Showing 27001 words to 30000 words out of 59972 words
Chapter 10 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf
Cike da matsananciyar damuwa d'auke saman fuskar beauty haka ta daddafa ta fito daga cikin
stop & chop sallamar da take musu in zata fita yau ko ita basu samu ba"mota ta nufa ta zauna
tare da d'aura kanta saman sityarin motar"muna fatan kuma bazaki bamu kunya ba?"wannan
maganar ta shamsy itace take ta faman kai komo a zuciyar beauty"A zahirin gaskiya bazan so
ni kai na na baku kunya ba,kuma bazan so wannan damar ta wuce ni ba ta k'ara shiga cikin
wasu wayayyun mutanen"toh amma ai babu wannan tsarin a cikin file d'ina hasali ma ban tsara
wannan rayuwar ta zama abin dawwama a gareni ba,sai gashi yau kwatsam kun shigo min
rayuwa da wani sabon abu mara misaltuwa"yanzu meye mafita???yanda ta lula kogon tunani
beauty ba kama hannun yaro,fahimtar daga k'arshe baza ta samu wata mafita bane yasanya ta
dole ta hak'ura akan in ta koma gida ta yanke shawara".motar ta kunna tare da sakin sauti ta
nufi lecture hall d'insu na ranar"duk da an kusa cimma k'arshe lecturen haka beauty ta banka
musu ciki tsagal-tsagal ba ko kunyar suturar jikinta,kallo ta kai ga lecturern da yake tsaye rik'e
da wata k'aramar takadda a hannunsa yana bayani tace morning sir,tana maganar ne a sa'ilin
da duk wata gab'a ta jikinta ke motsi"tana wani kwarkwasa kamar mai shirin b'allewa"washe
baki lecturern ya shiga yi da ganinta tuni ya taho yana mai laluben biro a aljihunsa yace ina kika
shiga tun d'azu 'yar albarka gashi har anyi attendance?abinci naje ci! Ok toh ai ba damuwa
dama shi gane karatu ai sai ciki ya k'oshi maza amshi sa sunanki daga k'asa!ba musu beauty ta
k'arba ta rattaba sunanta ta mik'a masa tare da sakar masa wata kasalalliyar dariya tace"thank
you sir,gaba d'aya theater tayi tsit ko wane d'alibi da d'aliba zaune suke suna kallon ikon
Allah,ace duk irin zafi na malamin nan da rashin yarda a shigo masa bayan ya shigo yau shi har
yake lallab'a wata"a gaskiya 'yar jami'a ta cika shu'umar kanta!cike da fara'arta ta mik'a masa
takardar had'e da bironsa ta haye sama"har tayi kamar zata shige can sama sosai ta hango
mace da hijabi gefenta babu kowa!da saurinta ta k'arasa wajen ta zauna"satar kallon yarinyar
dake zaune gefenta tayi"ta tabbatar da farin hijabin dake sanye jikinta"leb'enta na sama ta shiga
ciza da hak'oranta kafin ta janyo wayarta daga jaka ta shiga wajen aika sak'o"
I need red pen!!
Sak'on da ta rubuta kenan tare da lalubo lambar xee-xee ta aika mata"
Xee-xee na zaune taji alamar shigowar sak'o da kamar baza ta d'auka ba don tasan halin MTN
da turo sak'o kamar ka sa su!can kuma wata zuciyar ta bata ta duba haka ta bud'e ta
karanta"cikin ikon Allah kuwa tana da shi haka ta nad'e jan biro a tissue ta bayar ma ta gefenta
ta mik'a wa beauty!murmushi ta saki bayan ta amsa!taci gaba da latsa waya abinta tana game
yayinda ko wane d'alibi yayi nisa cikin rubutu saboda dictation yake musu"lura da shagaltuwa
da su kai hakan ya baiwa beauty damar d'akko biron nan a hankali ta bude shi,nan ta shiga
hura ink d'in biron a hankali yana d'iga jikin tissue d'in har ya k'are"haka ta kaikaici idon mutane
ta wullar ya zama saura tissue hannunta"hannu ta zura ta baya ta dai-daici k'asan farar hijab
d'in baiwar Allah nan ta shiga goga mata shi a hankali,sai da ta tabbatar da gaba d'aya k'asan
hijabin ya gama b'aci da jan biro sannan ta dawo da hannunta a hankali ciki ta cukuikuya tissue
d'in ta wullar k'asan seat!
Karatu ake sosai ba alamar shirin tashi gashi duk ta k'agu tabar wajen dole ta d'aga hannu tace
excuse me sir!"kamar jira yake daga can k'asa inda yake tsaye yana koyarwa yace yes go
ahead!narkar da murya beauty tayi"duk wani kalar tausayi ya bayyana fuskarta tace"ciwon kai
nane ya tashi please sir kai min izini wannan baiwar Allah ta rakani zuwa mota na tafi gida
bazan iya zuwa ni kad'ai ba"cikin hard'ewar murya yake amsata da toh kuje ai ba komai Allah
ya k'ara lafiya!
37 *'YAR JAMI'A*
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
í ½í²•
Badan ta so ba haka d'alibar ta kama beauty dake dafe da kai tana cuskune fuska ita ala dole
mara lafiya!da taimakonta haka suka shiga sauka daga matattakalar wajen suka nufo
k'asa!huuuuuuu huuu!!! Shewar maza kenan da kake ji tana tasowa daga can saman theater!
Kafin kace tak gaba d'aya wajen ya cike da hayaniya"tun lecturern yana buga tebur d'in
gabansa yana tsawatar musu har ya kai ga abin ya k'ufular da shi,yayi shiru ya zuba wa
sarautar Allah ido,har beauty suka cimma bakin k'ofar fita gaba d'aya hankalin d'alibar bai kai
akan su ake wa dariya ba,sai da suka k'araso kofa sai karaf idon lecturern nan ya kai ga hijabin
jikin d'alibar yaga duk ya gama b'aci da jini wannan ne ya k'ara tabbatar dashi cewa shine
abinda yasa mazan nan dariya"duk sai yaji wani iri don ganin kamilar mace abu irin wannan ya
sameta a bainar jama'a!gashi d'aliban mata suna son sanar da ita amma babu hali sakamakon
d'abi'ar lecturern da indai an fita toh babu dawowa ciki"dole yasa suka hak'ura,amma abin suma
bai musu dad'i ba don ciwon mace na 'ya mace ne"
Cika min jiki dilla shashasha"!abinda ya fito kenan daga bakin beauty inda a lokaci guda
kuma take k'ok'arin raba jikinta dana d'alibar"cikin rashin fahimta d'alibar ke kallonta don ko ba
komai ai ta gode mata da taimakon da tai mata bata saka mata da zagi ba"kafin ta kai k'arshen
tunanin nata taji an finciko ta da karfi har tana kai tuntub'e kan k'aramin dutsen dake
gabanta,beauty ta shiga jijjiga mata dogon hijabin dake jikinta tana fad'in!ustazu uwar imani!kina
gaba maza na bin ki a baya suna yabo!wai ke 'yar gidan malam me dogon carbi ko? Toh yau
naga abin so a jikinki,ko an gaya miki ana ja da 'yar jami'a da zaki saka malami ya wulak'anta ni
gaban aji wancan satin wai har kina ikirarin baki gane calculation d'in kan allo ba ko?toh tunda
baki gane wancan ba ai nasan zaki gane wanda ke bayan hijab d'in ki ko?tana kaiwa nan
beauty ta cika mata hijabin nata ta bita da wani banzan kallo!mai cike da jin dad'i"duk da har
yanzu d'alibar bata gama fahimtar kalaman beauty ba amma jin ta ambaci hijabi, haka ya baya
damar shiga laluben jikinta cikin sauri, gaban hijab d'in ta fara kaima kallo taga tsaf yake hakan
yasa ta juya bayansa!
Kasa yarda da abinda idanunta suka nuna mata tayi!jan abu ta gani gaba d'aya ya gama b'ata
mata farar hijab d'inta"bata ankara ba taji kamar daga sama ana magana!hak'ik'a wannan shine
sakayyar duk wanda yace zai shiga harkata"yanzu kinga sai ki koma cikin theater maza su ci
gaba da miki dariya ko kuma ki nufi toilet kafin ki je can kuma mazan makaranta sun gama shan
kallo"sai ki zab'i d'aya"
Cike da muguwar dariya beauty ta k'arashe maganar tana watsa hannaye sama ta wuce
zuwa motarta!
Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara kwaranya a fuskar d'alibar wanda ita kanta ta rasa
dalilin hakan"durk'ushewa tai k'asa ta shiga rera wani sabon kuka tana tariyo abinda ya faru
yanzu na yadda maza ke shewa suna ihu da ganinta haka!yanzu ina zata?tunanin daya fara
kawo mata kenan,ta jima tana tunanin mafita sai kuma can dabarar kama wajen ta rike da
hannu ta yadda zai b'oye jan dake wajen ya zo mata"haka kuwa akayi ta kama bayan hijab ta
rik'e ra nufi bayi ta cire sannan ta nemi taimakon wata d'aliba data shiga masallaci ta d'akko
mata hijab dake rataye na sallah ta saka"bayan data gama gyara jikin tane batai wata-wata ba
ta fice daga jami'ar duk wani karatunta na ranar haka ta rasa shi!
38 *'YAR JAMI'A*
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
í ½í²•
_Luv is so sweet when u meet the right person to show it out yeeeee! Oh yeeee!_
Wak'ar da beauty ke rerawa hankali kwance kenan cikin mota,hannu ta kai ga jakarta ta
zaro wani k'aramin dairy nata,wani shafi mai cike da Manyan rubuta ta bud'e nan da nan ta kai
hannunta ga wata da'ira da akai a wani k'aramin akwati da aka zana tayi tick aciki!alamun
yiyuwa na cimma wani abu!bayan da ta gama ne ta kalli agogon hannunta taga har lokacin
12:00p.m ba tayi ba!Tsaki ta saki had'i da kunna motar tata, ta sureta da gudu kamar mai shirin
tashi sama tai hanyar fita daga jami'ar!anan ne ta gamu da wani malami wanda ya d'auke su a
zangon karatunsu na farko,wanda shima ba laifi d'an harka ne don ko ba komai ya bata marking
da ta gamsu dashi"hakan yasa ya haska mata fitila itama ta haska masa na alamun
dakatawa"waje ya samu gefe yayi parking itama ta samu tayi sannan ta fito tayo wajensa"da
yake motar tasa itama bak'in gilashi ne haka ya bud'e mata motar ta shige ciki ta zauna!gaisawa
sukayi tare da maida bayan saduwa"sun d'au lokaci mai tsawo suna hira abinsa kai kace don
ita ya shigo"daga bisani ta nemi tafiya amma sam yak'i bari ta tafi,sai ma shiga bata wasu
labaran yayi masu matuk'ar tasiri a zuk'ata"
kwan! kwan! kwan!k'arar bugun gilas kenan suka ji daga b'angarensa,ba tare da nuna alamar
damuwa ba"ya kalle ta ya sakar mata wani kasalallen murmushi itama ta watso masa sannan
ya iya sauke gilas d'in motar k'asa".
Baki bud'e har kana iya hakaito hasken fararen hak'oransa ya ji ance c'mon! malam bani
laptop d'ina da aikin da zanyi da ita ka barni ina jira ka taho nan wajen......kalaman sameer
kenan wanda bai kai ga k'arashe su ba idanunsa suka sauka ga macen dake gefen kujera
zaune,wanda itama dai daga b'angaren nata shi take kallo"dimmm lokaci guda suka ji wani irin
matsananciyar bugawar zuciya"kasa danne yanayin da yake ciki sameer yayi dole ya katse
maganarsa ta farko ya fito da yatsa waje ya shiga nuna beauty yana fad'in"me wannan yarinyar
take maka a mota kamal?d'auke da wata siririyar dariya saman fuskarsa malamin wanda aka
kira da kamal ya kai duba a karo na biyu ga beauty kafin ya juyi gareshi yace wai wannan?ehhh
ita!!sameer ya bashi amsa a tak'aice"ko da yake ka gane ba na buk'atar ma na sani don nasan
abinda ya kori shaho daga shek'a bazai wuce yunwa ba!bani laptop d'ina na wuce"cikin fushi
kake jin zafafan kalaman sameer na tashi!da yake yasan halin mutumin nasa kamal don ko
suna office wani lokacin in ya d'au zafi ba mai iya masa sai in don kansa ya saki!haka ya mik'a
hannu kujerar baya na motar ya janyo jakar laptop d'in ba uhmm balle um'um ya mik'a
masa"karb'a sameer yayi duk da haka cikin fushi ya sunkuyo da kai cikin glass d'in yana
kallonta yace wallahi i hate u to the extend level baki da hali,baki da hali banza mara kamun
kai"!bai jira cewar su ba ya sa kai yayi gaba"
kamar a mafarki haka beauty ke jin kalaman sameer na dokar kunnuwanta"duk wasu k'ofofin
tunaninta sun riga sun kulle ruf,k'afe ido tai ga sararin wajen da sameer ya bari tamkar mai wani
nazari,can kuma sai ji tai ta saki wani irin k'aramin yak'e wanda ya fi kuka ciwo,bata jira jin wani
abu daga bakin kamal ba, ta bud'e k'ofar tana shirin fita,cikin sauri kamal ya rik'o hannunta yana
fad'in please dear wait ki ji wani abu"cikin zafin nama beauty tai wurgi da hannunsa gefe ta fito
da sauri daga motar ta nufo tata"a fusace haka ta fad'a cikin motar kamar wacce hankali yabar
jikinta haka ta finciki motar tayi waje!
39 *'YAR JAMI'A*
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
í ½í²•
Zaune yake cikin office d'insu da alama aiki yayi masa yawa yadda ya duk'ufa sosai akan laptop
d'insa dake ajiye saman tebur d'in gabansa yaji an turo k'ofa,sam bai damu da sannin wanda ya
shigo ba don kuwa su uku ke zaman office d'in,sallama yayi kamal yayi sannan ya shigo
ciki,kujerar dake kallon ta sameer ya zauna yana d'an gyad'a k'afa,alamun daya gani daga
sameer na bashi da niyyar kulasa ne yasa shi k'ara gyara zamansa yace"amma dai kaji
shigowa ta ko?eh kuma na amsa maka sallama ba!sameer yayi maganar kansa na sunkuye a
laptop!murmushin k'arfin hali kamal ya saki sannan yaci gaba da maganarsa"wai shin kuwa
sameer ina kasan 'yar jami'a naga tun da ka ganta d'azu tare da ni duk ka sauya gashi kamar ni
d'in ma fushi kake dani!
Banza sameer yayi da shi tamkar bai ji me ya ce ba har na kusan minti uku sannan ya d'ago
raunanan idanunsa da tuni sun gama k'ank'ancewa saboda gajiyar aiki ya sauke su saman
nashi"malam aiki fa nake ka zo zaka dameni,ina ruwa na da kai da ita,tunda kai ma ka zama
mai biye ma shashashan mata ai se kaje kai tayi,kar fa ka manta tare muka zo aikin bautar
k'asa jami'ar nan kuma ni baka ga ina biye musu ba toh ni ma kenan dana tashi cikin
hausawa,nasan illar abin ina ga kai daka tashi a birnin kudu,ya ci ace yanzu kasan me
kake,basai an gaya maka ba,amma fa shawara ce bazan hanaka jin dad'inka ba sai dai ka sani
yarinyar dana ganka d'azu da ita tun ran da na fara zuwa jami'ar nan na fara had'uwa da ita duk
da bata gane ni a lokacin ba amma ni na ganeta saboda mummunar shigar dake sanye
jikinta"don haka ina shawartarka please kaje kai dukkan abinda kake so amma ka rabu da
wannan yarinyar wallahi bata da tarbiyya!cikin wani irin mawuyacin hali da yanayi sameer ke
magana,kana ganinshi zaka fahimci tabbas duk kan abinda yake magana akanshi ba mai dad'i
bane!
Ba don kamal ya ji maganar abokin nasa ba amma ya zai yi dole ya nuna masa ya gane komai
kuma zai gyara da haka suka rabu kamal ya koma tebur d'insa ya fara aiki shima sameer ya
d'ora daga inda ya tsaya!
****
Misalin k'arfe hud'u na yamma 4:00p.m, kenan a agogon dake sak'ale a hannun sameer"ajiyar
zuciya ya saki lura da yadda lokaci ya tafi haka"kafin daga bisani ya had'a kayansa ya fito,a
harabar office d'in nasu yaga an had'a jam'i ana k'ok'ari tada sallah haka ya aje kayansa gefe
yabi jam'i sannan ya shigo motarsa ya fito daga jami'ar! Tafiya yake hankali kwance har ya kai ga kwanar da zata sada shi zuwa gidan aminin nasa
ameenu kamar yadda ya saba wuce wa can kullum sai kuma dare ya koma gida"maganar
ummah ce ta fad'o masa na cewa bayan ya tashi daga aiki zasuyi magana"dole ya juyar da kan
motar tasa sanin cewa in bai je lokacin ba dare zai zamanto dare yayi nisa watak'il ma tayi bacci
a sa'ilin,haka ya d'auki hanya sai gida!
Horn biyu yayi baba mai gadi ya fito don ganin wane ne da mamaki sai yaga motar sameer!har
ya bud'e masa gate suka gaisa ya shigo gaba d'aya baba mai gadi mamaki bai sake shi
ba!tunani ya shiga yi Allah yasa dai lafiya ya dawo yau da wuri!ko da sameer yayi parking haka
ya fito ya k'ara gyara zaman darkblue suit dake sanye jikinsa"sannan ya zura phones nashi a
aljihu ya nufi hanyar shiga babban falo!
Assalamu alaikum!Assalamu alaikum! Sallamar da sameer yake yi kenan amma da alama
babu motsin kowa a falon"ganin ya d'au lokaci tsaye ya sashi yanke shawarar ya wuce d'akinsa
kawai zuwa an jima sai ya dawo"ya yunk'ura kenan zai juya yaji an bud'e k'ofar!dawo da
kallonsa yayi wajen,inda hakan yayi dai-dai ga kallon ummah gareshi tace"aufff ashe kai ne? Eh
ummah! Ina yini!cike da girmamawa sameer ke gaisheta!haka ummah ta amsa masa da lafiya
lau!sannan tayi masa iso da ya k'ara so ciki! Cikin nutsuwa sameer ke bin bayan ummah har
suka k'arasa cikin falon, kujera tai masa nuni da ya zauna! K'ara gaisawa sukai kafin ummah ta umarci akawo masa abin tab'a wa baki!
Duk da ba wani iya cin komai yayi ba don sameer bai saba da cin abinci gaban mutane ba"in ba
dole ba, musamman ma yau da ya kasance gaban ummah!haka ya aje juice cup d'in dake rik'e
a hannunsa a centre table"ya d'ago kai yana kallonta da alamar son jin wani abu daga
gareta"matsakaicin murmushi ummah ta saki sannan tayi gyaran murya tace! D'azu nace in ka dawo kazo ina nemanka"saboda a ganina yaci ace kawo yanzu nasan da
wane irin mutumi muke zaune a cikin gidan nan!jinjina kai sameer yayi da nuna gamsuwa da
furucin ummah!sunkuyar da kai k'asa yayi sannan ya fara motsa leb'ensa!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
40-45
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
Ni dai sunana.......pinn pinn...k'arar wayar ummah kenan da ta fara ruri a lakacin wanda hakan
ya ba sameer damar tsayawa don ta amsa wayar!hannu takai ummah ga wayar dake aje
gefenta ta janyota!ta duba sunan wacce ta kira"yagana kuma?ba d'azu muka gama waya
ba?ganin kiran yana daf da katsewa yasa ta tayi saurin d'aga kiran ta kara a kunne!k'ara
gaisawa su kai amma duk yanayin da ta tsinceta tabbas a lamar tambaya!lafiya dai ko? Jimmm
yagana tayi na wasu 'yan lokaci sannan ta nisa tace jikin malam ne ya k'ara tashi yanzu gashi
babu wani babba a gida sai