Showing 51001 words to 54000 words out of 59972 words

Chapter 18 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf

Advertisement

08 Jul 2025

3231

A hak'ik'a njn gaskiya
sameer na lura da rashin amincewarka da wannan abin alkhairi da nayi,tunda duk cikinmu ba
yara balle su kasa gane halinda kake ciki,amma kasani banyi haka don na muzguna ma
rayuwarka ba a'a sai dan na inganta ta,duk da nasan halayyarka da hajara ba d'aya bace sai
dai kuma kai kad'aine zak iya zama da hajara a halin da ake ciki,don kuwa in har zaka iya rik'e
sirrinta toh mene kuwa baza ka iya jura nata ba"ka d'auka wannan aure da aka had'a cigabane
na rayuwarku baki d'aya kuma in har kayi hak'uri nan gaba zaka ji dad'in abin!
Shiru dai sameer yake,kai k'asa yana jinsa don haka ya ci gaba"sameer a yanzu ne ake auren
soyayya mu da mukai namu ina muka san wata aba soyayya ai sai wacce iyaye suka zab'a
maka amma kai fa har halayyarta ka sani kuma nasan duk wani abu nata ba wanda baka sani
ba ciki da bai,sai dai bazan tauye maka hak'k'in ka ba sameer kai ma d'ana ne yanzu kamar
yadda hajara take 'ya a wajena,gaya min meke saka kuka da har damuwa takai ka ga zazzab'i
don daga jin jikin nan naka ba lafiya!
Mai makon sameer ya bashi amsar tambayarsa sai hawaye da suka fara bin kuncinsa,nan
Alhaji yayi juyin duniyar nan amma sameer ya k'i magana har sai da yaji yace bari ya kira masa
mahaifinsa ko shi zai iya gaya masa sannan yayi k'arfin hali murya can ciki yace Alhaji ni fa ina
zargin hajara kuma kaga aure ai bazai yiyu da zargi ba?cike da mamaki Alhaji ya ke duban
sameer had'e da nanata kalmar zargi a cikin ransa, dayake Alhaji bana yau bane kuma yasan
halin da duniya ke ciki nan ya kamo hannun sameer yace,hakane maganarka d'ana aure baya
yiyiwa da zargi amma ina rok'onka wata alfarma,nan sameer yace wace irin alfarma kuma
alhaji?gyara zamansa yayi yace ina neman alfarmar ka tare da hajara a gidan nan kuma yau
d'in nan idan har ka sameta yadda kake so toh shike nan idan kuma ka samu aka sin haka
wanda bana fata toh ni zan baka alk'ami da takadda ka rubuta mata saki uku kwarara"d'ago kai
sameer yayi yana kallon Alhaji yadda yake maganar da sigar gaskiya ainun!shiru yayi kafin nan
ya gyad'a masa kao da niyyar amincewa sannan ya k'aro wani k'orafin yace"a aure na na ci
burin yin shagali na gani na fad'a gashi hakan bai yiyu ba!nan ma dai murmushi Alhaji ya sakar
masa sannan ya kuma ce waya gaya maka burinka bazai cika ba? Ai tun shekaran jiya dady ya
dawo garin nan kuma na labarta masa komai ta wayar mai gari,kuma ni na umarceshi da karya
sanar da hajara har sai ta dawo gida ta ganshi,yanzu haka maganar da akeyi yana can ya
tarasu ita da mahaifiyarta ni yake jira mu sanar da hajara halin da ake ciki!da zarar ta sani zuwa
dare dadynta da mahaifinka sun had'a k'ayatacciyar walima ko dinna ko me?a wani k'aton waje
kuma duk sun gama gayyatar duk wasu wanda ya kamata a halarta kaga bayan daren yau duk
shawarar daka yanke,inda yiyuwar ka tsara naka walmar daga baya kun tsara kai da
matarka!yanzu dai bara naje can naga yadda zamu kasance!yana kaiwa nan ya tashi yayi waje

ya bar sameer da wani sabon tunanin!
[10:25am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

166-170



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Beauty dake zaune gefen dady ta d'aura hanneyenta saman cinyarsa yana matsa mata su a
hankali sai ummah dake gefe guda saman kujera inda ta bisu da kallo da haka suka ji sallamar
Alhaji,k'ara so wa yayi ya samu waje shima ya zauna,wanda hakan ya dawo da beauty cikin
hankalinta,take ta janye jikinta ana dady tanutsu sosai kamar ba ita ba,k'ara gaisawa Alhaji yayi
da ummah sannan ya kalli dady yace masa toh Alhaji ai ina ganin sai ka sanar da ita komai
ko!wasu k'anana muzurai da ido dady ya somayo alamun Alhaji yayi magana kawai shi basai
yayi ba,don haka ya d'ora daga inda ya tsaya"hajara"Alhaji ya kira sunanta,cikin sanyayyar
murya beauty ta amsashi tana sauke kai k'asa,Alhaji ya soma magana,wannan zama da mukayi
anan ko kuma ince wannan taro da kike ganin ana ta yin shi tun daga can k'auye har kawo nan
ba ana yi don kowa bane sai don ke"cike da mamaki beauty ta d'ago suka had'a ido da dady
nan take dady ya kauda kai gefe,wanda hakan ya baiwa Alhaji damar cigaba a magana ina so
ki saurare ni da kunnen basira kiji me zan gaya miki,a matsayinmu na iyayenki wanda suka gi
cancanta da mu gina miki rayuwarki kuma mu zab'a miki mijin aure don haka yau mun sauke
hak'k'inmu akanki mun had'a ki aure da d'an uwanki sameer !firgigit beauty tayi take kuwa ta
mik'e tsaye cikin d'imauta tabi Alhaji da kallo idanunnan sun gama cika da hawaye amma sun
kasa samun muhallin zuba k'asa,dumm...taji kanta yayi mata ta yadda take ganin abin uwa
mafarki,lokaci d'aya kuma ta saki wata irin k'ara ta shiga shure-shuren k'afa uwa zararriya,dady
ne ya yunk'ura zai yo kanta Alhaji yayo saurin tsaidashi da hannu badon ya so ba haka dady ya
tsaya shima tuni hawaye ya gama cika idanunsa na tausayin 'yar tasa,wata irin gigitacciyar

tsawa Alhaji ya watso mata take ta shiga hankalintabta tsaida shurin k'afar amma ta kasa dai na
wayayen don tasan basu tab'a wasa irin haka da Alhaji ba,abinda ya faru tun daga had'uwarsu
da sameer,zuwanta k'auye,kai kawo yai da zasu bar garin minjibir babu wanda ya k'ace mata a
tunani,yadda baba yagana ta gaya mata nad'in sarautar Alhaji ashe duk ba haka bane,kukan da
ya sameer yake yasan da aure na dashi ne?toh waye ya k'ulla abin nan,sameer?Alhaji ko kuwa
tsoho?tunani sosai beauty ta duk'ufa yi ganin ba mafita yasa ta sulale wa kasan kafe ta shiga
maida ajiyar zuciya mai cike da kukan zuci,ba ummah ba hatta shi kan shi alhaji sai daya
tausaya wa halinda take ciki mazantaka kawai ya nuna don yasan aikin gama ya riga ya gama,a
karo na biyu ya k'ara kiran sunanta,shiru ta bishi dashi,don haka sai bai damu ba ya ci gaba da
magana cikin fad'a"aure d'aurashi yau akan sadaki dubu d'ari,wanda tuni na damk'asu ga
mahaifinki,sannan ki zauna da shirin biyayyar aure ba hauka ko wauta ba,in kuwa naji wani abi
sab'anin zaman lafiya, zan wanko k'afa har muhallinki na baki mamaki,kin dai san ni
sarai?sannan daren yau ki shirya za'a yi walimar biki akai ki d'akinki!

Ko da Alhaji yazo nan a maganar shi sai ji tayi beauty ta kasa d'aukar girman maganar,ace
yadda zamantakewa tasu take da sameer yau ita za'a kai d'akinsa?ai tuni ta mik'e wiwi ta shiga
kuka tana buge-buge surutai barka tai marasa kan gado,sosai beauty take sharar kukanta kowa
ya ganta a halin da take ciki dole ya tausaya mata,kasa jure hakan dady yayi da saurinsa ya
k'arasa gabanta bai bi ta kan Alhaji ba tsum ya rungumota ta fad'a jikinsa ta shiga rero wani
sabon kukan,kasa danne zuciyarsa shima dady yayi kafin kace me sun had'a kai da juna suna
kuka,
Sororo Alhaji yayi yana kallon abin mamaki,takaici duk ya gama cika shi na yadda dady ya
gama sangarta beauty,wani dogon tsaki ya saki tare da fad'in toh Allah dai ya kyauta,da haka ya
nufi hanyar fita yayi b'angaren bak'i inda aka tanadar wa mahaifan sameer!

Bayan fitar Alhaji ne kuma ummah ta mik'e jiki ba kwari ta nufi wajen da su dady ke tsaye
rungume da juna,hannun beauty ta rik'o a hankali ta d'ago kai tana kallonta,janye ta ta shiga yi
daga jikin dady nan tayi hanyar d'akinta da ita amma har lokacin hawaye bai bar zuba a idon
beauty ba" K'ofar d'akinta ta bud'e tare suka shiga ciki, ta nufi bakin gado ta zaunar da beauty k'aramar
kujera dake sak'ale gefen gado ummah ta janyo ta jinginata gaban gado ta zauna suna kallon
juna!
Sunanta ummah ta kira,cikin kuka beauty ta amsata"nan kuma ummah ta fara magana"ya
kamata ace kin tsaya da kukan nan hajara don bazai anfanar dake komai ba,tunda Alhaji ya
zartar da hukunci,duk da d'an uwana ne amma a zahirin gaskiya ban ji dad'in sigar da yabi ya
sanar dake wannan al'amari ba,sai dai ki sani hajara mu iyayenki muna sonki kuma baza mu
tab'a aurar dake ga mutumin banza ba!amma abu d'aya da na lura dashi daga ke har sameer
d'ib babu mai farin ciki da wannan abu,kamar yadda na lura da ranar tafiyarku minjibir karo na
farko da kuka had'u a tsakar gida razanar da ki kayi bayan kin ganshi ce ta tqbbatar min da kun
san juna a baya,don haka hajara ina miki magana a matsayina na mahaifiya agareki da ki ji
tsoron mahaliccinki ki sanar dani shin meke tsakaninki da mijinki sameer??!!.
[10:25am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

171-175



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Meke tsakina da mijina sameer kuma?yanzu shike nan kowa kallon matar sameer zai na yi
min?zancen zucin da ya k'are zagayensa cikin zuciyar beauty kenan,jin kuma ummah ta tab'ota
da hannu yasa ta dawowa daga matsakaicin tunanin data shiga,hawaye na bin kuncinta haka
beauty ta shiga zayyano wa ummah duk abinda ya faru bata b'oye mata komai ba kama daga
kana principal d'insu har zuwanta k'auye'salati da sallallami ummah ta shigayi bayan da beauty
ta gama bata labarin cike da mamakin yadda d'iyar cikin jal a duniya wannan abu ya faru da
ita,abinda take ji a gari yau gashi a gidanta,ganin hakan bazai anfana mata da komai ba yasa ta
share mak'alallen hawayen dake manne idonta ta d'ago kai tana duban beauty kafin daga bisa
ni ta ci gaba da magana"hak'ik'a hajara na so tarbiyyarki ta k'arfafu fiye da yadda kike zato,na
so na baki soyayyar da ke kanki sai kinyi alfahari dani nan gaba,amma ina kaddara ta riga
fata,mahaifinki ya d'auki son duniya ya d'aura miki inda har ya cusa miki wasu d'abi'u da har
kike ganin tamkar na tsaneki,baya son ganin laifinki akan komai,yanzu wa gari ya waya?ke
kuka shi kuka,don ma Allah ya taimake mu raya sunna zaki ba wani abu ne maras kyau ba
hajara da ya zami da kanmu,yanzu kina ganin da wanda zai miki kallon mai mutunci a jamiar da
kike ikrarin wai ke 'yar jami'a!hak'ik'a ban ga laifin sameer don yayi kuka da aurenki ba!don shi
ya san mai ya gani na aibu game dake!sai dai kuma koma meye hannunka baya lalacewa ka
yanke ka wurgar dole nid'in nan dai nice uwa wacce kukan ki dana mahaifinki ya zama dole na
share muku,zanyi anfani da kowacce irin hanya ta gari naga na dawo miki da martabarki ta 'ya
mace wacce nasan shi kanshi sameer zai dawo yayi alfahari dake!
Yanda kuka ke bin kuncin beauty haka dariya ya bayyana saman fuskarta,da sauri ta matso
gaban ummah ta rumgumeta ta shiga wani sabon kukan tana mai jin son uwartata sosai a rai!

_8:00p.m(na dare)_
Bugun k'ofar da ake a cikin gidan ne ya sanya sameer da ke kwance lullub'e da bargo fitowa
daga ciki ya nufo a tsammaninshi zai ga Alhaji,saurin ja da baya yayi abin da ya gani yayi
matuk'ar d'aure masa kai,amininsa ameenu ya gani tsaye cikin wata dakakkiyar shadda,fuskar
nan d'auke da fara'a,dariya ameenu ya saki ganin yadda sameer yayi sororo yana
kallonsa,tureshi ya d'an yi da hannu da zummar ya bashi waje ya shigo,haka ya matsa masa
ya wuce ciki ya bar shi nan tsaye!kunya duk ta gama cika sameer ga mamaki tsagwaronsa da
yake yi ta yadda ameenu yasan gidan dady,dole ya katse tunaninsa a daddafe haka yabi
bayansa!zaune ya sameshi gefen gado don haka shima ya nemi waje ya zauna,kana ganin
sameer kallo d'aya zakai masa kasan damuwa ta gama cika shi,fahimtar haka da ameenu yayi
ne yasa ya kira sunansa a sanyaye ya amsa ba tare da ya kallo shiba,bai jira cewar ameenu ba
ya yi gaggawar furta,wallahi ameenu ni kam an cuce n....hannu ameenu ya kai ya toshe bakinsa
yace kar ka yi sab'o ko ka zargi iyayenka sameer,dady yayi min bayanin komai game da lamarin
kuma ni banga wani ai bu ba tunda iyaye sun aminci wannan gyaran tsakaninku zaku yi shi,ba
tare da wani yaji kanku ba,ka d'auka duk abinda ya faru tsakaninku a baya k'adsara ce da silar
ganawa,wasu zafafan hawayen bak'in ciki ne suka fara kwaranya fuskar sameer,sosai ameenu
ya tausaya masa amma ya zaiyi dole ya danne damuwarsa akai yayi masa nasiha kamar yadda
dady ya umarce shi,nasiha da lallami sosai ameenu yayi masa wanda tun yana kukan harvya
fara sauka a hankali yana biye masa a maganar,in da a k'arshe ameenu ke shaida masa ya rok'i
dady da ya janye maganar dinner daya shirya a daren zuwa wani lokaci ba da jimawa ba ta
yadda za'ai abu kowa na so ba ana ganin bak'in juna ba" haka kuwa dady ya amince,ya mutsa
fuska sameer yayi kawai bai tanka saba don shi baya tunanin da ranar da zai iya son beauty a
ransa!haka suka ci hirarsu ta ranar wanda duk akan maganar aurensu ne har dare ya fara
ratsawa ameenu yayi sallama da sameer akan gobe zai dawo da yamma!!
[10:26am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

176-180




💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Ko da ta fito beauty cikin kaya na atamfa riga da skirt d'inkin umbrella shape kayan sunyi
matuk'ar karb'arta sai wani d'an yalelan gyale data bi jikinta dashi bayan jaka da takalmi k'irar
vinci data cakare jikinta dashi, cikin nutsuwa da jin kunya haka ta k'arasa bakin motar da taga
alamun mutum aciki duk da bata tab'a ganin motar a gidan ba da alama ya nemi anfani da itane
don kar a gane suna tare, wanda ta ke da tabbacin tuni yana ciki ita yake jira,a hankali ta bud'e
marfin motar,jikinta har wani gyarma yake wanda ita kanta ta rasa dalilin hakan ta shiga ciki ta
rufo k'ofar,wani sanyin dad'i daya doki hancinta na turarensa yasa ta lumshe ido a hankali kuma
ta bud'e su,ya sameer ina kwana,abinda ta iya furtawa kenan murya can k'asa!shiru taji tare da
tada mota kamar bazai amsa ta ba har suka isa fita gate sannan taji yace lafiya,daga haka bai
k'ara cewa komai ba har suka yi nisa da tafiyarsu amma da mamakinta maimakon su nufi
hanyar jami'a sai taga ya karya kan motar ya shiga wani titi,zagaye ya shiga yi yana 'yan
dube-dube da alama wani abu yake nema can taji yace yes tare da take burki,gaban wani kanti
da aka rubuta womens parlo a saman shi,fita yayi ya nufi kantin, haka bai wani jima sosai ba sai
gashi ya dawo hannunsa d'auke da leda mai layi-layi,haka ya shigo yaci gaba da tafiyarsa,bai
zame ko ina ba sai bayan ZAHRAIN TWINS THEATER inda yasan yau lecture d'inta ana
zatayi,waje ya samu ya tsaya tare da bud'e ledar kallo d'aya yayi mata yaga kalar kayan dake
jikinta don haka wata hijab pink colour ya zaro ya wulla mata,kallonsa kawai tayi ba ikon
magana don haka ta d'akko hijab d'in ta bud'e tare da sakawa,duk abin nan da take idon
sameer na kanta har ta gama ta shiga k'ok'arin bud'e k'ofa zata fita,ke???ya fad'a wanda ya
tabbatar da ita yake,tsayawa tai ta juyo ta kalleshi,kansa ya mayar a titi duk da duhun motar
yace ki aje wayoyinki cikin motar kafin ki fita sannan in kin gama ki same ni anan sannan ki
saka a zuciyarki yanzu ba da bace!daga haka bai sake cewa komai ba,ganin haka yasa beauty
zaro jakarta a hankali tayi kamar yadda ya umarta sannan ta fita!.hannu sameer ya buga da
k'arfinsa a kan sityarin motar had'e da cije harshe yace u re my destiny!can kuma kome ya tuno
a hankali ya shiga jero addu'oi kafin ya kunna motar ya wuce office d'inshi!




Duk wani iri take jin ta cikin hijab karo na farko kenan da ta tab'a shigowa jami'a da hijab,duk
inda ta waiga sai gani take kamar kowa kallonta yake duk ta gama tsarguwa da kanta,haka ta
nufi cikin theater d'in can lungu haka ta manne jikin ta da bango,ta kuma kwantar da kai a jikin
tebur d'in wajen,ba ita ta d'ago kai ba sai da taji alamar shigowar malami ciki,tana juyo fuska ido
hud'u su kai kicib'is da wata d'aliba wacce idan bata manta ba a wasu lokutan baya itace wacce
ta watsa wa jan biro jikinta sakamakon yabonta da sameer yayi,saurin kauda kai tayi zuwa
gabanta nan ma dai idonta ya sauka akan lecturern da ya shigo Prof KAS ta gani sanye da

tabaronsa hannu rik'e da marker yana 'yan dube-duben wasu takaddu,tun da tayi tozali da
wad'annan abubuwan biyu beauty ta sadda kanta k'asa a kan wata k'aramar jotter dake
gabanta ba ita ta d'ago ba sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login