Showing 96001 words to 99000 words out of 102125 words
Chapter 33 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx
duka daga wajen Allah suke, ashe bawa bazai jajirce ba domin ganin ya cimma manufa ta hanyar rungumar ƙaddarorin da fatar cinye jarabawar…? lallai Allah na tare da masu haƙuri da kuma jajircewa, Akalla an shafe kusan watanni biyar kenan da afkuwar wa"ennan munanan al"amarun da suka gabata awatannin baya da suka shuɗe, acikin wa"ennan watannin kuwa abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa hadda sabon auren da Mustapha yayi, ya auri ɗiyar mai girma Gwamna mai suna Samha, alokacin da Gwamna ya tursashi akan lallai sai ya fada mishi damuwarsa toh shine ya sanar dashi irin cin amanar da tsohuwar matarsa ta mishi wanda har takaisu ga rabuwa, sosai mai girma Gwamnar jihar Kaduna Alh.Idris Aliyu ya tausaya masa shine har ya bashi auren ɗiyarsa Samha wacce gama karatunta kenan ah London ta dawo gida,
kuma sai aka taki sa"a dama can tana sonshi dake tana cikin sahun mata masu tsananin kunyar bayyana sirrin zuciyarsu shiyasa babu wanda ya taɓa sanin cewa tana son Mustaphan don ko shi bai taɓa dago hakan atattare da ita ba, shi kansa Mustaphan baiyi gaddama ba ya amsa wannan tsaddaden tayin don Samha Idris Aliyu ta kasance acikin jerin matayen nan wa"enda bazaka iya denying ba, ga ƙyau, ga gayu, ga ladabi da kuma kyautatawa mutane, uwa uba addini don samun damar fitarta wata kasa yin karatu bai sa ta canja daga yadda aka santa ba, infact ta ko wani angle sun dace ne ita da Mustapha, yanzu haka watanninsu uku da aure, wani abun ikon Allah kuma shine tana shiga Allah ya bata rabo, murna awajen Mustapha da yan"uwansa kuwa ba"a magana, sosai Mustapha keson matarsa kuma yake ganin hakurinsa ne yasa Allah ya azurtashi da mace ta gari, don kuwa watakila da"ace ya dauki kwakkwaran mataki ne akan Azeema da Mustapha toh kila da Allah yayi fushi dashi sa"annan ya kyaleshi da wayonsa, shiyasa fa hakuri kamar yadda DCP Gidado yace mabudi ne na fita daga kunci da kuma buɗowar kofofin alkhairi,
sanda zancen auren da kuma samuwar cikin Samha ya cimma Azeema, kadan ne kawai ya rage bata haukace ba, sosai tayi kukan nadama awannan ranar, ta dora laifin kacokam akanta akan cewa da tayi hakuri da yanzu itace da wannan cikin, sai dai kuma ta wani fuskar ba da don ta nemi kasim da kuma tonuwar asirinsu ba tofa da Hajiyarsu Kasim bata tona kanta har ah ƙarya sihirin data musu ba, Allah kenan mai yin yadda yaso aduk kuma lokacin da yaso, yakan tsara al"amari ne ya afku ta dalilin wani al"amari can, zata dai rungumi kaddararta ta kuma cigaba da neman gafarar ubangiji don ayanzu bata da wani sauran amfani arayuwar mutane sabida har gudun shiga sabgarta ake ma, da ita da useless duk daya suke, bata da wani sauran jindadi ko agidan iyayenta, tsangwama, kyara da tsana duk suke gwada mata, awajen kanwarta Zuby ne kawai take dan samun sassauci wasu lokutan, Azeema duk ta jeme ta lalace gami da ramewa tamkar mai ciwon Aids, ƙarshen alawa dai dama ance kasa ce,
Aɓangaran su Gidado kuwa, tuni Baddo dasu Ramlah suka jima da zana waec ɗinsu, adaddafe Baddo ta karashe jarabawarta sabida laulayin daya tasata agaba, ayanzu haka cikin yadan taso gaba, kuma sosai yayi mata kyau abun dai gwanin ban sha"awa, Allah mai iko dama ance mahaƙurci watarana Mawadaci Ne, ai haka ne al’amarin yake kasancewa, amma fa sai da dauriya, sai an daure, jarabawa ce ba kuma kowa bane yake samun nasarar cinta ba. , sai dai ana dan dadewa ba a je ba, yawanci abinda aka rasa ke nan wato shi hakurin kome so ake yi ayi shi cikin gaggawa, to amma ai shi kamar yadda na fada, dole ne sai an samu amfani da shi hakurin tukuna kafin a samu damar cimma buri na rayuwa. Ita watarana din ai bata da wani tsawo ko kuma wata gajarta, saboda ai cikin dare daya ne Allah kan halicci shi Bature. Ire iren wadannan abubuwa sun faru al’amarin kuma ana iya cewa yafi kudin duba, sai dai kawai idan ba ayi kacibis da irin hakan ba. Wasu suna ganin hakuri kasawa ce, da kuma gazawa ga mai yin shi ,tamkar ma wani bata lokaci ne, to amma sannu a hankali, watarana da zarar al’amura sun canza, sai kuma a manta da dukkan, al’amarun wahalar da aka shiga, kafin a samu shigowar wannan hali. Jarabawa ce a al’amarin yin hakuri sai duk wanda ko wadanda suka shiga cikin irin wannan sun daure, amma fa abin yana da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Saboda ana shiga wani babban gumurzu da gwarmayar rayuwa, kusan wani zai ga duk inda ya dosa ko abinda ya nufa ai ba wata sa’a, har ma ya rika tunanin yaya dai shi rayuwar ta shi bai gane ba, kamar ma ya rako wasu ne ko ina yaje yaga tamkar duk an tsane shi, al’amarin duk ba haka bane. Shi al’amarin sai ana yi ana kawar da kai, ko an ji a nuna kamar ba aji ba, ko kuma an gani sai a nuna tamkar ma makahon daya rasa danjagora ne, sai abubuwa su tafi yadda ba ayi tsammani ba. Idan kuma ba haka ba, da ance kulle shi wanda ko kai wanda aka yi wa ita maganar ka ce cas, ko kice, ko kuma kuce, to idan ba sa’a aka yi ba, ana iya haduwa da bacin zuciya. Dalili kuwa ai su wadanda ke irin wadannan maganganun , ai suna ganin kamar da akwai alamun wani haske ne a gaba, shi yasa hakan take faruwa, watakila idan suka yi sa’a, sai ayi hushi a daina yin ita gwagwarmayar , dama ai haka suke bukatar gani. Idan kuma hakan ta samu sai su bullo da wani sabon salon, saboda ai su suna dasu daban daban, na nuna hassada da kuma keta ,wadda ake cewa ga mai rabo taki ce, ai shi Allah madaukakin Sarki shi ke da na shi al’amarin duk yadda suke so ba haka bane suke gani, saboda shi yasa ma wadanda suka iya azancin magana, su kan ce. Kana naka Allah na na shi, ko kuma suna nasu Allah na shi, kowa kuma ya san na Allah shi ne bai faduwa kasa banza. Wasu sai dai su gaji su bari saboda murucin dake ruwa shi sam bai san ana rana ba. yau ina Azeema…?bata fadi ba...?
Ita fa Jamila...?Bata ci ribar hakurinta ba...?tabbas kuwa taci riba domin kuwa wani babban dadadar albishir ɗin shine an wayi gari watarana Jamila nata haraswa, koda akaje asibiti gwajin farko aka tabbatar musu da cewa tana dauke ne da juna biyu, murna awajen Gidado, su Baddo ,mutanen Jamila da dangin mijinta abun ba"a cewa komai sai kallo, hatta dasu mamin Hafsa wacce ta saukko duk sun tayata murna da kuma addu"ar Allah yabawa yarta itama ,mamin Hafsa itace hadda zuwa neman gafarar Tsoho da Yumma kan su yafe mata kazafin da tayiwa Yummar, suka nuna mata cewa su din yan halak ne ta hanyar yafe mata, yanzu watannin cikin Jamila 3 ne cif cif ayayin dana Baddo keda watanni 5 da sati uku, ko kadan Hafsa bata musu Hassada don zama da Jamila yau da gobe yasa ta hankalta, ta zamo mai tsananin hakuri da kuma tawakkali, ammh duk da hakan dole ta shiga cikin damuwa ta rashin samun nata rabon, sai dai kuma zata zamto mai hakuri kamar dai jamila don da haihuwar da kuma rashin duk yana ga Allah ne,
Aɓangaran kasim kuwa sosai yayi nadama yakoma ga Allah don ah iya tsawon arayuwarsa ya ɓatashi ne wajen saɓon mahaliccinsa, ya dukufa sosai wajen neman gafara da kuma rahamar ubangiji ta hanyar yawan azumi, tsayuwan dare da kuma yawaita sadaƙa, yakoma shiru shiru abun dai gwanin ban tausayi, dakyar alakarsa data su Mustapha ta daidaita ammh kunsan na ciki na ciki, baza"a ta6a mantawa ba haka kuma trust ya riga ya rushe, Sagir abokin Gidado kuma an aura masa muradin ranshi wato Surayya,haka Aliyu da Ramlah da aka gano cewa suna soyayya aɓoye shine aka musu aure, ko wani angle is equal and balance now, Hafsa ce kawai ta rage Allah ya amsa addu"ar,
watarana tana zaune ah falonta tana kallon wani india film, taga wata mai ciki yadda mijinta ke tarairayarta habawa ai batasan sanda hawaye ya soma zubar mata ba, ahaka Jamila da Baddo suka shigo suka sameta, bata masan sun shigon ba ji tayi kawai an taɓota, dago idanunta da zatayi sai kawai suka haɗa idanu da Jamila, fashewa tayi da kuka mai taɓa zuciya gami da rungumo kafarta tana fadi"Anty Jamila sai yaushe Allah zai dubeni ne...? kodai haka zan karashe rayuwata babu haihuwa…?in har kuwa hakane matar nan tafi cutata…" kuka ya sake cin ƙarfinta, Jamila da Baddo suka kalli juna hawaye na shirin ziraro musu na tausayin yar"uwar tasu wanda ya gama zame musu jiki don kusan kodayaushe acikin wannan halin suke kasancewa har sai Gidado ya tsawar musu suke ɗan sassautawa, cike da dauriya Jamila ta zauna agefenta tana mai sakin jererren ajiyar zuciya kan tace"Haba Hafsa meyasa ke baki jin kalmar hakuri ne...?shikenan hakanan zamu cigaba kullum muna jefa kanmu cikin damuwa, bake ba bamu ba haka kuma ba mijin namu ba salon mu ballowa kanmu wata ciwon...?ki duba fa na kwashi kusan shekaru 10 ina kukan haihuwa ammh yau fa...? ba gashi gari ya wayemun ba...? Shin banci ribar hakurina ba...?ko kuwa kinason kicemun niche na bawa kaina haihuwar ko kuma Hajiyar Kasim...?
saurin girgiza kai tayi tana fadin"A"a ko daya Allah ne ya baki ba ikon mutum ba..." cike da tausayinta Jamila ta cigaba"Toh meyasa kema bazakiyi hakuri ba ki zubawa sarautar Allah ido...?kai bai ma ci ace har kin soma sanya damuwa aranki agame da rashin haihuwa ba sabida dududu ko cikakken shekaru 2 baki cike ba da aure, haba Hafsa meyasa kike da gajen hakuri ne...? ki sani fa Ita watarana din ai bata da wani tsawo ko kuma wata gajarta, saboda ai cikin dare daya ne Allah kan halicci shi Bature....yar"uwata mu cigaba da addu"a insha Allahu Allah na sane dake bai manta ba, sa"annan kuma ki sani abunda zamu haifa kema naki ne domin kuwa baki da banbanci damu....."
"Hakane kam don kuwa ke ɗinma mahaifiyace ga abunda zamu haifa……" acewar Baddo tana kuka, da azama ta mike ta rungumesu duka tare da fashewa da sabon kuka tana gode musu, suma din kukan sukeyi, basu san da zuwan Gidado ba sai ji sukayi yahaɗesu ya rungume yana fadin"Allah ya muku albarka matayena....aljannah itace makomarku insha Allah....." da ameen suka amsa don sosai yake jin dadin yadda suka haɗe kawunansu wuri guda tamƙar yan"uwan juna, haka zalika kuma yana matukar jindadin yadda suke bawa Hafsan magana da kuma kwantar mata da hankali, aransa yace da"ace haka matan duniya suke gabaki dayansu, toh da kowani namiji yaso ajje mace fiye da daya don agaskiya bazai ɓoye ba ayanzu sosai yake samun farin ciki da kwanciyar hankali agidansa, ga kulawa ta kowacce ɓangare don har sai ya rasa ma ko waccece tafi iya kula da miji aciki, ammh yasan abu daya ne, sarauniyar mata wato Jamila ce ta dorasu akan hanya,
_*AFTER 8MONTHS 3WEEKS*_
kwanci tashi dai babu wuya awajen Allah, gashi dai an shiga watan haihuwar Baddo, don haka at any moment from now ana jiran taran baby ne, shirye shirye ake bana wasa ba, idan kaga yadda Gidado yafi kowa dokin zuwan babyn sai abun ya saka babbaka dariya ma ishi, domin kuwa muddin ya saka kafa ya fita sai ya dawo da kayan baby kona 'ya mace kona ɗa namiji, acewarsa ba"a san wanne ne za"a haifa ba kuma gana Jamila ma na kan hanya ai, abu hadda kayan wasa fa kai Gidado ba sauki,
Ayau litinin aka wayi gari da tashin hankali mai girgiza zuciya domin kuwa tun adaran jiya ne akayi rushing Hafsa zuwa asibiti, gwajin farko aka gano cewa hawan jini ne yayi mata yawa sosai ah 'yan kankantar shekarunta 28, an dai bata taimakon gaggawa ammh abun sai dai kawai mu zubawa sarautar Allah ido, tana dakin da aka kwantar da ita, sai da aka kwashi kusan awanni uku tana hutawa kafin abari ashiga ganinta, yan"uwanta ne da kuma dangin mijinta duk sune suka cika dakin, Jamila da Baddo zaune kusa da ita sun rirrike mata hannu suna.cizgar kuka, dakyar Hafsa ke magana"Anty Jamila Anty Baddo (kasancewar haka take kiran Baddon itama) kubar kuka akaina donni na riga nasan tawa ta kare, bazan sake kwana aduniya ba, zanyi kewar zamantakewarmu Anty Jamila ko kin tuna..?irin kalar rikicinmu abaya...?
Daga mata kai tayi alamun ta tunan, murmushin karfin hali ta sakar kan tacigaba" Hakika na fitineki afarko kafin daga baya na dawo kan hanya tare da taimakonki, kiyi hakuri ki yafemun, Baddo kema inason ki yafeni, mami kuma ku yafemun kuma ku tayani nemar gafarar Daddy da Suleiman donna tabbata bazamu kai ga ganawa ba....ina sonku dukah...." maganarta ta yanke bayan taja wani dogon nishi da kalmar shahada, wani irin zabura Jamila tayi tana fadi da karfi"Hafsaaaaaaaaa! dan girman Allah ki tashi bazan iya rayuwa babu ke ba, karki tafi plssss..." sauran yan"uwa ma suka yo kanta da kuka, wasu suka je kiran likitoci, isowarsa kenan aka ga Baddo ta zube akasa shock ya kamata sosai, don ba"a taba yin mutuwa agabanta ba, can sai ga jini ya balle mata, idanuwanta tamkar zasu fado waje tsabar shock din da take ciki, tuni aka koma kanta, aka kira wasu nurses suka azata kan wani gado aka gurgura da ita dakin haihuwa don likitan fadi yake da karfi"ku hanzarta haihuwa ce..."
Jamila ta rasa inda zata saka kanta alokacin da likita ya tabbatar da cewa Hafsan rai yayi halinsa, asibiti ya ruɗe da kukan masoyanta, shi kansa Gidado sanda zancen mutuwar ta iskesa yasha kuka, ga kuma halin da Baddo take ciki ayanzu, itama din sai du"a"i, haka ya daure yaje don ganin gawar matarsa yana fadin"Allah sarki Hafsa..! Allah yaji kanki yasa aljannah ce makomarki..."
Alokacin daya bude zanin da aka rufe gawar Hafsan dashi Jamila na kusa dashi ta dora kanta akan kafadarsa tana rusar kuka, fuskar Hafsan dauke da murmushi tamkar ka kirata ta amsa, cikin muryar kuka Jamila tace"Gidado yanzu shikenan yar"uwata ta tafi bazamu sake ganinta ba...?da gaske ne Hafsa ta rasu..?" Cike da jarumta yace hawaye na ziraro mishi"kwarai kuwa Hafsa ta tafi ta banmu, saidai kuma naji dadin ganin yanayinta don ga dukkan alamu ya nuna cewa tayi mutuwar shahadace, Allah sarki tana ta neman na duniya bata samu ba sai gashi Allah ya bata na lahira, Allah yasa can ya fiye miki nan matata, Allah ya rahamasheki..."
Dasauri ya maida zanin ya rufe yana mai rusar kuka, can yace"Ah hanzarta kaita gida ah suturtata domin kuwa mamaci bayason jinkiri.." babu ɓata lokaci aka gurgura da gadonta zuwa waje inda ambulance already yana jira, yan"uwa sai kuka.............✍
_*wani hali Baddo take ciki ayanzu..?*_
_*HAFFY MOUSTY🌷*_
_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_
_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_
_*KISHIN MATA...!*_
_Na marubuciya Hafnancy..._
_akan naira 200kacal👌_
_ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_
_*💫BABI NA ARBA'IN...💥*_
🔚
……Samha matar Mustapha da kuma Goggo Boddiya sune aka bari awajen Baddo, Jamila kuma ta tafi gida don ashirya yar"uwarsu akaita gidanta na gaskiya, Aliyu da Ramlah kuma suna kan hanyarsu ta zuwa da kayan baby don tunda akace haihuwa ne aka kirasu awaya akace su bi gidansu Gidadon su kwaso mata kaya, kasancewar alokacin su basu riga da sunzo asibitin ba, basu wani ɓata lokaci ba suka iso ammh duk da hakan likita nata faɗa, su dai hakuri ne kawai suke ta bashi, ita Ramlar ta haɗe ne dasu Samha ayayin da Aliyu ya koma don ya samu sallar jana"iza, ba"a wani ɓata lokaci ba aka suturta Hafsa aka miƙata zuwa ga gidanta na gaskiya, masoya sunsha kukanta bama kamar Jamila wacce sau biyu tana suma, tama fi bawa kowa tausayi akan mamin Hafsan ma, don itace ta koma tana lallamin Jamilar,Allah sarki Mutuwa tilas ce babu makawa daga gare ta, kuma ba a guje mata, za ta riske mu a cikin gidajenmu da kan duwatsu da sararin sama da karkashin ruwa. Mala’ikun da ke cikin sama ma ba su tsere mata, haka mala’ikun da ke cikin kasa. Babu wani mutum ko aljani ko dabba da zai tsere mata, koda ta kasancewa a cikin gidajen masu tsaro da dogayen katanga ne, “Duk inda kuka kasance mutuwa za ta riske ku, koda kuna cikin gidaje masu cike da tsaro.”
Da ana kubuta daga mutuwa da mutum ya ba da jikinsa da karfinsa da dukiyarsa da wadatarsa da iko ko mulkinsa da duk abin da ya mallaka domin ya kubuta daga gare ta. Haka ayau Gidado yake ji inama ace idan ya sadaukar da duk wani abunda ya mallaka ana iya dawo mishi da Hafsarsa daya sadaukar ammh ina idan lokacinka yayi dole ka tafi, cikin kankanin lokaci ya shiga ransa sabida sosai ta canza zuwa mutuniyar kirki, dama zaka ga mutum yana aikata ba daidai ba arayuwarsa ammh da zarar mutuwa tana kusantoshi sai kaga Allah ya shirya abunsa fiye da zatonka, Wanda Allah ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda kuma ya ɓatar to babu mai shiryar da shi.Allah yaji kanki Hafsa yasa can ya fiye miki nan, Allah ya cika miki burinki acan (Ameen)
**
Acan ɓangaran Baddo kuwa ansha baƙar wahala akanta don ta kasa haihuwa da kanta, gabaki ɗaya kuma yan"uwa sai hankali yakomo kanta, ita karan kantan batasan inda take ba, sosai Gidado ya sake shiga cikin tsantsar tashin hankali mara misaltuwa, tsoronsa ɗaya karya sake rasa wata matar, hakan yasa yace da babbar likitan sanda yazo yake fada masa cewa dole ne fa ashigar da ita theatre if not ana iya rasata, cike da tashin hankali yace"Likita koda za"a rasa ɗan ne babu damuwa