Showing 39001 words to 42000 words out of 59972 words
Chapter 14 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf
waiga ya kalli sameer yace wai kuwa ina hajjo?sakin
baki sameer yayi cike da kid'ima bai jira basa amsaba ya mik'e ya zuri takalmi da sauri yayi
hanyar zaure".
Koda ya isa gaban motar kwance ya Taradda beauty sai had'a zufa take kana ganinta kasan ta
galabaita,cikin sauri ya bud'e k'ofar ya shiga lek'enta!..
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: í ½í³“ *'YAR JAMI'A*í ½í³“
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
91-95
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
Lura da alamun bacci da ta shiga yi na wahala yasa sameer bubbuga gefen kujerar
yana fad'in ke!ke!firgigit beauty tayi ta mik'e zaune kana ganinta kasan ta wahala,fuska cuskune
ta kallo shi babu ko kwakwkwaran nauyi a jikinta ga tsamin duka da jikinta ya riga yayi,koma
wa da baya yayi sameer wanda hakan ya bata damar fitowa a motar a daddafe ta maida k'ofar
ta rufe,cikin sanyin jiki haka ta shiga tafiya sai yaji duk babu dad'i abin bai masa ba,amma dole
ya dake ya kallota ta wutsiyar ido yace ke!kike wani cilla k'afa uwa summy cillare(Loh) in zaki
saki jiki gara ki saka in ko ba haka ba na fasa kwai yau kowa na k'auyen nan ya san halinki,da
sauri beauty ta d'ago raunannun idanunta ta kallosa cike da takaici,murmushin mugunta ya
sakar mata had'e da kashe mata ido d'aya yace kinsan dai xan iya don haka sai ki zab'a yana
kaiwa nan yayi gaba abinsa ya shige ciki ya barta nan tana jan jiki uwa wacce kwai ya fashe wa
a jiki!
A cikin zaure beauty ta tsaya nan ta k'ara gyara jikinta sosai,cikin k'arfin hali kuma ta saki
fuska ba yabo ba fallasa ta nufi cikin gida,Da sallamarta ta shigo tsakar gidan babu kowa sai
k'arar muryar d'an ladi dake tashi duk ya karad'e gidan da surutu shi ala dole labari yake ba
sameer,muryar beauty da yaji yasa shi tsagaitawa da hirar ya juyo baki a washe yana kallon
k'ofa,har ta k'araso wajen sameer bai d'ago kanshi daga duk'en da yayi ba tun jin
sallamarta,cikin k'arfin hali beauty ta kalli d'an ladi tace ina tsoho yake,yana d'akinsa"d'an ladi
ya bata amsa,bata k'ara cewa komai ba ta sa kai ta wuce su zuwa d'akin,yadda ta gifta ta gaban
sameer haka ya d'ago kai ya bi bayanta da kallo,k'arewa tafiyar kallo yayi sam babu wani
alamar sauyi ko canji daga tafiyarta,murmushin gefen kunci sameer ya saki a kasalance ya raya
a zuciyarsa"lallai yarinyar nan a iskanci ita yarinya ce har da take tsoron k'aramin k'auye kamar
wannan susan sirrinta,toh ko dai tsoho ne bata so ya sani? Bai kai aya a tunanin nasaba yaji an
tab'o shi a kafad'a,a d'an tsorace ya juyo,lafiya dai ko bak'on birni?tambayar da d'an ladi ya jefo
masa kenan,gudun kar d'an ladi ya fahimto abinda yake kallo yasa shi kauda kai gefe ya d'an ja
numfashi yace ai da kaga na kau da kai ba wani abu nake mazari ba illah b'aci da rai na yayi
ace yadda kake suburbud'amin wannan labari ka kasa bani labarin budurwarka?(kwana ba sai a
mota ba)bud'e idonsa sameer yayi da sigar son jin wani abu ya k'ara langwab'ar da kai gefe
sannan yace toh ko dai baka da ita ne?
K'afa d'an ladi ya d'aga sama ya dire a kan tabarma sai kuma ya kwashe da wata irin
muguwar dariya mai cike da mamaki,sai da yayi ma'ishiyarsa sannan ya d'ago kai a gadarance
yana wani faffad'a kafad'a yace Wato d'an birni ni d'in nan da kake gani na duk ranar da naje
dandali sai 'yan mata sunyi fad'a akai na,shiyasa kaga samarin garin nan duk kishi suke da ni
don mero 'yar gidan mai gari wancan satin da naje dandali baka ga yadda take nuna kauna
k'arara akai na ba,har wani kod'a ni take wai tana son tsagun fuskata,amma ni duk basa gabana
,jin maganar d'an ladi na k'arshe yasa sameer k'are wa bak'a k'irin d'in fuskar d'an ladi mai cike
da tsagu kallo,jinjina kai yayi cike da mamaki,ganin yadda d'an ladi ke ta faman kod'a kanshi ba
ji ba gani,surutan 'yan mata barka tai yasa shi d'aga masa hannu yace toh suda sarkin magana
yanzu dai gaya min wace zab'inka acikin nasu?cikin sauri d'an ladi yayi hanzarin kai hannunsa
ya rufe fuskarsa shi ala dole yaji kunyar tambayar"
Murmushi sameer ya saki ganin yau ya had'u da wani garan yace sai kuma can yace haba d'an
ladi meye na rufe fuska kuma kai dai gaya min ko wace zan baka shawarar yadda zata so ka
fiye da tunaninka, jin haka tuni d'an ladi ya zare hannunshi yace wai da gaske?eh mana kai de
gaya min,turo baki gaba d'an ladi yayi uwa mai shirin surb'ar koko yace bawata bace illa
haj...hajj...sai kuma yayi shiru! haba kai kuwa meye haka ka fad'i sunan sosai mana ni ban gane
wannan yaren ba, jin hak a kunyace d'an ladi ya nok'e kai ciki-ciki yace ni fa hajjo nake so tun
dana ganta d'azu"
Hahahahahahahahaha!wata irin muguwar dariya sameer ya saki wacce shi kansa bai ma san
lokacin data kwace masa ba don kid'ima da abinda yaji,ido waje ya zaro yana fad'in wace
hajjon?ba dai hajjo ta birni ba?washe baki d'an ladi yayi don jin dad'in yadda sameer yayi saurin
gano shi yace alqur'an ka gano ni sarkin wayo!k'ara kecewa sameer yayi da wata muguwar
dariya ta k'eta ganin bazai iya dai-daita kansa da dariyar ba yasa shi mik'ewa da sauri ya kamo
hannunsa yana fad'in kaga taho muje a siyo maganin,a can ma tattauna komai,ba shiri d'an ladi
ya mik'e ya bishi sukai waje!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: í ½í³“ *'YAR JAMI'A*í ½í³“
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
96-100
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
Tun bayan shigar beautu d'aki hira kawia suke da baba yagana don abincin ma kasa cinsa
tayi don yunwar taci ta har ta cinye,duk da kuwa ta jin zugin jikinta,a tsammaninta su sameer
suna zaune a tsakar gida,shiko tsoho na kwance yana bacci tun bayan abincin da baba yagana
ta bashi,jin kiran sallah da baba yagana tayi ya sata mik'ewa da sauri tana fad'in yau naga
yarinyar kawai duk na biye miki da hira gashi ko abinci ban aje miki balle na baki ruwan
wanka,dariya beauty ta saki sannan tace ai dama ba sona kike ba yanzu dai bara nai sallah sai
ki bani jagolgolon da kike yiwa tsoho na ci,dariya duka suka saki kafin nan baba ta fita ta barta
anan!
Gyalen data yale kanta dashi shi ta cire ta k'ara gyara tukkuwar gashin kanta sosai sannan ta
janyo wani k'aramin d'ankwali data gani nan gefen shinfid'ar tsoho ta d'aure kanta dashi ta nufi
tsakar gida!wayam taga wajen babu alamar mutum wanda hakan ya tabbatar mata cewa su
sameer sun tafi sallah ne!k'aramar tsuka ta saki cike da b'acin rai ta furta d'an masifa kawai
mutum kamar maye se shiga harkar mutum gaskiya ya kamata ko ba komai na gaya wa daddy
abinda duk yake faruwa tunda nan ummah bata nan balle ta tsawatar min in ma dawowa zai yi
gara yayi amma duk mutanen nan biyi sun takura wa rayuwata kamar ni kad'ai ce mutum a
duniya?wata tsukar ta k'ara saki cike da cin haushi haka ta nufi bakkin tijiya da zummar kafin tai
bacci daren yau zata sanarwa dady duk kan abinda ke wakana bayan tafiyarsa,butar dake gefe
sanye da ruwa ta d'auka ta nufi bayi!
_8:00p.m na daren ranar!_
Ruwa ta watsa beauty ta shigo d'akin baba yagana wanda ke jere da na tsoho,zaune ta isketa
saman gado tana k'idayar kud'i, eyyeemba su baba an yi arzik'i irin wannan kud'i ince dai kayan
d'aki zaki saya mini dasu?tayi maganar tana yarfe ruwan hannunta,dariya baba yagana ta saki
nan ta d'ago kai tace mata toh sarkin son banza wannan ba kud'in tsoho bane balle a jere miki
d'aki da kumbo wannan kud'in dashi ne da muke yi jiya aka kawo min d'ibata ko k'idayasu banyi
ba don dama na maganin gargajiyar tsoho nake tari sai gashi yaron kirki yazo ya share mana
hawayenmu,abinda shekara da shekaru ake magani yau lafiya gobe babu amma kiga jikinsa
yau har da cin abinci da shigowa gida da k'afafunsa aiko lafiya ta samu,jinjina kai beauty tayi
had'e da tab'e baki ta kauda kanta gefe,tana rayawa azuciyarta"lallai baba baki san wanene shi
ba da har kike yabonsa mutum mugu azalumi wanda babu tausayin 'ya mace a zuciyarsa,da
har zai mun dukan ajali kusa!
Gafaranku dai masu gida,maganar d'an ladi kenan wacce ta dawo da beauty cikin hayyacinta ta
k'arasa shigowa da sauri ta nemi gefen gadon kusa da baba yagana ta zauna! Waige ta shigayi
ko ta samu abu ta rufe jikinta don zanin atanfar baba yagana ne d'aure a k'irjinta,sai alokacin ta
tuna da akwatin kayanta na motar sameer da suka zo basu fito da kayan su ba haka suka tafi
asibiti,bata an kara ba taji an yaye labule sama, cikin rawar jiki,ido na kyarma ta d'ago ido sama
me zata gani?d'an ladi rik'e da hannun sameer tsaye a bakin k'ofa!yarda ta matsar da kwayar
idonta akan d'an ladi sai gashi ta kasa sauke idonta daga kallon da suke mayarwa da juna ita
da sameer!ko wannen su da abinda zuciyarsa ke raya masa,cikin k'arfin hali da mazantaka
sameer yayi saurin sunkuyar da kansa gefe tare da jan hannun d'an ladi cikin zafin nama yace
fito nan waje musha iska mubarsu ciki!bai jirayi amsar d'an ladi ba sai ganinsa d'an ladi yayi an
finciko shi da k'arfin tsiya tsakar gida,inda farin wata ya haske su!
Duk kan abin nan daya faru akan idon baba yagana dake rik'e da kud'i a hannu ta tsaya da
k'idaya tun shigowarsu!juyowa tai sosai ta fuskanci beauty wacce ke zaune kanta a duk'e ta
zuba wa zanen ledar tsakar d'akin ido,wanda ita kanta bata san dalilin yin hakan ba taji baba ta
dafo kafad'arta! Da yake hankalinta ya d'an gushe zuwa tunani sai ya zamana a tsorace ya
d'ago kai ta kalli baba!murmushi mai cike da fassara baba ta saki sannan ta saukw ajiyar zuciya
ta kira sunanta!hajara! Beauty ta amsa kanta na k'asa!
Allah yasa ayi damu!
Me za'ayi daku baba?ido waje ta d'ago kai tana tambayar,jin baba tayi shiru tana dai 'yan
murmushin nan nasu na manya da suka san me duniya ke ciki!nan ta ci gaba da magana Allah
kuwa baba ki yara da n... bata iya sauke lumfashin ta ba baba ta tsayar da ita ta hanyar nuna ta
da yatsa tace kul hajara naji kince wani abu!ki tashi ki shirya ki sallah kawai shi ya fi miki ga
kuma tuwonki can rufe a tasa!daga haka baba yagana ta mik'e ta maida kud'inta ma'ajiyarsu
tayi waje abinta!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: í ½í³“ *'YAR JAMI'A*í ½í³“
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
101-105
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
Cikin sark'ak'iya tare da b'acin rai haka beauty ta mik'e ta shiga zagayen d'aki kai kawon da
take ne ba tare da samun wata mafita ba yasa ta tsagaitawa da zagayen nan ta shiga laluben
d'akin,a saman wata ghana most go taga sallaya tare da hijab ai kuwa cikin sauri ta janyota ta
zunbula har tana jan k'asa nufo k'ofa tayi da niyyar fita,amma ina tana kaiwa bakin k'ofa sai tai
turus ta tsaya jin sautin hirar da suke a tsakar gida shi ya bata raunin gwiwar fita,ta d'an jima
nan tsaye sai kuma can dabara ta fad'o mata labulen k'ofar ta janyo ta bud'e shi kad'an ta lek'a
kanta ta shiga magana da k'ara tana cewa"d'an ladi ka je mota ka duba jakata na ciki ka d'akko
min!
Hira suke sosai abinsu su sameer su kaji kamar daga sama ana magana!jimmn sameer ya d'an
yi kad'an kafin nan ya tuna ashe kayansu na mota!d'an ladi ne ya fara cewa murya k'asa"d'an
birni kaji wai jakar gimbiya na mota,murmushi sameer ya saki da jin kalmar gimbiya sai kuma
yace toh je ka d'akko mata!kallo ya watso masa yace ai kasan ban iya aiki da na'urar bud'e
mota ba!auff ashe fa haka ne muje toh,haka suka mik'e sameer na gaba yana biye dashi suka
fita ba'a wani jima ba sai gasu da kaya nik'i-nik'i sun shigo,mai makon jakar beauty ta kasance a
hannun d'an ladi sai gata a hannun sameer,yana k'ok'arin wucewa d'akin baba da k'aramar
jakar sameer don ya kai mata sameer ya tsaida shi yace a'a wannan fa malam tawa ce kai min
ita d'akin ka bara na mik'a mata tata!toh kawai d'an ladi yace ya wuce, shi ko sameer ya nufi
k'ofa, a bakin k'ofar shima dai ya tsaya amma bai kai ga d'aga labule ba,wanda har lokacin
beauty na tsaye wajen sai dai ta saki labulen ta jingina da bango ta ji sautin magana!
Tabbas mai hali baya tab'a canja halinsa,a gaskiya dai anyi asarar shekaru,girma ya
fad'i,wallahi ina mamakin kasancewarki tsatson wannan dangi na mutunci da girmamawa,sai
dai kuma ta wani fannin ba laifi bane don naga haka don ko 'YAR JAMI'A shahararriyar karuwa
ce!mai neman maza,wacce bata son kamun kanta ba,wacce take ikirarin kanta da beauty
ma'ana kyakykyawa ko?toh Allah dai ya raba mu da kyawun d'an miciji!ameen! Yana kaiwa nan
da maganarsa sameer ya wulla mata jakar ciki da k'arfi har ta kai ga buge k'afarta!amma ba
yadda ta iya dole ta toshe bakinta da rad'ad'd'in da k'afarta ta bayar lokaci d'aya!
Sameer ko daya wurga mata bai zame ko ina ba daga nan sai d'akin d'an ladi,itako beauty
abinka da wacce rai bai saba b'aci haka ba komai ace dady sai ya zamana sabon abu a
wajenta,haka ta daure ta ja k'afar da tuni dama ta gama tsami don dukan da ta sha da rana a
asibiti,ta k'arasa gefen akwatin ta bud'e wata doguwar rigar kalar ruwan toka(ash)dai ta k'ara
janyowa ta zura da yake duk dogayen rigunan ta kwaso don tasan halin tsoho sarai tun tana
yarinya ba'a shigo masa ita gida da k'ananan kaya!
Haka ta kammala shiryawarta tsaf tayi sallah sannan ta ci tuwo,Alhamdullah ta fad'a bayan ta
gama cin abincin, duk da ba wani cin kirki tayi masa ba!abinka da ba'a saba ci ba! Tana k'ok'arin
hayewa gado ne taji muryar baba yagana tana fad'in toh ina kuma kuke shirin fita haka,ko
wacce amsa suka bata sai ji tayi tace toh ku jira ku kai min kifin rijiyata yawo tun zuwanta ba
inda ta lek'a,
Kafin ta iya wani kwakwkwaran motsi ina har baba ta shigo,yi tayi kamar bata ji shigowarta ba ta
ci gaba da hayewa gado,ke meye haka kuma hajara?bacci tun yanzu?ai kuwa baki isa ba
tasowa zaki ku tafi,kai baba mu tafi kuma ina? Fuska sake baba yagana tace dandali mana kije
kisha kallo in da rabo sai ki sama wa d'an ladi mata daga nan ma! Don naga da alama ruwan
ido ya masa yawa!cuskune fuska beauty tayi kamar me shirin kuka tace dan Allah ni dai su je
kawai gajiyar hanya tayi min yawa gobe naje ni,had'e girar sama data k'asa baba yagana tayi ta
matso saitin kunnenta tace mata kaga ja'irara banza mara wayo,ki shigo da yaro santalele fari
sol wannan k'auyen ko kishinsa bakya yi ai ya ci ace duk motsinsa kuna tare,haka d'azu fa ina
kallo suka fito ko ki bi su,saurin katseta beauty tayi ta shiga bubbuga k'afa na shagwab'a tana
cewa ni wallhi baba yagana ki shiru don tsakaninmu ba dangin iya bana baba kawai had'in
ummah ne tace ya rako ni!
Janyo ta baba yagana tayi cikin fushi ta tsaya k'em a tsaye sannan tace toh yi maza zura
takalmin ki mu wuce,yadda taga baba tayi fuska ba annuri yasa ta tilas ta zuwa suka fito daga
d'akin a jere da juna!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: í ½í³“ *'YAR JAMI'A*í ½í³“
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
116-120
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
A daddafe beauty ke binsu da kallon mamaki, to shin me d'an ladi ya shirya musu haka?kallo
takai ga inda su d'an ladin suke nan taga sameer tsaye gefen dama sai wani matashi wanda da
alama shine d'an mai garin, a hankali ta k'arasa inda suke badon taso ba haka ta koma gefen
sameer ta tsaya don ta tabbatar ta tsaya d'ayan gefen sai ya mayar mata da magana!
Tun tsayuwarta a wajen wasa ya fara kad'e-kad'e da wak'e-wake ke tashi sosai,a inda ko wane
makad'i ke baje irin nashi basirar a salo na