Showing 51001 words to 54000 words out of 102125 words

Chapter 18 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx

02 Jun 2025

1832

salon na daban,domin kuwa ƴa"yan Amina are not loosers and will never be one......"

Dasauri Nabeelah tace"haba mami yanzu saiki bari Ya Hafsa takoma gidan..?ni aganina kawai data haƙura dashi Allah zai kawo mata wanda yafishi…" ah kufule Hafsa ta tari numfashinta"kisa aranki kamar na gama komawa gidan mijina ne…" tana gama fadar hakan ta miƙe ta shige daki tabarsu,mami ma ta miƙe tace"saiki hanata komawa shashashar banza wacce batasan dadi ba,harke kina tinanin idan yar"uwarki ta kuskura Gidado ya suɓuce mata zata samu gidan maiƙo ne kamar nashi…?toki sani Hafsa zata koma gidansa muddin tana dani..." ta kada kai ta shige ciki,Nabeelah tayi kokarin danne hassada da kuma baƙin kishin dake cinta arai tace aranta"mami ni kuwa nasan dadi kuma ni ɗinne yakamata in faɗa miki yadda take bakece zaki faɗamun ba,nima nadau alƙawarin yin waje dasu gabaki ɗayansu dukah insha Allah,zan zame muku *KISHIYAR WAJE* don awajen ne zan dunga haɗa cakwakiya wanda zai hana muku samun kwanciyar hankali da zaman lfy,tunda babu ta yadda za"ayi in samu Gidado toh bari nima in bullo muku bayan gida… *MEELAT GIDADO* let's play the game and see who wins..." ta fada tare da kada yatsun hannunta biyu wanda suka bada wani sauti......

   ****

Yau ne za"ayi walima da misalin ƙarfe hudu na yamma,jama"a sai dira suke tayi agidan sai ka ransa ba bikin da aka shirya bane akurarren lokaci ba,kai kace ko ansan da zancan ne tun da can,shiri ake ba kama hannun yaro musamman Jamila wacce ta kasa tsaye haka kuma ta kasa zaune,burinta kawai ace amaryarta ta fito dakyau,wani tsadadden leshi ruwan hanta da ratsin ruwan goro ne ta kawowa Baddo ta saka na fitar walima,sai wani bakin alkyabba mai ƙyan gaske da zata dora asaman kayan kai kace ko ƴar wata sarkin ce…an gama mata shiri sai tayi wani ɗan karan ƙyan da bata taɓa yin irinsa ba tunda uwarta ta haifeta,su Ramlah suka tasata agaba suna tsokanarta wai ta zama matar yayansu sannan matar uniform man wanda ko amafarki bata taɓa burin son kasancewa matar wani uniform man ɗin ba ammh sai gashi yau tana shirin zama *MATAR DAN SANDA* .... *DAN SANDAN* ma wanda take mugun tsoronsa da tsananin shaƙƙarsa.....

Kuka ta fashe musu dashi mai tsuma zuciya,Jamila data shigo dakin dauke da turare ahannunta wanda zata feshe mata,hankali tashe ta karaso wajenta tana fadin"Amaryata yadai...?waya saka munke kuka kuma..?" Rungumeta tayi tana mai sake rushewa da wani sabon kukan tana fadin"Antina wallahi kwata kwata banason wannan auran ku taimaka ku hana faruwar hakan plssss,wallahi ni tamƙar uwa ma na daukeki ba yar"uwa bama…"

Tissue ta yanko tasa tana goge mata hawayen dake malala saman kuncinta tace"Mubeenah zamuyi faɗa dake idan baki bar kukan nan haka ba,meyasa bazaki haƙura ki rungumi kaddararki ba…?ni nasan tsoronsa kawai kikeji ba wani abu ba ammh inason kisan cewa babu wani ɗa namijin daya isa ya gagari wata ƴa mace saidai idan har itace ta bashi damar hakan,kowacce mace da kike gani ba haifarta ake da kissa da kisisinarta ba a"ah koyansu takeyi sannan kuma tayi aiki dasu,don haka idan zaki tuna dan zaman da mukayi dake agidana na koya miki wasu abubuwan musamman yadda zaki tafiyar da rayuwar auranki nan gaba,ayau Mubeenah lokacin amfanin nasu yazo,nina gama nawa aikin now its let to you kiyi amfani dasu koki watsar…"

Su Ramlah suka saka sowa suna yiwa Jamila kirari,Hanifa ta shimfiɗa fuskar tausayi tace"Allah sarki wallahi babu ta inda Baddo ke bani tausayi kamar yadda zata je ta cigaba da zama wuri guɗa dasu chief har ƙarshen rayuwarta…" sauran cousins ɗin suka saka dariya,wata Rahma tace"kai Mr.Oscar ɗinnan kusan kamar yama fimun wannan chief ɗin girma ga fitinar bala"i..." Baddo ta gwalalo eyes gami da fashewa da kukan tsoro don itadai tasan nata ya ƙare,Jamila ce ta tsawatar musu sannan suka bar tsokanar,

Baddo tasha kuka irin kukan da bata taɓa yin irinsa ba sanda malama Zuwaira ke nasiha agame da zamantakewar aure,tayi bayani akan haƙƙokin miji da mata akan junansu,sai taji duk bazata iya aikata ko ɗaya acikin haƙƙokin data lissafo ba don ko ganinsa bata sha"awar yi balle akai ga batun zama akusa dashi,kai ita datasan ma hakan ne zaizo ya kasance wallahi da bata biyo iyayenta bikinsa da Hafsa ba,tun farko ai datayi zamanta acan kano,an raba ƙyaututtuka ba laifi,sai shidda da arabi aka watse...

 

   ****

Washegari wanda ya kama asabar dubban jama"a suka shaida daurin auren _*DCP SULEIMAN ALASSANA GIDADO*_ da amaryarsa _*MUBEENAH BADDO SHAGARI*_ akan sadaki dubu dari,sai taya ango murna ake tayi wanda shikam yaƙe kawai yaketa musu aransa yace"Goddd!! finally it has happened...an auramun ƴar cikina…" su abokan aikinsa yawancinsu sun samu zuwa hadda Acp Salim kumo shima ya cika alƙawari yazo,sai tsiya yaketa mishi wai mijin mata uku,Daddy da Ya mukhtar ma sun halarci daurin auren,sosai yabban Gidado yaji kunya ya nuna musu cewa wannan ba yinsa bane yin Tsoho ne,daddy yace aishi wallahi abun yayi masa dadi sosai aiko bakomi Hafsa da mahaifiyarta zasu gane kuransu,Tsoho dan duniya saida yasa aka gayyato ƴan gidan TV donsu kwashi rahoto su watsa duniya ta gani duk nan yayi hakan ne don ya kunsawa Hafsa da mamin tarin baƙin ciki kuma yaci nasara don har Suma saida Hafsa tayi,ita kuwa uwar zage zage ta dunga gundumawa tana taya ƴarta bakin ciki,

Ashe abunda Gidado be sani ba shine iyayensa sun shirya musu reception ne ah *CUNNINGHAM MARQUEE* , wani wedding event venue ne dake kusa dasu,dakyar da sudin goshi aka samu Gidado ya shirya cikin well ironed uniform ɗinsa na ƴan sanda,asaman shoulder ɗin kayansa an manna one diamond star and a crossed tipstaves surrounded by a laurel wreath….tamƙar zai kashe kansa don haushi,itama Baddo anata ɓangaran an shiryata ne acikin wata doguwar english gown wanda bayansa ke jaa har kasa bonvita colour,kayan sai sheƙi sukeyi ajikinta,aka dakko wani wedding net kalarsa aka yane mata kai dashi,komi nata hatta purse ɗinta da shoes dark brown shinning bonvita colour ne,sosai tayi ƙyau kamar ba ita ba,mota ɗaya suka shiga da gogan naku,tana ta rera kuka kasa kasa har abun yasoma isarsa ya jawota da ƙarfi yana mata raɗa akunne"Dnt think nima inason wannan auran,wallahi da"ace zaki buɗe zuciyata kiga tarin bakin cikin dake cikinta da kinsha mamaki ba kadan ba,abunda yafi karamun takaicin ma bai wuce yadda aka tashi aka haɗani aure da wacce ta gama tambaɗewa ba agari…an liƙamun raguwar wani in karashe suɗewa,wanin ma wai ƙanin baya bayana…gaskiya an cuceni…" dasauri ta fuzge jikinta tana mai sake sakin wani sabon kukan jin yadda yake masu mummunar zato ita da Kasim wanda ko hannunta ma bai taɓa tabawa ba ammh shine Gidado ke tunanin har samun wani abu yayi daga gareta don kawai ya kamasu ah lungun gidan suna zantawa sau daya kuma fa,kukanta ne ya janyo hankalin Aliyu dake zaune agaba,sagir na tuki afusace ya dubi Gidado wanda ya ɓata rai sosai yace"meka mata…?" kafin yakai ga.bashi amsa yaji an buɗe ɓangaran dayake,Jamila ce,itama tasha ƙyau sosai ta kamo hannunsa tana mirmushi tace"Our groom kasha ƙyau sosai harka tunamun da ranar namu auran,hoooo DCP namu...…"ta fada tana kokarin danne kishinta,wani uban harara ne ya watsa mata tare da kwace hannunsa ya koma gefe yana jujjuya white cane ɗinsa ahannu,bata sani ba wallahi haushinta yakeji sosai,bata damu ba takoma ɓangaran Baddo ta fito da ita tana mata tsiya itama ɗin,more than 20 police men ne suka sakasu atsakiya,wasu na gaba ayayin da wasu ke baya,sai sune atsakiya,Jamila da Baddo kuma suka sakashi ah centre sai abun ya bada citta,ƴan sanda suka soma parade zuwa cikin hall ayayin da piano sound da kiɗin ganga ke tashi sannu ahankali abun dai gwanin ban sha"awa,suna shiga kowa ya miƙe yana sara musu har aka sadasu da wajen da aka tanadar domin zamansu duka,zuciyar Gidado tamƙar zatayi bindiga ta faɗo waje don tsabar bakin ciki,this reception was a blast tonight ammh fa Baddo tasha haƙuri don tym to tym yake kamo hannunta yadan matsa don mugunta ko kuma ya mata raɗa da bakaken maganganu akunne har wani photographer ya daukesu ahakan sanda yakai baki yana gaya mata magana akunne,sosai suka burge jama"a,sai kirari ake tayiwa Jamila ana shi mata albarka,awajen yanka cake ma,su ukun ne suka haɗa hannu suka yanka,aka umarci Jamila dashi da su soma feeding juna,bayan sun gama aka ce shida amarya Mubeenah suyi feeding juna,gaban Baddo ya shiga bugawa dasauri dasauri,shi kuma wani takaici yaji wai yanzu wannan ficikar yarinyar ce take amsa sunan matarsa?itace ta soma yankawa ta daga kafa sosai tana nema kara tsayi kasancewar yafita tsawo sosai,shi kuma dan mugunta da gangan yaki ranƙwafowa sai jama"a suka saka musu dariya don azatonsu wasa ne sukeyi,sai hotuna ake musu da video coverage ahakan,abun ya soma bawa Jamila haushi ganin Baddon na neman faduwa tace bayan ta matsa kusa dashi sosai"haba wallahi ba girman bane DCP karkasa mutane su gano cewa bakason auran…" tsaki yaja sannan ya ranƙwafa asannan ne hannun Baddo yasamu ya isa ga bakinsa,ya karbi cake ɗin tare da cizar yatsarta idanuwansa ƙyam acikin ƙwayar nata idanun yana mai son tantance yanayin dazata shiga,ƙara tadan saki ayayin da wani guntun hawaye ya ziraro mata,aka saka tafi,now turn ɗinsa ne yayi feeding nata,babu yadda ya iya illa yankawa yakai bakinta,dkyar ta buɗe karamin bakinta ta karba tare da gantsarawa yatsarsa cizo shima,idanuwanta itama ƙyam acikin nasa tana mai son tantance halin daya shiga,dake shi namijin gaske ne ko girgiza da hakan baiyi ba kuma yagano so take taga yanayin dazai nuna ammh sai ya ciza ya ranƙwafa yana mata raɗa akunne"nasan kin sone na nuna naji zafin hakan right..?karki damu zan nuna miki ammh sai munfi haka yawa..." ya ida magana tare da dagowa yana kallon jama"an wajen dauke da mirmushi asaman fuskarsa,babu wanda be burge ba awajen,Jamila da kuma sauran wa"enda sukasan ba sonta yake ba,sun tabbata ba abun alheri bane yake ta faɗa mata ammh dayawan mutane sun dauka cewa kalaman soyayya ce da kuma kulawa yake nuna mata,sun karbi kyaututtuka sosai,sai goma aka tashi taron don anaso ne daga nan awuce da amarya gidanta kamar yadda Tsoho ya umarta don tun jiya aka haɗa kawunansu aka musu faɗa sosai don haka no need for dat again,wannan karon tare da Jamila suka shiga mota ɗaya toh shiyasa bai samu sararin musguna mata ba har suka isa gida,Su Haj.Hafsa an dawo tana nan zaune ah barandar gidan tana jiran isowarsu,sai karkada kafa kawai take tayi gami da huhhura hanci,ita kadai tazo don ta hana su maminta biyota gudun karsu karasa damaging igiya ɗayan daya sauran mata…………✍

~KUYI HAKURI KISHIN MATA KUMA SAI FRIDAY DON INA DA TESTS WEEK DIN NAN KAMAR YADDA NA FADA MUKU,INA GODIYA SOSAI DA ADDU"O"INKU AGARENI,YANZU ZAMU SHIGA AINIHIN PLAYING GROUND DIN~

~INTERMISSION👐~

_#*KISHIN MATA*_

_#*MEELAT*_

_#*HAFSY*_

_#*MUBEEY*_

_*KU DUBI GIRMAN ALLAH KU RIKEMUN AMANA KARKU FITARMUN DA LITTAFI👏*_

_LITATTAFAN NAN NA SIYARWA NE DON HAKA KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI_

   

_*KISHIN MATA…!*_

     _Na marubuciya Hafnancy…_

         _akan naira 200kacal👌_

_*MALIKA-MALIK…!*_

    _Na marubuciya Janafty..._

       _shima akan naira 200kacal_

          _Idan kuma duka biyun kikeso toh kin samu garabasa zaki biya 300 ta hanyar turo katin mtn ta layin nan 07065481260 ko transfer ta acct 0824409678 ~*HAFSAT MUSTAPHA*~ ~*ACCESS BANK*~ saiki aiko da screenshot na transaction_

_*💫BABI NA ASHIRIN DA DAYA..💥*_

…………Motoci uku ne agaba wanda duk cike suke da ƴan sanda aciki,sannan ga wani baƙin _*'HUMMER H2 JEEP'*_ biye abayansu wanda couples ɗinne ke ciki,sai guda uku abayansa cike da yan"uwa da abokan arziki and lastly motar ƙarshe ƴan sanda ne aciki,duk nan an rako amarya da ango ne gida,sauran motocin awaje suka tsaya ayayin dana couples ɗinne ya shiga ciki,Hafsa na ganin shigowar motar ta miƙe da hanzari gabanta na dukan uku uku,ana ida parking Jamila ta buɗe kofa ta fito ta nufi ɓangaran da Baddo take zaune don atsakiya suka sakashi,sai kuka take rerawa ahankali,takaici duk yabi yacika Gidado yasa hannu ya jawota ta faɗo jikinsa,bakinta ya laluɓo ya shiga tsotsewa cike da salo na mugunta,can ya cikata tare dayi mata raɗa akunne"kin tuna dazu nace miki idan muka fi haka yawa zan nuna miki cewa naji zafin abunda kikamun...?" Bai jira yaji ta cewarta ba ya cigaba"toh gashi nan na nuna miki kinga munyi 2-1 kenan and get ready don saina tabbatar danayi 3-1 diz nyt..." adaidai lokacin Sagir ya ƙwanƙwasa masa kofa yana fadin"wai kai don ubanka bazaka fito bane...?meh kakewa ƴar mutane ne aciki?"

Jamila itama ta buɗe side ɗin Baddo dauke da murmushi akan fuskarta take fadin"Amarya welcome to ur matrimonial home as matar _*MATAR DCP SULEIMAN ALASSANA GIDADO*_ ...." fashe mata dakuka tayi sanda ta kamo hannunta don dama mai neman kukan ne sai aka jefeta da kashin awaki,sauran yan"uwa ma da sukayo musu rakiya suka karaso wajen da guɗa,abun hadda ƙara don hatta da kannen Jamila acikin ƴan rakiyan,Hafsa sai kallonsu take daga inda take tsaye zuciyar nan tata tamƙar zatayi bindiga ta faɗo waje tsabar baƙin ciki,su maminta kuwa sai jero mata ƙira suke tayi akai akai don suji yadda ta ƙaya mata ammh taki dagawa sai danna musu reject take tayi,aka nufo da amarya ciki,hannunta sarke cikin na Jamila sai kuka take rerawa ahankali kanta aduƙe tana jin yadda lips ɗinta ke mata mugun zogi,Hafsa na ganin nufowarsu tayi saurin komawa ta zauna tare da ƙawar da kanta gefe gudun karsu shaidata batasan ta riga ta makaro ba,duk da cewa inda ta zauna akwai duhu sosai ammh Jamila ta ganeta,daidai entrance door Jamila tasa aka dakata sannan ta dubi Hafsa tace tana murmushi"Sis Hafsa welcome back,naji daɗi kwarai da gaske da kika dawo don tarban amaryarki,don haka ki taso mu shiga da ita ciki,gaban Hafsa ya bada rasss ita ta rasa ko wacce iriyar macece wannan Jamilar da sam bata kishin mijinta,kishiyoyi har biyu akayo mata acikin wata guda ammh ita sam bata damu ba sai rawar kafa ma takeyi akan abun,itace ma take jin zafin wannan al"amarin ammh banda Jamilar,Jamila ce ta katse mata tunani ta hanyar sake maimaita maganar,dogon tsaki taja kan ta waigo garesu tana fadin"malama karki dameni da zancen banza kina jina ko..?idan amaryar jira take in taso in mata rakiya zuwa ciki toh ashe duk zamu kwana kenan anan ɗin…"

Goggo Binta ce tayi saurin taran numfashinta tace cikin tsananin fushi"lallai Hafsan nan ashe dagaske ɗinne baki da kunya kamar yadda aketa fada…?aiko bakomi ƙya dubi darajar idanunmu kidan sassauta wasu abubuwan naki ammh dake ke din fitsararriyace ansha ah nono dole ki takamu son ranki,ni wallahi bansan dalilin dayasa kika dawo gidan ɗanmu ba,kinga tun wuri ki kama hanya ki koma inda kika fito don bamu son fitina,wa'ennan mata biyun da kike gani sun ishi Gidado rayuwa…" kukan baƙin ciki ta fashe dashi don sosai ta shaƙa da baƙaƙen maganganunta,sauran tawagar suka ja tsoki suka shigar da Baddo ciki,Gidado dake tahowa shida su Sagir ya daga murya yace da Goggo Binta wacce ta sake baki tana kallon yadda Hafsa ta yagale baki wai ita tana kuka,yace"Goggo ki shiga abinki ki rabu da ita ni zanji da ita..." ya fada idanunsa ƙyam akan Hafsa don tun fitowarsa amota yasan cewa itace anan wurin tun kafin ma kowa yayi tunanin hakan, dasauri Goggon ta waiga tana kallonsa kan tace daƙyar"A"ah babana banda ɗanyen aiki dai…" wani ƙayataccen murmushi ya sakar mata kan yace"karki samu damuwa Goggona babu abunda tirr ɗin da ɗan naki zai sake aikatawa…"

maida masa da murmushin tayi tana fadin"madallah da mai sunan Tsoho…Allah yayi maka albarƙa" tana gama fadar hakan tasa kai ta shige ayayin daya bita da kalmar ameen...kamshin turarensa ne ya soma daƙar hancinta,dasauri ta daga idanu tana kallonsa gabanta yayi wani irin bugawa don bata taɓa ganinsa cikin uniform ba,sosai yayi mata wani irin mugun ƙyau har yasa taji yayi mata ƙwarjini,duk masifa da ruwan bala"in data tanadar masa sai ta nemesu ta rasa,saurin maida kanta ƙasa tayi don bazata juri irin kallon dayake jifarta dashi ba,shi kuma sai yaji duk ta bashi tausayi har yaji ya huce da abunda maminta tayi masa,duƙawa yayi tare da tallafo habarta hakan yasa adolenta ta kalli ƙwayar idanunsa da take ta shakkar kallo,cikin wani sanyin voice yace"Hafsa are you now ready for marriage...?" runtse idanu tayi sai ga hawaye ya zubo mata sharrr cike da rawar murya tace"Yes yes am ready pls i dnt want to loose you na canza..." soft smile ya sakar mata kan yace"bayan nan kuma ina fatar kin shirya zama da namijin da baya haihuwa har ƙarshen numfashinki…?

nan ɗinma tace masa eh yace"Good tashi ki shiga ciki..."da gudu ta miƙe tayi ciki tana cizgar kuka duk suka bita da kallo gami da girgiza kai,Sagir ya dafa kafadarsa yana fadin"Ammh abokina kana ganin zaka iya rayuwa da mata uku..?i dnt think Hafsan nan ta canza aganina ladabin kunnama kawai tayi maka don ka mayar da ita..." dauke da murmushi asaman fuskarsa yace"karka damu abokina koka manta da wanda ke tsaye agabanka ne…?DCP Gidado nake,kafin na taka wannan matsayin saida aka tabbatar da cewa ina da lasisin jarumtaka da kuma gwarzontaka,i can handle the three of them…" daga sagir har Aliyu saida suka jinjina masa......

Acan ciki kuwa tawagar ƴan kawo amarya sai santin part ɗin Baddo suke tayi tamƙar su aza akai su wuce dashi,tuni Tsoho ya samu labarin dawowar Hafsa,yaci dariya sosai har ya gode Allah kan ya dauki waya ya latso Gidado,bayan ya daga yake ce masa"kai daɗa kuma ashe wai mutuniyar taka ta dawo…?" Gidado da dama haushinsa yakeji sosai yace"Eh ai dama zata dawo ɗinne tunda ce mata nayi idan ta koyi da'a ga miji sai ta komo gidan nawa ammh sai akamun saurin shisshigii......"

Shiru yayi ya kasa karisawa da abunda yaso fada,cike da zafi Tsoho yace"Ni kake fadawa cewa an maka saurin shisshigi Gidado...?kayya ina mai jiye maka ranar da zakayi nadamar faɗar wannan maganar,insha Allahu nan bada jimawa ba zaka tako kazo da kafafunka ka russuna agabana kana godemun da wannan haɗin danayi…" yana gama fadar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login