Showing 69001 words to 72000 words out of 102125 words

Chapter 24 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

1848

son da take mun ke bakimun irinsa ammh dede da rana ɗaya bata taɓa nuna haukan kishi akaina ba sai ma jawoni kan hanya da take yawan yi idan har na nemi kauce hanyar,juz take a look at her she's so different in many ways,why cant you juz be lyk her..?Allah na tuba ba dadun fitinar tsoho ba an gaya miki zan auri mace kamarki ne marasa tarbiyya..?infact da babu kishiyar dazan karawa my meelat sabida ko kusa bata cancanci hakan daga gareni ba,don haka kidauki aurena dake amatsayin kaddarar rayuwarki sabida azahirin gaskiya bamu dace ba kawai Allah ne ya kaddara aurena dake,infact Hafsa idan kika kuskura kika kaini bango zan karashe yanke igiyar data sauran mana,in jefar da ƙwallon mangwaro kowa ma ya huta da guɗa……………"

Jamila ce tayi saurin katseshi don ta lura ɓacin rai na neman sakashi aikata ba daidai ba"Sahibu pls stop it....bai dace ka mata fada agabanmu ba kamata yayi kaja hannunta ku shiga daga ciki cuz you all need a privacy...." afusace ya dubeta yace"Ita bata isa in ja hannunta zuwa ciki don nutsar da ita kan abunta ta sani ba,tunda har ta iya cin mutuncin mijinta agaban matayensa bbu ko daraja toh meh zaisa ni naji kunyar disgata agaban kishiyoyinta...?" Baddo tace daƙyar cikin dauriya"Hamma kayi haƙuri Allah ya huci zuciyarka....." sai yaji duk zuciyarsa ta ɗanyi sanyi ya dubeta yace ahankali yana murmushi"Thanks baby..." ita kuwa Hafsa wani irin kukan haushi ne ta rushe dashi don sosai ta shaƙa da wannan irin cin fuskar da yayi mata agaban kishiyoyinta,ba don tana tsoron ya saketa ba da wallahi saita shuka masa rashin mutuncin da har ya mutu bazai taɓa mantawa da ita ba,ammh haka dai ta hakura ta koma part ɗinta tana cizgar kuka…duk suka bita da kallon Allah ya shiryeki,

Ba"a wani jima ba sai ga DR.Anwar ya iso ya dudduba jikin Baddo sannan ya haɗa mata magunguna,hadda allura ma saida yayi mata sannan yace akyaleta ta samu ta kwanta ta huta bayan tasha magunguna sabida zafin jikin ya sauka,haka ko akayi bayan tasha magungunan ta kwanta,ba"a wani jima ba bacci ya kwasheta don idan zaku tuna taci bashinsa adaren jiya,shi kansa gogan agefenta ya kwanta ya rungumota jikinsa,Zafin jikinta na gogan nashi jikin ahakan bacci mai nauyi shima yayi awon gaba dashi dauke da murmushi asaman fuskarsa,bayan awa biyu Jamila ta leƙo dakin don ta gaya mishi cewa lunch is ready sai kuma ta iskesu acikin wannan yanayin,murmushi kawai ta sakar tare dasa hannu tana dauke guntun hawayen daya ziraro mata kana ta koma main parlour tana jiran farkawarsu,Hafsa kuwa tunda tayi shigewarta bata sake fitowa ba....

Sai kusan azahar suka farka,itace ta rigashi farkawan don motsinta yaji sannan ya buɗe ido,murmushi ya soma sakar mata tare da taɓa jikinta yaji shi sanyi qalau alamun zazzaɓin yadan sauka kenan,sake kankameta yayi yana shafar kanta yace"Babyn Dee ya jikin dai...?hope da sauki dai ko..?" murya kasa kasa ta amsa mashi"Da sauki sosai..." yace"Bari in kira Yumma ku gaisa don dazu ta kira tana tambayarki nace mata baki ji dadi ba tace idan kin tashi in kirata ta gaisheki...." bata ci masa musu ba ya latsota suka gaisa ɗin haka kuma ya ƙira ummanta itama suka gaisa har yabbanta sai congratulations suke ta mata akan makarantar da zata cigaba,sun mata fada sosai akan ta daraja auranta dakyau banda wasan banza da samari,sun dade suna wayar kafin daga bisani sukayi sallama,Jamila sai nan da nan take tayi da Baddo tamkar zata maidata ciki don tattali da kuma kaunar da take mata,haka shima Gidadon wata irin kulawace ta musamman yake gwada mata kamar bashi ba har dai kwananta yakare ya koma wajen Jamila...kuma sosai Baddon ta ware ta samu lafiya da kuma ƙwarin jiki.....

******

Akwana atashi dai babu wuya awajen ubangiji,rayuwa ta shuɗa,kwanaki nata sauri,awanni da mintuna kam ai ba"a cewa komai don abubuwa da yawan gaske sun faru acikin watanni hudun nan,ciki kuwa hadda soma makarantar Baddo ah AMERICAN INTERNATIONAL SCHOOL ABUJA....dama SS2 zata shiga toh Gidado yace ah SS2 din yakeson ta zana waec ɗinta tare dasu Ramlah kenan,sannan kuma ya siya mata waya na kanta wanda hakan bakaramin dadi yayi mata ba,babbar kawarta amakaranta wato Maryam ta sanyata ah groups na gyaran jiki,girke girke da sauransu dai,akullum boys ɗinsa ke kaita su kuma dawo da ita ammh koda wasa bai taɓa zuwa makarantar ba,wani irin soyayya ce da kuma shaƙuwa mai tsananin gaske ne ya shiga tsakaninsu gashi kuma tana tsananin ganin girmansa da kuma darajashi,sanda akayi hutun first term ya barta taje ganin iyayenta acan kano harma tadan musu kwana biyu sannan ta dawo,yanzu haka satinsu biyu da komawa makaranta kuma sosai take bada himma wajen karatu don tana cikin sahun best students ɗin da akeji dasu amakarantar,sannan kuma idan ka cire maryam da sauran school authorities ɗin ba kowa ne yasan da cewa tana da aure ba…

Aɓangaran Azeema da Ƙasim kuwa abun nasu ba"a magana don akullum lamarin sai kara girmama yake,dazarar mustapha yasa kafa yabar gari tofa babu ɓata lokaci zata nemi Ƙasim yazo sai su sheƙe ayarsu son ransu,wani abun tashin hankalin da suke ciki ayanzu bai wuci yadda shi Kasim ɗin ya haukace akan sonta ba don har cewa yayi bazai iya rayuwa ba tare daya lasa zumarta ba😅,har kuka yake mata kan dan Allah ta nemi saki wajen mustapha ta fito sannan su gudu subar gari suje can adaura musu aure awani wajen,har mari yasha aranar daya kawo mata wannan zancen ta rufeshi da masifa tamƙar zata cinyeshi ɗanye,tace ahir ɗinsa karya kuskura ya sake kawo mata makamancin wannan zancen in kuma ba haka ba ransa zaiyi mugun ɓaci,ya tsaya amatsayin data ajjeshi kawai....

***

Ayau ne Andrew ya yanke shawarar neman Hafsa awaya kuma ayau ɗinne Gidado keda kwana awajenta,bai tashi ƙira ba sai misalin tara da rabi na dare alokacin Hafsan na wanka shi kuma gogan na miƙe saman gado yayi matashi da pillow,idanunsa acikin wani farin glasses sai danna dannen system yake tayi,wayar Hafsa tun dazu ya dameshi da kara kuma new number ne gashi ita kuma kamar an riketa ah bathroom ɗin taki fitowa,can yaja tsaki cike da haushi yayi picking call ɗin ya kange akunne ammh uffan baice ba ya kasa kunni yana sauraro,ajiyar zuciya Andrew ya sauke sannan yace"Haba baby ada bakiso daga wayar bane…?kiris ya rage kisa zuciyata neman yin bindiga sabida rashin ji daga gareki........."

Cike da tsananin mamaki Gidado ya doka masa tsawa"waye kai...?are you aware dat matar aure ce ka kira kuwa.....?" with greatest shock Andrew yayi saurin yanke call ɗin atsorace tare da kashe wayar gabaki ɗaya jikinsa na mugun rawa don bai taɓa kawowa aransa cewa mijin Hafsan ne zai dauka ba ita ba,

Zuciyar Gidado ya shiga bugawa da sauri sauri yana mai jin wani irin ɗaci aransa,wato ashe Hafsa ma wasu mazan take bi awaje da auranta,adaidai lokacin ta fito wanka ko kallon inda yake batayi ba ta nufi dressing mirror,afusace yace cikin hargowa"ke Hafsa zonan...." ya fada babu ko digon fara"ar atattare dashi hakan yasa ƴan hanjin cikinta canza wajen zama…ganin zata ɓata masa lokaci ganin irin kallon mamakin datake binsa dashi yasa kawai ya miƙe ya tunkare inda take zuciyarsa na suya…………………✍

_*HAFFY MOUSTY🌷*_

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

_LITATTAFIN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

_*KISHIN MATA...!*_

_Na marubuciya Hafnancy..._

_akan naira 200kacal👌_

_ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

_*💫BABI NA ASHIRIN DA TAƘWAS...💥*_

"Hafsa yaushe kika fara bin maza ne da aurenki ban sani ba...?" ya fada cikin murya mai bayyana zallar ɓacin rai yana mai tunkaro inda take,ai batasan sanda ta jefar da comb ɗin hannunta ba tsabar kaduwa da tayi da kalaman da suka fito daga bakinsa,da rawar murya tace tana buga ƙirjinta"Ni Hafsa Bilyaminu nake bin maza kuma da auranka akaina...?wannan wani irin kazafi ne haka plsss dear in wasa kake ma ka daina banso bcoz this is an expensive joke....." ta ida magana tana sakar masa murmushin yake ammh acikin zuciyarta ji take tamƙar ana luma mata wuƙa ne tsabar radaɗin da takeji da irin wannan sharrin daya liƙa mata,wani irin gigitacciyar tsawa ya doka mata yace in high degree of annoyance"Keep shut...! mutuniyar banza da wofi kawai wacce batasan darajar aure da kuma mutuncin kanta ba,zan miki ƙarya ne bayan ina da ƙwaƙƙwaran shaida da kuma hujjar hakan...?dake nake answer me now nace zan miki ƙarya ne...?"

Ya ida magana tare da shaƙo wuyarta sosai,ta shiga kakari da fidda numfashi dakyar don ba karamin shaƙa bane yakai mata,Gidado ko bayason mace ya tsani ya ganta tana aikata kazanta irin wannan balle kuma abune wanda yake matsayin mallakinsa ai kuwa yazama dole yaji zafi da kuma kishin hakan sosai,hannaye tasa tana kokarin ɓanbare hannun daya shaƙeta dashin ammh ta kasa don ƙarfinsu ba ɗaya yake ba,yace cikin rauni uwa zai saki ɗan marayan kuka"Inata zargin baby akan tana biye biyen maza tun ban aureta ba,infact har ƙiranta nake da ƴar iska kuma saita amsamun don kawai kuskure ɗaya data so tafkawa ammh ban tsaya wani dogon bincike ko nazari ba nayi concluding akanta har nake mata mummunar zato,sai dai kuma kinsan meh..?"

Yasan bata da damar amsawa hakan yasa yacigaba da maganarsa dauke da mirmushi asaman fuskarsa"Wato wani abun mamaki shine ashe baby ta tsaremun mutuncin kanta har ta kawo munshi cikin gidana and dat made me to love her so much,inata mata kallon ƴar iska wacce ta gama tambaɗewa tun awaje ashe gani da tantiriyar ƴar iskar acikin gidana wacce ta gama rabawa kattan banza kayan dadin tun awaje kuma har yanzu binsu take da aurenta akanta.........Hafsa gara kawai in kasheki kowa ma ya huta..." ya ida magana tare da hankaɗata ta faɗa saman gado,wani irin wahalalliyar kuka ta saki mai tattare da kayan haushi da takaici,tace tana zubda ruwan hawaye"Suleiman ka kirani da kowani irin suna ne daka ga damar kirana dashi bazan ji zafi ba donna san tabbas kafin dai nayi aure nayi biye biyen maza ammh banda yanzu da nake da auranka akaina,wallahi ka yarda dani ni Hafsa duk iskancina dai bazan taɓa iya cin amanar aure ba,plsss na hadaka da girman Allah ka gayamun inda ka jiyo wannan baƙin kazafin wanda babu abunda na fahimta aciki illa so ake kawai ashiga tsakaninmu don asa ka karashe warware igiya ɗayan data sauran mana......"

kasa tayi ta dafe kafafunsa tana cizgar kuka tamƙar ranta zai fita take fadin"Suleiman sai mun dunga kai zuciyoyinmu da nesa don tabbas muna cikin tsaka ne mai wuya,wato saki ɗayan daya rage atsakaninmu dole zamu dunga fuskantar kalubale ne da yawa,shaiɗan zai dunga haddasa faɗa tsakaninmu don kawai karmu zauna lafiya wanda aƙarshe zaka sakeni,plssss ka zauna kayi nazarin kalaimana karka kuskura ka yanke hukunci ba tare daka tsaya kayi dogon nazari da kuma bincike ba,wallahi so ake arabamu ammh wallahi ni Hafsa bana committing adultery sharri ne kawai,Suleiman karka sakeni don darajar iyayenka...." ta ida magana cikin matsanancin kuka tare da kankame kafafunsa,wani irin sanyi ne jikinsa yayi sai yaji kawai ta bashi tausayi har kuma zuciyarsa na neman aminta da cewa tabbas nema ake ashiga tsakaninsu,runtse idanu yayi yace cikin sanyin murya"Tashi kije kisa kayan bacci..." dasauri ta miƙe tana kallonsa da jajayen idanu kan tace cikin shessheƙa"Waya faɗa maka wannan maganar Suleiman...?" Wani irin takaici ne yaji kawai ya lulluɓe masa zuciya na ganin kamar ita bata masan anata ƙiranta awaya ba,ajiyar zuciya ya sauke kan yace"Karki damu i can handle everything myself..." yana gama fadar hakan yakoma kan gado riƙe da wayarta ahannu yana kokarin son yaga ya haddace lambar Andrew akai,ita kuwa wawiyar tunanin wai kiranta akai awaya ko kadan bai faɗo ranta ba illa Jamila data faɗo ranta,tasan tabbas itace ta kulla mata wannan sharrin tunda dama can tasan da bad side ɗinta,wani irin baƙin ciki da kuma tsanar Jamilar ce ya kanainaye mata zuciya,ta dauki alƙawarin cewa insha Allahu sai itama ta rama kuma ramuwar gayya mafi muni...

Bayan Gidado ya gama haddace lambar sai kawai yayi deleting ɗinsa ah call log ɗinta sannan yayi connecting ɗuk ƙiran da zai shigo wayarta tofa shima ɗin zai shigo nashi ne,tanan ne zai gano bakin zaren,haka dai duk suka kwana kuma suka wayi gari cikin rashin walwala da kuma annurin fuska.

washegari da wurwuri yafice wajen aikinsa,Baddo ma an tafi kaita makaranta sai gida ya rage daga Hafsa sai Jamila aciki duk da cewa itama Jamilar very soon zata fice don tana son taje boutique ɗinta ne ta dubo kayayyakin da tayi ordering wa"enda suka iso adaran jiya,gama shirinta kenan har ta dauki jakarta da kuma tsaleliyar wayarta sai kawai taga Hafsan ta banko mata ƙofa ta shigo tafe da tashin hankali,cike da rashin jindadin abunda tayi Jamila tace"wai ke sai yaushe ne zakiyi hankali ne...?shin kishi hauka ne...?uban waya baki izinin shigowa har cikin dakina without my prior written permission...?tambayarki nake kin kura mun idanu da bloodshot eyes ɗinki..." ta ida magana cike da zafi tana tunkaran Hafsan,wani irin tsananin tsoronta ne ya lulluɓe zuciyar Hafsan ammh sai tadaure tace itama cike da zafin"Kinyi abunda yasa kika cancanci ama miki fiye da hakan ne.....how could you...?meh namiki ne da zafi haka wanda har yasa kika zaɓi haɗani da mijina...?na lura so kike na fita nabar muku gidan daga ke har wancan kucakar yarinyar ammh ki sani daga ke har ita ɗin kunyi kadan...zaman Hafsa daram agidan nan insha Allah…"

Afusace Jamila ta katseta"excuse me pls spare me the insults and drama…kinata haushi sai kace karen daya fita farauta,malama ki natsu ki gayamun abunda nayi duk da cewa ni nasan ba irin wawayen matayen nan bane masu haɗa faɗa tsakanin kishiyarsu da miji ammh am suprised da kike fadamun cewa nina haɗaki da mijinki…ki gayamun tayaya na hadaki dashi...?bayan keda ma bana kawoki akai,infact nakan manta ma da zamanki acikin gidan tunda bawai shiri muke ba....."

Wani irin wawan kallo Hafsa ta watsa mata kan tace"Ai kin fini sanin abunda kikai in banda halin sheɗanci har zaki iya tunkaran Suleiman ki kullamun sharri kice ina biye biyen maza da aure akaina,idan har gulma kikeson kiyi toh meyasa baki fada masa gaskiyar cewa ai azamanin ƴan matancina ne nayi irin wannan rayuwar ba ammh sai kika zaɓi yi mashi ƙarya don ki ɓatani awajensa sabida kinsan tabbas zai fusata har ya ƙarashe warware igiya ɗayan daya sauran mana…?Meelat Gidado in tambayeki man,shin wani riba ne zaki samu idan har kika zamo sanadiyyar lalata aure sunnar ma"aiki..?ke atunaninki Allah SWT zai barki ne ahakan...?"

Aruɗe Jamila ke fadin"Innalillahi wa"inna ilaihi raji"un Hafsa shi Gidadon ne ya fada miki cewa nine na gaya mishi hakan...?" HAFSA ta daga kafadu tana fadin"No bai fada mun cewa kece kika gaya mishi ba ammh ni zuciyata kawai tabani cewa kece zaki iya wannan aika aikar sabida baki ƙaunar budan idanu ki ganni acikin wannan gidan…" kuka sosai Jamila ta barke dashi mai daga hankali ta shiga kokarin latso Gidadon awaya hannunta na mugun shaking haka kuma muryarta na rawa sosai take fadin"Ba..bari..in...kirashi...ya...yazo...ya..sakeni...yau..ni..zan..bar..miki…miki...gidan..Hafsatouh.."

Atake kawai Hafsa taji wani irin mugun tausayinta ya lulluɓeta wanda bata taɓa jin irinsa ba,haka kuma sai ta tsinci kanta da yarda cewa ba Jamila ce ta kulla mata wannan sharrin ba,dasauri tasa hannu ta warce wayar daga hannunta ta jefar asaman gado tana fadi cike da zafi"what do you think you are doing..?atunaninki ni zan iya rayuwa babu ke ne acikin gidan nan..?duk da cewa ina tsananin kishinki ammh hakan bazai taɓa sani inso ganin rabuwarku ba,kar Allah ya nunan mun wannan ranar never!!...tare na ganku haka kuma tare zan barku....." dasauri ta juya zata bar dakin tana cizgar kuka,Jamila da jikinta yayi mugun sanyi da kalaman Hafsan da kuma tsananin mamakinta,cikin azama ta cafko hannunta tana fadi cike da sanyin murya"Hafsaaaa are you the one talking...?"

Fuzge hannunta tayi ba tare data juyo ba tace"Yes am the one....ina tsananin kishinki ammh bazan so ganin rabuwarku ba don kece fitilar dake haskaka rayuwar mijinmu,kinga kuwa yau idan aka wayi gari babu ke tofa tabbas rayuwar Gidado zata zama abar tausayi ne...." tana gama fadar hakan tabar dakin aguje tana kuka,Jamila ta fada saman gadon itama tana cizgar kukan cike da tausayin yar"uwarta Hafsa,

Gidado dake ta sauraronsu awaya yana juye juye akan kujera ya lumshe idanu cike da farin ciki,don bayan Jamila tayi dialling lambarsa ta manta wai ta latsoshin har kuma call ɗin ya shiga,adaidai lokacin da Hafsa take magana ya soma tsintar zancen,wani irin farin ciki ne kawai yaji yana ratsashi ba kadan ba,sosai yaji dadin wannan al"amarin kuma haƙika zaiso ace matayensa su zauna lfy dukah,yana jin sanda Jamila ke fadi tana kuka"Hafsa wallahi ban hadaki da mijinki ba,na rantse da girman Allah bani bace na fada masa cewa kina biye biyen maza ba......"

Jinjina kai yayi bayan ya ɗago rigimar data hadasu,wato kenan Hafsa na tunanin cewa Jamila ce tayi gulmarta awajensa ko…?wani irin haushin kansa ne yaji don tabbas laifinsa ne,da"ace ya zaunar da ita ya fada mata gaskiyar wanda ya kirata awaya da hakan bai faru ba ammh kuma da alamun ɓoye matan da yayi shine alheri agaresu duka,don da dukkan alamu ya nuna cewa Hafsa da Jamila are getting to know more about each other,kuma yadau alkawari bazai nuna musu cewa yaji komi ba haka kuma bazai shiga tsakaninsu ba sbd har yanzu suna da sauran lokaci da kuma dama na zaunawa suyiwa kansu fada don su ɗin ba yara bane sai dai Baddo wacce itace kawai zai dunga sakawa idanu,ammh daga yanzu nashi tsakaninsa dasu idanu ne kawai saidai ya dauki mataki kan abunda yake neman wuce gona da iri......

*****

Yau kimanin sati ɗaya kenan kuma har zuwa wannan lokacin Andrew bai sake ƙiran Hafsa ba wanda kuma abunda Gidado yakeso kenan don ya kama bera ah tarko,ayau ɗinne kuma school authority ta nemeshi da gaggawa kan yazo fa _*MUBEENAH SULEIMAN SHAGARI*_ bata da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login