Showing 45001 words to 48000 words out of 102125 words
Chapter 16 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx
mustyna kar muje kawai ka rabu dashi bazan kara ba..." juyawa yayi ya fice yana fadin"ai fa kisa aranki kamar mun gama zuwa ne...."
Bazan iya misalta muku irin tashin hankalin da Azeema ta shiga ba,sai kuma duk taji ta tsani kasim daya kawo dabarar wai ta saka kayan,ai data sani tayi tahowarta da nata kayan don ta tabbata ko zata samu wani matsala da mustapha bazai kai irin na wannan ba,tasan tunda yace sai sunje plazar nan tofa kamar sun gama zuwa ne......
********!!
Ayau ne ake zaman meeting ɗin gaggawa wanda tsoho ya haɗa adalilin irin cin fuskar da mahaifiyar Hafsa tawa Gidado da kuma kazafin da tayiwa mahaifiyarsa Yumma,kusan duka zuri'ar tsoho da yaransa ne,surukai ne da manya manyan jikoki duk an hallara don kiran tsoho ba kira ne wanda za'a shashantar ba,infact hadda iyayen Baddo sun baro bakin aikinsu sunzo,tsoho yayi gyaran murya ya soma magana cike da ɗacin rai"kuyi hakuri da kiran gaggawan danayi muku don abun ne yazo babu shiri,basai na tsaya nanata magana daya ba don na kwana dasanin cewa babu inda zancen rabuwar Gidado da hafsa bekai ba acikin zuriar nan kai hatta da waje ma,mahaifiyar Hafsan taci mutuncin Gidado agaban idon yabbaninsa tare da yiwa mahaifiyarsa kazafi akan dasa hannunta acikin rashin haihuwar ƴa'ƴanta wato su Gidado,tabbas munji zafin wannan magana kuma ina da damar makata akotu saidai bazanyi haka ba,ammh ina da hanyar da zanbi wanda zaisa duk su jishi ajikinsu duka,zan nuna mata cewa ba kowane yake zuwa rafi da tulu sanda ya dawo dashi da ruwa aciki ba,asabida hakan ne na yanke shawarar haɗa jiƙana _*SULEIMAN DAN WAJEN DANA ALASSANA AURE DA jiƙanyata MUBEENAH BADDO ƳAR WAJEN DANA SHAGARI*_ nan da sati daya cur sannan kuma na sauke duk wasu al'adu da akeyi acikin wannan zuriar,kamawa daga wankan ruwan ƙwarya da shanta dasauransu,ayau ni SULEIMAN TSOHO NA riga da nasa albarƙa awannan auren haɗin dana kudurta araina………………✍
_*Hafnancy😘*_
_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_
_LITATTAFAN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_
_*KISHIN MATA…!*_
_Na marubuciya Hafnancy…_
_akan naira 200kacal👌_
_*MALIKA-MALIK…!*_
_Na marubuciya Janafty..._
_shima akan naira 200kacal_
_Idan kuma duka biyun kikeso toh kin samu garabasa zaki biya 300 ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_
_*💫BABI NA SHA TARA…💥*_
........Dakin ne ya karade da hayaniyar jama'a,yawancinsu na tsananin farin ciki da wannan babban al'amari da Tsoho ya haɗa don karfafa zumunci atsakani wanda ba'a taɓa yinsa acikin wannan zuri'a ba wato _*'AUREN DANGI'*_ ,sai kuma ya kasance an fara shine akan yaron babban ɗan gidan da kuma ɗiyar autan gidan,babu abunda kake ji sai masha Allah daga bakunan wa'enda suka so wannan haɗi gami da murna kan al'adun da aka sauke wanda basu da wani amfani,kalilan ne basu so wannan haɗin ba don acikinsu kuwa na hangi kasim wanda idanunsa sukayi jajawur dasu tamƙar garwashi,jijiyoyin kanasa sun mimmiƙe tsabar tashin hankalin daya shiga,babu wanda ya lura da halin daya shiga sai Azeema wacce jefi jefi take kai kallonsa gareshi,afusace ya miƙe yabar falon,fitarsa keda wuya abun mamaki sai ganin Jamila akayi ta miƙe tana rangaɗa guɗa iya ƙarfinta take fadin''masha Allah tsoho wannan abu yayi dadi ba kadan ba don dama can na kudurci niyyar zuwa in sameka da batun nan,na dade ina sha'awar ahaɗa Mubeenah aure da mijina donna tabbata nan gaba tabbas kana iya haɗashi aure da wata acikin dangin nan,toh ni kuma aɗan zaman da nayi da Baddo na gano cewa yarinyace nitsatssiya mai hankali shiyasa na gwammace akawomun ita amatsayin abokiyar zama akan kowacce yarinyar zuri'ar nan....''
kowa sai kallon mamaki yake binta dashi,da yawa ta birgesu ayayin dawasu ke ganin cewa iyayi da feleƙenta yayi yawa,da gani ba shakka bekai zuciyarta ba kawai tadai faɗa ne,cike da farin ciki Tsoho ke nunata da ƴar yatsa yace''madallah da Jamila mace ta gari shiyasa akullum kike daɗa samun matsayi acikin zuciyata kedai Allah yayi miki albarka ya kuma azurtaki da wa'enda suma zasu dunga miki biyayya da kuma kyautata miki" aka amsa mishi da ameen,itama ta amsa tana sharar ƙwalla,sai ayanzu ne Baddo ta dawo cikin hankalinta ta saki wani irin gigitacciyar ƙara gami da kankame Jamila dake tsaye kusa da ita,ta fashe da kukan tausayin kanta tana fadin"Don girman Allah antina karki bari su auramun mijinki,wallahi bazan iya cin amanarki ba plsss ki fahimtar dasu hakan...." dasauri Jamila ta duƙa tana share mata hawaye ta shiga lallashinta"haba kid sis karki manta fa keda bakinki kika daukarmun alƙawarin cewa zaki dawo ki zauna dani kuma zaki karbeni da hannun bibbiyu amatsayin ƴar'uwarki kuma abokiyar zamanki,dnt forgt munyi planning yadda zamu tafiyar da rayuwarmu tare da juna so pls dnt spoil it for us,juz accept ur faith ki yadda dama can Allah ya kaddara cewa dan"uwanki Suleiman shine mijinki...."
mutanen falon sai kallon mamaki ake binsu dashi,shi kam gogan naku tunda Tsoho ya soma magana har ya kammala kansa aduƙe yake,jiyayi kawai zuciyarsa takasa yin gaddama dawannan hukuncin da aka zartar dashi akansu,infact bazai iya daga kai ya kalli ƙwayar idanun Tsoho agaban idon Baba Shagari yace bayason jininshi ba sabida halaccin daya nuna masa arayuwa,baya mantawa shida kansa ya samo mishi admission ah police academy dake wudil ya kawo masa admission letter har gida,haka zalika kuma shine yashige masa gaba har ya samu aka daukeshi aikin ƴan sanda ya fita da two star wato ACP bayan ya kamalla karatun nashi,ko shekara biyar be haura ba aka bashi promotion zuwa DCP sabida kokarinsa da kuma jajircewarsa,toh taya ayanzu zai kalli wannan bawan Allahn yanuna bayason jininsa bayan yaga kamar abun shi ya masa dadi..?inaaa wallahi ko amafarkinsa bazai iya ba zaibi umarnin Tsoho kodon albarkacinsa,ayanzu babu wacce take bashi mamaki kamar Jamila,wato duk abubuwan bakin cikin da danginsa keta cusa mata koda rana daya bata taɓa nuna musu ɓacin ranta afuska ba balle takai ga magana,ji yayi ta sake samun wani babban matsayi acikin zuciyarsa,kasa kunnuwa yayi ya cigaba da sauraronsu,
Kuka ta sake rushewa dashi take fadi"Antina aini bansan shirin haɗani aure kike da mijinki ba ai da ban amince ba tun farko,makarantana fa yakukeson inyi dashi…?" mirmushi Jamila ta sakar mata tana fadin"karki manta nace miki zaki cigaba da makarantarki idan kika aureshi,don haka kowani irin makaranta ne kika ga ya miki aduk fadin Abujan nan saiki fadi mana mu kuma mun dau alƙawarin sakaki aciki…" dasauri Tsoho ya tari numfashinta yace"A"ah karki mata alƙawari don baki da wannan hurumin,wannan ra"ayi ne na mijinta in yaso ya barta ta cigaba agidansa idan kuma yaki toh babu yadda aka iya dashi sai ta rungumi haƙuri…" sabon kuka ta sake rushewa dashi tana fadin"Nidai kuyi hakuri karku auramunshi mugu ne sannan ni bazan iya cin amanar anti Jamila ba kuma....." mahaifinta ne yayi saurin katseta azuciye yace"Ke kinci gidanku kina jina ko..?nace kinci gidanku waye sa"anki anan..?kece zaki gayawa mutane yadda za"ayi don baki da kunya ko...?shi bece baya sonki ba sai kece zakice baki sonsa don baki da hankali ki dubi tsabar idanunmu kice baki son dan"uwanki jininki ko...?toh kisa aranki kamar anyi angama wannan auren ne mutuniyar banza kawai…"
Baba Haruna ne ya shiga kwantar masa da hankali yace"haba Shagari kabita ahankali man yarinya ce fa dole saida rarrashi da kuma ban baki…" Baba Alseny ne yakaiwa Gidado duka abaya yana fadi cike da tsokana"Kai kuma shashashan ɗan sandan fa ya akayi ne naga kayi shiru ko kaima baka sonta ne…?" firgigit yayi ya dawo cikin hayyacinsa ya shiga binsu da idanuwa tamƙar mara gaskiya can ya furta ahankali"Allah yasanya alheri ya kuma bamu zaman lfy duka…
gabaki ɗaya aka amsa mishi cike da farin ciki bama kamar mahaifinsa wanda yafi kowa murna da haɗin kan daya bada don ada azatonshi zai bashi kunya ne sai kuma gashi ya bada mamaki don har Tsoho ma yaji mamakinsa ba kadan ba,Tsoho yace"masha Allah haƙiƙa bazan iya misalta muku tsananin farin cikin dana tsinci kaina aciki ba don ban taɓa tunanin cewa za"a ƙarbi wannan hukunci dana yanke da hannu bibbiyu ba don azatona za"a barbaɗamun ƙasa ne ah idanu wannan karon ammh sai gashi an nunan cewa har yanzu ni ɗinne dai mai jan ragamar ahalina,ubangiji Allah yayi muku albarka zuri'ata,Allah yasa mu wanye da juna lfy,Suleimanu!Jamila…!mubeenatu…! rabbi ya saka muku kwatankwacin irin ƙyautatawar da kukemun…" ya ida magana yana sharar ƙwalla abun mamaki abun kuma tausayi,Sai duk jikin kowa yayi sanyi wasu masu raunin kamar matan hadda tayashi,can yasa hannu acikin katotuwar aljihunsa ya zaro bandir ɗin kudi yana nunawa jama"a kan ya direshi gaban ƴa'ƴansa maza yana fadin da iya ƙarfinsa"jama"a ku shaida gashi na biya kudin sadaƙin Mubeenatu naira dubu ɗari don haka aure ya tabbata tsakanin _*SULEIMAN GIDADO ALASSANA DA ƘUMA MUBEENAH BADDO SHAGARI*_ rana ita yau,Sagir da Aliyu nabar komi ahannuwanku ayi maza abuga kati arabawa mutane kuma kar ah manta akai gidansu Hafsa suma ɗin muna gayyatarsu bikin jikokin _*TSOHO*_ …"
Gabaki ɗaya mutanen katafaran falon suka dauki sowa ammh banda Aliyu wanda ƙarfin hali kawai yakeyi,sagir kuwa sai tsiya yaketa tsulawa abokin nasa don shima ya riga yazama ɗan gida,meeting daya daya ne baya halarta,Baba munniru yace"Ni dasu yaya alseny kuma mun dauki nauyin kayan lefe set ɗaya da kayan daki…"
"Ni kuma nadauki nauyin set ɗaya idan aka haɗa ya zama set biyu kenan" gabaki ɗaya aka zubawa Jamila idanu hatta da Gidado,kowa sai mamakinta yake yana fadi aransa cewa wannan wacce irin macece da sam bata nuna kishin mijinta afili..?agaskia samun mace kamarta mai tafiyar da rayuwarta akan kishin ilimi yana wuya,aka shiga shi mata albarƙa,su Baba Alseny hadda mallaka mata wani madaidaicin gida don nuna godiyarsu agareta da irin halaccin da take gwada musu,ita kanta Hajju ba"a batta abaya ba wajen kada nata taimakon duk da cewa zuciyarta ta cunƙushe da bakin cikin tsoho agame da al"adun daya sauke ammh ai bata isa ta nuna ba yaƙe kawai take tayi…
daga ƙarshe aka sallami kowa sai ya rage daga Tsoho sai ƴa"yansa maza da matan da kuma matan ƴa"yan nasa,suka shiga tsara yadda wannan biki zai kasance wanda yazo ah kurarren lokaci,awaje kuwa wasu acikin cousins ɗin Gidado sai congratulations suke ta mishi hadda Aliyu wanda daga baya ya fawwalawa Allah komi,yasa aransa cewa dama can ba alherinsa bace shiyasa Allah ya hanashi,shi kansa kasim bayan yaci kukansa sai yabarwa Allah komi donshi ayanzu haka bazaiyi ƙarya ba haduwar ƙarshen nan da sukayi shida Azeema yadan soma jin wani abu agame da ita,kodon yawan sex ɗin da suke having ne ya jawo masa hakan har yaji ya fara sonta shine be sani ba,ammh abun da mamaki mata nawa ne yayi tarayya dasu abaya kafinta,be taɓa jin wani abu dasunan soyayya agame dasu ba sai daukanmu yake useless and sex machines ammh meyasa sai ita ne yakejin kamar ya fara sontaa…?abun haushin ma ta mishi nisa sosai kasancewarta matar aure wanda ko amafarkinsa yasan bazai taɓa samunta ba…Azeema is juz quiet different from the ladies he mingled with ada,komi nata daban ne akan sauran matan sannan kuma sam baya ganin laifinsa sai nata don itace ta koya mishi yadda zai sota,da"ace idan sun hadu kawai they will juz quickly rush into sex ne without romance toh watakila da hakan bata faru ba ammh salon romance ɗinta ma daban yake sai ka rantse kamar da masoyinta take,shi yanzu abunda yake kokarin ganowa shine,soyayyar gaskiya ne yake mata ko kuwa sabida sweetness ɗinta ah bed yasa yakesonta?
Katon tukunya irinna biki aka dora awuta kowa yaci yayi nak dashi sannan wa"enda kenan kusa suka kama hanya,ƴan nesa kuwa sukace zasu tsaya ayi bikin gaba ɗaya kafin su koma,iyayen Azeema sai takurata suke tayi da ƙiraye kiraye kuma taki dagawa,sai da sukayi shirin tafiya ne ta samu wani wuri take amsa call ɗin bayan ta tabbatar da cewa mustapha ya shiga sallamar iyayensa,tana dagawa tace cike da ɓacin rai nearly in tears"momy don girman Allah ku kyaleni karku rabani da mijina,na rokeku karku raba aure sunnar ma"aiki tunda bani nace bani sonsa kuma ba ko kuwa yanamun abunda banaso ba,a"ah sam nida mijina muna zaune lafiya qalau sannan ita haihuwar ta Allah ce in muna da rabon samunta toh Allah yakawo masu albarka,in kuwa mu ɗin kwata kwata ba masu haihuwar bane toh Allah yabamu nacan,don Allah karku rabani da mustyna..." ta ida magana tana kokarin danne kukan dake neman cin ƙarfinta,sosai momy ta fusata ainun da maganganunta don haka tace"haka kikace ko...?toh Azeema mun barki ammh ki sani daga yau mun cire hannu acikin lamuran dasuka shafi rayuwarki tunda kin nuna mana cewa kedin ba ɗiyar kirki da mutunci bace,sam baki san masu ƙaunarki ba,kina nan zaije ya karo aure kamar yadda dan"uwansa yayi kuma kar wata shegiya tazo mana da tashin hankali gida tunda mun nuna mata hanyar mafita ammh tasa kafa tayi ball da shawarar tamu agareta,ki turo mana Zuby daga yau ta gama zaman gidanki karki sake nemanta da sunan tazo ta tayaki zama idan baya gari stupid gal kawai..." ta yanke wayar ranta na mugun suya,ta labartawa Papa yadda sukayi da ɗiyar tasa,azuciye shima yace"maijidda kawai mu rabu da yarinyar nan tunda taurin kai ne da ita,haba shekaru kusan shidda ba haihuwa ammh ita na lura ko ajikinta,kamar abun ma sam baya damunta,bari idan ya soma wulakantata zata nememu ne kuma kinji nace wallahi babu mai sauraronta acikinmu,Zan maida auren ɗan senator Rufa'in akan Zubaida donna riga na masa alkawarin bashi ɗaya acikin ƴa"yana,dama itace naga tafi dacewa dashi ammh tunda ta barbaɗamun kasa ah idanu toh bari na maida abun kan yar"uwarta Zubaida don ita nasan bazata taɓa bani kunya ba…"
****
Azeema sam bata wani shiga damuwa akan zafin da iyayen nata suka dauka akanta ba illa ma dadi da abun yayi mata na ganin zasu fita daga harkata ta sakata ta wala ta kuma shaƙi iskan duniya dakyau,kallo ɗaya zaka mata ka karanto tsantsar tashin hankalin dake kwance saman cute face ɗinta,acikin wannan halin ne mustapha yazo ya sameta,ganinta cikin damuwa yasa hankalinsa dagawa yace"Zeettyna why looking paled..?meya faru...?" Amaimakon ta faɗa mishi damuwar da take ciki amatsayin life patner ɗinta kamar yadda akasan mata da miji sukeyi,don ance problem shared is half solved ammh saita ɓoye mishi gudun kar yayi abunda iyayenta sukeso ya sawwaƙe mata,sai ce masa tayi"kaina ne ke ɗan mun ciwo…" kallon ban yadda da zancenki ba yashiga binta dashi ita kuma ta kawar da kanta gefe tana ciccije lips duk akokarinta nason ganin ta danne kukan dake neman taho mata,lura da hakan yasa ya fuzgi hannunta sukayi waje,kasim dake kallonsu ta tagar dakin mominsa yasaki labule yana mai sauke ajiyar zuciya yace"Ya Allah kasa wannan banzan mutumin be ankara da halin da muke ciki badai..." ya fada yana squessing face tare da watsa yatsun hannunsa akai yana shafa sumar kansa..
Da motarsu ya sadata saida ya turata ciki sannan yayi saurin zagayawa ya shige driver's side,sai alokacin ta samu sararin sakin kuka mai taɓa kahon zuciya,shi kansa ji yayi hawaye yadan tarun masa acikin kwarmin ido don basai an fada masa ba tabbas yasan abunda takewa kuka,jawota yayi ta fado jikinsa yace cikin wani cracking voice"Zeettyna haihuwa ko…?" dasauri ta daga masa kai alamun eh tana mai cizgar kuka,yace"Toh share hawayenki Azeema na samo mana solution kuma muna saka ran cewa insha Allahu it will work.." ya fada yana dariya hawaye na ziraro masa,cike da farin ciki takai masa duka akirji tana fadin"kai love muffin u cant be serious...tell me about it plssss…" ta kura masa eyes feeling so eager taji batu,kwantar da murya yayi ya raɗa mata akunne"na yanke shawara nace why not mu gwada _*ARTIFICIAL INSEMINATION*_ ……?"
Afusace ta tureshi tana fadin"kana nufin ayi collecting sperm ɗinka azuba ah mahaifatba…?nooo i cant allow dat to happen it can be very risky,mudai mu cigaba da addu"a kawai Allah yabamu haihuwa ta hanyar data dace basai munyiwa Allah shisshigi ba..." ta ida magana tare da rushewa da kuka tunawa da tayi na cewa ita ta riga data bi ɓatacciyar hanya,lallashinta ya shigayi yana ɗan bubbuga bayanta yace"Gaskiya kuma kinyi magana anan zeettyna naji shikenan ngd kwarai da saurin dawo dani kan hanya da kikayi..."
Tace"Nidai Allah yasa karsu tursasaka ka karo wani auran kamar yadda akayiwa dan"uwanka Gidado mata har uku haba...." ta sake fashewa da kuka,sun jima anan yana lallashinta da kuma fahimtar da ita cewa insha Allah babu wanda zaisa ya karo aure ita kadai ta isheshi rayuwa ko da ƴa"ya ko basu,daga ƙarshe yaja mota suka bar wajen,saida tasan yadda tayi ta mantar dashi batun biyawa saloon ɗin dayace zasuje bayan sun taso daga meeting,
**
Aɓangaren su Hafsa kuwa aranar da maminsu ta tafi gidansu da sunan an saketa,washegarinsa kawunta wanda shine ya riketa har ya aurar da ita kasancewarta marainiya toh shine ya taso ƙeyarta ya maido da ita gidan,ya hadasu ita da Alh Bilya ya musu faɗa sosai musamman ita yafi bawa laifi don ko kadan bata ƙyauta ba,yace karya kuma ji tawa mijinta rashin da"a don zaiyi mugun saɓa mata ne sannan yace maza Hafsa ta koma dakinta nan da kwana biyu bayason ya sake dawowa ya cimmata agidan,akarshe ya nemi gafarar Alh Bilya shi kuma yace ya hakura kuma ya maidata kodon albarkacin ƴa"ƴanta…
Awannan ranar Nabeelah ta sulale taje ta sami Andrew wanda ya matsa mata kansu hadu,ashe dai lambar Hafsa yakeson ya sata daga wayarta bawai ita din yakeson gani dagaske kamar yadda take tunani ba,shammacenta yayi ya cire lambar Hafsan wanda tayi saving da 'sweet sis' bata wani jima awajensa ba tayi gida gudun kar ah soma neman inda ta shige don tasan karamin aikin Ya Mukhtar ne yasamu information ɗin inda take ya biyota yaci kutumar ubanta ko agaban idon wanene babu abunda yasha masa kai dukanta zaiyi…
Su mami aka shiga gyaran Hafsa kai kace ko sabuwar amarya ce za"a