin,aka kuma bashi guides na yadda zai dunga kula da ita da sauransu dai....bai bari ta taka da kanta ba ya sunkuceta cak! sai mota,aka bisu da kallon sha"awa ita kuwa kunya tamkar zai kasheta....
Saida yasa yara suka fara saukeshi ah unguwarsu Mustapha don mustaphan ne ya dameshi da kira kan don Allah ya taimaka ya dubo mishi Azeema sunyi waya kuma tace itama tana kwance bata da lfy,abun dayafi tayar mishi da hankali ma bai wuce kiranta da yayi tayi ammh taki dagawa ba,kuma alokacin rikici suke da kasim,wayarta na silent shiyasa bata ji karar shigowar kira ba,yace da yaransa sukai Baddo gida zai kira su Jamila suyi zaman jiran isowarta don har yanzu ya kasa kiran kowanne acikinsu ya gaya mata gashi gashi.....abunda kuma yasa bai ciwa Mustaphan musu ba shine don akwai ƙyakkyawar alaƙa ne atsakaninsu toh shiyasa ya amince zai je ya dubota kuma yaji dadin yarda dashi da yayi dahar ya zaɓeshi akan kowa ya nemi alfarman dayaje ya dubo lafiyar iyalin nasa…
Ah buɗe yaga gate ɗin gidan don haka sai kawai yasa kai ya shige ciki…… _*PEN'S DOWN✍*_
_*HAFFY MOUSTY*_
_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_
_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_
_*KISHIN MATA...!*_
_Na marubuciya Hafnancy..._
_akan naira 200kacal👌_
_ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_
_*💫BABI NA TALATIN...💥*_
……Yana kusa kai cikin gidan ya zaro wayarsa ya latso Jamila,ringing daya,ana biyun ta daga,bai jira yaji ta cewarta ba yace"gasu Musa nan dawowa da baby ku kula da ita bata jindadi,nima ɗin zan karaso nan da mintuna ashirin…" yana ida magana ya katse call ɗin,ita kuma jiki na rawa ta dubi Hafsa dake danne dannen waya tace da ita"Anty Hafsa maza tashi ƙanwarmu ba lafiya ance gasu Musa nan dawowa da ita gida…" wuf itama ta miƙe jiki na rawa tana fadin"meh yake damunta..?"
Jamila tace"Nima wallahi ban sani ba Gidado ne ya kira yake sanar mun,taho muje waje mu jira isowarsu..." Jamila tayi gaba ayayin da Hafsan ta mara mata baya zuwa wajen,sosai suke zaman lfy yanzu don Hafsa ta gano kura kuranta,taga kuma bariki babu riba shiyasa tayi watsi da duka iya shegenta ta kama Allah.fitarsu da kamar 5mins sai gasu sun iso,dasauri suka nufi motar bayan anyi parking ɗinta,da rawar jiki Musa yafito ya