Showing 57001 words to 59972 words out of 59972 words
Chapter 20 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf
akace amarya ta sha k'amshi,muryar data
doki kunnenta yasa ta saurin juyawa don tabbatar da zargin da zuciyarta ke yi mata,nan tayi
tozali da zee-zee dake tsaye cikin ankon da ita kanta bata san dashi ba don ta lura kusan kowa
yayi ankon,a d'an rikice ta kira sunanta tana nunata da yatsa,cike da jin dad'i zee-zee ta matso
tace mata juya bayan dinner mayi magana,haka beauty ta juya sameer ya k'ara manna
hannayensu suka nufi ciki!
Sabon kid'a aka saki inda jama'a kowa ya mik'e don tarbar ango da amarya a nutsu suka nufi
ciki k'awaye da abokai na take musu baya har suka k'arasa mazauninsu daga nan ne kuma
shagalin biki ya fara a yanayinda kake iya hango abokan ango da danginsa suna zubar kud'i
sam babu k'anshin tausayin naira tare da su,haka daga b'angaren dady da ummah kowa ya
baje kwanintarsu ga 'ya d'aya tilo da suka mallaka a duniya,taro yayi taro can ummah ta hango
dady na kwaso shoki na kud'i yana sauke wa a goshin 'yar tashi,dariya kawai ta saki cike da jin
dad'i don in da sabo ummah ta saba da halin mutanen nata biyu,jama'ar waje kowa ya gani
dariya yake,haka shagali ya ci gaba har kusan 11:na dare inda daga haka jama'a suka shiga
watsewa,shima ango ya rik'o amaryarsa suka shiga mota zee-zee na biye da su!hira akai tayi
cikin motar ana maida zancem dinner haka har suka k'araso gida nan ne zee-zee tai sallama da
ameenu itama dai haka sukai sallama da sameer har ta juya zata tafi ya kira sunanta murya a
k'ank'ance yace pls kar ki late bacci nake ji" a kunyace beauty ta shige gida da gudu zee-zee ta
bi bayanta,a tare suka saki wata irin dariya sameer da ameenu ganin abinda ya faru da haka
suka shige mota suka fita a gidan!
[10:26am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: í ½í³“ *'YAR JAMI'A*í ½í³“
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
191-195
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
Tun bayan shigar beauty gida basu zame ko ina ba sai d'akin da aka ware mata inda ta
shigar da zee-zee ta kuma kullo k'ofar,saman kujera suka zauna beauty duk ta gama d'okin ta ji
labarin,sai kuma ta ji zee-zee tayi shiru tab'o ta tayi da hannu tace wai ke dilla ki fara bani
labarin mana,murmushi zee-zee ta saki sannan ta gyara zamanta sosai tace,toj sarkin son
labari bud'e kunnenki kiji da farko dai kamar yadda na labarta miki a waya nayi sabon saurayi
mai kayan harka,toh wannan yaron kusan shine silar duk wani abu daya faru domin kuwa bayan
sati da had'uwarmu ya min kyautar mota ta azo a gani dole na je inda nake aje waccan
tsohuwar motar wacce nace miki itama bani akai amma ba wanda ya sani a gida bayan
mama,na had'a su biyu yau na hau wannan gobe na hau waccan,fantamawa kawai abuna nake
har ta kai a unguwa kowa yasan da sake mota ta,ana haka kwatsam na dawo daga jami'a wata
rana ina shiga ma'ajiyar motar kwatsam muka ci karo da baba wanda nasan ba makawa ni yake
zaman jira,ranar nan k'arshen danasani sai da nayi ta,don dukan da nasha ranar kamar bazanyi
rai ba ga horo mai tsanani na ya cireni daga jami'a babu inda nake zuwa kullum ina gida
zaune,na tak'aice miki labari mai kai bolar gidan mu wato almajirin layi ya fini daraja a gidan
nan,ba anan abin ya tsaya ba har mama sai da ya shafa gida baba ya turata a karo na farko
azamantakewarsu halin yanxu dai bai jima da dawo da ita ba,maganar bikinki kuma lamba na
gani an kira ni a waya koda naji namiji ne da kamar bazan magana ba saboda 'yar jami'a na
wahala....kul kar ki sake ce min 'yar jami'a kirani da sunana hajara,beauty ta katseta!dariya
zee-zee ta saki tace shegiyar gari wato kin ji jiki ai na samu labarin komai ke dai bari na gama
miki,haka taci gaba da cewa bayan na amsa wayar ne ya labarta min komai cewa shi abokim
sameer ne wanda zai aure ki kuma yana da buk'atar mu had'u da yake hajara na shiryu sam
banji nauyin b'oye masa komai nawaba don kar yaga na hana sa gamuwa dani yayi zaton ko
wulak'anci ne bayan ya gama ji ne yace ma bashi lambar baba,duk da ina gudun yim wani laifin
amma daya matsa dole na bashi,da haka mukai sallama!
tun lokacin ban sake jin shiba sai lahadin data wuce ina zaune tsakar gida ina wankin kayan
yara naji shigowar baba kallo d'aya yayi min ya kauda kai sai ji nayi yace kiji waje da bak'o
zakuyi magana,wani rass gaba ya fad'i sanin cewa bazai wuce cikin abokan baba yake son
had'ani da wani don ya zama horo a gareni ashe abin ba haka bane sai dana fita muka gaisa
naga saurayine kuma ba laifi kallo d'aya na yaba dashi amma dana ji shine ameenu da mukai
waya a baya sai na saki jiki mukai magana ya kuam shaida min da baba ya amince kuma akan
gobe litinin tare zamu taho anan abuja na yi wasu shirye-shiryen biki,da yake had'uwar farko ce
sai na kasa sakewa dashi sai da muna kan hanya zuwa nan yake shaida min cewa ya nemi
aure nane a wajen baba duk da bai ganni ba amma ya yarda da nadamar da yaji daga
gareni,tuni na shiga godiya ga mahalicci na hajara na k'ara yadda cewa Allah na tare da mai
tuba yayin laifi,toh tun daga haka kawo yanzu wani son shi nake ji har bana son naji bana tare
dashi,ai kin gane,k'arashe maganar zee-zee tayi tana kashe mata ido na wasa haka suka
wkashe da dariya a tare,suna haka suka ji ana bugun k'ofa beauty ce tace waye?can suka ji
muryar yarinya tace wai aunty hajara ke zo d'akin sama ana nemanki!toh kawai beauty ta amsa
da sannan ta mik'e tace ina zuwa da haka ta nufi hanyar fita!
D'aki ne cike da iyaye mata hira sosai suke yi haka beauty tayi sallama ta shiga can
tsakiyarsu ta hango ummah don haka ta nufe ta,ummah gani ta fad'a kanta a k'asa,kafin ummah
tayi magana Aunty balaraba tace tashi ki shiga bayi gani nan zuwa"toh kawai tace nan ta mik'e
ta nufi bayi,waje ta samu a ciki ta tsaya tana 'yan dube-dubenta ciki taji shigowar aunty,wankan
magarya tare dana turaren mata aunty tayi mata duk wan sak'o da lungu na jikin beauty sai data
tabbatar data wanke shi tas sannan ya samh turare, bayan sun gama ta rik'o hannunta suka fito
wani k'aramin labule da ke sak'ale a d'akin suka nufa suka shige ba wani abu cikin banda kayan
mata da turaruka ga wata drawer can ta kaya nan ta ciro mata kayan da ummah ta tanada mata
lace ne dark blue tasaka sannan ta d'aura mata alkebba d'inta bak'i a sama,k'arshen kyau
beauty tayi shi ita kanta dubin kanta amadubi ta hau yi,sai data gama shirya caf bayan kayan
shaye-shayen data bata,kafin nan suka fito,gud'a tsofaffin gurin suka hau yi ummah dake zaune
tabi 'yar tata da kallo don sosai tayi kyau tankar ba ita ba,tasan cewa tabbas yanda taso ta
aurar da 'yarta hakan ya kasance, tsakiyar d'akin aunty balaraba ta zaunar da ita sannan ta
samu waje itama ta zauna,nasiha da fad'a haka mutanen nan suka shiga yi mata tun tana iya
jure hawayenta har suka fi k'arfinta,suna haka suka ji alamar bud'e k'ofa wanda hakan ya
tabbatar musu cewa dady ne ya dawo tare da mijin aunty balaraba,kuka ne ya k'ara ciyo beauty
sanincewa dady ne da kansa yace zai kai ta d'akinta,mik'ewa tayi da gudunta ta fad'a jikin
ummah ta shiga rero wani sabon kukan,tsintar kansu sukai daga ita har ummah cikin kuka,can
aunty taga wannan kukan nasu ba mai k'arewa bane dole ta rabo beauty da ummah tayo waje
da ita,a bakin motar dady beauty ta iske zee-zee na ta kukan rabuwa da k'awar tata nan itama
ta k'ara kecewa da wani kukan dady dake gaban mota zaune tuni ya fara matsar kwalla jin rurin
kukar 'yar tasa,da haka tana kuka tana ihu aka sata mota suka tafi!
A tsadadden gidanta wanda a hak'ik'anin gaskiya sameer yayi k'ok'ari matuk'a wajen tsara shi
dady ya kai beauty har d'akinta sai dai sam ya kasa ko kwakwkwaran magana sai kuka da suka
d'unguma sunayi rarrashin duniya mijin aunty yayi amma ina sam sun k'i ji dole ya kamo hannj
dady tare da rufo mata k'ofa suka fito! Sameer dake sashensa zaune shin da ameenu da jin k'ugin tashin motar su dady wani tsalle ya
doka yana fad'in yes ta shigo gidana!tuni ya soma sauri yana shiryawa,wanka yayo har da d'oro
alwalarsa sannan ya fito shadda brown colour ya saka ya feshe jikinsa da turare sannan ya
d'ago kai yace da ameenu ya ka gani?jinjina da hannu ameenu yayi masa sannan yace gaskiya
mutumin ba k'arya yau zaka koya wa 'yar jami'a hankali,wani mugun kallo sameer ya watso
masa,take ameenu ya saki dariya yace sorry aboki mantawa nayi princess,mik'ewa tsaye yayi
daga zaman daya ke yace to ni dai baru na wuce tunda an kawo mana ita but pls kabi ta a
hankali kasan ita fa yarinya ce kar la sauke mata nauyi,wani wawan duka sameer ya buga
masa a baya har yana duk'adda da baya ameenu yana dariyar mugunta yayi waje yana fad'in
sai mun had'u gobe, bai amsa shi ba sameer sai ma wata nannauyar ajiyar xuciya daya sauke
ya k'ara duban kansa a madubi sosai sannan ya fito ya nufi sashen beauty!
[10:26am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: í ½í³“ *'YAR JAMI'A*í ½í³“
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
*THE END*
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
Ko da ya isa bakin k'ofa sameer turowa yayi ya shiga inda ya sameta can zaune tsakiyar
gado ta had'a kai da gwiwa da alamun kuka take,sallama yayi sannan ya k'arasa ciki saman
gadon ya nufi a hankali ya shiga yaye mata alkebbar daga fuskanta,d'ago fuskanta yayi cike da
tausayi ga kuma wani sonta da yake fizgarsa a halin yanxu ya shiga share mata hawaye yana
manna ta a jikinshi,sai da ya tabbatar tayi shiru sannan ya d'ago fuskarta ya sakar mata
murmushi,a daddafe itama ta mayar masa sannan yace my princess yau bani da sauran
magana tunda Allah ya mallaka min ke don haka tashi muje mu fara gabatar da sunnah sai mu
dawo nan,ba musu ya rik'o hannunta suka tashi bayi ya shigar da ita tayo alwala sannan suka
gabatar da sallah,gaban kanta ya kama kamar yadda yake yayi mata addu'a sannan ya mik'e ya
fita bai jima ba sai gashi ya dawo rik'e da tray na kayan tab'a wa a baki,ba wani sosai ta ci ba
haka ya d'auke kayan yana mai ce mata ki shirin bacci bara na kai kayan waje,yana fad'in haka
ya fice!
Tashi tayi beauty ta shiga cire kayan jikinta zuwa na barci kamar yadda aunty ta nuna mata
night gown d'in da zata saka wata light pink iyakar gwiwa haka ta janyota ta saka hannu ta saka
tana d'an janyo rigar k'asa amma ina tak'i sauka,beauty take taji duk kunya ta gama kamata can
kuma ta tuna da wani abu da sauri ta nufi wata k'aramar jakarta dake nan ta fiddo wani k'ulli
neman ruwa tayi ta rasa nan ta bud'e k'aramin fridge da ke d'akin ta janyo ta zuba a cup,k'ullin
maganin da baba yagana ta bata ne ta tuna don haka ta d'akko ta kad'a a cikin ruwan ta
shanye,haka kuma cikin sauri ta maida ta ajiye ta nufi gado,bargon dake linke a saman gadon
ta shiga yaye shi kwanciya tayi ta rufa ruf har kanta!
Tana kwance har bacci ya d'an fara fizgarta taji alamun bud'e k'ofa shigowa sameer yayi amma
ganin har ta kwanta yasa shi laluben madannin wutar ya rage hasken d'akin, kafin ya wuce can
d'ayan gefen gadon ya kwanta,koda ya kwanta sunanta ya kira amma da mamaki yaji shiru,jim
ya d'anyi sanin cewa ba bacci take ba yasa shi murginawa a hankali har inda yake,hannu ya kai
ya sak'alo bayanta dashi take ya sauke ajiyar zuciya"jin har lokacin babu alamar zata motsa
yasa ya maida hannunsa saman kanta,hular dake sanye akanta ya zame take ya hau shafar
suman kanta a hankali uwa mai neman wani abu aciki!
Yadda yake wasa da gashin kanta sosai take jin tsigar jikinta tayi yarr ta tashi,saurin kai
hannunta tayi saman nashi tajanye,ya sameer ka bannj ni bacci zanyi,haka ta fad'a tana
maganar uwa wacce ta fara bacci,k'ara matsowa sameer yayi sosai har yana iya jiyo saukar
lumfashinta haka ya kara bakinsa saitin kunnenta ya fara magana yana ci gaba da shafar
gashin nata,my princess bazan hanaki bacci na kinji amma yana da kyau ki min abinda zanyi
marking dix night as my best night ever kinji,na son kina so na kuma zaki iya sadaukar da komai
naki domin ni pls baby ki bari ko tab'a jikin ki nayi na samu relief,kin ji?em em ni ka rabu dani ya
sameer bacci zanyi?beauty ta fad'a har lokacin tana k'ok'arin raba jikinta da nashi amma ta
gaza hakan,can ya nisa yace ok naji but atleast tell me something pls,nan ya matso da kunensa
saitin bakinta yace all ears dear?duk a takure beauty take jinta yadda ya ke shige mata se take
jin duk ba dad'i haka ta rad'a masa in na fad'a zaka sake ni nayi bacci na? Da sauri ya bata
amsa da yes dear had'e da ci gaba da shafan kanta!
Da jin haka a hanakali beauty ta shiga juya harshenta tana fad'in:
_To night i feel so happy,i feel that i have not reached any where in my lyf,i have not made my
goals,my dreams,i feel that i was just born again,that i have to start over,and it makes me a little
scared bcox i have never comes across such moment in my lyf till now,and i have never thought
i would feel this way;you have showed me all over wit ur luv and carez thanks yuh so so much
my prince!_
Wani wawan hugging sameer ya kai mata yayinda ya k'ara manne jikinta da nashi sosai yana
fad'in
_My angel u must be a fantastic runner bcox now u are always running in my mind before i neva
thought sameer will fall this way but now i do so for dat pls permit me 2 know more of u!_
Yanayin da sameer ke maganar kad'ai ya wadatar ya gama kashe wa beauty jiki take ya fara
aika mata wasu irin zafafan sak'onni tun tana kauda kai tana janye jikinshi daga nata har ya kai
ta fara karb'a tana maida martani,take jikin sameer ya hau kyarma yamda yake jin beautu sosai
tare da shi,labari ya soma canja wa laluben jikinta ta ko ina yake har ya cimma burinsa,kuka da
ihu babu irin wanda beauty batai tun kana iya juyo sautin kukanta har muryar ta ya dishe dan
azaba sosai sameer ya shigeta,haka daren sababbin amaren biyu ya zama cike da jin dad'i!
Bayan da sameer ya dawo daga sallar asuba ne ya shigo d'akin wanda har lokacin beauty
kwance tale tana maida baccin wahala,gabanta sameer ya je ya zauna tare da yaye bargon da
take rufe da shi can kuma wata zuciyar ta shiga raya masa abinda ya wakana daren jiya k'arar
kukan beauty kawai yale tinowa yana dariya summ haka ya rungumota jikin nan nata gaba
d'aya ya gama d'aukar zafi ya shiga fad'in thanks yuh so much my princess u make me feel
morethan my expectation!k'ara matseta yayi gam jikinsa kamar wacce za'a kwace masa ya
fad'a da k'arfi;wallahi alhaji beauty tayi ba kad'an ba ni da ita kuma mutu ka raba!k'ara k'are
mata kallo yayi kafin yakai mata hot kiss a baki yace i luv yuh *'YAR JAMI'A* bayan nan ne
kuma ya tashe ta domain sallah wanda haka rayuwarsu ta ci gaba cikin so da girmama juna!
*TAMMAT BI HAMDULLAH!*
```Godiya ta tabbata ga ubangijin halitta daya bani ikon kammala wannan littafi nawa na 'yar
jami'a wanda ya zamanto k'irk'orarren labari,sannan ya zaman sadaukarwa ga masoyana biyu
wato ANEESAH ABUBAKAR RIMI TARE DA UMMIE ADNAN! Na k'addamar da wannan littafi
domin ya zama darasi ga 'yan uwa mata sannan ya zama hujja abin duba ga iyayen wannan
zamani,fata na dai har kullum Allah yasa in an karanta ayi anfani da sak'on dake ciki ameen ya
rabb!```
```Kunfi kowa bibiyar littafin nan;
Asma'u maman yasmeen
Fiddausi rabiu
Innah
Maman sadiya
Salaha fallata
Da wanda ban samu damar fad'a ba!```
```JINJINA DA GODIYA GA DUKKAN GRPS DA NAKE CIKI:
â—†NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
â—†EXCELLENT HAUSA WRITERS
â—†HAUSA ONLINE WRITERS GRP
â—†WRITERS PLANET
â—†HERWERH JIDDERH FANS
â—†DANDALIN FEEDOO-DEEDO
â—†HAUSA NOVEL GRP2
â—†HAUSA NOVELLA HOUSE
â—†.MUSAN JUNA GRP
â—†.MATAN KWARAI GRP
â—†DANDALIN SADY JEGAL AND MUM FATY
â—†FUTHA LURV GRP
â—†HUMMY BEE GRP
â—†AYSHA GANA GRP
â—†PBENA GRP
WANDA BASU JI SUNAN NASU BA SUYI WA HERWWERH JIDDERH UZURI JAMA'AR NE
DA YAWA!!```
TAKU HAR KULLUM
HERWWERH JIDDERH
A.K.A
PRINCESS'QUE~DEE!