Showing 78001 words to 81000 words out of 102125 words

Chapter 27 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

1847

shi ba tare da sun samu karuwa ba, don ita burinta a rayuwa shi ne ta haihu musamman ma ta samu karuwar ’ya mace.  

Bayan mijin ya rabu da ita ne sai ta sake yin wani aure, cikin ikon Allah kafin shekara guda sai ta haifi ’yan biyu.  Ita ma waccan matar da ya saka tun da farko Allah Ya sa ta shiryu kuma ta yi wani sabon aure a wani gari, ita ma kafin ka ce wani abu ta samu karuwar ’yan biyu.To cikin ikon Allah mijin nasu nan ido ya raina fata, ya gano ashe matsalar daga wajensa take.  Nan ya shiga neman magani da kuma rokon Allah.  Allah Maji rokon bawa, cikin RahamarSa shi ma bayan ya sake wani auren ba a dade ba sai ya samu karuwar ’yan biyu.Kin ga wannan wata aya ce Allah Ya nuna a nan,Abin da ake nufi a nan shi ne idan irin hakan ta faru to ma’aurata su rika mayar da al’amarinsu ga Allah ta hanyar yin addu’o’i.Sannan awasu lokuta watakila rashin haihuwar ga wasu ma’auratan taamƙar rahama ce daga Allah,don sau da yawa wasu kan haifi ’ya’yan ne ba tare da ba su kyakkyawar tarbiyya ba,da hakan ke sa su gurbata al’umma.Toh a nan ina amfanin irin wannan haihuwa?

Fatarmu da addu’armu dai ita ce Allah Ya ba ma’aurata zuri’a tagari wacce za ta taimaka musu da sauran al’umma har su yi alfahari da su.Garemu wa"enda kuma bamu samu ba,muna addu’ar Allah Ya bamu,idan kuma bazamu samu ba toh mu cigaba da yin dangana mu mika al’amarinmu ga Allah,don Shi ne mabuwayi da daukaka.abu na ƙarshe kuma inason ki daina zargin kowa da rashin samun rabonmu don ki sani babu wani mahaluƙin daya isa bada haihuwa ko kuma ya hana face Allah,Hafsa inason ki dauki Mubeenah amatsayin ɗaya muke da ita don haka gudan jininta namu ne……mu cigaba da hakuri Hafsa karmu gaji watakila akwai wani abun alherin da Allah ya tanadar mana nan gaba...." Jamila ta ida magana tare dasa hannu tana dauke guntun hawayenta,sosai jikin Hafsa yayi sanyi kalau,zuciyarta ta cika da tsantsar nadama da kuma ƙaunar jamila,haƙika Jamila ta cika mace ta gari wacce tayiwa yawancin mata fintiƙau don ta tara abubuwa da dama,kamar:-kiyaye lokutan ibada,kiyaye sirrin miji,juriya da hakuri,wanka da ado,gyaran jiki,kwantarwa miji da hankali,gudun zargi,taimakawa miji,da kuma danne fushi...sam bata aikata kishiyoyin hakan kamar:-daga sautin murya akan na mijinta,cin mutuncinsa da kuma zubar mishi da daraja,da sauransu dai,ita dai burinta arayuwa shine ta kyautata masa da kuma ganinsa yakasance cikin farin ciki akodayaushe,haka zalika taga kansu ahaɗe ita da sauran abokan zamanta,toh meh zaisa itama bazatayi koyi da ita ba sannan ta watsar da makaman yakinta tunda dai babu riba azaman bariki...?

Rushewa tayi da kuka mai tsuma zuciya gami da kaiwa Jamilar wani zazzafar runguma tana fadi da rawar murya"Yah Jamila ki gafarceni wallahi na gano gaskiya kuma nadau miki alkawari daga yau zamu koma zaman lfy ne har karshen rayuwarmu,Ya Jamila ke ɗin ta dabance wallahi kuma rashinki acikin rayuwar Gidado tamƙar gurbacewar rayuwar tasa ne,nagode kwarai da gaske da kikayi namijin kokari wajen dawo dani kan hanya,wallahi ina kaunarki kuma zamu zauna lfy daga yanzu har zuwa sanda Allah zai kawo karshen zamanmu da juna....."

farin ciki fal zuciyar Jamila sai ambaton kalmar 'Alhamdulillahi' kawai take tayi aranta,ashe Baddo na tsaye ajikin kofar part ɗinta tana ta sauraron hirarrakinsu tana zubda ruwan hawaye,tsananin tausayinsu ya cika mata zuciya har taji aranta cewa bazata iya jure ganin ita ta haihu agabansu ba,yaushe ma har tazo gidan..?gaskiya ya zama dole tayi wani abu agame da wannan cikin,tasan yadda dan"uwan nata ya dora dukkan burinsa akan cikin ammh gara kawai ta zubdashi kodon azauna lfy,ta share hawayenta tare da yanke hukuncin neman shawara awajen maryam ƙawarta……



*****

Acan part ɗin Yumma ma,an kasa samun wanda zai lallashi wani don daga Gidadon,Yumma har Surayya da Ramlah rungume juna sukai suna ta kuka wanda ya cakuɗe da kukan murna dana baƙin ciki,Gidado sai maimaitawa yake tayi"Surayya Allah yasa kuci jarabawarku keda Mustapha!..." toh babu wanda ya dago abunda yake nufi akan shi mustaphan ,sun dai raya aransu cewa watakila yana musu addu"a ne akan rashin samun nasu rabon,bai wani jima ba yace zai tafi,su Ramlah da surayya suka matsa wai sai sun bishi suga Baddo,toh dayake bada mota yazo ba sai ya kira su Musa awaya yace suzo family house su daukeshi,ba"a wani dau tsawon lokaci ba suka iso alokacin yana tare da Hajju suna fira,bayan ya sallameta yabi sauran matan babannin nashi ya gaidasu sannan yafito suka wuce tare dasu Ramlar,har ya wuce koda wasa bai hango koda mai kama da Kasim ba,kuma hakan ba karamin dadi yayi mishi ba don ganinsa kadai zai tunzurashi aikata abunda bai shirya yi ba ayanzu...

Acan gida ma wani abun mamaki na musamman ne ya cimma,wato matayen nashi ne suka mishi kyakkyawan tarba tare da masa congratulations,sosai abun yashayar dashi madarar mamaki don baiyi zaton abun zaizo masa da sauki haka ba,gida ya rude anata celebrating kai kace ko abun cikin ƙwan ya riga yazo duniya ne,ana haka sai ga Sagir da Aliyu suma sun fado gidan,Sai tsiya suke ta mishi wai yakusa zamowa baban baby,can sai ga Surayya sun fito daga ɓangaran Baddo ita da Ramlah zasu wuce gida,idanunta dana Sagir suka sarke cikin na juna,gabansu yayi wani irin mummunar bugawa,atake duk suka ji taɓon soyayyar junansu da yayiwa zuciyoyinsu illa na neman komawa ɗanyen ciwo,itace tayi karfin halin dauke kallonta daga gareshi ta hanyar rausayar dakai kasa,cikin sanyin murya sagir ya dubi Gidado yace"Ashe mutuniyar ta shigo gari ban sani ba...?"

Daga masa kai kawai yayi ba tare daya ce mishi kala ba,su surayya suka karaso suka gaidasu duka sannan ta dubi Gidado tace cikin sanyin muryarta"Toh Hamma mu zamu tafi Allah ya inganta ya kuma raba lfy..." duk aka amsa da ameen,Aliyu ne ya kada baki yace"Am sury bari mu saukeku agida man don muma tafiyar zamuyi..." ya fada yana kallon Ramlah wacce sai wasa da jelar mayafinta kawai take tayi don gabaki daya acikin kwanakin nan ta rasa gane kanta,sosai take jin kunyar haɗa idanu da Hamma Aliyu,Gidado na lure da irin sakonnin da suke ta aikawa juna ammh sai ya fuske yayi kamar bai dago komi ba,saida suka sallami sauran matan sannan suka fito don tafiya,Ramlah da surayya da kuma Aliyun ne agaba suna hira ayayin da Gidado ke baya shida Sagir yana bashi labarin sakin da akayiwa Surayya,sosai abun ya girgizashi,hakika ya tausaya mata kuma har yanzu yana sonta don haka yace"Abokina idan har zaku bani ita toh zan aureta bayan ta gama iddah don har yanzu ina sonta....dama ni ban taɓa fidda rai akanta ba…" ya ida magana tare da sakin lallausar murmushi,

Hawaye ne yadan ciko idanun Gidado yace"Sagir hakika ka cika aboki na gari kuma masoyin kwarai....Allah yabar zaman tare..." ya fada tare dakai mishi side hug...bayan wucewarsu ne abokinsa wanda ya bashi aikin tracking Andrew ya kira yake fada masa cewa ai an gano inda yake zaune kuma cikakken sunansa shine *ANDREW ISAAC*

Godiya yayi masa sosai sannan ya yanke call ɗin,cikin hanzari ya umarci su Musa da suje har inda akace yana zaune suyi arresting ɗinsa sannan akaishi station gashi nan zuwa………✍

_*Addu’ar samun dukiya da ‘ya’ya masu albarka*_

Ga addu’ar nan kamar haka :

اللهم



أكثر



مالي



وولدي



وبارك



لي



فيما



أعطيتني

.

ALLAHUMMA AKTHIR MALIY WA WALADIY, WA BARIK LIY FEEMA A’ATAITANEE.

FASSARA : “Ya Allah ka yawaita dukiyata da ‘ya’yana. Kuma ka albarkaceni a cikin abinda ka bani”.

Albarkacin wannan addu’ar da Manzon Allah (saw) ya yi wa Sayyidina Anas bn Malik (ra), Sai da Sayyidina Anas ya rayu kusan shekaru ɗari (100) a duniya. Kuma da idonsa sai da ya ga fiye da ƴaƴa ɗari daga cikin zuriyarsa.

Haka nan sai da ya zamanto dukiyarsa ta yi albarka ta yawaita sosai. Har ma bishiyoyin dabinon gonarsa sau biyu suke haihuwa duk shekara.Allah ya azurtamu da ƴa"ya da kuma dukiya masu albarka (amin)👏





_*kuta hakuri mun kusa karewa kowa ya huta da zuba idanu akan hanya😊...*_

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

_*KISHIN MATA...!*_

_Na marubuciya Hafnancy..._

_akan naira 200kacal👌_

   _ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

   _*💫BABI NA TALATIN DA BIYU...💥*_

………Andrew da Nabila na manne jikin juna yana koya mata yadda ake zuƙar sikari,can ta ƙware don bata saba ba,hasalima wannan shine karonta na farko,ta bukaci daya bata ruwa ta kurba,dasauri yakai hannu ya dakko tumbler ɗin dake cike da ruwa yakai bakinta,babu ɓata lokaci ta kafa kai tana kurba sosai,ana haka nefa yaji ana bugun ƙofar apartment ɗinsa da ƙarfin bala"i babu sassauci,azatonsa ko abokan cin mushensa ne don sau tari sukan zo mishi abuge suta dukan ƙofa hakan yasa ya miƙe afusace yana gunduma musu ashariya,bayan ya buɗe ƙofar sai ya tura kansa waje,gabansa ne yayi wani irin mummunar faduwa ganin ƴan sanda biyu kowanne riƙe da akurki,har zai koma ciki sai Musa yayi saurin cafko hannunsa yana fadi da kakkausar murya"Are you Andrew Isaac...?" Ya furta yana sake duban hotonsa da aka turo mishi ta waya kuma tabbas ba ƙarya shi ɗinne azahiri…

Cike da tsoro Andrew yace"Yes yess am the one....meh nayi kuma..?" toh suma ɗin dai umarni ne kawai aka basu su kamoshi ammh ba"ayi musu bayanin laifinsa ba,hakan yasa Musa fuzgoshi waje yana fadin"Idan mukaje station zakaji laifinka acan..." wani irin kallon ƙasƙanci ya watsa masa kan yace"Excuse me plss..agaskiya babu inda zani don ban taɓa ji ko kuma ganin anzo arresting ɗin mutum ba tare da an gaya masa laifin da ake tuhumarsa dashi ba…ko kai ka taɓa jin anyi hakan…?" yayi tambayar yana duban ɗayan ɗan sandar wato inspector Ƙabir,sosai inspector kabir ya haɗe rai yace"Ashe kai kazo duniya don wasa ne...na sau nawa kuma...?wani ma har ah yanke masa hukunci ba tare da sanin takamammen laifin da ake tuhumarsa dashi ba,don kai kama gode munzo maka da suffar muminai shiyasa har kake da guts ɗin tsaremu da fitsararrun tambayoyi right…?

har ya buɗe baki zai sake magana sai inspector Ƙabir yayi saurin fuzgo hannayensa biyu yana fadi azuciye"Da alamu so kake muyi wasan ƴan gareji anan kuma ni ba"a haifeni don tsayawa ɓatar da lokacina akan ababen banza ba…i have many important things to do arayuwata don haka muje idan kaje can kayi bayani..." ya soma jansa bayan ya makala mishi handcuffs,hayaniyar da Nabila taji yayi yawa ne yasa ta fito sai gani tayi ana jan sarkin nata yana turjewa,aguje tabi bayansu tana fadin"su wayeku kuma ina zaku kai mun shi ne haka...?"

Afusace Kabir ya dubeta don shi baya barinta ta kwana yace"Baki ganin irin kayan jikinmu ne kike tambaya ko kuwa baki je school bane...?toh mala"iku ne kuma munzo tafiya dashi ne don ayi masa hisabi...." sosai abun yaso bawa seargent Musa dariya ammh sai ya cije don ba lokacin wasa bane,tabbas ta shaƙa da wannan baƙar maganar daya jefa mata ammh ta kasa maida martani don da gangan tayi tambayar if not kallo guɗa zaka musu kasan cewa ƴan sanda ne,haka tana ji tana kuma gani suka ingiza ƙeyarsa cikin mota,dama akwai wani ɗan sandar aciki ya kishingiɗa akan driver's seat,suna shigewa yaja motar sukayi gaba,

kuka ta rushe dashi sannan ta juya da gudu ta koma apartment ɗin,dake gidan haya ne shiyasa wasu suka firfito daga nasu apartment ɗin don ganin abunda ke faruwa sabida hayaniyar data janyo hankulansu,Nabila ta rasa ina ne zata saka ranta taji dadi ganin anyi gaba da masoyi,dama gashi hankalinta atashe yake don sati biyu kacal ya ragewa Andrew ɗin ya kammala abunda ya kawoshi sannan ya koma kasarsa ta haihuwa,haƙiƙa taso Gidado wanda har taci alwashin yin waje da ƴar"uwarta da kuma sauran abokan zamanta ammh yau da gobe shaƙuwarta da Andrew ya daɗa ƙarfi har take jin bazata iya rayuwa babu shi ba,shi kuma yace sai dai fa tayi hakuri bazai iya auranta ba sannan kuma tafiya zaiyi kasarsa da zarar ya kammallah abunda ya kawoshi,toh dalilin shiga tashin hankalin nata kenan har yakai shi da haɗata da codein da sikari don ya mantar da ita damuwarta.……ta kwashi kusan 30mins tana koke-koke can dai taga babu sarki sai Allah,ya zama dole ta dau hakuri da dangana in ba haka ba kuwa rashin hakurinta yana iya kaita ya baro,gashi dai yanzu batasan abunda ya aikata ba ƴan sanda sukazo suka tafi dashi,kuma idan ba Allah ya kiyaye bane matsalar tana iya shafarta,ga shaye shayen banza da wofi sannan kuma haka take fama dashi akan biye biyen ƴan mata,wai donma tayi nisa akan ƙaunarsa ne da tuni ta jima da rabuwa dashi don sam bata ƙaunar abu kishiya arayuwarta,worst part ɗin ma arne ne,ɗan aljihun baya na gaba da pastor ma,wato wanda kwata kwata baya sha"awar komawa wani addinin face nashi,sosai ya dulmiya acikin addinin kristanci,sai dai kuma ga riƙo da addinin ammh sam sam babu halin kirki……

Wangale baki tayi wai tana kuka gami da dora hannaye akai tana fadin"Wayyo Nabila kin kashe kanki...kin ɓata rayuwarki abanza gashi kazamin arne ya kaiki ya baro,wallahi na cuci kaina...." ta sake fashewa da wani sabon kukan,sai datayi mai isarta sannan tace"Lokaci yayi daya kamata na koma ga Allah don babu riba abariki,yanzu shikenan kazamin arnen nan ya mori banza kenan...?wayyo abun takaicin ma ba sau ɗaya ba kuma ba sau biyu ba,ya mori gangar jikina fiye da tunanin mutum don koshi karan kansa ma bazai iya kirga iya adadi ba....." kuka yaci mugun ƙarfinta ,daƙyar ta iya miƙewa ta shiga hargitsa kayayyakinsa tana fadin"Nima insha Allahu saina ɗanci wani ribar abun dakai,duk da cewa ka manna mun baƙin fentin da bazai taɓa gogewa azuciyata ba ammh still kaima ɗin saina ci moriyarka koda kadan ne…"

Idanunta ne suka sauka akan wani Rolex wristwatch ɗinsa worth 1.5million,sai sheƙi kawai agogon keyi hakan yaja ra"ayinta taje inda yake ta daukeshi tana jujjuyawa ahannu,tunowa tayi da randa suke tare,da ita dashi da kuma wani abokinsa,har abokin ke cewa idan har za"a siyar da wannan agogon ah Nigeria zai kusan clicking 2million sabida babu irinsa sosai anan,wani irin tsallen murna ta saki gami da juyawa da sauri zuwa ga jakarta ta jefashi aciki sannan ta kwashi yanata yanata tabar gidan bayan ta kulle apartment ɗin ta baiwa next neighbour ɗinsa makulli ya ajje masa………

*****

Baddo na zaune abakin gado riƙe da biology note ɗinta tana karantawa don very soon zasu soma WAEC,dazu ah makarantar ma shi take karantawa zazzaɓin ya rufeta (karku manta nace ah ss2 zata zana WAEC dinta tare dasu Ramlah) ta bada hankali sosai wajen karatun har batasan lokacin da Gidado ya fado dakin ba,sai ji tayi kawai an wufce takaddar daga hannunta,atsorace ta dago kai tana dubansa,taga ya rufe inda take karantawar ya ajja littafin still idanunsa akanta,ashagwaɓe tace"Haba Dee meye haka plss bani littafin in cigaba da karantawa kaga jarabawarmu na karatowa fa..." cikin sanyin murya yace"Anki abayar keda baki da lafiya shine kike karatu amaimakon kiji da jikinki da kuma lafiyar babyna you are here stressing yourself...exams ba gobe ba haka kuma ba jibi ba.....yanzu idan nace bazaki sake zuwa makarantar bafa...?"

Baki ya saki yana kallon yadda har hawaye ya soma cika idanunta,dasauri ta miƙe zata bar masa dakin hakan yasa yayi azamar cafko hannunta,ba tare data juyo gareshi ba tace"plsss sakarni in tafi…" da mamaki yace"haba uwar ya"yanah meh kuma yayi zafi ne haka...?" dasauri ta tari numfashinsa tana fadin"lallai abun mamaki baya karewa,wai ayau nine na tashi daga matsayin 'yarka na koma uwar ya"yanka,ko meyasa...?" ta ida magana tare da juyowa tana fuskantarsa dakyau,shiru yayi mata sai murmushin yaƙe da yaketa saki,dage masa gira ɗaya tayi tana fadin"uhmmm! am listening yi bayani..." ido cikin ido yake kallonta kan yace bayan ya sauke ajiyar zuciya"Tun aranar dana soma haɗa shimfiɗa dake ne kika tashi daga matsayin _*ƳATA*_ kika koma matsayin _*MATATA*_ ....ayau kuma bayan an tabbatar mun da cewa kina dauke da guɗan jinina shine kika samu ƙarin wani matsayin wato _*UWAR YA"YANAH*_ ....."

Rungumota zuwa jikinsa yayi gami da fashewa da kuka yana fadin"Mubeenah inasonki matuƙa don ke ɗin alherina ce…na rokeki plss karki bari wani mugun abun ya samu babyna,dan Allah ki daure ki haifomun shi lafiya,Mubeenah na dora dukkan burina ne akan cikin jikinki so pls try to make me the happiest man on earth ta hanyar haifomun shi...wallahi idan kika haifomun wannan ɗan kin gama mun komi arayuwa haka kuma na samu cikar burina………"

wani irin kukan tausayinshi ne ta fashe dashi ammh ta kasa furta komi,tunawa yayi da shawarwarin likita don haka yakai bakinsa kunnenta yana mata raɗa"Stop it uwar ya"yanah likita yace kibar shiga damuwa don hakan zai iya cutar da babynmu.." tureshi tayi tana mai kai masa duka aƙirji take fadi ashagwaɓe"Toh bakai bane kake jefamu cikin damuwar ba...?" riƙe hannayenta yayi yana dariya ƙasa ƙasa yace"Toh na bari bazan sake ba uwar ya"yanah..." yakai mata light kiss ah goshi,adaidai lokacin ne Inspector Musa yayi kiransa yake gaya masa cewa ai sun kamo Andrew gasu ma ah station dashi,yace gayanan zuwa yanzu yanzun nan,acikin mintuna goma yashirya ya fito ammh bai gayawa kowa cewa ga inda zashi ba ya fice....

****

Acan station kuwa Andrew ne ya matsawa su Inspector Musa wai sai sun gaya mishi wanda ya aikesu suyi arresting ɗinsa,inspector kabir ya dubeshi yace azuciye"Malam ka ishemu da tambayoyi fa...idan bakayi hankali ba wallahi zaka shiga cell,Allah na tuba ma ai kana jin sunan wanda yace ayo arresting ɗinka saika kusan cire kanka da hannunka,mtsww banza dakai kawai...."

Andrew yace shima afusacen"Toh waye shi inason na sani...?" Daga bayanshi yaji ance _*"DCP SULEIMAN ALASSANA GIDADO..."*_ dasauri ya waiga kallonsa ya sauka akansa yasha baƙin shade wanda baka iya ganin ƙwayar idanun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login