Showing 45001 words to 48000 words out of 59972 words

Chapter 16 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf

Advertisement

08 Jul 2025

3230

mai cike da buk'atar amsa sameer ya jefeta dashi ran nan sam babu alamar annuri haka
yasa hannu ya tureta can gefe daya ya shige gida abinsa!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

136-140



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Bai takura mata sameer ba har sai da tayi kukan ma'ishinta don kanta ta tsaya,sannan ta
d'ago kai a hankali ta kalle shi,har lokacin sameer kan shi na gareta don haka ya kauda kansa a
sanyaye ganin yadda beauty tai narai da ido,murmushin k'arfin hali ta saki mai cike da tambaya
sannan ta dai-daita nutsuwarta ta shiga magana,"yau zata zamo rana wacce ban yi tsammanin

kasancewarta a rayuwata ba,sai dai ina k'addara ta riga fata,babu yadda na iya dole na bud'e
sirrin da bai kamata na bud'e shi ba don kuwa bani da wata mafita,ya sameer kamar yarda
kasha kirana da sunan karuwa ban tab'a inkari akan haka ba, don duk wanda yasan hajara da
halayya irin tawa dole duk sunan da aka kirani dashi na amsa,sai dai abinda baka sani ba koma
ince jama'a basu sani ba game dani shine,wannan d'abi'a dole ta sakani yinta ba don naso
ba!don kuwa na samo wannan halin ne"
Adalilin principal d'in makarantarmu ta secondary school,da jin haka k'ara gyara zama sameer
yayi sosai yana fuskantar ta don jin abinda ta ambata,nan ta ci gaba da magana,eh haka ne
magana ta ba k'arya principal d'inmu itace ummul abaisi na duk rayuwar da muka tsinci kanmu
aciki,sanin kan kane dai dady bazai sani makaranta mai arha ba,makaranta ta ajin k'arshe
wajen tsadar kud'i wanda duk 'ya'yan masau kud'i yawancinsu nan suke yi anan nayi primary
don haka bayan na gama na d'ora secondary,anan ne kuma wata rana muna zaune a aji da
yake mun zo s.s.s3, bazan tab'a mantawa ba muna karatun geography sai ga discipline master
yazo har aji ya kiramu mu uku,jiki na gyarma muka bishi duk mun gama bayarwa dukanmu
zaiyi,sai bayan da muka fita ne yake shaida mana cewa principal ke nemanmu,haka ya samu
gaba har office d'inta,bayan daya kaimu ne labari ya fara canjawa dayake mace ce principal d'in
tana washe baki ganinmu ta shiga zayyana mana buk'atarta ta hanyar wayo da dabara"ta
shaida mana cewa yanzu mune ajin k'arshe sannan tasan fatan kowannenmu shiga jami'a nan
ta cigaba dacewa ita jami'a ba'a shigarta haka nan sai an shirya haka dai taitayi mana bayani
muna ganewa ta kuma shaida mana da tazab'e mu muyi mata wani aiki ne saboda tasan 'yan
gidan masu hannu da shuni kamarmu babu zancen takurawa ko matsantawa ta iyaye a tattare
damu!bamu gama gane inda ta dosa ba sai da discipline master ya k'ara wayar mana da kai da
cewa duk kanmu yana so mu kar muyi applying makaranta d'aya ta yadda zamu cimma burin
janyo hanakalin malamai maza,ko wacce d'aliba ta yi k'okarin kawo nata toh darajarta zata k'aru
sannan akwai wasu mak'udan milliyoyin kud'i da bayan shekara hud'u za'a bata!jin yadda suke
jaddada miliyoyin kud'in anan yasaka kowannen mu amincewa,hakan ya saka bamu tashi a
wajen ba duk sai da aka bamu somin tab'i na naira dubu d'ari biyu da hamsin!tare da
yarjejeniyar ya zama sirri a tsakaninmu,toh tundaga wannan ranar kullum sai mun je office d'in
principal bayan an tashi a makaranta ta k'ara wayar mana da kai yadda zamu janyo hankalin
malaman jami'a yayin da muka shiga!


Hankalin ummah ya fara tashi in ban manta ba tun daga ranar data fara ganin d'abi'u na da
tarbiyyata ta canja duk da dama ba wani tsauri nake samu ba tunda dady na nan kuma baya
son b'acin rai na,kullum rigimar daddy da ummah bata wuce akai na,haka har mukayi jarabawar
waec da neco amma duk ummah ta lura ba wani karatu nake ba illah dai kad'e-kad'e da
wak'e-wak'e da suka zama jikina,ga kud'i da nake kashewa baji ba gani,wasu dady ke bani
wasu kuma principal ke turamin ta account tunda duk ta bud'e mana account,wata rana dana
karb'o kud'i daga banki ko dana shigo gida na taradda dady a parlo dole nima na zauna,dana
tashi mik'ewa ne tsautsayi hannun jakar ya bud'e wasu mak'uden kud'i suka zubo,wato a
lakacin ba ummah da dady ba harta ni kai na sai da gaba na ya yanke ya soma gyarma,amma
da yake dady baya son ganin laifi na sai yayo sauri mik'ewa ya fara kwasar kud'in ya mayar min
jaka sannan ya kamo hannu na mukayi d'akina,turani ciki kawai yayi shi kuma ya wuce nashi

d'akin a ranar ne ummah ta fara gaba da ni wai na fara samun kud'i daga waje,wanda ni kuma
tun daga lokacin na fahimci ummah bata so na,bata son cigaba na arayuwa daddy ne kad'ai ke
so na!


Haka rayuwa ta jin dad'i da daula taci gaba da wanzar min har ya kawo lokacin da na samu
admission zuwa jami'a ranar ji nayi tamkar na zama millioner gani nake nesa tazo min kusa,da
murna haka na kira na shaida musu,wanda suma murnar sukai tayi min!

Tun kafin sati d'aya da fara shigowata jami'a tuni na ziyarci duk wani kanti na kaya,mak'il haka
na cika drawers dina kaf da k'ananan kaya,takalma da jakunkuna,duk da naso siyan gyale ko
da k'anana ne amma principal ta hanani acewarta zasu rage min kwarjini kuma zasu b'oye min
kyaun halitta! Shiru beauty tayi da ta kawo nan a hirarta ta kai hannu fuska,mak'alallen wahayen dake shirin
sauka a kuncinta ta goge had'e da jan majina!tsintar kanta tayi beauty ta k'in ci gaba da labarin
har sai da ya nemi da taji gaba sannan tayi gyaran murya taci gaba!




Tun daga ranar dana shiga jami'a tunani na bai wuce ta wacce hanya zan samu na cimma
burina cikin sauk'i ba,sai kuwa gashi na samu malam umar,mutum na hannun dama a
b'angaren neman mata da kud'i na iya samo kanshi don na sakar masa kud'i iyakar sakarwa
kafin ya had'a file guda na duk wasu sirrika na malaman makarantar ya bani,ita kuma k'awata
zee-zee tunda na fahimci 'yar abi yarima asha kid'a ne sai na rik'eta na fara sakar mata kud'i
don sune matsalarta duk da agidan ma bata tsiraba,mahaifinta mutumin kirki ne ga kula da
hak'k'in iyali amma mahaifiyarta 'yar Allah bamu musamu ce,ita dai a bata kud'i shiyasa kullum
cikin samari masu mota take wai a haka baban na sa ido kenan!
Ina ganin wannan shine abinda kake son ji ko?
Tana tambayar ne tare da maida dubanta ga sameer tana kallo!d'ago kai yayi shima dai ya
kallota don abinda yake da muradin ji har kawo yanzu bai jiba nan take kuwa ya fara jefo mata
tambayoyi!

"Daga shigarki jami'a zuwa yau malamai nawa kika had'ata dasu?kuma ke nawa ne sukai
anfani dake?
A kid'ime beauty ta zaro ido cike da mamakin tambayarsa ta k'arshe inda shima ya zaro mata
nasa da zummar eh amsarta yake jira!tab'e baki beauty ta yi sannan ta kauda kai gefe guda
cikin murya can k'asa tace mutum goma na kai mata,ni kuma babu,ban gane babu ba?babu
me?sameer ya tambaya! sunkwui da kai sosai beauty tayi don tasan bai zama lallai sameer ya
yarda da amsarta ba ta k'ara nanata masa da babu d'a namiji ko d'aya da muka tab'a keb'ewa
ko ta minti biyar a wajen makaranta dukkan ninsu a waya muke magana bayan na fahimci
yanayin mutum toh sai na bashi address nata,wannan shine silar da ya saka ko wane course
bana fad'uwa tun shigata jami'a kawo yanzu!

Shima prof KAS da kaga abu ya had'amu na zagaya kuma na zagayo na ga babu wata hanya
da zan iya samun makin da nake so dole sai nayi masa abinda nayi masa shiyasa hakan ta
faru,bata kai ga rufe baki ba wata tambayar tabiyo baya"toh abincin da kike rabawa na stop and
chop shi kuma sadaka ce ko kuwa zakkah?kai duk'e tana kallon k'asa tace shi kuma neman
suna ne kawai da son shahara don sun tabbatar min hakan zai saka kowa ya san da zamana a
jami'a!




Shi kuma kamal dana ganku tare a mota wancan satin darasi yake koya miki?
a'a beauty ta bashi amsa sannan tace shima munje can sau biyu!
Wani gauran numfashi sameer ya saki mai cike da tuhuma ta b'angare d'aya kuma yana jin
dadin yadda yake kallon gaskiya tsagoronta a idanun beauty !dole ya danne yanayin da yake
ciki kwallon hannayensa wanda yake wasa dasu ya watsa mata su cikin zafin nama wanda
hakan ya matuk'ar raxanata ta d'ago kai a tsorace ta dubeshi"ta mau fuskar nan babu alamar
wasa balle murmushi haka ya shiga binta da wani mugun kallo sai can kuma cikin dakewar
murya ya shiga magana yana nuna ta da yatsa"kin cuci kanki wallahi,banza, wawuya,
asharariya,wacce bata san ciwon kanta ba balle na wasu shin kina tsammanin da haka zaki
samu kud'i da wannan mummunar d'abi'ar,amma dai tur da halin kawaliya mace mai neman
maza a gari tana kai wa wata can!kin zama akuya mai komai tq samu ya zama nata!don haka
ina so ki sani wannan labarin naki karki tsammani abin so ne a wajena,babu abinda ya haifar
miki illar tsantsar k'iyayya a fili wanda in kin lura zaki ganta cikin kwayar idanuna!kuma da kike
batun kina samun nasara a jami'a toh ki rubuta ki ajiye wannan semester d'in sai kin samu
matsala da course d'ina,don na d'au alwashin haka tun ranar da kika tozarta prof a gabana,kika
wulak'anta tsohon da bai ji ba bai gani ba!maganata ta k'arshe a wajenk kuma sak'oni d'an ladi
ya bani cewar yana sonki da aure,kuma a matsayina na wanda Alhaji yake ganin girma har
yakan zauna muyi wasa da raha na furta masa na bashi ke,sai dai kuma kash ina ji masa
takaicin namiji salihi zai auri mace mai hali irin naki wacce take wa kanta kirari da 'yar jami'a!


Yanda ya gama lura sameer da k'ofofin kan beauty sun riga da dun gama kullewa da munanen
kalaman da yake jefarta dasu ga wasu zafafan hawaye da suka kasa tsayuwa a kumatunta ya
sashi mik'ewa a fusace har yana buge k'afarta ta hagu yayi gaba ya barta nan jikin bishi cike da
damuwa! [10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

141-145

💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*

Cike da damuwa tare da danasani haka beauty ta mik'e ta nufi gida cikin mawuyacin
hali"shiru ta samu gidan wanda hakan ya tabbatar mata cewa tsoho sun fita da Alhaji zagayen
yamma don ya motsa jikinsa, bata zame ko ina ba sai d'akin su d'an ladi a ganinta wannan
shine mafi kyawun lokaci daya dace ta yi magana da sameer,sallama biyu tayi amma duk ciki
babu wacce ya amsa mata,ga kuma takalmansa a bakin k'ofa wanda hakan ya k'ara tabbatar da
ita cewa yana ciki,ba ta damu da jin haka ba sai ma kamo labulen d'akin tayi ta rik'e ita bata
shiga ba,ita kuma bata lek'a ciki ba ta fara magana cikin murya k'asa uwa mai rad'a"nasan ya
sameer duk abinda ka kira ni dashi wallahi na cancanta amma kayi wa girman Allah wannan
magana ta zama sirri tsakanina da kai don idan har sirrina ya tonu a gidan nan wallahi na
mutu,nasan dai zuciyarka akwai Allah a ciki,kaji k'aina ya sameer tunda kaga dai ban b'oye
maka komai game da ni ba,kai ma ka tausaya min!dariya sosai ta juyo daga ciki har kana jiyo
shak'ewarsa saboda dariyar mugunta can kuma sai ya nisa yace ho ho ho gaskiya yaro a
kullum dai yaro ne,ke baki ji kunyar aikata laifi ba sai ni kike rok'on naji kunyar tona miki asiri,ai
ki d'auka asirinki a fili yake,yanzu dai ki shirya karb'ar hukunci daga Alhaji kawai!cikin wani
mawuyacin hali na jin sunan da sameer ya ambato yasa ta yaye labulen da saurin ta ta afka
cikin d'akin tana fad'in kayi wa Allah kayi hak'ur.... chak ta tsaya tsaye idanunta suka kafe waje
d'aya sakamakon toxali da idonta yayi da sameer kwance saman katifa daga shi sai vest da
k-aramin short,kasa dauke ido daga kallonsa tayi wanda shima a tsorace ya tashi zaune yana
d'an kare jikinsa da hannu!ganin abin bana k'arewa bane haka yasa shi saurin mik'ewa ya nemi
jallabiyarsa ya zura sannan ya juyo a fusace ya wurgo mata wani mugun kallo yace lafiya zaki
shigo min d'aki ko sallama babu!a sanyaye beauty ta iya sauke kanta k'asa don bata da abinda
zata iya cewa yanzu!komawa sameer yayi gefe da gadon ya zauna yad'anyi shiru!
Dan girman Allah ya sameer kayi hak'uri mana tun d'azu fa nake baka hak'uri ko dan kaga ana
lallab'aka shine kake ta wani ja min rai"cike da b'acin rai beauty ke d'aga murya tana
maganar!bata tsaya nan ba taci gaba abinta,toh wallahi kaje duk wanda zaka fad'a mawa ka
gaya masa tunda kai baka da tausayi,kaje kai tayi,juyawa tayi ta nufi k'ofa sai faman banbami
take ita ala dole rai ya b'aci!tana kai k'ofa bakinta ya furta"bama Alhaji ba kaje ka gaya wa mai
garin garinnan shine zaka nuna min cewa kai sunanka sameer!

Yaye labulen d'akin tayi a zuciye zata fita taji tayi karo da mutum tsaye!k'ara kai hannu tayi
beauty ta yaye labulen baki d'aya!karaf ta dawo a baya ganin tsoho tayi tsaye gefensa Alhaji
duk kanninsu fusa babu annuri musamman Alhaji,k'arasowa cikin d'akin sukayi baki d'aya kafin
kowa ya ankara ji kake tasss ... Alhaji ya kaiwa wa beauty wani zazzafan mari! sululu beauty
tayi nan wajen ta zube k'asa sumammiya!wani irin tsalle sameer yayi sai gashi gaban beauty
yana jijjiga ta!amma ina babu alamar motsi take duk wani launi na sameer ya rikid'e daga fari
zuwa ja don rikita,ganin yadda ta kafe bata motsi yasa tsoho fashewa da kuka yana fad'in
wallahi zuciyarka ta sa yau ka kashe min jikata d'aya da bani da kamarta a doran duniya!kuka
sosai tsoho ke yi yana sambatu,lura da haka da sauri Alhaji yayi waje bai jima ba sai gashi rik'e
da butar ruwa a hannu baba yagana na biye dashi domin bacci take tayi abinta kukan tsoho ya
tasheta!ruwan sameer ya karb'a ya shiga yayyyafa mata inda baba yagana ke jijjigata,wani
gauran numfashi na wahala beauty ta saki a hankali kuma ta fara bud'e idonta wani dishi-dishi
ta fara gani har ta kai ga bud'e idanunta gaba d'aya"sannu kowa ya shiga yi mata ita dai ba
magana sai gyad'a kai,hannun Alhaji tsoho ya kamo yace tashi muje waje mu basu waje,ba
musu haka ya tashi ya bisu ya rage saura su uku,baba yagana itama mik'ewa tace bara je na
samo miki ruwa ki sha!tana fad'in haka ta fice!k'ara lumshe idonta tayi can ciki-ciki ta ji sameer
ya ce sannu!ido rufe ta amsa shi,daga nan kuma shiru ya biyo baya!


_08:00p.m(na dare)_


Tsoho ne zaune gefensa Alhaji sai sauran mutanen gida in banda d'an ladi da duk yammacin
yau baya gida!gaba d'aya suna zaune a d'akin tsoho kamar yadda ya umarta!bayan da suka
gabatar da sallar isha'i!" Sallama da salati ga fiyayyen halitta ya farayi wanda hakan ya ke nuna
akwai wata muhimmiyar magana da zaiyi sannan ya fara da"na taraku ne ba don komai ba sai
dan abinda ya faru ga jikata hajjo,duk da dai bamuji komai akan hirar da kuke d'azu ke da yaron
nan sameer ba amma tunda har kike rok'on kada Alhaji ya sani hak'ik'anin gaskiya abin bazai
xamanto mai kyau ba,don haka baza mu takura ku da sanin wani sirri game daku ba sai dai
yana da kyau duk yanda nake ji dake hajjo in naga kinyi wani abu ba dai-dai ba na tsawatar miki
don hakan shine mafi k'ololuwar soyayya da zan nuna miki! haka tsoho ya cigaba da yi musu
nasihohi masu tsuma jiki da sanyayasu,bayan ya gama ne Alhaji ya d'aura daga inda ya tsaya
duk da Alhaji kusan duk fad'a ne nashi da jan hankali,sosai nasihar ta shige su musamman
beauty da taron don ita ne! Inda daga k'arshe tsoho ya rufe taro da addu'a yana musu albishir
da su xauna cikin shiri gobe akwai abin al'ajabi A k'auyen nan!Dariya duka suka saka inda
anan beauty ta samu bakin magana tace watak'il in tsoho zai raka mu mota in zamu tafi zai
mana rawa da k'afa d'aya don ya tabbatar mana ya samu lafiya!baki daya suka k'ara kwashewa
da wata dariyar tsoho yana mai bata amsa da in har ta kama gobe na juya jiki ai sai nayi!cikin
raha,da wasa da juna haka suka rabu kowa ya nufi d'akinsa don kwanciya shiko Alhaji yayi
sallama dasu ya fice!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

146-150



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*

Bayan fitar Alhaji da kusan awa guda sai ga d'an ladi ya shigo hannunsa rik'e da bak'ar leda
guda biyu,zarcewa ya yi d'aki inda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login