Showing 84001 words to 87000 words out of 102125 words

Chapter 29 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

1842

Baddo komi bata saka aciki ba sai aikin kuka kawai take tayi,tunda al"amarin ya faru za"a iya kirga sau nawa ta saka abu aciki don sai anyi da gaske kafin take cin abincin,gata da juna biyu shiyasa ake tsoron kar wani abun ya shafi lafiyar cikin don yadda kusan kowa ya dora buri akansa abun ba"a cewa komai,yau ɗinne ake saka ran farfadowar Gidadon kamar yadda likitoci suka fada,idan har kuwa ya wuce tsakanin yau da gobe bai tashi ba tofa sai dai azubawa sarautar Allah ido,shiyasa yau tun safe yan"uwa da abokan arziki aka cike asibitin ana jiran aga abunda mai iko zai yi,saidai an hana kowa shiga inda yake sabida ba"a son su dameshi da hayaniya,kowa ka gani bakinsa motsi yake da addu"ar samun lafiya ga Gidadon,masu ƙaryayyen zuciya wanda tuni suka sare da tashiwar tasa sai kuka sukeyi ciki kuwa hadda Tsoho wanda ya kasa zaune hakanan kuma ya kasa tsaye,sai safa da marwa yakeyi yana mai addu"ar Allah ya tashi kafadun mafi soyuwar jikan nashi don ayanzu ta Gidadon ake,wasu ma har neman tashin hankalin sukayi suka rasa kasancewar ba"a wani jima da gama cin kukan Baba Munniru ba,

Baddo ce zaune tare da Ramlah acan gefe sun ƙebance kansu daga sauran ƴan"uwan da suke zaune wasu kuma atsaye ana jiran rabbi yayi ikonsa don akalla an kwashi kusan awa ɗaya kenan da rabi ana jiran fitowar likita ammh shiru kakeji,Jamila da Hafsa su ɗinma sun ƙebe kansu ne awaje guda bayan tafiyar yan"uwansu da suka zo dubiya,sosai Jamila take ta kokarin danne zuciyarta tana lallashin ita Hafsan don ga dukkan alamu ita tafi rauni shiyasa nata damuwar ya bayyana,baya ga haka kuwa damuwa da bakin ciki sun fi yiwa ita Jamilar rubdugu ne,tana ji kuma tana ganin yadda masoyinta,mijinta wanda suka wanki juna budurwa da saurayi kwance rai ahannun Allah ammh wai itace ke bawa wasu hakuri kan su daina kuka,baya ga tsananin hakurin da take dashi da"ace zata biyewa zuciya ne da tuni wallahi ta daɗe da yin karamar hauka,dakyar ta samu Hafsan ta nutsu sannan ta mayar da kallonta gasu Baddo wacce ta kifa kai akan cinyar Ramlah tana cizgar kuka,ayayin da ita kuma Ramlar ke lallashinta itama da jikakkun idanu,

Sai Jamila duk taji Baddon ta bata tausayi,hannu tasa ta dauke guntun hawayen daya ziraro mata sannan ta miƙe ta nufi inda suke zaune bayan tace da Hafsa tana zuwa,

  

"Haba kanwata!Haba kanwata!!…yanzu ke aganinki kina ƙyautawa kenan…?yanzu shikenan ba za"a hanaki abu ki bari ba sai abunda ranki yaso kike yi ko...?Mubeenah meyasa kike neman halaƙa mana babynmu ne…?ansan damuwa ya zama dole ammh kiyi hakuri ki cije don kasancewarki cikin damuwa yana iya shafar abun cikinki……" Jamila ta ida jawabinta bayan ta zauna akusa da Baddon,

Dagowa tayi tana kallon Antin nata da jikakkun idanu tana fadi cike da tashin hankali"Anti taya kuwa zan daina damuwa akan halin da dan"uwana yake ciki...?he's lying uncouncious fa sannan kuma kina ji likita yace idan bai tashi yau ko gobe ba then mu cire rai akanshi,ni wallahi ayanzu bata abun cikina nake ba ta dan"uwana nake,ubana kuma mijina.....idan baki sani bama toh yanzu ki sani ban damu idan cikin ya ɓare ba don dama can ina da niyyar aborting ɗinsa…………"

cike da tsantsar mamakinta Jamila tayi grabbing kafadar Baddon,dube dube ta shiga yi taga babu kowa akusa balle ace yaji kuma Allah yasa ma tuni Ramlah tabar wajen,Jamila tace cike da tashin hankali"Mubeenah wat did you juz said...?aborting...?anya kanki ɗaya ne kuwa…?cikin da ubansa da kuma kowa ya dora buri akai shine kike tunanin zubarwa...?meyasa...?gayamun meyasa kikayi irin wannan kazamin tunanin…?ko baki son ki haihu da Gidado ne...?"

Hawaye ne yacigaba da ziraro mata saman kunci tace tana girgiza mata kai"wallahi ko ɗaya antina…ina masifar son naga na cikawa Hamma ƴa"ya agidansa wanda hakan shine cikar burinsa arayuwa amma saidai zan fison ke ki fara haihuwar kafin ni shiyasa nake son na zubar da cikin...." wani irin haushin Baddon ne taji kawai ya lulluɓe mata zuciya,ji take kamar ta daka hannu ta yanka mata mari ko taji ɗan sassaucin abunda take ji azuciyarta,ammh sai tayi kokarin dannewa don batasan ƴan dangi susan abunda ke faruwa sabida sanin hakan ba karamar case bace,tace tana binta da wani irin kallo"Mubeenah ashe ke ɗin girman agric kikai ban sani ba…?ashe ashe baki da tausayi da kuma tsoron Allah...?zubar da ciki sai kace wacce bata da ilimi...?ko kuwa mantuwa kikai da azabar da Allah ya tanadar wa duk wata ƴa mace data zubar da ciki da gangan…?dama ace babu abinda za"a ciyar dashi ne idan ya fito duniya toh sai ace ai gashi gashi ammh da gangan fa kike neman kashe ran da bai ji ba kuma bai gani ba,meye laifinsa Mubeenah dahar ya cancanci hukunci mai girma haka daga gareki amatsayinki ta mahaifiyarsa..?ki sani tabbas masu zubar da ciki bisa son rai ko kuma kan wani dalili mara tushe tofa su sani akwai babban aiki agabansu,ranar tana nan tafe wacce Allah zai busa rai wa abunda suka zubar ɗin nan, kuma sai yayi jayayya dasu agaban Allah akan shin wani dalilin ne yasa suka hanashi rayuwa…?suka kasheshi tun bai zo duniyar ba...?ki sani acikin laifi mafi girma wandanda annabi SAW ya gayawa sahabinsa Abdullahi Ibn Mas'ud (ra) ciki harda *KASHE DANKA DON KAR YAZO DUNIYA...* "

"Haba 'yar ƙanwata karki shiga jerin wa"ennan jahilan matan mana wanda ko kadan basu da tunani da kuma hangen nesa...wani irin zance ne haka da babu dadin ji wai zaki kashe ɗanki ne don kinfi son ni na fara haihuwa kafin ke…?aganinki da kuma karancin tunaninki ke kinfi Allah wayau ne dakuma finsa sanin abunda yake yi…?shi bai san abunda yakeyi bane da har ya hanani haihuwar sannan ke ya baki...?agaskiya kin matuƙar bani kunya da kuma mamaki don ban taɓa zaton hakan daga gareki ba…"

Kuka sosai ta sake barke mata dashi,sosai kuma taji wani nadama ya lulluɓeta don ita sam bata taɓa koda kwatankwacin tunanin da ita Jamilar tayi ba, kodayake idan idanunka suka rufe da abu tofa idan ba aikatawa kayi ba hankalinka bazai taba kwantawa da kuma samun sukuni ba,sai ayanzu ne kuma ta tuna irin halin da zata sake jefa dan"uwanta idan har ayau ya wayi gari yaga ta kashe masa abun tinƙahonsa,muradin ransa,istigfari ta shiga yi acikin zuciyarta tana mai neman gafarar ubangijinta,sosai ƙaunar da take yiwa Jamila ya sake samun matsugunni acikin zuciyarta,Hafsa dai na can zaune ta zuba uban tagumi,azahirin gaskiya idanunta akansu yake ammh ahak'ik'anin gaskiya ta lula duniyar tunani ne,watakila hakan baya rasa nasaba da rashin lafiyar mijin nasu,

Baddo ta kamo hannayen Jamila tana shessheƙa,duk fuskarta yayi daɓa daɓa da hawaye,tace"Anti Jamila bazan taɓa gajiya da cewa ke ɗin wata haske ce acikin rayuwata ba, haka kuma bazan taɓa daina miki kallon wata aba mai daraja da kuma ƙima awajena ba,ki sani ko acikin matan ma ke ɗin sarauniyarsu ce, wallahi ina miki son da ko ruwa bazai iya kashe kishinsa ba don ke ɗin kin kasance wata halitta ce wacce keson ganin farin cikina da kuma ganin kin dorani kan hanya madaidaiciya,halittar da ko kadan babu son zuciya atattare da ita, halittar da tafi son ganin dariya da kuma farin cikin wani akan nata, halitta mai karamci da kuma tsantsar hakuri....." rushewa ta sake yi da kuka tana fadin"Kai Anti Jamila Allah ya kara miki hakuri ya kuma cika miki burinki ta samun rabon haihuwa...."

Bata yi wata wata ba takai mata runguma,Jamilar ta amsa da ameen tana kokarin cije kukan dake neman cin mugun ƙarfinta,duk wani awurin idan ya dubesu sai sun bashi tausayi don atunaninsu kan rashin lafiyar mijin nasu ne yasa suka shiga cikin wannan halin,Umman Baddo ce ta taso daga inda take tazo wurinsu,sai fada take ta musu akan wani dalili ne zaisa su zauna suta shirga uban kuka bayan ayanzu addu"a ce kawai Gidadon yake nema daga gunsu...?

Tsawa ta dokawa Baddo"Idan na sake jin koda tarinki ne toh wallahi saina yi kasa kasa dake anan wajen tunda ke baki jin rarrashi mutuniyar banza kawai...." Yumma ce ta karaso wajen tana bawa Umma hakuri,ta kamo hannun Baddo suka je can gefe ta shiga bata magana ammh ita kanta dauriya kurum take yi don babu uwar da zata ga ɗanta acikin irin halin da Gidadon yake ciki sannan ace bata shiga cikin wani hali ba,ammh she has to be strong, idan ta nuna damuwarta sannan yara ma suka nuna toh waye zai lallashi wani..?

     ****

Tunda mummunar al"amarin nan ya afku sam Mustapha ya kasa samun kwanciyar hankali don gani yake ta dalilinsa dan"uwan nasa ya shiga cikin wannan halin haka kuma ta sanadinsa ne Baba Munniru ya rasa ransa, don da"ace bai ɓatawa Gidado rai ba da duk hakan bata faru ba,tunda aka kwantar da Gidado shine ke kwana dashi tare da Baba shagari wato mahaifin Baddo,babu abunda yafi jefa Mustapha acikin tashin hankali idan ka cire halin da dan"uwansa ke ciki kamar zantuttukan Mal.Musa taxi man dake ta masa yawo akai har yake neman tarwatsa ƙwaƙwalwarsa,

    

"wallahi tun ranar dana barku ban sake samun sukuni da kuma kwanciyar hankali ba don tsorona ɗaya ayau idan na fadi na mutu sai Allah ya kamani da laifin haƙƙinka dana ci, ma"ana tamkar cin amanarka ne nayi daban fadi maka gaskiya ba kamar yadda ka bukaci hakan, ammh sai na gwammace take gaskiyar sannan na rufe da ƙarya, aganina hakan ze kawo maslaha da kuma wanzar da zaman lfy duk da cewa nasan hakan ba daidai bane, bani burin ace nine sanadin kunna wutar fitina atsakanin ma"aurata don zan zamo tamkar munafiki ne, koda na koma gida ban sake samun kwanciyar hankali ba har yau da nake maka magana shiyasa kawai na yanke shawarar zuwa na fada maka gaskiya ko zan samu sukuni, wato matarka dai awannan ranar ba daga *HAIR & NAIL PALACE* na dakkota ba, daga gate ɗin *5-STAR HOTEL* na dakkota kuma nayi imani da Allah daga nan ta fito, sannan kuma kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da cewa hankalinta amatuƙar tashe yake donko acikin motar ma waya take tayi tana kuka, acikin zancen nata kuma na ɗan tsinci wani abu aci bayan ta ƙare wayar ah inda tace _*"Don girman Allah mami kuyi hakuri ku barni da mijina ai ita haihuwar ta Allah ce, karku rabani dashi sannan kuce zaku aurani ga wani kamar yadda suke kokarin yi."*_

"kalaman nan nata sun matukar dauremun kai kuma atake na tabbatarwa kaina da cewa tabbas wannan baiwar Allahn tana cikin halin ha'ula'i, shawarata agareka shine karka dauki mataki kai tsaye ka zauna kayi nazari akan al"amarin, sannan kuma yanke ɗanyen hukunci cikin fushi duk ba naka bane, kabi komi asannu na barka lafiya...." daga haka ne sukayi sallama,toh tun asannan nefa Mustapha bai sake samun natsuwa da kuma kwanciyar hankali ba, akullum sai zantuttukan wannan bawan Allahn ya faɗo ransa kuma yanason yayi bincike ammh halin da dan"uwan nasa yake ciki ne ya hanashi, tambayarsa kullum kuma itace, mai Gidado keson nuna masa ne agidansa..?ba fata ake ba yanzu idan rai yayi halinsa kuma shikenan bazai taɓa sanin komai wanda ya danganci abunda yake niyyar nuna masan ba…?

YA ILAHI...! waya sani ma ko duk akan Azeeman ne...? tuni yaji wani muguwar tsanarta yakaiwa zuciyarsa cafka, afusace ya miƙe daga inda yake zaune yaje inda yake tunanin Azeemar take zaune acikinsu Hafsa ammh koda yaje bata nan, duban Hafsa yayi wacce take zaune ita ɗaya ta lula cikin duniyar tunani,

"Ina Azeema ta shiga ne...?" yayi kokarin tambayarta ammh shiru,saida ya sake tambayarta akaro na biyu sannan tayi firgigit tace"Uncle Musty magana kake...?" saida ya haɗiyi wani miyau mai ɗaci kan yace"Cewa nayi ina Azeema ta shiga...?"

Ajiyar zuciya ta sauke kan tace"Au! ai tuntuni ta fita rakiyar ƴan"uwanta kuma har yanzu bata shigo ba....akalla tafi 30mins awaje..." bai sake sauraronta ba yaja jiki yabar wajen zuwa waje......



Bayan Azeema ta sallami yan"uwanta wa"enda suka zo dubiya sai suka jame ita da Kasim awaje, har ta tsaya tana masa kara mishi gaisuwar rashin da akayi,can tace cike da damuwa"Kasim ban dai fada maka bane sabida tashin hankalin da muka tsinci kanmu aciki ammh sosai nake cikin wani hali, kwata kwata maganar kirki ta daina shiga tsakanina da Mustapha tunda wannan mummunar al"amarin ya afku,tsakanina dashi sai hantara da kuma jefamun baƙar magana adunƙule, afarko na masa uzuri ne don atunanina watakila halin da ake ciki ne ya kawar masa da duk wata walwalarsa ammh sai naga kamar abun ba haka bane, akullum lamarin sai daɗa girmama yake, ko jiya ma daya dawo wanka gida sai nayi kokarin tsareshi da tambayoyi ammh kasan mai..?wani zafafar mari ya yankamun sannan yace kar in takura rayuwarshi don baida lokacina ayanzu, idan ya gama da tashin hankalin dake gabanshi zai waiwayo gareni alokacin yagama tanadar da duk wasu gamsassun hujja akaina....."

fashewa tayi da kuka tana fadin"Kasim what do you think..?baka tunanin ko Mustapha ya gano alaƙata dakai ne…?" cike da tashin hankali Kasim ya dora hannunsa akan fuskarta inda shatin mari yaɗan fito,ammh sai ka kura mata idanu ne zaka ga shatin marin, toh dayake ana cikin tashin hankali shiyasa babu wanda ya lura da hakan,yace da jajayen eyes"Yanzu shine ya mareki haka...?"

Kafin takai ga magana sai hango Mustapha tayi yafito waje kuma idanunsa ƙyam akansu, fuskar nan babu alamun annuri akai, hannayensa zuɓe acikin aljihun wandonsa, zuciyarta ne kawai taji yayi wani irin tsalle tamƙar zai fasa ƙirjinta ya fito waje, da rawar murya tace"Kasim...duba...bayanka...gayanan..ya...fi...fitooo..." da hanzari ya waiga idanunsa ya sauka akansa, shi kansa ji yayi tamkar zuciyar tasa zata faso waje tsabar tashin hankalin daya daɗun masa,kafin sukai ga nemar shawarar abun yi sai ganinsa sukai ya nufosu gadan gadan, ahankali Kasim ya soma ja da baya fuskarsa na nuna tashin hankali muraran mabayyani,ko kallonsa Mustapha bai yi ba ya fuzgi hannun Azeema ya nufi motarsa da ita,

sai turjewa take gami da fashe masa da kuka tana fadin"Mustyna am very sorry ba abunda kake tunani akai bane..." hannu yasa ya datse lips ɗinsa "shhhhhhhhhhhh..!! karki cikamun kunne da hayaniya ko kinji na ambaci cewa kinyi wani abun ne....?"

Ya fada da jajayen idanu nearly in tears al"amarin dayasa ƴan hanjin cikinta canza wajen zama,asanyaye ta saki jikinta ya cigaba da janta har wajen motarsa,bude front seat yayi ya jefata sannan yakoma ɓangaran direba ya tayar da motar yafice daga cikin asibitin da gudu, kuma duk akan idon Kasim wanda ke cikin tashin hankali mara misaltuwa....samun kansa yayi da son bin bayansu yaga inda zasu duk da cewa zuciyarsa ta raya masa cewa gida ne zasu ammh sai yaji kawai yana son bin bayansu...hakan yasa ba tare da wani dogon tunani ba ya isa ga mashin ɗinsa lifan wanda ake kira da roba roba ya haye kana ya bata wuta sannan yabi bayansu……

Fitar Mustapha da kamar mintina biyar Gidado ya farfado dauke da salati abakinsa yana mai kokarin dafe kansa, da sauri su likitoci suka yo masa caaa akai........✍

_*HAFFY mousty🌷*_

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

_*KISHIN MATA...!*_

_Na marubuciya Hafnancy..._

_akan naira 200kacal👌_

   _ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

   _*💫BABI NA TALATIN DA BIYAR...💥*_

"Innalillahi wa"inna ilaihi raji"un...wayyo Allah ku taimaka kaina,meya faru dani ne..?kuma ina nake…?" ya fada yana dafe kan dake barazanar fashe masa,likita ne ya karisa kusa dashi dasauri yana fadin"kabi ahankali kadan samu rauni akai…" shiru yayi jin abunda likitan ya fada,ya shiga tunano abunda ya faru dashi,hoton mummunar yanayin da suka tsinci kansu aciki awannan ranar ne ya shiga hasko masa tamƙar yanzu abun ke faruwa,da sauri ya runtse idanu gami da ciza kasan leɓunansa sosai tamƙar zaya hudashi,kara ya saki gami da fashewa da matsanancin kuka yake fadi arikice yana dube dube"Baba Haruna..! Baba Munniru..! don Allah ku tashi karku mutu...."

Likitocin suka shiga girgiza kai suna mai cike da tausayinsa,likitan dake kusa dashi ne ya sake cewa"DCP sir kayi hakuri kabi asannu karka maida mana aiki baya…satinka kusan ɗaya kenan fa bakasan inda kake ba sakamakon mummunar hatsarin da kuka samu amma alhamdulillah ka farfado alokacin da muka fidda rai da tashiwarka……" jin abunda likitan ya fada yasa ya waro idanu waje cike da mamaki yana fadin"Har an fidda rai akaina kace fa..?" daga kai likitan yayi alamun tabbatar masa da zancensa,hawayen tausayin kansa ne ya ziraro masa yace ahankali"Ya Allah  ina matukar godiya daka sake aramun wani ran...nayi alƙawarin bauta maka fiye da da don nasan duk jarabawace ka saukar akaina domin na gyara alakata da mutane, hakkin Mubeenah kadai ma ya isheni....." ya fada yana matsar kwalla,likitoci dai sai kallonsa suke cike da tausayawa,can ya sake kallon likitan yana fadin"Ina sauran wa"enda muka samu accident dasu...?"

likitocin suka shiga ƴar kallo kallo atsakani domin kuwa basu da amsar bashi,bazasu iya gaya masa cewa ai ɗaya aciki ya rasu ba don yana iya sake shiga cikin wani hali,dakyar Dr.Rufa'i ya iya haɗo zance yace"Ai su sun samu lafiya dama kaine kawai ka rage amma yanzu alhamdulillah tunda gashi ka farfaɗo…" ajiyar zuciya ya sauke yana mai furta kalmar alhamdulillah ajere,can ya sake cewa"Toh ina sauran mutanena…?akirasu muga juna ko hankulanmu zai kwanta duka..." likita ya amsa da Toh sannan yace"Bari mu gama dubaka tukunnah kafin abawa wani damar shigowa..."

Bayan likita yayi gwaje gwajensa ya tabbatar da cewa babu sauran wata matsala sai ɗan abunda ba"a rasa ba, dama can farfadowar tasa kawai ake fata kuma yanzu alhamdulillah tunda anci nasara,fita waje yayi don gayawa mutanensa good news ɗin,domin kuwa duk wani mai kaunarsa da wanda ba"a kaunarsa duk an cike asibitin ne ana jiran aga ikon Allah akanshi,abu fa hadda su ƴan sanda aciki,manya da kuma kananunsu..

 

***

"Haba mustyna magana nake maka fa ammh kayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login