Showing 42001 words to 45000 words out of 59972 words

Chapter 15 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf

Advertisement

08 Jul 2025

3233

gargajiya,murna da farin ciki sosai kake iya ganowa
a fiskokin kowane saurayi dake wajen inda kuwa 'yan mata ke cikin fili suna taka rawa d'an ladi
da d'an mai gari sunai musu lik'i,wayarsa sameer ya fitar daga cikin aljihunsa a yayinda ya shiga
vedio ya hau yo saboda wannan shne karonsa na farko da yaga abun gargajiya irin haka,sai ya
zamana abin ya k'awatar da shi nesa ba kusa ba,beauty dake gefensa tana tsaye jugum tana
binsu da kallo sosai ta shagala da kallo bata ankara ba taji an janyo hannunta cikin tsakiyar
fili,d'ago kai tayi don taga wacece ai kuwa tayi ido hud'u da wata matashiyar bafulatana
fuskarnan cike da fara'arta ta shiga juya mata hannu da nunin su yi rawa,duk da yadda rawa da
wak'a suka zama jiki a wajen beauty sai gashi yau ta tsinci kanta da jin kunyar hasali ma duk
sai take jin nauyin kasancewarta a filin,haka bafulatanar nan ta ci gaba da juya mata hannu
amma sam tak'i yadda ta taka,ganin haka d'an ladi jiki na rawa yayo kanta ya shiga yi mata
lik'i,can gefe guda kuma ya hango sameer tsaye sai d'aukar su yake a waya ai da saurinsa ya
k'arasa ya kamo hannunshi sameer na kaucewa amma ina sai da ya kawosa cikin fili,kunya ya
aje gefe sameer ya kamo hannun d'an ladi suka sha rawarsu suna yiwa juna lik'e,haka dai sukai
ta sharholiyarsu a ranar abinda aka jima ba'a yi irinsa a dandalinba,sosai daren ya k'awatu ga
kowanne saurayi da budurwa,ba su suka tashi a dandali ba sai 12:30,da haka ne kuma kowa ya
kama hanyar gida inda su sameer suma suka nufo gida,beauty kuwa anyi k'awa bafulatana don

har k'ofar gida ta rakota anan sukai sallama ta kuma shaida mata sunanta ladiyo!


suna shiga kai tsaye d'akin tsoho duka suka wuce,beauty da ge gaba ita ta fara shigewa ciki
inda ta iske d'akin cike da mutane har kawo wannan lokacin ga tsoho na kishigid'e gefe yana
dariya wanda hakan ya nuna abin dariya akayi,sallamar tace ta katse su don haka suka juyo
baki d'aya zuwa ga k'ofa,a d'an razane beauty ta ja da baya sanadin fuskar data gani yana
dubanta,jiki na gyarma ta zube k'asa ta shiga gaisuwa,Alhaji ina wuni?
Fuska d'aure wanda ta kira da Alhaji ya amsa da lafiya lau! ya wajensu ummantaki?
Duk suna lafiya!sannan ta iya gaishe sauran bak'in dake wajen wanda da alamun Alhaji ne da
iyalansa suka shigo don dattijuwar mace ke gefensa da matashin yaro!baba yagana ce ta
katseta da tambayar ina kika baro mazan kuma? Nan ta amsata da gasu nan tsakar gida
tsaye!bata kai ga rufe baki ba Alhaji ya jefota da tambayar ke wane maza kuma?yarda take
mutuwar tsoron Alhaji yasa ta kasa basa amsa sai baba ce ta tari numfashinsa da cewa loh ai
su d'an ladi ne sai kuma bak'on da suka taho dashi daga birni,bara na kira ku gaisa,nan take ta
kwala musu kira suka shigo cikin girmama wa dukkan ninsu suka gaisheshi kafin nan tsoho
cikin murya k'asa-k'asa yace sannu dai d'an nan naga magunguna dazu bayan fitarku yagana ta
kawo min kuma nasha kamar yadda kayi mata bayani,ubangiji Allah yayi maka tukwici da gida
ln aljannah yasa kaima kasamu mai yi maka!d'aki kowa ya amsa da ameen!

Alhaji ne ya nemi su tashi su tafi tunda ya zama kamar al'ada duk dare sai sun raba hira a gidan
k'anin nasa!haka sukai sallama suka fita har Alhaji ya kai bakin k'ofa ya juyo ya kalli beauty ake
zaune manne da bango yace zuwa gobe sai ki shigo da bak'on naki waje na ina
nemanku!mutuwar zaune kusan beauty tayi don da an auna jininta awannan lokacin babu
shakka ya daskare!tsawa ya doka mata sosai yace baki jini bane, asukwane ta amsa da toh
sannan ya fita!
Mtsss kai Allah dai ya shirya wannan muguwar zuciyar taka wallahi ace mutum zafi kamar
zaki,tsoho yayi maganar yana k'okarin mik'e,da sauri beauty ta taso ta fad'o jikinsa ta shiga rero
kuka don tasan yadda ya yink'ura d'in nan wajenta yake son zuwa,babin lallashi da bada hak'uri
sabo tsoho ya bud'e inda duk suka zama 'yan kallo a d'akin!can beauty ta tsagaita da kukan ta
d'ago kai tana ajiyar zuciya tace wallahi tsoho shiyasa ko ummah tace nazo bana son zuwa kai
kana sona amma Alhaji baya sona kullum fad'a se duka!janyota tsoho ya kuma yi ajiki yace yi
hak'uri mutuniyar maza ce yagana ta kai ki d'aki kiyi bacci gobe in jiki na ya k'ara sauki zaki sha
labarai!murmushi beauty ta sakar masa sannan ta tashi ta bi bayan baba yagana suka fita,inda
suma dai su d'an ladi sukai bankwana dashi suka nufi d'akinsu!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

121-125

💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



_Karfe 07:00 na safe!_

Zaune take beauty ta gama cin karin kumallo kenan bayan wanka data gama,tashi tayi ta janyo
wata jar doguwar riga mai ratsin fari a ciki ta saka kayan masha Allah abinka da farar mace sun
karb'i jikinta ainun,k'aramin gyalen kayan ta yale kanta dashi kamar yadda ta saba ta shirya
tsaf,baba yagana dake kwance saman gadonta na k'arfe tace sai ina kuma?fari beauty tai mata
da ido tace sai d'akin tsoho kema dai kinsan wannan kwalliyar tsoho ce!dariya baba yagana ta
kwashe da ita sannan tace ja'irar banza kya dai gyara zancen naki,don kin rai nani zaki ce haka
mana tunda jiya da murnarki kika dawo daga dandali,toh kar dai ki manta da zuwanku gidan
Alhaji,lokaci guda beauty ta d'aure fuska ta juyo ido narke tace dan allah baba yagana ki wani
abu akai wallahi ni bana son zuwa don nasan tabbas fad'a kawai zan sha kinsa fa halinsa!fuska
baba ta yamutse da jin maganar beauty sannan ta iya cewa toh ni me zance akai bayan kinsan
halin kayanki,yanzu dai tsoho bacci yake don tun safe ya ci abinci yasha magani ya kwanta,ki
tashi ki yiwa bak'onki jagora ki tafi can gidan tun safe kafin ya fita gona don kinsan ya d'akko
zafin gona kanki zai huce!dariya duka suka saka tare sannan beauty ta zari takalmi da jakarta
tayi waje!



Tsaye take beauty bakin k'ofa ita bata shiga ba kuma bata koma d'aki ba,can dai ta lura
tsayuwar nan ba yi mata zatai ba dole ta matso daf da k'ofar ta manne jiki da bango murya
k'asa-k'asa tayi sallama,d'an ladi ne ya amsa mata amma da mamaki sai gani tai sameer ya
bude labulen k'ofar ya fito,kallo d'aya yayi mata ya kauda kai,ita d'in ma dai kauda kan tayi k'asa
tana son gaishe shi amma tana tsoron dizgi,dole ta iya bakinta ganin bata da niyyar magana
yasa shi tamke fuska a kasalance yace zaki iya wucewa mu tafi ko?ba tare data tanka masa ba
beauty ta shige gaba abinta ta nufi hanyar fita waje,bin ta tayi a baya,haka suka yi ta tafiya da
yake safiya ce babu duk jama'a sai harkokinsu suke yi haka har suka isa k'ofar gidan, anan ne
kuma ta ta tsaya a tafiyar ta juyo ta kalleshi tace nan ne gidan!wani kallon raini sameer ya fara

binta dashi kafin yace in nan ne gidan ni zan shiga nai miki iso ki shiga kome?ta ji haushin
kalamin nasa sosai duk da dama tasan bai zama lallai ya bata kyakykyawar amsa ba haka ta
saka kai gaba ta shige gidan!kusan minti uku da shigarta sai gashi ta fito tace da sameer wai
yace ka shigo! Kallonta kawai yayi ba tare daya ce uffanba, da haka ta fahimci abinda yake nufi
ta shige ciki shi ko yabi bayanta!



Alhaji na zaune tsakar gida rike da ludayi a hannunsa sai gabansa da kwanon koko ya cika shi
taf,a hankali yana surb'ar kayansa yana had'awa da k'osai ya ji sallamar sameer!ludayin
hannunsa ya maida cikin kwanon lokaci guda kuma ya shiga gyara babbar rigar dake sanye
jikinsa,zama na kamala da manyance Alhaji yayi kafin yayi wa sameee iso daya zauna dama
dashi,k'ok'arin zama beauty tayi kafin kace wani abu Alhaji ya da mata wata uwar tsawa ke
shige ciki ki baiwa mutane waje, jiki na gyarma haka beauty ta afka cikin d'aki!kallon sameer
Alhaji yayi akaro na farko ya sakar masa murmushi inda sameer ya sunkwi da kai cikin jin kunya
a ladabce ya gaishe sa,amsa Alhaji yayi da fara'arsa har yanayi masa tayin koko,cikin dariya
sameer ya amsa masa daya gode,shiru ya biyo baya na 'yan wasu lokaci sannan Alhaji ya nisa
yace yaro ya sunanka?cikin nutsuwa ya amsashi da sameer!
Jinjina kai Alhaji yayi na gansuwa da hakan kafin yace toh malam sameer tak'aitaccen tarihin
rayuwarka nake son ji,sannan ka sani a hira dani ba'a k'arya don haka sai ka kiyaye,tom
sameer ya amsashi sannan ya k'ara gyara zama sosai ya shiga motsa leb'ensa!



Da farko dai sunana Sameer Al-qaseem maji dad'i ni haifaffen garin yola ne mahaifina
Alh.Alqaseem maji dad'i ya kasance k'asaitaccen d'an kasuwa a garin yola gashi kuma d'an
siyasa,bayan sarautar gado da muke da ita ta maji dad'i da aka nad'a masa,hakan ne yasaka
bayan zab'en da akai shekara uku baya muka dawo garin abuja da zama sakamakon zab'arsa a
kujerar senator da akayi,mu uku ne a gurin mahaifina,na kasance babba sai k'anne na biyu
mata aysah da salaha wanda duk suna zaune yanzu haka da mahaifana a garin abuja suna
karatu,ni kuma nayi karatuna tun daga matakin karatu na primary kawo yanzu dana kamala
jami'a nake bautar k'asa da nake yanxu a garin kano,gaba d'aya nayi a garin abuja wajen yayan
mahaifina Alh.Aliyu maji dad'i da yake shi can yake zaune sai ya zaman to tun tashi na babana
ya maidani wajensa saboda Allah bai bawa matarsa haihuwa ba sai dai in anyi hutu naje
wajensu!bayan karatu na kuma a b'angaren kasuwancu yayan mahaifina tare muke harkokin
company d'insa dani yanzu haka jira yake na gama bautar k'asa d'ina takaddun company daya
bud'e min yana nan a garin lagos inda zan fara jan ragamar kula dashi dazarar na gama bautar
k'asa! Wannan dai shine tak'aitaccen tarihin rayuwata!
Ajiyar zuciya ta gamsuwa da abinda ya fad'a Alhaji yayi,yadda ya lura da tsantsar hankali da
nutsuwa irin ta sameer yasa shi umartarshi daya rubuta masa lambar wayar mahaifin nasa
dana yayan mahaifinsa a takarda,haka kuwa akayi sameer ya janyo wani k'aramin memo daga
aljihunsa na gaba tare da biro ya rubuta masa,karb'a Alhaji yayi ya linke takardar ya zura a
aljihu,da haka suka shiga 'yan k'anan hirarsu wacce duk bayanine akan sameer da zuriyarsa!

[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

126-130



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Duk labarin nan da sameer ke labartawa Alhaji akunnen beauty dake mak'ale baki k'ofa tana
jinsu da yake d'akin bak'i ne sai ya zamana babu kowa ciki,shiru ya biyo baya nan take kuma ta
shiga nazarin rayuwar sameer da yadda taji tsantsar nasaba da girma irin na gidansu,lallai
wannan mutumin mai girma da karamci ne dole ya ki ni da duk wata halayya tawa toh yanzu da
ace yana nan akai birthday d'ina inda muka sha rawa da maza a lokacin ai da bansan daga jiya
zuwa yau wane irin zagi da tozarta zansha ba!tana cikin wannan tunane taji kamar daga sama
Alhaji yana magana,lallai indai wannan itace rayuwarka ka tashi gidan girma da mutuntaka
kuma ka dace duk inda kaje kaga abu kuma har ka yaba dashi toh abaka,don haka yanzu inaso
ka gaya min gaskiya domin Allah daga saninka da hajara zuwa yau wane irin halayya ka
fahimta tattare da ita!


K'ululu.....k'arar cikin da sameer ya bayar kenan don shi kam anyi masa tambaya mai matuk'ar
tsauri wanda shi kansa bai ma san ta ina zai fara ba inda akan rayuwar beauty ne,a yayinda
beauty tuni ta gama daskarewa jikin k'ofa tana jiran shigowar Alhaji tasha duka don tasan yau
kam kashinta ya bushe, jin yadda sameer yayi shiru yasa Alhaji k'ara jefo masa tambayar ta
wata siga,yace kar ka d'auka na tambayeka haka da wata manufa ne a'a illah dai kawai ya
kamata ace kasan wacece hajara sosai don kuwa ni azamana da ita akwai matsananciyar
soyayya dana lura a tsakaninta da mahaifinta wanda hakan ya sanya ta sangarta mafi muni,har
ya janyo bata ganin kowa da gashi ga shiga mara ma'ana amma zuwansu na k'arshe garin nan

na horar da ita mafi k'ololuwa don a lokacin tana gab da fara shigarta jami'a don haka nake
rok'onka daka gaya min meke wakana tun yanzu na gyara ta basai tayi aure abin yafi k'arfi na
ba!duk da haka shiru sameer yayi don duk wasu k'ofofin kansa ji yayi an gama kulle masa su
wai yau shine ake wa tambaya akan beauty haka?kafin yayi wani k'wak'wk'waran motsi suka ji
sallama daga waje!tuni sameer ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya don kuwa yasan neman
Alhaji akazo yi! Yun k'urawa Alhaji yayi yace ina zuwa daga haka yayi waje!bai jima ba sai gashi
ya dawo nan ya nufo sameer ya zauna yace kaga abokin tafiya ta gona wato makwabcina yazo
don haka zan baka damarka ka je gida yanzu,bazan d'au lokaci da yawa a gona ba saboda
wannan muhimmiyar maganar dazarar na dawo can gidan malam zan nufa sai mu k'arasa
maganar tamu!
Cike da murnar zuci sameer ya amsa shi da toh Alhaji,
Kwalawa beauty kira Alhaji yayi cikin sauri sai kuwa gata ta fito hannu rik'e da takalma don
rikita,kallonta yayi yace ki mai dashi gida zuwa anjima zan shigo bai jira cewar taba ya nufi
hanyar fita ya fice abinsa bayan daya d'auki kayan aikinsa a gona yayi waje!


Duk da jikinta ya gama bata sameer ita yake kallo a lokacin amma sam ta kasa d'ago kai ta
kalleshi balle kwakwakwaran magana, takalmin dake mak'ale a hannunta ta zaro ta saka
sannan ta nufi hanyar fita!ba tare da shima ya damu da hakan da tayi ba sameer ya bi bayanta!
Shigarsu zauren gidan ne kuma labari ya canja don beauty ta gama fahimtar tabbas sameer zai
tona mata asiri dole ya yanke shawarar ta sauke koda kad'an ne daga cikin girman kan da take
ji ta nemi gafararsa!don hakan ne kad'ai zai ceceta yau a hannun Alhaji,yanke hukuncinta yayi
daidai da tsayuwarta haka kuma sukwane ta juyo har suna kusan cin karo da juna ta tsaya,
shima dai tsayawar yayi da sauri ganin yadda jikinsu ke kusan had'uwa yace lafiya dai?? Murya
can k'asa beauty ta kira sunansa"ya sameer!! Shiru yayi yana bin ta da wani wulak'an taccen
kallo har sai da ta k'ara kiran sunan nasa"ya sameer fa magana nake"anan ne ya iya samun
bakin magana ya amsata"ya sameer kuma?yaushe na zama yayanki?ko kuma ince yaushe
daddynki ya gaya miki bayan ke ya haifa miki wani d'an uwa sameer? Bata damu da zancen da
yake ba haka taci gaba da magana,ya sameer don girman Allah kayi hak'uri da duk wani abu
daka sani nayi maka ko kaji labari nayi ma wani wallahi sharrin shaidan ne!!what?? Kinsan
kuwa me kike fad'a 'Yar jami'a??shaid'an fa kika ce?yarinya karki kuskura kiyi wa shaid'an
k'azafi don kuwa bai miki komai ba!ganin yadda sameer lokaci guda ya tada jijiyoyon goshi yasa
beauty sulalewa da gwiwoyi k'asa ta d'ago hannayenta sama tace ba don hali na ba ya sameer
don girman mahaliccinka ka taimaka ma rayuwata,wallahi kana son jefa min rayuwata acikin
mawuyacin hali!
Dariya sosai sameer ya sakar mata har yana sark'ewa,sororo beauty ta bishi da kallo don tasan
tabbas hakan zai faru dama!ke malama ki tashi muje ki nuna min hanya na koma gidan tsoho
na jira Alhaji acan lokaci na k'ure min!cewar sameer yana gyad'a kai na mugunta!narai beauty
ta kuma yi da ido tace haba ya sameer yanzu lokaci kake dubawa ba hatsarin da rayuwata take
ciki ba?yanzu ashe yadda kake kiran sunan Allah dama duk a baki ne?ya sameer ka tausaya
min mana!ganin yadda beauty ta duk'ufa da rok'onsa yasa shi had'e rai a karo na biyu ya daka
mata tsawa"wai ke wace irin mace ce? nace ki tashi muje ko in baza ki ba just tell me sai na
nemi mafita ama ba ki tsaya kina min wani zance mara anfani ba!

Ajiyar zuciya beauty ta saki can kuma ta mik'e jiki ba kwari ta kad'e k'asa da ta shafi kayanta
ta shiga tafiya,bin ta sameer yayi tayi yana kuma k'ara gane hanya sosai har suka iso,har ta sa
kai tana k'ok'arin shiga zaure taji yace ke? Da sauri ta juya kamar dama jira take tace na'am ya
sameer!wani irin duka ya kai ma bango a zuciya kafin nan ya d'ago kai da tuni sun rud'e sun ja
jur yace ba na ce karki k'ara kirana da ya sameer ba?call me wit my real name sameer don
bana karb'ar tuban d'an muzuru,sannan kisani in har kina so asirinki ya rufu sai kin min
Alk'awarin zaki sanar min da duk wani labari naki da dalilin da yasa kike wannan mummunan
halayyar taki!saurin d'ago kai tayi jiki na b'ari beauty ta amsashi tana nuni da hannu wallahi duk
abinda kake son ji zan gaya maka amma ba yau ba sai ana gobe zamu koma kaga yanzu
lafiyar tsoho ya kamata mu kula da ita,kai kuma in Alhaji ya kiraka sai kasan abinda zaka gaya
masa wannan shine kad'ai alfarmar da za kai min!
Kallo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login