Showing 18001 words to 21000 words out of 59972 words

Chapter 7 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf

Advertisement

08 Jul 2025

3239

cewa ke 'yata ce zai so kuyi kyakykyawar mu'amala ba mummuna ba"inda san
samu na ne har ki gama karatunki ba wanda zai san ki in ba 'yan ajinku ba"suma d'in se dan ya
zama dole amma yanxu ni naje nasaka a kori wani ai se a watsa a kafafan yad'a labarai wanda
hakan ba karamin zubar min dq k'ima ze yi ba"pls beauty dadynki na baki hak'uri da ki bar
maganar nan tunda kince kinyi nasara a jarabawarki watak'il abu kika mai ba dai-dai ba kawai
ki bashi hak'uri duk randa kuka had'u kuma ki fita a harkarsa,kinsan fa bana so ummanki ta

fahimci wani abu so nake ki bata mamaki duk da tana ganin bazaki iya karatun nan ba ki
taimaka mu bata mamaki"ki fita da flying colours se mu had'a wani gagarumin shagali"koya kika
ce beauty??fuska ba yabo ba fallasa beauty ke bin dady da kallo duk da hakan da ya fad'a sam
be yi mata ba toh ya ma za'ai kamar ita ace ba wanda zai santa sai mate d'inta ashe bata cika
*'yar jami'ar*ba,banda cincirun don malamai gogaggu da beauty ke harka da su"dariyan yak'e ta
sakar me tare da langwab'ar da kai a jikinsa ta lafe tace ok dady na ji ba komi zan fita a har
karsa amma kai ma de kasan bazan je na bashi hak'uri ba but believe me duk randa ya k'ara
shiga har kata Se ka d'au fansa daddy"
Dady promise me mana kayi shiru"
Sanin rigima irinta beauty dole dady ya amsa mata da yes"da haka ya kamo hannunta suna ta
hira abinsu duk da beauty ta gama k'udurta bin wata hanyar don ganin ta muxguna ma sameer
da haka suka sakko dinning inda ummah ta gama jera kayan abinci nan suka zauna don cin
dinner" Sosai beauty ke cin abincin don wata irin matsananciyar yunwa data wuni da ita nan ummah ta
samesu itama tai joining d'insu"bayan sun gama ne dady ya k'ara jan hannun beauty falo inda
sukai ta kallo suna hira ala dole dady naso ya ga ya kawar ma beauty da damuwarta"
K'arar horn na shigowan mota suka ji dady ne yace toh ga d'an albarkan nan ya dawo"
Hmmm kai da ka sanshi ba? ace yaro tun zuwanshi gidan nan ban tab'a saka shi a ido na ba"ko
tunanin yazo ya gaishe ni be yi ba?cewan momy tana kalon dady"beauty ko kamar jira take nan
ta soma"ai wallahi umma shiyasa ni tun farko nace ban yarda kowa yazo mana gidan nan ba
don duk basu da tarbiyya dady ya nace se yazo". Hannu dady ya kai ga bakinta yayi saurin tsayar da ita a magana yana cewa kai beauty na kin
manta ke kika ce min kin yarda yazo amma bakya son ganinsa a hara bar gidan nan"shine fa
nai masa iyaka da cikin gida dan kar yazo ya damar mun ke".
Dariya sosai kake gani d'auke saman fuskar beauty sorry dady kaga na manta,gaskiya dady na
k'ara tabbatar wa kana so na fiye da tunani na me too luv you dady"peck ta kai masa a kumatu'
nan suka hau dariya na jin dad'i abinsu nan-da-nan beauty ta shiga yi mai surutai kala-kala wani
abun ma duk shirme kamar ba wacce ta mallaki hankalin kanta ba" Mik'ewa ummah tai don takaicin yadda suka maida ita gefe guda suka watsar suna ta
hirarsu"duk abin duniya ya isheta ita ba abin tai kishi da 'yar cikinta ba'dole ta nufi sama abinta
ta bar su nan falo zaune"

Ba ita ta shiga d'aki ba beauty se wajen 12p.m haka watsa ruwa tare da haye wa gado"wayarta
ta janyo ta shiga laluben numbers na wasu daga cikin lectures din abokan harkarta"a inda duk
wanda takai ma batu na korar sameer daga aiki se a nuna mata gazawar hakan,wasu kuma su
nuna mata yiyuwar hakan amma indai har zata kai musu ziyara a wajen had'uwarsu"dole take
amsa musu da eh tunda bata da wani buri yanxu wanda ya wuce taga ta kori sameer daga
jami'a kafin shi yayi kamar yadda ya furta mata".

📓📓25 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*

💕





Yau take litinin wanda yayi dai-dai da dqwowar d'alibai daga hutun sati biyu da aka basu na
gama zangon karatu na farko (wato first semester),kowa ka ganshi cikin shirinsa tsaf na
komawa karatu wasu fuskoki na shek'i na samun nasarar jarabawar baya wasu kuma akasin
haka"
Zaune take a bakin wata theater rik'e da takadda a hannu"ta na yamutsa fuska xee-xee ta
d'ago kai ta dube ta".wai beauty lapiya naga duk kin wani had'a fuska?banxan kallo me cike da
jin zafin tambayar beauty ke kallonta dashi can kuma ta kai ajiyan lumfashi tana fad'in ai dama
ke baxa kiga komi ba" amma fa ki kalli time table d'in nan har da statistic bayan kinsan bana son
harkar calculation"ni wallahi duk naji karatun ya fita a kaina"baki xee-xee ta bud'e cike da
mamaki toh da har wani karatu ma beauty ke yi a haka?a xahiri kuwa tace haba beauty ke da
jami'a ke hannunki ai bake ba har ni xan so A1 ko ya kikace kawai first lecture d'in xamu shiga
da haka xamu gane wa xe d'auke mu in me xafin kai ne na bar ki dashi in kuwa ruwa-ruwa ne
ki watso min number d'insa"
Tabbas beauty na matuk'ar jin dad'in yadda xee-xee ke yawan yabonta haka'suna cikin haka
sqllama suka ji an sakar musu cikin wata siririyar murya"yi sukai uwa basu jiba haka aka k'ara
rangad'a sallamar cikin kasalanci xee-xee ta d'ago kai tana kallonta"matashiyar yarinya ce kana
ganinta kaga kamilar mace me cike da addini basai an gaya maka ba"don sanye take da atamfa
d'inkin riga da skirt ga doguwar hijab har k'asa"sannan k'afafun nan an suturcesu da safa"
Sannunku"matashiyar ta fad'a"
Yawwa meke faruwa kika xo saman kanmu kikai mana inuwa kamar wata ice?xee-xee kenan
tana magana tana wani taunar cingom"cikin halin ko in kula matashiyar ta saki wani k'aramin
ajiyan zuciya tace eh dama naga kamar kuma class d'inmu d'aya kuma naga yawanci duk ba'a
da time table shine nace bari na tambaye ku? D'agowa tai cikin sauri beauty daga jinginar da tai
da kujera ta d'ago kai a karo na farko tana dubanta"
Me kika ce?time me??time table?? Eyyee kaga director kai koma ince rector saboda ga
sa'anninki ko?duk fad'in makarantar nan baki ga maraina wayonki cikin sanyin safiyar nan ba se
mu ko?bakusan ku yak'in nema ba se an samu kuyi photo copy ki??toh ga time table d'in a
hannu na xo ki karb'a?cikin fad'a-fad'a beauty ke maganan tana gyada k'afa" Jin yadda beauty ke magana yasa matashiyar k'ara san yaya murya tace kiyi hak'uri ni ba
fad'a nazo yi ba"k'ok'arin juyawa ta shiga yi don barin wajen don tasan tsayuwarta kan iya haifar

da wani abun" wani dogon tsaki mtsssss... xee-xee ta saki a gurin tare da k'ara kare wa
matashiyar kallo ta baya"dubeta kucakar banxa ko an gaya mata nan tsangayace ko xauran
wa'axi da xata xumbulo mana hijabi luuuuuu....se kuma ta katse maganar sakamakon wata
muguwar dariya da taji ta kufcewa beauty"da sauri ta d'ago tana tambayar lpy de?se da tai
dariya me isarta beauty sannan ta waigota tana nuna ta da hannu cike da mamaki"
Dilla can kin ganki wai har kura ce xata cewa kare maye" ko kema ba hakan kike tahowa daga
gida ba ki shigo mana jami'a uwa matar malam se an xo abi lungu a canja"se kuma ta k'ara
tuntsurewa da dariya tana fad'in gaskiya duk ranar da na ganki cikin kayan zafin can dole na ja
ki miyi selfie" Yanda take dariya abin ya matuk'ar bawa xee-xee haushi"wannan ma ai cin fuska ne"cikin fushi
ta mik'e wqnda tuni beauty ta rik'o hannunta nan ta shiga bata hak'uri"zama ta koma tai fuska
ba yabo ba fallasa take fad'in ok komai ya wuce yanxu ina ki kai?
Yamutsa fuska beauty ta d'anyi kafin ta saki tace'gida xan wuce dama kinga abinda ya shigo
dani ta nuna time table"yanxu haka kuma xan fitq a school sede hanxari ba gudu ba yanxu ma
na koma gidan ummah ta hau jero min tambayoyin na dawo da wuri"kai duniya wannan wacce
irin uwace"?dafe kai beauty tai cike da damuwa kafin ta nisa tace any way daddy ai nasan be
fita ba tunda yanxu 9:00a.m be yiba barq nai sauri na koma na samu me karemin"xumbur
beauty ta mik'e had'e da sak'ale jakanta a wuya ta juyo ta kalli xee-xee tace kin gane xan wuce
se munyi waya"a haka suka rabu beauty ta shige mota ta fice a jamiar ta nufi gida!.






📓📓26 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*





Da isarta gida q haraba ta tadda motar daddy ali driver na wanke masa cike da murna ta k'ara
so ciki"falo ta dosa kai tsaye tana shirin bud'e labule ta ji an bud'e cikin hanzari ta ja da baya ta
tsaya"ummah ce ta fara fitowa rik'e da brief case"daddy na biye da ita"hajara lpy kika dawo gida
yanxu ko kin yi mantuwa ne?cewar ummah tana dubanta fuska had'e" dama tabbas tasan haka
xe faru beauty don haka tai saurin kai idonta ga daddy inda tai nare da su"gyaran murya daddy
ya saki tare da kamo hannun ummah kad'an ya ja da alamun ta sauke idon ta haka daga kallon
da take wurgar beauty dashi"burus ummah tai tambar bata ji shi ba inda ma ta sake jefo mata
tambayan"da ke fa nake kikai min shiru ko?? Ganin yadda ummah yanayinta ya sauya ya baiwa
beauty damar daurewa murya cike da sark'ewa tace emm..emm dama yau ba lecture se gobe

bayan munje ne monitor ya sanar"
Badan ummah ta yarda da xancen beauty ba amma dole yasa ta shareta lura da sauyawar
fuskar daddy".
"Beauty nah tafiya ce fa ta kamani yanxu haka,bayan fitar ki d'axu governor ya sanar dani wani
taro da zashi jarmany na harkar farfad'owar tattalin arxikin kasuwanci"ya kuma nemi dana
shirya muje tare yanxu haka jakata na mota xan wuce"
Yeennnnnnn.....kuka beauty ta saki tuni ta shiga buga k'afa tana wani langab'ar da kai da hannu
ta hau magana a shagwab'e"yanxu da bandawo ba haka dady xaka tafi ban sani ba"toh Allah
nima ka tsaya na had'o kayana mu tafi tare"yunk'urawa tayi da niyyar shiga ciki dady cikin sauri
har yana tuntub'e da labule ya biyo bayanta yana kiran sunanta" Ya ilahi"me xan gani haka?allahu qadirun ala man yasha'u"ita abin ma dariya ya baiwa ummah
yadda dady ke biye ma beauty uwa wani rak'umi da akala ganin da gaske sun haye sama sun
barta tsaye bakin k'ofa yasa ta dawowa ciki ta nemi kujera ta xauna tana fad'in kuyi ku gama
kwa iske ni nan"ba inda xan biku na tadda takaici"
Beauty kam bata zame ko ina ba se gaban wardrobe d'inta ta tsaya saurin rik'o hannunta
dady yayi inda ta fincike da k'arfinta tana murgud'e baki tace"ni allah kar ka ce min wani abu se
na bika baran zauna ni kad'ai se ummah a gida ba nasan ba fad'a ba wataran duka na
zatai"cike da tashin hankali dady a karo na biyo ya k'ara kai hannunshi ga beauty ya rik'ota" Murya can k'asa uwa me shirin kuka ta shiga bata baki"_beauty na ki yi hakuri ki banni na tafi ni
kad'ai kinsan fa wannan ba personal tafiya bane balle nace zani da ke kuma duka-duka fa
bazan wuce 1week ba,bqtun ummah kuma tun da naji maganar tafiyar nan na ja mata kunne
sosai akan kar ta takura min ke,kinji ko ki dai na damuwa indan wannan ne"da alamun yarda da
maganan daddy'beauty ta gyad'a kai tace are sure daddy kai mata fad'an?yes my daughter
believe me nai mata"yanxu de gaya min me kike so na baki kafin na wuce"abin ne ma ya samu
ga beauty washe baki tuni ta shiga yi nan ta fara zayyano buk'atunta wanda duk basu wuce
kayan sakawa ba"nan daddy ya lalo kud'i himili guda ya aje mata wanda ita kanta se da kud'in
ya firgitata don bata tab'a ganin dady ya bata kud'i masu yawa haka ba"wani wawan hugging ta
kaima daddy cike da jin daddy tana fad'in thank yuh my amaxing dady yanxu kam xance maka
safe journey"
Dariya sosai suke abinsu nan dai su kai sallama dady ya fito ya nufo falo nan ma dai jan kunne
sosai ya k'ara ma ummah kafin tarakashi har mota suyi sallama cikin alhini da nuna tsantsar
missing ma juna da haka sukai bankwana"ali driver ya tada mota se government house"




📓27 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*

Tsaye take bakin window tana lek'en dady har ya fice kafin ta maida wata nannauyar ajiyar
zuciya ta maido dubanta ga d'akin"gefen gado ta taka a hankali ta zauna tare da kai hannunta
ga ajiyar da dady yayi mata ta janyo su ta shiga k'irgasu"ta k'arashe lissafasu had'e da kwarma
wani uban ihu na farin ciki can kuma tai saurin toshe bakinta da hannu tana sak'awa arai"_kai
ashe fa dady baya nan nake sakin wannan shewar kar na jama kaina fad'a"a fili kuwa ta furta
N200,000 cab lallai yau akwai shiga mall bara na kira xee-xee"nan ta mik'a hannu a haka ta
xaro waya ta shiga lalubar number xee-xee"k'ara biyu wayan ta saki kafin daga bisani xee-xee
ta amsa wayan da fad'in kina wuta tawan"murmushi beauty ta fara saki sai kuma ta amsata
itqma da kema haka k'awas yanxu de ba lokacin hira bane ki shirya bayan sallar la'asqr xanxo
har gida na d'aukeki muje shopping dan haka se ki min text na address d'in gidanku" jimm
xee-xee ta fara yi a farko dan sarai ta san halin gidansu da yadda mahaifinta yake gashi da
xarar anyi sallar la'asar yake dawowa gida,in yazo yaga beauty a gidansu me xe ce don tana da
tabbacin da irin shigar da beauty xata xo gidan nasu"toh amma ai mama na nan kuma nasan
bazata hanani zuwa ba don haka ba damuwa"nan ta amsa wa beauty da toh se na ganki"sun
d'an tab'a hira ba wani sosai ba da haka sukai sallama"



_Yammacin ranar:_
4:15p.m

Tsaye take bakin k'ofar d'aki rik'e da jakar hannu,jikinta kuwa ta zumbula wani dogon hijabi har
k'asa"taji sallamar mama d'aki"wai har yanxu k'awar taki bata xo bane zainab?eh mama amma
na kira ta tace min ta kusa tana hanya"toh gara dai kuyi sauri dan kina ganin lokaci yanxu gyaji
sallamar mahaifinki" ya mutse fuska xee-xee tai tace wallahi mama nima abinda nake ta ji ma
tsoro kenan nasan yanxu yana xuwa fitar nan ta fasu"kuma ze iya wulak'anta min k'awa ko ya
koreta"saurin katseta mama tayi da inah yaushe xan bari haka ta faru ya korar miki k'awa ba ita
ce wacce kike ban labari 'yar babban mutum nan ba?eh mama ita ce"toh kinga ko in zaki huld'a
da 'ya'yan masu hannu da shuni a hankali mijin aurenki ma ta nan tsatson xe fito ke dai kawai ki
bar min komi a hannuna bari naje na k'arasa wasu ayyuka a can d'aki na" toh xee-xee ta amsa
da tai waje"
Zagayen d'aki kawai take tana duban agogo kamar daga sama taji k'arar horn na mota ai cikin
sauri-sauri gudu-gudu ta fito a d'akin ta nufi wajen mama ta shaida mata ta k'araso"nan mama
ta nuna mata tai sauri toh su wuce dai kafin baban nata ya dawo" da saurinta ta fito inda ta iske
motar beauty kafe bakin gate d'in gidan nasu nan ta nufota"
Zaune take beauty cikin mota cikin wasu arnan kaya riga da skirt sai wata k'aramar hula data
sak'ale kanta dashi"idannunta kafe a gidansu xee-xee nan ta shiga xancen xuci'gaskia ba laifi
gidan yayi duk da dai unguwar lunguna sunyi mata yawa ga hayaniyar jama'a amma ade xaman
gidan k'aramun ma'aikacin kwamnati ba laifi yayi k'ok'ari"tana cikin tunani taji an bud'e mota an
shigo se a lokacin hankalinta ya dawo jikinta ta maida dubanta ga k'ofan"me zata gani?xee-xee
murk'ushe cikin k'aton hijabi har k'asa" ai beauty bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba ta
nuna ta da yatsa tana fad'in me xan gani haka xee-xee kode kema kin koma matar malam

ne?"cikin wasa xee-xee ta watso mata harara tana ci gaba da k'ok'arin yaye hijabin jikinta da
yake motar me duhu ce tana fad'in banda lokacin ki ni dai yanxu yi sauri mu fita a layin nan
koma meye kya tsokane ni dashi"batabar dariyar ba dai haka ta kunna motar tahau tuk'i'dai-dai
kwanar hawa babban titi suka ci karo da baba cikin motarsa honda 307 yana k'okarin karyo
kwana"
Na shiga uku"xee'xee ta fad'a tana b'oye kanta k'asa"me ya faru ne?ko kin manta na waje baya
ganin na ciki?beauty ke tambayarta"se alokacin ma xee-xee ta tuna da hakan nan dai ta d'ago
kai ala dole ta sha mur don kar beauty ta tsokaneta"tace ai na sani kawai de tsohon nan ne se a
slow yanxu haka se kiji yace jikinsa ya basa ina cikin motar nan"na rasa me yasa sam ya kasa
yarda dani"kome nawa se yasamin ido,ko shi haka akai masa da yana saurayi oho?itade dariya
kawai beauty take har sukai nisa da unguwar sannan ta iya cewa dama dady ya auri mamanki
se umma mu had'ata da baba suje suyi ta wa'axinsu mu kuma muna jin dad'in rayuwarmu koya
kikace k'awas?dariya itama xee-xee ta saka tace ehh wallahi da mun huta da b'acin ransu
duka"se de nasan baba ko ana muzuru ana shaho baxe saki mama ba kamar wanda akai wa
asirin natau da ita"ke nima fa haka umma ke nanik'ewa dady na ko de su ustaxannan shigewa
mutum suke? Xee-xee ta amsata da oho musu su suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login