Showing 24001 words to 27000 words out of 59972 words
Chapter 9 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf
ta faman yi amma ba taga alamar mutum a wajen ba"fitowa tai ta nufo gate d'in
ta bude k'aramar k'ofar ta shige ciki tabar motar a nan waje,d'akin baba mai gadi ta nufa nan ta
shiga yaye labulen k'ofar!me beauty zata gani? baba ne kwance saman tabarma sai faman
gurnanin bacci yake abinsa daga gani kasan baccin nasa yayi nisa"dube-dube ta soma yi can ta
hango buta a kusruwar d'akin,da saurinta ta k'ara sa wajen ta janyota,ruwa ne cike cikinta haka
ta nufo baba"shaaaaaa kake ji ruwa na malala saman fuskarsa"firgigit baba mai gadi yayi ya
mike zaune yana nanata kalmar shahada"cilli beauty tai da butar gefe sannan ta fice a d'akin
tana gungunin cewa gobe ma ka sake baccin rana mu gani"bai iya cewa komai ba baba mai
gadi illah cire kayan nasa ya sauya da wasu!
K'ofar falo ta murd'a a zuciye ta shiga da mamakinta sai ji tai an fincikota da k'arfi k'asa ta fad'i
saman kafet ta inda ake shiga bata nan ake fita ba saukar duka take ji ta ko ina"kuka beauty ta
shiga rerawa tun kana iya jin k'arar sautin kukan har ta daina"sosai ummah ta farfasa mata
jiki"tana fad'in sakaryar banza da wofi,uban wa zaki kawowa raini a gidan nan? ko dan kinga
ana zuba miki ido shiyasa ko?toh wallahi baki isa ba,baxaki sanadin shigata wuta ba,dan nasan
alhakin tarbiyyarki na hannuna,bakya ganin kowa da gashi se ubanki ko?shi baba mai gadi
sa'an ki ne?toh bari kiji daga yau har ran da uban naki zai dawo shima ya same ni duk na
tanadar muku sai dai ki silar mutuwar aurena,amma tabbas ko kin k'i ko kin so sai ki
kyaru"shasharar kawai"maganganun da ummah ke yi kenan tana ta haki inda su ko masu aiki
ke zagaye da ita sai bata hak'uri suke"sam ummah bata bi ta kansu ba har sai da tayi dukkan
don kanta ta gaji ta haye sama ta barsu anan,carko-carko sukai gaban beauty don ba damar
lallashi"don sarai sunsan halin ta yanzu ta huce akansu"
Kuka beauty take yi wi-wi kamar an aiko mata da mutuwa haka tai mai isarta tayi shiru dan
kanta,ko da ta tsagaita da kukan sai ta mik'e don falon shiru kake ji su kan su ma'aikatan sun
koma bakin aikinsu,ta nufi sama,d'akinta ta bud'e ta shige"bata zame ko ina ba sai saman
gado"ta fad'a nan ta ci gaba da kukanta har bacci yayi awon gaba da ita!can cikin bacci ta ji
kamar ana tashinta"k'ara gyara kwanciyarta tayi sai taji an kai mata duka a k'afa cikin sauri ta
bud'e ido"nan sukai ido hud'u da ummah"ina mukullin motarki?tambayar da ummah ta fara mata
dashi ke nan" murya can ciki-ciki beauty ke fad'ar yana cikin motar"bata tanka ta ba ummah
daga jin haka tayi waje"beauty na nan kwance ta ji alamar bud'ewar gate tare da shigowar
mota"wanda hakan ya tabbatar mata da akwai abinda ummah ta shirya da hakan!duk da ciwo
ga rad'ad'i da jikinta ke mata haka ta k'ok'arta ta mik'e ta shiga bayi tayo wanka" bayan ta fito
tana zaune gaban mirrow tunani ya fad'o mata na jakarta da wayoyinta da ta bari a cikin
mota"haka tai sauri-sauri ta shirya ta nufi hanyar fita daga d'akin har ta isa falo kenan tunaninta
ya kai ga mukullin motar"jim beauty ta yi na wasu 'yan dak'ik'a kafin tayi k'arfn halin koma wa
sama ta doshi sashen ummah!k'ofar d'akin ta murd'a a hankali ta shiga da sallamarta"ummah ta
amsata kai duk'e ga wata jarida dake hannunta"hajara lafiya dai ko?ummah tace"cike da tsoro
beauty ta amsata eh dama umma key na motana ina son d'aukar kayana aciki? Daga jin haka
ummah ta d'ago ka tana dubanta tace Key na mota kuma?da munyi dake zan dawo miki da shi
ne da har zaki biyo ni d'aki?shiru beauty tai cike da mamaki ta na jin ummah inda taci gaba da
magana"eyyeh tambayar ki nake?toh wai da wace tsiyar kika aje a motar in banda wayoyinki da
jaka?sukansu na karb'e ran da duk kikai hankali na baki"sannan kuma kina jina ko daga rana
irin ta yau kar na sake ganin kin bai wa maaikata wanki sunyi miki"tunda kema macece kamae
kowa dole ki koyi wanki don gidan wani zaki"kina jina ko?ido cike da hawaye beauty ta d'ago kai
tana gyadawa da zummar ehh!k'ok'arin barin wajen beauty tayi ummah ta kira sunanta ta
juyo"ina zaki kuma?ai ban gama da ke ba"don na fahimci zaman kad'aici ke saki koyon wasu
munanan d'abi'un dan haka wuce can ga wuri ki zauna'tai mata nuni da kujera"jiki na kyarma
haka beauty ta shigo d'akin ta nufi kujerar da ummah tai mata nuna ta zauna!
í ½í³“í ½í³“33 *'YAR JAMI'A*í ½í³“í ½í³“
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*
í ½í²•
Tun bayan fitowar sameer daga jami'a bai zame ko ina ba sai gidansu abokin nasa
ameenu"kamar yadda ya saba"yau ma dai zaune ya tarar da ameenu rik'e da jarida yana
bibiyar kanun labaran ciki"cike da farin ciki d'auke saman fuskarsa ya nufo shi"daga sallamarsa
kad'ai zaka ji ka tabbatar da yanayin da yake ciki mai dad'i ne"ameenu ne ya katse shi da
tambaya"gaskiya yau dai prince akwai magana bakinka ko? Murmushi sameer ya saki tare da
jinjina kai da zummar haka ne kafin ya samu waje ya zauna ya maido kallonsa ga ameenu yana
fad'in wato yau na ga ribar hak'uri"ribar hak'uri?na me kuma?ameenu ya tambaya,kasan fa
abaya nayi niyyar bin duk wata hanya don naga na kori yarinyar nan a jami'a amma ka hanani
toh yanzu maganar da nake yi maka tazo hannu don kuwa ni nake d'aukarsu statistic yau baka
ga wulak'ancin da nai mata ba"
Baki bud'e cike da mamaki ameenu ke kallon sameer shima dai farin cikin yake da wannan
labari na abokin nashi haka sameer ua ci gaba da zayyano masa duk kan abinda ya faru a
jami'ar, yinin ranar gaba d'aya anan sameer yayi ta kamar yadda ya saba yi,wanda hirarsu ta
yau bata wuce akan beauty bane,bayan sun dawo daga masallaci ne sameer yayi sallama da
ameenu akan zai wuce gida har ameenu na tsokanarshi ko dai wajen wata zashi haka ya fake
da tafiya gida da wuri don sanin kansa ne kullum basa rabuwa sai 9 koma fiye da haka na
dare"haka nan dai su kai sallama shi dai sameer bai biye ta ciwarsa ba" ya nufi gida abinsa"
Kamar yadda ya sabayi kullum haka yau ma yayi, yana yin horn d'aya baba mai gadi ya fito ya
bud'e masa gate,cike da girmamawa sameer ya gaishe shi kafin ya shigar da kan motarsa zuwa
parking space na gidan"jakar aikinsa ya d'akko ya fito aciki ya rufe motar ya shiga waige-waigen
gidan don yau ya ga sabon al'amari na rashin tashin kid'a daga sama kamar yadda ya saba ji
kullum,se yaji gidan duk ya sauya masa"tambayar ko lafiya yake yi a zuciyarsa amma sanin
cewa bazai samu amsar tamabayar tasa bane yasa shi sauke wata guntsuwa ajiyar zuciya tare
da fad'in toh Allah yasa dai mutanen gidan yau lafiya suke da haka kuma ya nufi sashensa"
Wanka ya fara yi sannan ya d'auro alwala ya fito,nafilfilinsa na dare ya shiga jerawa ba shi ya
gama ba sai wajen 10 saura,yana cikin addu'o'i ne yaji wayarsa ta fara k'ara,wanda ko dama
abinda yake jira kenan,da saurinsa ya k'arasa ya d'auko wayar ya kara akunne cike da shauk'i
yace sweet momy nah"daga d'ayan b'angaren ma aka amsashi da my prince"wani sassanyan
murmushi sameer ya saki don ba abinda ya fi so kamar ya ji momy ta kirasa da my prince,cike
da kulawa suka gaisa yana ta faman nuna yadda ya ke kewar momyn tasa itama haka don
kuwa akwai shak'uwa mai k'arfi a tsakaninsu"bayan sun d'auki tsawon lokaci suna hira ne
momy ke tambayar sameer akan lafiyar mutanen gidan"shiru ya biyo baya hakan ya baiwa
momy damar sake tambayar nasa"nan ma dai ba amsa,sameer!momy ta kira sunansa"amsata
yayi muryan nan k'asa-k'asa,sai tace ko dai ba lafiya bane sameer naji ina ta tambayar ka
mutanen gidan amma kayi shiru"daga jin haka sameer bai b'oye wa momy komi ba tsakaninsa
da su da mutsnen gidan akan yadda daddy ya hanasa ko da lek'owa harabar gidan "sosai
momyn sameer tai mamakin abin don har tana nuna masa ko dai zai samu wani masaukin
kawai in nan bai masa ba"nuna mata yayi babu komai zaman nasa da ya kusa zuwa k'arshe
,don a lokacin sameer bai wuce 'yan watanni ya gama bautar k'asarsa ba"ba don ta so hakan
ba amma ya zatai da ra'ayin prince dole ta hak'ura ta bishi a haka"sun tab'a hita sosai kafin yayi
sallama da ita ya kashe wayar"
Kayan bacci ya iya canjawa tare da gyara komai na d'akin yayi tsaf-tsaf don ya zaman to d'abi'a
ta sameer kullum kafin ya kwanta sai ya gyara muhallinsa tun agida"bayan da ya gama ne ya
rage wutar d'akin tare da bin lafiyar gado!"
í ½í³“í ½í³“34 *'YAR JAMI'A*í ½í³“í ½í³“
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*
í ½í²•
Misalin k'arfe bakwai na safe sameer tsaye yake gaban motarsa yana k'ok'arin bud'eta ya
shiga ya ji kamar daga sama an kira sunansa da alamar manyance,saurin juyowa yayi cike da
mamaki ya dawo da dubansa ga inda sautin kiran ke tashi,ido ya kai ga dattijuwar dake tsaye
bakin k'ofar sanye cikin dogon hijabinta fari fat, tunani ya fad'o masa kan tabbas ko bai
tambaya ba wannan ita ce hajiyar gidan,cikin sauri ya k'arasa har inda take ya russuna yana
gaisheta kai a k'asa,sosai ummah ta ji dad'in yadda ya gaisheta'amsashi tayi kafin tai masa nuni
daya mik'e tsaye"kasa mik'ewa sameer yayi se ma shiga susa k'eya da yayi yana fad'in ba
damuwa hajiya nan ma yayi,murmushi ta k'ara saki wanda ke nuni da farin cikinta gareshi tace
dama magana ce zamuyi amma kaje in ka dawo daga aikin sai muyi"toh kawai sameer ya
amsata dashi da haka ya mik'e ya nufi mota ita kuma ummah ta shigo ciki"
Da yake daren jiya beauty na tare da ummah don a d'akin ta ma tai bacci sai ya zamana
yau tashin wuri tayi,saboda tun kiran sallar farko ummah ta tasheta haka zalika bayan sun idar
da sallah ta mik'a mata al'qur'ani nan beauty ta shiga karatun dole ba don taso hakan ba,har
wajen shida na safe sannan ta rufe shi ta nufi gado ta kwanta"dawowar ummah cike ne ya batar
damar komawa d'akin nata ta tashi beauty da tai d'ai-d'ai saman gado tana bacci"har a sakko
daga gadon ba alamar motsi a leb'enta"hakan ya baiwa ummah damar kallonta cike da takaici
tace ita addu'ar tashi daga baccin ni zan tofa miki ko kuwa ya akai?cikin mawuyacin yanayi
beauty ta ji tambayar"ita mamaki abin ya bata yanzu ace har da wata addu'ar tashi daga
bacci"amma gudun fad'an ummah hakan yasa tilas badan taso ba ta hau mutsu-mutsu da
bakinta kai kace da gaske adduar take har ta bar d'akin"
Ba ita ta gama shirin taba sai kusan tara na safe sai gata ta fito cikin wasu matsatstsun kaya
riga da wando wacce rigar bata wuce gwiwa ba"sai wani yalelan gyale da ta rufe kanta dashi
wanda dashi da babu duk d'aya ne"ko takan breakfast bata bi ba don yanzu duk abinda zau
had'ata da ummah bata so don ko jakar makarantar yau wata sabuwar ta d'akko,sand'a ta shiga
yi a hankali har ta sakko daga sama ta kai bakin k'ofar fita daga falo kenan ta tuna da key na
motar da ke wajen ummah"dafe kai beauty tai kamar zatai kuka don takaici amma ya ta iya dole
hakan zata koma"kallo ta fara kaiwa ga suturar dake jikinta tasan tabbas ta je wa ummah da
wannan shigar baza su rabu ta dad'in rai ba"shiru tayi kamar me nazarin wani abu se can
dabara ta fad'o mata"yes!yes ta fad'a cike da murna cikin sauri ta haye sama ta nufi sashenta"
drawer d'in ta na kaya ta bud'e ta shiga lalube"tsohuwar ajiyar da tafi shekara uku a ajiye ta
janyo wani dogon hijab da tun zuwan daddy dubai ya siyo mata akan tana sallah dashi ta d'akko
cikin murna da wannan shawara data samo ta saka shi cike da yiwa kanta dariyar abinda tayi ta
nufi wajen ummah!!
35 *'YAR JAMI'A*
_BY_ *HERWWERH~JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*
í ½í²•
Beauty cikin nutsuwa ta tura k'ofar d'akin ummah ta shigo,zaune ta tarar da ita saman kujera
hannunta rik'e da remote tana k'ok'arin sanya channel d'in MBC 4,ciki-ciki kamar mai koyon
magana beauty ta shiga tambayanta key,banza tai da ita kamar ummah bata san da mutum a
wajen ba har sai da beauty ta k'ara nanatawa sannan ta d'ago fuska a dak'ile ta k'are mata kallo
tas,tai mamakin yadda taga shigar 'yarta ta yau amma a hakan ta cije ta b'oye narkakken farin
cikin dake kwance saman zuciyarta na ganinta haka, tace gashi can saman madubi wuce ki
d'auka,gefe kuma ga wayar ki can ki d'auki babbar ki anfani da ita kuma da zarar kin dawo ki
maido min key d'in nan!toh kawai beauty ta iya cewa jiki na rawa ta d'akko su ta fito had'i da
janyo mata k'ofa ta rufo,tana fad'in yes!yes!!cike da murna beauty ta sakko ta nufo waje!A
gaban motar beauty ta cire hijab d'in ta bud'e ta wullashi ciki,kallon motar ta sake yi,sosai motar
tayi kyau yadda taga an wanke ta sosai ta fita"haka ta shiga yau kam ba yabo ba fallasa
gaisawarsu da baba mai gadi bayan sallamar kullum ta kud'i da tai masa"ta wuce abinta sai
makaranta"!
Da yake batayi wani breakfast ba ta fito dole tana shigowa ciki ta wuce STOP &
CHOP,shiru wajen yau yake tunda safiya ce sai ma'aikata da suke ta faman kai kawo suna
gyaran wajen"da shigarta kowa ya yo kanta suna kwasar gaisuwa,meenu kamar yadda take
kiran yaron nata na wajen haka ta kirashi bayan ta zauna ta zayyana masa abinda take buk'ata
ba'a d'auki wani lokaci mai tsawo ba sai ga shi ya dawo cike da kayan abinci da na sha haka ya
jere mata su gabanta beauty ta shiga ci hankali a kwance"bayan data gama ne tana k'ok'arin
fita daga wajen bayan da su kai mata total na duk abincin da su kai na ranar ta biya su kud'in da
zummar ayi yadda aka saba na raba wa d'alibai da sunanta"wasu mata ta gani su hud'u kana
ganinsu kaga rik'ank'un mata masu zaman kansu"don lalatattun shigar dake jikinsu kad'ai ya
gama fassarasu"takowa su kai suka shigo har gaban beauty sannan ko wacce ta ja kujera ta
zauna"!
*'Yar Jami'a*!!sunan da d'aya daga cikin matasan kenan ta kira beauty dashi wanda hakan ke
nuna itace gaba da su"
Ya mutse fuska beauty tayi tana kallonta kafin ta amsa mata da lafiya dai ko?ki ke kiran
sunana da sanyin safiyar nan??
K'ara gyara zama sosai matashiyar tayi saman kujerar ta fuskanto beauty sosai sannan ta hau
magana" A gaskiya wato kin gane kina d'aya daga cikin matan da muke yawan jin labaranki
daga maza kai har da mata na jam'ar nan akan yadda kike rayuwarki cikin jin dad'i da
gogewa"sai muka ga abin ya burge mu shine muka yi tattakihar cikin makarantar nan don
samun damar ganinki,amma ko da muka nemeki sai aka shaida mana baki shigo ba sai dai aka
nuna mana aminiyarki"ita ta shaida mana kina nan"toh agaskiya dai 'yar jami'a duk da ban san
ya zaki karb'i abun ba amma mun zo miki ne da tayin wani babban rabo"wanda muke ganin zaki
iya"wannan abin ba komai bane illah muna so ki shigo cikin k'ungiyarmu wanda take da reshe
da yawa a sassan jahar nan,muna so ki zama cikin ta biyar agaremu,kinga taron sati da za'ai a
gidan uwar d'aki sai mu gabatar dake"yanzu dai tare dani wannan ta hannun damar tawa
sunanta nusaiba amma anfi kiranta da nusy,wannan kuwa ta gefen hagun sunanta shamsiyya
wato shamsy kenan!sai kuma ta gefenta surayya ko kice sury daga haka sai ni mai gayya mai
aiki miss lollipop wato lawiza"bata kai ga aje numfashinta ba lawiza kamar yadda ta fad'i
sunanta beauty ta katse mata hanzari da hannu tana fad'in toh kin gama?caraf sury ta amshe
maganar don taga kamar beauty baza tai na'am da buk'atar su ba"tace ehmm kina jiko 'yar
jami'a ba wai muna nufin da ordinary men fa zaki na harka ba nooo!ba haka bane manyan
Alhazawan k'asar nan ba ma jaha ba duk namu ne sai wanda kika zab'a in ma kince ba da
maza zaki harka ba, suma matan akwai su kala-kala(wa'iyazubillah)sai kin zab'a kin darje,ta
k'arashe maganar surry tana wani kashe wa beauty ido d'aya!kafin beauty ta samu damar yin
magana har shamsy dake can gefe ta ciro wani k'aramin kati mai d'auke da suna har da
lambobin waya ta aje gaban beauty"tace kar ki saurin yanke hukunci ki je ki nazari,wannan
lambobin mu ne,don haka sai mun ji daga gareki,muna fatan kuma baza ki bamu kunya
ba!mik'ewa sukai a tare suka fice"ido kad'ai beauty ta iya binsu dashi wai gaba da gabanta
aljani ya taka wuta"yanda beauty ke ta faman had'a zufa ze tabbatar maka da shigar sabon abu
cikin kwakwalwarta"a sannu ta kai hannu kan katin ta d'akko shi a hankali ta shiga juyasa a
hannu!toh wad'annan mutanen me suke nufi da hakan? Na fara mu'a mala da wasu mazaje a
waje ko me??? Wannan itace tamabayar da take ta faman kaikawo a kan beauty!
36 *'YAR JAMI'A*
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
í ½í²•