Showing 36001 words to 39000 words out of 59972 words

Chapter 13 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf

Advertisement

08 Jul 2025

3225

kina so kice min har akwai wasu na xahiri?ehh
toh lallai ke tashin shuri ce don daga gani bade rainon mutim basai dai aljani!

Ganin yadda sameer ya samu damar ci gaba da gaya mata magana son ransa yasa itama ta
mik'e tsaye ta shiga jijjiga jiki uwa mai shirin dambe kana tace na lura kana wasa dani ko?da
sigar ko in kula sameer ya bata amsa da,ni kuwa yaushe zanyi wasa da wacce tayi ikrarin kiran
kanta da sunan 'Yar jami'a ai ban isa ba tunda ban tab'a bin wani malami tsoho mai nauyin
shekaru ya prof KAS na buk'aci b'ata masa mutunci ba,ban kuma tab'a nuna tsiraici na afili don
samun distinction ba kin ga kuwa baxan tab'a had'a kanki da ni ba!

Hucin da beauty ke fitarwa kad'ai zai zayyanar dakai irin halin da take ciki na k'unar rai na lura
da duk wata gab'a da tabi don taga ta d'au fansa sameer ya kasa bata wannan damar!
Awulak'anceta watsa masa wani mugun kallo had'e da sakin wani mugun zagi ta koma ta nemi
waje ta zauna jiki ba kwari"abubuwa kala-kala ta shiga sak'awa a zuci ganin yadda ko da sau
d'aya zatai nasara akan sameer amma nazarinta ya kasa bata,dole haka ta hak'ura na lokacin
ba don ta janye k'udurinta arai ba dai don ta gama da jinyar tsoho tukunna!
shi ko sameer lura da yadda ta yi lagwas yayi don haka ya shiga murmushin mugunta ala dole
ya iya furta hmm kad'an kika gani yarinya in dai kin ce ke 'yar jami'a ce toh mu masu gyara
jami'a ne kuma dole ki ladabtu ko kin k'i ko ki so!daga haka shima ya nemi can nesa da ita ya
zauna tare da janyo waya a aljihunsa ya shiga yin game na zima revenge ko ya samu sauk'in
rai!

Haka sukai zaune har wajen azahar kafin nan dr ya fito hannunsa rik'e da wani abin kwajin

numfashi ya nufosu,ko da sameer ya hangoshi tashi yayi fuska a sake ya nufi wajensa yana
fad'in dr. Ya jikin nasa?murmushin k'arfin hali ya saki kafin nan yace c'mon down prince ba wani
abu ne na tada hankali ba jimawa da yayi a gida ba tare da an kawo shi asibiti ba shiya
haddasa masa hawan jini amma yanzu cikin ikon Allah mun samu munyi controlling nasa sai dai
tarin da yake ne wannan sai a hankali kuma ana shan magunguna,yanzu haka yana ciki ya
samu sauk'i sosai don nayi masa allurar bacci zaku iya shiga ku ganshi in har jikin naga ba
matsala zuwa yamma kafin na tashi a aiki na sallame ku!

Amsa masa sameer yayi da toh sannan ya k'ara gode masa da namijin k'ok'arin da yayi yabar
duk wani aiki nasa yayi nasu!musabaha suka yi kafin ya basu izinin shiga ciki shiko ya wuce
waje,jami'an lafiyar da suke tare suka mara masa baya!

Duk bayanin dr. a kunnen beauty ake yi duk da tana can zaune amma hankalinta na kansu
haka bata jira cewar sameer ba duk da tasan ba wani abu zai ce mata ba yana shiga d'akin ta
biyo bayansa ta shiga!kwance suka iske tsoho yana bacci hannunsa d'auke da ledar k'arin ruwa
da aka saka masa,cikin sauri beauty har tana bige kafad'ar sameer ta k'ara gefen gadon ta rik'o
hannunsa cike da tausayin halin da yake ciki ts shiga rero kuka!.
Cike da b'acin rai sameer ke binta da wani wulak'antaccen kallo shi ala dole ta buge masa jiki
gashi yak'i jinij yaga mace tana kuka balle wannan daya lura kamar ita jin dad'in kukan ma
take,tsawa ya daka mata a tsawace yace dalla malama ki wa mutane shiru uban me akai miki
da zaki cika mana waje da k'ara?wannan shegen kukan naki ai se ya tashe shi" Bata iya tanka masa ba beauty illah tsagaitawa da kawai ta iya yi da kukan!ta nemi waje gefe
dashi ta zauna ta k'urawa tsoho ido, a sukwane shima sameer ya koma can baya ya jingina da
bango tare da hard'e hannayensa biyu a k'irjinsa cike da damuwa ya ke kallon yarda robar
ruwa ke d'iga cikin kwaroron robar hannunsa! [10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

81-85



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*




Har wajen k'arfe d'aya na rana tsoho na kwance bai tashi ba,jin kiran sallah na tashi daga cikin
masallacin ya baiwa sameer damar fita ya barsu anan,yana sa kai ya fita beauty ta waigo ta
k'are ma wajen daya tsaya kallo nan ta saki wata doguwar tsuka tare da fad'in"aikin banza ai
na zaci bara kaje sallar ba gafin mu zaka zauna yi ka wani kafe mutane da ido uwa soja
gona,tsukar dai ta kara saki don yadda duk take jin ta atakure ita bata saba wannan zaman ba
musamman ma na asibiti ga yunwa data fara addabarta,k'are ma wajen kallo tayi tas taga dai
babu wani abun ci a wajen balle tai tunanin ci,ga babu bayi da xatai alwala ballantana
daddumar sallah cike da b'acin rai beauty ta shiga gunguni wanda ita kanta baza ta tantance
abinda take fad'i ba do takaici!

Tana haka taji an turo k'ofa an shigo, sanin wanda zai shigo yasa ko takan k'ofar bata bi ba
da mamakinta sai ta ji muryar mace,hakan ya bata damar d'ago kai ta kalle ta"
Sannu dai" jami'ar asibitin ta fad'a, yawwa sannunmu,bata k'ara tankawa ba matar ta shiga jere
mata kayan dake d'auke a hannunta,ledojine guda hud'u bak'ak'e sai sallaya da hijabi data
mik'a mata sannan ta iya cewa dama yallab'ai ne yace a kawo miki kuma in kina son wani abu
ga d'aki nan na kusa da wannan kina fita daga hannunki na dama sai ki min
magana"murmushin karfin hali da jin dad'i beauty ta sakar mata don ko ba komai tasan dai
abinci ke cikin ledojin nan don haka ta ce toh nagode amma ina bayi yake?hannu jami'ar takai
ga wani labule da ke manne a saitin gadon tace gashi nan madam"madam kuma? Abinda
beauty ta furta kenan a ranta,toh me yace musu game da ni?kar dai fa ya gaya musu wani abu
na b'atance don k'aramin aikinsa ne?ciskune fuska tayi na dole ba don taso sunan ba tace ok
zaki iya tafiya yanzu,da haka jami'ar ta fice tare da janyo mata k'ofar!


Bayin ta nufa ta d'oro alwala ta fito,inda ta aje hijab d'in je ta janyo ta ta saka dogone har yana
d'an ja mata k'asa,haka ta janyo sallayar da shirin sallah sai kuma tayi turus tana bin d'akin da
kallo ?can kuma ta nisa tace wayyo ni ina ne yanzu kuma gabas d'in?ganin ba fahimtar hakan
zatai ba yasa ta yanke shawarar zuwa ta tambayo matar,aje sallayar tayi ta doshi k'ofa don
fita,tana murd'a k'ofar taji an murd'o ta daga waje an turo,saurin matsawa da baya tayi don kar
ta bige,har ya shigo kallo,sameer kallo ya bita dashi cikin hijab kwanan sha'awa kamar tayi ta
zama kullum haka sai kuma can ya basar ya juya kai gefe cikin izzah ya jefota da tambaya,ina
kuma zaki?ita madai kauda kai gefe tayi uwa bazata amsashi ba sai kuma can ciki-ciki tace
gabas zan tambayo,kamar be jita ya tab'e baki yayi mata nuni da hannu,kalli nan! Kallo ta kai
wajen,bai k'ara tanka mata ba ya nemi guri ya zauna!
Bango ta kai wa harara beauty kamar yana kallonta ta juya ta zare sallayar cikin fushi ta
shinfid'a ta fara sallar!

Tana idarwa kenan ta fara azkhar ta ji k'arar wayarta cikin jaka,kallo ya bita dashi sameer ya na
jiran yaga cikin biyu wanne zatai azkhar ko waya,da mamakinsa sai yaga ta share wayar taci
gaba da addu'ointa,k'arar da cikinta ya bayar da k'aramin sauti yasa ta dole badan taso ba
tsagaita adduarta ta shafa,wani abu ta ji ya tsaya mata a rai kuma gashi dai tana son janyo
ledojin abincin amma kunya ta hanata don yadda k'afafunsa suka tokare ledar" jim ta d'anyi
tana nazarin abin amma lura da yadda yunwa ke nuk'urk'usarta yasa ta dole ta maze had'e da
tsuke fuska uwa wata 'yar dambe ta saka hannu ta shiga janyo ledojin,karaf ledar k'arshe ta
buge masa k'afa, ai kamar jira yake sai ji kai d'asss.. ya kai ma hannunta duka da k'arfi,ledar
beauty ta saki a razane ta d'ago kai ta kalle shi,me kuma nai maka?cike da mamaki take
tambayar,mugun kallon nan dai nashi ya k'ara jefo mara ya galla mata wata harara yace"ehh
lallai kam tunda kin maida tab'a jikin namiji abincin ki ai baza ki san me kikai min ba,toh wallahi
na bar kyaleki kina tab'ani kina cin na jaki banza akuya,zunbur beauty ta shiga yi har tana
hard'ewa da hijabin jikinta ta mik'e tsaye ta kama k'ugu ta rik'e tana wani karkad'e-karkad'e tace
kasan Allah wannan abin naka ya ishe ni ehe,don ba jaka aka kawo maka ba,mutum sai bala'in
naci da shishshigi idan baka son alak'ata dakai tun farko wane karanbanin yasa ka neman
tahowa dani? Me yasa baka jefar dani a hanya na san inda dare yayi min ba?ko an gaya maka
bani da wajen zuwa?meya hanaka zaman wajen da ka dawo yanxu tunda ban kama hannunka
nace zo zauna kusa dani ba?toh dan haka malam kasaurara min ko na ci uban.....ba ta k'arasa
k'arshe zagin nata se ji kake fau..fau..fau wasu zafafan mari har biyar da sameer ya sauke mata
a fuska,bai jira wani abu ba yayi wulli da ita gefe har tana karo da bango ya zari sallayar dake
shinfide a k'asa ya shiga jibgarta da ita,kiciniya suka shiga yi sosai dukkan ninsu a wahalarce
musamman beauty dake kwance k'asan tiles jiki duk shatin duka,shiko haki ya shiga furzarwa
na wanda bai saba shan wahala irin hakaba!

Ganin yadda ta galabaitu yasa sameer dakatawa da dukan yayi cilli da sallayar gefe ya
nunota da yatsa yana maida haki yace"wallhi duk randa kika kuskura kika k'ara magana irin
wannan sai kin raina wa aya zak'inta mutuniyar banza kawai,har ni zaki kalli mahaifina ki zaga
wanda ya bani cikakkiyar kulawa da tarbiyya?toh baki isa ba wanda duk kike tunanin ya tsaya
miki shima bai isa ba,da kuma kike cewa na takura miki,eh naji na takura miki don bazan zauna
ina kallo karuwa ta lalatamin rayuwa ba,don haka ki kama kanki!
Yanda take kwance k'asa tana maida numfashi haka ta shiga nuna kanta da yatsa tace,ni ka
kira da karuwa?karuwa fa?k'ok'arin mik'ewa zaune tayi amma ina jikin yayi tsami dole ta komar
da kai ta kwanta k'asa wasu mugayen hawaye suka shiga anbaliya a kuncinta!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

86-90

💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Yarda take maida hak'i na kuka haka sameer ke maida hakin wahala suna haka sai rurin waya
ya k'ara tasowa daga jakar beauty,sai alokacin ta tuna da d'azu an kirata tana addua haka da
janjiki ta isa gaban jakar ta sa hannu ta fito da wayar,lambar zee-zee ta gani rass gabanta ya
fad'i ba tare da wani dalili ba,d'aukan kiran tayi ta kara akunne tana fad'in hello"murya
k'asa-kasa beauty ke amsa ta can kuma kome zee-zee ta gaya mata sai cewa tayi what??kina
so kice min yau akayi test d'in?toh ba cewa akai se last week ba?har nawa akayi?biyu?wanne
da wanne?sir p... maganarta yayi dai dai da kallon sameer wanda ke zaune gefen tsoho ya dafe
kai da alamar damuwa tare dashi,a sanyaye ta k'arashe wayar sukai sallama da beauty duk jiki
ba kwari,tana kashe wayar ta k'ara sulalewa k'asa ta kwanta,tunani kala-kala tun tana iya danne
zuciyarta har ta gaza a fili ta shiga dukan tiles din dake shinfid'e k'asa tana fad'in
mugu,mugu,azalimi wallah Allah sai ya sakamin!

Tana cikin wannan hali taji daga sama rurin wayar sameer dole ta tsagaita da kukan ta maida
kanta ta had'e da gwiwoyinta, zaro wayarsa sameer yayi daga aljihu ya amsa kiran bai wani
jima ba ya gama wayar,wata lambar ya shiga laluba beauty na kwance taji cikin wayar yana
fad'in kamal yanzu za'a zo a kawo maka test d'ina pls ka adana min kafin na dawo! Da haka
suka ci gaba da hira har ya gama,aje wayarsa ke da wuya yaji alamun motsi daga bayansa,da
sauri ya juya idonsa ya ci karo da tsoho dake kwance yana k'ok'arin tashi,k'arasawa sameer
yayi ya tallabo shi yana tai masa sannu,wanda hakan ne ya tabbatar ma da beauty cewa tsoho
ya tashi ,a hankali ta d'ago ta zauna,dishi-dishi haka ya shiga bud'e idonsa har Allah ya saka ya
bud'e su gaba d'aya,alama ya fara nuna masa da yana buk'atar ruwa don haka cikin sauri
sameer yayi waje don kiran dr.

Sameer na fita tamkar ya baiwa beauty damar k'arasowa wajen tsoho ne cikin jan jiki haka ta
k'araso suna had'a ido suka sakar ma juna dariya haka ta rungume shi da haka ta hau masa
sannu!suna haka sai ga sameer ua shigo tare da dr.dole ta basu guri dr yayi 'yan
bincike-bincikensa ya gama da yake ruwan hannunsa ya kai k'arshe zare masa yayi kafin nan
ya rubuta masa magunguna yace su zauna nan ya k'ara samun k'arfin jikinsa zuwa anjima sai a
sallame su!dad'i sosai ya lullub'e jn yadda cikin k'ank'anin lokaci tsoho ya samj sauk'i,takardar

maganin dr. Ya mik'a wa sameer sannan ya basu waje,ledae dake aje sameer ya hau bud'ewa
har ya gano wacce ke dauke da ayaba,hannu yakai ya d'ebk yadawo gefen tsoho a hankali ya
shiga bashi yana ci har ya gama dai tsoho ba emm ba em em duk tunani ya gama cika game da
dabuwar fuskar daya gani tare da jikarsa amma lura da yadda beauty ta kasa sakin jiki suyi hira
sosai kamar yadda suka saba sai yayi zaton ko kunyar had'uwarsu da sirikinsa yasa ta shiru(loh
tsoho bai sai su beauty duka aka sha ba)da haka ya kauda tunanin a rai"!


_4:30 na yamma:_


Tsaye suke bakin asibitin rike da takardar sallama inda sameer ya rik'o hannun tsoho duk da
jikin da kwarinsa sai dan bashi kulawa kawai,ita ko beauty tafe take nik'i nik'i da ledoji ,baya ta
bud'e ta shiga inda sameer ya sanya tsoho gaba ya zagaya ya shiga motar suka fita a asibitin!

Tun saka kan motar sameer a layin tururuwar jama'a kad'ai kake gani ta ko ina ana biye dasu
ana ihu na farin cikin tsoho ya dawo,yara ko se d'ane motar suke da yake yamma tayi duk wasu
magidanta sun dawo k'ofar gidan tsoho mak'il yake haka suka tsaida motar,inda da kyar
Sameer ya iya bud'e wa tsoho k'ofa ya fito dan jama'a,k'ok'arin bud'e marfin motar beauty ta
hau yi don ta fito taji an buge hannun daga waje,sanin waye yasa bata ma bi takai ba da sauri
ta bud'e k'ofar ai ko yayi saurin maida marfin motar ya kulle kafin ya fidda tsoho yasa mata
lock,tururuwar taron jama'ar data gani shi ya hanata magana dole ta koma ciki tai zaune ta bi su
da ido har suka shige cikin gida!don tasan sarai sameer na iya dizgata gaban bainar jama'a!


Juyi da murna babu irin wanda baba yagana batai ba,sam zama ya gagareta,d'akko wancen aje
wannan shine kad'ai aikin kai kawo da take wa sameer sai da ta tabbatar ta cika masa gabansa
taf da kayan abinci da fura sannan ta iya samun waje ta zauna,baba yagana sameer ya kalla
yace baba wai ina d'an ladi kuwa?nisawa tayi kafin nan tace ai d'an ladi ya tafi gona tun bayan
tafiyarku watakil ma yanxu duk inda yake yana hanya,wani abu zai yi?a'a dama maganin tsoho
zai rakani na siyo cikin gari"sameer ya fad'a"
K'aramin murmushi baba ta saki sannan tace ai ban baka labari ba d'azu bayan tafiyarku
drammer aka sha ni da shi,wai ala dole anyi masa haramiyar jin rab'ar mota,da gunguni haka ya
fita ko ta kansa ni kam ban bi ba ina tunanin yadda tsoho zai samu lafiya duk na gama tada
hankali,tunani ya kasa yarda cewa zai dawo da rai sai gashi ya shigo da k'afafunsa kai amma fa
mungode da wannan taimako naka!
Ba komai baba ai yiwa aki ne yanxu dai ki sama wa tsoho wani abu yaci kafin ya dawo mu siyo
maganin"haka baba ta amsa da toh ta mik'e ta nufi cikin uwar d'aka!

Hankali kwance sameer ya gama cin tuwon alkama miyar gyad'a da baba yagana tai masa ya
bishi da fura wacce tasha kindirmo,ya jingina kenan da bango yana son abincin ya ratsa masa
yaji maganar d'an ladi yana shigowa"
Maimakon ya shigo da sallama sai 'yan wake-wake da yake sakin kamar d'an makid'i har ya

zauna dariya kawia sameer yayi masa sannan yace,har ka dawo daga gonar?banza yayi dashi
kamar be ji shiba da haka sameer ya ci gaba,dama kai nake jira ka dawo muje mu siyo wa
tsoho magani a mota,da jin haka cikin sauri dan ladi ya waigo yana kallon sameer yace wai da
gaske kake zaka shigar dani mota?gyad'a kai sameer yayi da zummar eh,ai lokaci d'aya d'an
ladi ya saki fuska hira ta b'arke tsakaninsu ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,har da
alk'awarta wa sameer yau zai had'a masa taro mai kyau a dandali suje kallo,da haka dai sukai
ta hira,sai can da hira ta nisa d'an ladi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login