Showing 99001 words to 102000 words out of 102125 words
Chapter 34 - KISHIN MATA Book Complete 1-End by Hafnancy Lurv.docx
ammh dai kayi kokari ka ceto uwar…" duk yadda yakai ga son ganin gudan jininsa aduniya zai hakura domin kuwa rayuwar Mubeenah tafi mishi muhimmanci, idan Allah bai tsayar musu da wannan ba ai toh zai azurtasu da wani nan gaba tunda akwai hope dai, fatanshi ayanzu dai Mubeenarsa ta tashi koda kuwa hakan na nufin za"a rasa abun cikinta ne, dafa kafadarsa likita yayi yana mai sakin murmushi kan yace"Karka damu insha Allahu da uwar da ɗan zasu rayu tare da amincin ubangiji…" haka dai yasa hannu kan aikin da za"a mata, yan"uwa nata rusar kuka don wannan ka"ida ne muddin kika ji wai za"a yiwa wani naki aiki dole ne hankalinki ya daga domin kuwa option biyu ne, koki rayu ko kuma ki mutu,
Daƙyar da sudin goshi aka matsawa Gidado yakoma gida don cigaba da karban ta"aziyyar mutane, ammh koda ya koma hankalinsa kwata kwata bai kwanta ba, bayan kamar 30mins har an gama shirye shiryen zuwa dakin aikin sai kawai suka ji Baddo tana fadi awahalce"Wallahi banison akaini dakin aikin nan, Ku taimaka ku bani kwalbar coke ko fanta in jarraba wani dabara ko za"a dace...." cike da mamaki suke kallonta ammh sun kasa magana, can dai babban likitan yace"Dnt waste tym yi maza ku samo ba"a kin ta mutum watakila kaga an dace..." Tunawa tayi Ummanta ta taɓa bata labarin cewa sanda za"a haifota tasha baƙar wahala wanda har aka fidda rai da ita, wata makobciyarsu ce ta bada shawarar asamo kwalbar coke kota fanta abata ta dunga hura iska aciki da karfi, cikin sa"a kuwa sai gashi ta haifo Baddon da kanta, yanzu haka Umman Baddon nacan gidan rasuwa ta keɓe kanta tana nafilfili domin rokarwa 'yar tata fatar sauka lafiya, can itama ta tuna da dabarar da tayi amfani dashi asanda zata haifeta, dasauri ta dauki waya ta latso Goggo Boddiya, tana dagawa tace"Umman Aliyu don girman Allah ataimaka asa Baddo tayi dabarar dani nayi sanda zan haifota watakila adace……" atake itama Goggon ta tuna wannan dabarar don gabaki daya sun sha"afa ne, ai kuwa taci sa"a sai ga nurses sun fito daga dakin zasuje samo mata kwalbar, cikin sauri Goggon ta taresu take fadi musu bukatarta, da mamaki suke gaya mata cewa itama Baddon haka ta bukata kuma shi suka fito samowa, "Alhamdulillah! ashe itama bata manta ba..." shine abunda ta furta...
Cikin ikon Allah! kuwa ana kawo mata kwalbar ta shiga hura iska aciki da dukkan ƙarfinta, in the next 5mins sai ga katotuwar ɗiya ta faɗo tana canyara ihu cikin jini, nurses suka dakko zani suka dorata akai, can mahaifa ya biyo baya, cire kwalbar tayi daga bakinta tana sauke wani wahalallen ajiyar zuciya, har wata nurse na shirin karbe kwalbar daga hannunta sai kawai suka ga ta shiga murkususu alamun wata sabuwar nakudar ce ta taso mata gadan gadan, likita yace da karfi"Ku dakko wani zanin ina zaton ƴan biyu ne…" wannan karon bata sha wani wahala ba ta sake haifo wata ɗiyar ƙosasshiya dai kamar ta farkon, tuni aka tsaftacesu tare da uwar kana aka gurgura dasu dakin hutu, wata wahalalliyar bacci ne tayi awon gaba da Baddo, sanda labari ya riski yan"uwa cewa ai 'yan biyu ta haifa kuma duk mata, kowa farin ciki ya lulluɓe zuciyarsa ammh babu damar bayyanawa afilli sabida halin rashin da ake ciki, sai sam barka dai kawai ake tayi, shi kansa uban gayyar kasa bayyana farin cikinsa yayi sanda aka buga ake sanar mishi, ga ranar taka rawar murna ammh baƙin ciki ya yakiceta, shine wai yau da samun kyautar ya"ya har biyu daga tsatson wacce ya raina harma yake tunanin ita bata isa ta haihu dashi ba sai dai ma shi ɗin ya haifi irinta, Ya ilahi! lallai ya yadda da mutane da suke yawan cewa" Dan hakin daka raina shike tsole maka ido..." gashi ayau ta tsole masa idon, ayau ta cika mishi burinsa arayuwa, ta bashi farin cikin da ayau baza"a iya kamantawa ba, atake yaji ta sake samun wani daraja da kuma babban matsayi azuciyarsa, sai Allah ya sakawa Tsoho da wannan hadi na alherin daya haɗa yake tayi aransa, gaisuwa biyu ake tayi mishi, dana baƙin ciki da kuma na farin ciki……
**
Ajiya ne akayi addu"ar uku na Hafsa, sai dai har yanzu Jamila da Baddo basa cikin yanayi mai ƙyau, bama kamar Baddo wacce tunda ta haihu abun kirki ma baiga cikinta ba, anyi fadan anyi lallashin duk abanza, akace idan har bata ci abu mai kyau ba toh taya takeson yaranta su samu ruwan nono har su koshi yadda akeso…? yanzu haka ma Goggo Binta ce takai mata kunun ƙanwa da kuma ferfersun kayan ciki ammh taqi kallonsa sai kuka, ga yaran ma yunwa suke ji sosai ammh taqi basu mama, suka saka yatsun hannayensu abaki suna tsotsa abun dai gwanin ban tausayi sai kace marayu, hakan ya kara fusata Gwaggo Binta ta mike tana fadin"Tunda kinki jin tamu toh bari inje in kirawo miki uban ya"yan ko kuma uwarki Meramu sai ta gaya mana idan haka ke ta miki sanda kike jinjira……" kafin Baddon tayi magana Gwaggon tabar dakin da sauri, hakan yasa Baddon fashewa da kuka takai kallonta ga ƙyawawan ya"yanta mata yadda suke tsotsan hannu abun gwanin ban tausayi, har takai hannu zata dakko ɗaya wacce tafi tsaya mata arai mai tawadar Allah ah ɓangaran kumatu ɗaya sai ji tayi an buɗo kofar dakin an shigo,
waigowar da zatayi sai kawai suka haɗa idanu da Gidado, ahankali yakaraso inda take jiki asanyaye, amaimakon taga ya kifa mata wawan mari sabida tana neman maida mishi ya"ya marayun karfi da yaji, da mamakinta sai gani tayi ya karya gwiwowinsa zuwa kasa agabanta tare da kamo hannayenta ya shiga murza 'yan yatsunta, farin ciki ya bayyana karara akan fuskarsa wanda bai samu damar nunawa tun ranar da ya"yan suka zo duniya ba, alokaci guda kuma ruwan hawaye na kwaranyo mishi, cikin shesshekar murya yake fadin"Mubeenah gani agabanki ayau na durkusa ina neman yafiya da kuma afuwarki, inaso ki sani zuciyoyi na yin afuwa ga sashensu koda kuwa basu san juna ba, don haka nasan cewa zuciyarki zatayi hakuri ta yafemun laifin dana mata tun kafin na bada haƙurin, Mubeenah kimun uzuri domin kuwa kowani ɗan adam ajizine, bai yiwuwa asamu mutumin da sam baya kuskure, mahallicinmu ma kullum cikin yi masa laifi muke ammh muddin muka tuba sai kaga ya yafe mana, nasan ban taɓa kyautata miki ba gashi ke kuwa kin jefani cikin farin cikin da har abada bazan taɓa mantawa dake ba, uwar ya"yanah ki gafarceni kuma nagode nagode da wannan babbar kyautar da kika bani......"
Yana ida magana ya rushe da matsanancin kuka tamƙar wani karamin yaro kana ya kifa kansa asaman cinyoyinta, cike da rauni ta dago kansa tana mai kokarin danne nata hawayen sa"annan tasa farin tafin hannunta tana share masa nashi hawayen, da rawar murya take fadin"Uban ya"yanah zan iya juran komai arayuwata ammh banda zubar hawayenka, akwai wasu igiyoyi dake riƙe da zuciyata kuma sunansu hawayenka, aduk lokacin da suka fito daga cikin idanunka kuwa zuciyata na cutuwa, ka sani ni baka taɓamun laifin komai ba inma kayi toh na yafe maka, ammh gashi dai ayau 'yar cikinka ta haifa maka ya"yan da suka fito ta tsatsonka...." ta ida magana cike da zolaya, rungumota yayi tsam ajikinsa yana murmushi, can ya cikata yana fadin"An kawomun kararki wai kina neman maida mun ya"ya marayun karfi da yaji ammh koda yake zan miki uzuri sabida ko har yanzu kina cikin jimamin rasuwar yar"uwarki ne...." habawa ai ya ballo ruwan august, nan da nan ta fashe da kuka ko dama can mai neman kukan ne sai kuma gashi an jefeta da kashin awaki, acikin wannan halin Jamila tashigo ta riskesu da tikeken cikinta agaba kai kana iya cewa ma haihuwar yau ko gobe ne ammh anan watanninsa 7 da 'yan kwanaki, itama ta shige layinsu suka cizgi kuka son ransu daga baya Gidado yakoma lallashinsu, bayan an natsu Gidado yace"Inason nayiwa ya"yana huduba...don haka Mubeenah na baki zabin daya don hakkinki ne, daya kuma nine zan bada..."
Baddo ta dubi Jamila tana mai fari da ido kan tace"Antina na baki wannan damar ki zaba mana..." cike da mamaki Jamilar tace"Kai kuji mun mata fa...?ina kika taba ganin anyi hakan...? A"ah kidai zaɓa kar inyi abunda baza"a so ba kuma nasan bazaki ƙi ba ammh watakila ranki bazai so hakan ba kinga kuwa an shiga hakkinki…" cike da rashin jindadin maganarta Baddon tace"Haba Anti meyasa zaki fadi hakan ne...?shin kin taba mun abunda banji dadinsa bane...? na hadaki da girman Allah da darajar iyayenki idan har kin daukemu daya toki zabawa 'yarki suna...." har ta buɗe baki zata sake magana Baddon ta kuma insisting da"please....." Jamila ta dubi Gidado taga ta daga mata kai alamun ta zaba kawai....
Bata da wani option illa choosing ɗin tunda shi kansa uban gayyar ya bada goyon baya, ba tare da wani dogon tunani ba tace"Na zaɓawa ɗaya acikin ya"yana suna *NANA HAFSAT* ...amaida mata da sunan marigayiya...." ajiyar zuciya Gidado ya sauke yana fadin"Alhamdulilah! dama hakan na raina tuntuni ina son dai naji sunan da zaku zaɓa ne tukunna kafin nayi magana, sunan yyi miki...?" ya furta yana duban Baddo, ada taso ayiwa Jamila kara ne ammh kuma da Hafsan da Jamilar duk daya ne ai, sai dai ta kudurta aranta insha Allahu acikin ya"yan da zata haifa aduniya sai ta saka sunan Jamilar, sai dai kuma idan Allah yace biyun nan ne kadai babu kari toh shikenan.Daga masa kai tayi alamun yayi matan, yacigaba"Good ....yanzu its my turn to choose, na zabawa dayar sunan hajju wato *NANA KHADIJAH* kuma inaso adunga kiran mai sunan Hafsat da *NANA* mai sunan Hajju kuma da *UMMI* , yanzu sai ku zaba mana wacce kukeson abawa sunan Hafsat ɗin da wacce kukeson abaiwa Ƙhadijah…"
Alokaci daya duk suka kai hannu ga wacce take da tawadar Allah abangaren kumatu daya suna fadin"Wannan itace Hafsat wancan kuma Khadijah..." murmushi ya sakar yana fadin"Wato don Hafsa itama tana da tawada akan fuska shiyasa kuka zabar mata waccen ko...?" ya fada yana nuna 'yar, dariya duk suka saki, da wasa da 'yan dabaru yasa Baddo ta shanye kunun ƙanwar tass sannan ta dan taɓa ferfesu kana yasata ta shayar da ya"yansa, saida ya tabbatar da cewa duk sun koshi sa"annan ya daukesu daya bayan daya yayi musu huduba, yaso tun ranar da aka haifesu ne yayi musu hudubar ammh sabida ba"a cikin nutsuwa shiyasa bai yin ba sai yau......
***
Ba ayi musu suna acikin wannan satin ba saida ta zagayo, kuma ya cika alkawari ya baiwa yara suna *HAFSAT(NANA)* da *KHADIJAH(UMMI)* yaran dai gasu nan tamƙar ya"yan turawa don kyau, abun dai tubarkallah masha Allah, idan kaga Baddo bazaka taɓa tunanin cewa itace ta haifesu ba sabida jikinta nada kyau sosai ga wani irin fresh da cika da tayi, sosai zata burgeka ita da ya"yan nata......Jamila na dan iyakacin kokarinta wajen ganin ta taimaka mata duk da cewa ita kanta tana fama ammh hakan bai hana ta tayata rainonsu ba har dai itama lokacinta ya iso, makurci dai mawadaci wato Allah dai ya azurta Jamila da haihuwar 'yan uku, maza biyu mace daya, Gidado da Baddo da.kowa ma sun rasa inda zasu saka ransu don murna, ita kanta Jamilar ta kasa ɓoye farin cikinta ne kuma awannan ranar ta kara tabbarwa kanta cewa lallai haƙurina yana da riba,
Aranar suna yara suka ci sunan, daya abban Jamila wato Ahmad, za"ana kiransa da *AYAN* daya kuma sunan baba Munnir, za"ana kiransa da *ADNAN* macen kuma sunan Yumma, za"ana kiranta da *AFRA* ,sosai mutane suka ji dadin yadda yayiwa Baba Munniru kara duk da cewa baya araye ammh yana tune dashi, bama kamar Kasim wanda har kuka sai dayayi yana gode mishi…Kasim ya sauya sosai ya zamo na gari, ahalin yanzu haka ma zancen bikinsa ake kasancewar ya samu aiki ah supreme court, sai kuma Allah ya tashi ya hadashi da natsastsiyar yarinya ma"abociyar addini *RUQAYYA* diyar wani shaharrarren malami, itama Azeema anata ɓangaran da aka ga har zuwa wannan lokacin babu mashinshini sai aka haɗata da mai gadin gidan, taci kuka wai itace yau Azeema da auran mai gadin gidansu, from grace to grass..? Allah sarki rayuwa kenan, mai gadin baici musu ba ya amsa tayin da aka mishi don aganinsa wani mukami ya samu idan ya aureta, dake matarsa ta rasu shiyasa ya kara karban tayin da kwarin gwiwa, aka hada bikin dana yar"uwarta Zubaida, Abba ya bawa Bello mai gadi madaidaicin gida mai kyau inda zasu zauna shida Azeema don ko ba komai har yanzu yarsa take, kuma daga wannan ranar yabar gadi sai Abba ya samo mishi aikin masinja awajen aikinsa kasancewar SSCE WAEC result gareshi, kuma sosai suke zaman lafiya don Azeema tayi laushi sosai ba kamar da ba, gashi kuma tana kular mishi da marayun ya"yansa biyu Zaynab da Awwal, hakan yasa ta samu soyayyar miji domin kuwa idan kana son ya kaunaceka tofa kaima saika kaunaci ya"yansa, cikin ikon Allah kuma sai ya aurtata da samun nata rabon....
Ba"a wani jima ba da haihuwar Jamila itama Samha ta sauka, ta haifi danta namiji mai kama da ubansa sak, sunan mahaifinta aka saka mishi, sai ana kiransa da *AMEER* , su Surayya da Ramlah suma duk sun haihaifa,
*AGURGUJE pls*
in takaice muku labari acikin shekaru biyar kacal su Yumma bazasu iya lissafa iya adadin jikokan da suka tara ba domin kuwa kowanne acikin ya"yansu kamar gasar haihuwa ake, ahalin yanzu Gidado nada ya"ya takwas domin Allah ya sake bawa Jamila haihuwar 'yan biyu, mace da namiji, Baddo kuma ta haifi namiji, idan kaga yadda suka hade kawunan ya"yayensu abun zai baka sha"awa don idan ba sanin gaske ka musu ba zaiyi wuya ka gano ɗan wani da ɗan wance, kuma koda rana ɗaya basu taɓa mantawa da Hafsa ba, tana nan makale acikin zuciyoyinsu kuma duk ya"yansu da suka dan tasa sun basu labarinta, kuma suka ce su dunga mata addu"a domin itama mamarsu ce, abangaran su Samha dasu Surayya suma duk sun kakkara haihuwar, rayuwar farin ciki da kuma kwanciyar hankali kowanne bangare ke gudanarwa abun dai gwanin ban sha"awa, tunda Baddo ta kammala sec scul nata bai bari ta cigaba ba sai ma jari daya bata itama ta buɗe babban shago na classic shoes and bags, Jameelah nada boutique mai suna *MEELAT GIDADO'S BLOSSOM BOUTIQUE* ayayin da nata yake *MUBEENAH GIDADO'S CLASSY BAGS AND SHOE STORE* sosai kuma suke kwasan customomi donko daga jin sunan shagunan kasan an tara classic and quality things.....
Hajiyar Kasim kuwa shekararta uku kenan da rasuwa bayan dogon jinyar da tayi na hauka ammh bata warke ba ta rasu......
*TAMMAT BIHAMDULILLAH👏*
Ayau kuma anan na kawo ƙarshen wannan littafin mai suna *KISHIN MATA* mai cike da darussa da dama, ina godiya kwarai da gaske da kukai hakuri dani har muka kawo karshen wannan littafin ayau, ina kaunarku matuka *HAFNAN PAID GROUP* & *KISHIN MATA PAID GROUP* ....Allahu yabar zaman tare kuma Allah ya yaye mana wannan babbar cutar data addabi al"ummah *COVID-19 PANDEMIC* (Ameen)
Ku kasance dani acikin sabon littafina dazai zo muku bayan sallah idan Allah ya ara mana rai da kuma Koshin lafiya, ko kunsan sunansa...?
_*SAWUN GIWA...!🐘*_
_*SAWUN GIWA...!🐘!*_
ai ko daga jin sunan kunsan za"a kwafsa ba kadan ba, wannan salon na daban ne don gayen ciki ba👇
*MAHMOODAN ZAHRA* _bane (SHIN SO DAYA NE?_
ba *USAMAHN ZAYBA* bane _(FATALWAR MIJINA)_
ba *SAWAD DIN ASMA* bane _(KAICON SO)_
shi
wannan
ɗin
*
ABDULHAMEEDUN
AMATULLAH
*
ne
,
littafin
nan
zaisha
banban
da
sauran
litattafaina
don
yana
cike
ne
da
salo
mai
karsashi
da
kuma
taɓa
zuciya
ammah
sai
dai
ina
da
bukatar
masu
hakuri
da
kuma
karban
kaddara
mai
kyau
ko
mara
kyau
🙌
idan
zaku
duba
all
my
write
ups
ina
tabo
bangare
bangare
ne
na
ababen
dake
faruwa
arayuwarmu
ayau
,
don
haka
salon
bai
canza
ba
ina
nan
ayadda
nake
,
don
haka
idan
har
kinsan
baki
da
heart
karki
bibiyi
littafin
nan
don
tabbas
zaki
zubda
hawaye
,
idan
kuma
ke
mai
dauriyace
duk
da
hakan
zuciyarki
zata
taɓu
,
тhe
¢
σηтєηт
¢
σηтαιηѕ
α
∂
єтαιℓє
∂ ∂
єѕ
¢
яιρтιση
σƒ
ємσтισηαℓ
ѕ
¢
єη
¢
єѕ
,
υ
мιgнт
gєт
тσυ
¢
нє
∂,
ѕσ
ιƒ
αηу
σƒ
уσυ
ƒєєℓѕ
ℓук
нє
σя
ѕнє
ιѕη
'
т
ѕтяσηg
єησυgн
тσ
ѕυв
נ
є
¢
т
нιѕ
ηєяνєѕ
тσ
ѕυ
¢
н
α
ѕтяαιη
,
ησω
ιѕ
υя
¢
нαη
¢
є