Showing 30001 words to 33000 words out of 59972 words
Chapter 11 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf
ni kad'ai!innalillahi wa innah ilaihirraji'un"toh yanzu yana
ina?ummah tayi tambayar,gashi nan a gida na jik'a masa saiwa yasha ya d'an samu
bacci!sosai jikin ummah yayi sanyi da jin rashin lafiyar mahaifinta,cikin k'arfin hali tace mata
yanzu gashi baya gari kuma waya dashi sai dai cikin dare don aiki yawa yake musu,amma zan
gani zuwa anjima duk yanda na yanke zan kira!toh yagana ta amsa dashi kafin nan sukayi
sallama t ma kashe wayar!
A sulale wayar tabi jikin ummah ta sauka kan cinyarta inda tuni ruwan hawaye ya gama cika
idon ummah"damuwa tsagwaronta kake gani d'auke saman fuskarta"yanayin da ta shiga yasa
sameer bin ta da kallo a hankali ya iya furta,lafiya dai ko ummah?sam hankalin ummah ya
gushe a kanshi har sai da ya k'ara nanatawa,sannan ta juyo guntun hawayen dake mak'ale a
fuskarta suka gangaro,a rud'e sameer ke fad'in"subhanallahi dan Allah ummah menene ke
faruwa?naga daga d'aukar wayarki haka ta faru ko dai anyi rashi ne,girgiza kanta ummah tayi
sannan ta share hawayen nata ta d'ago kai a dak'uke tana kallonsa,can kum tace ba'ai rashi ko
d'aya ba sameer k'anwar mahaifiyata ce ta kirani akan rashin lafiyar mahaifina;yanzu haka yana
can kwance jikin ya k'ara tashi kuma ba kowa a wajensa sai ita sa yake mahaifiyata ta
rasu,kuma dangin namu mazan ba masu d'aukar zumunci da wani abu bane,shiyasa kaga duk
na damu,in dama ace daddyn hajara na nan da da sauk'i zan iya tambayarsa gobe na shirya
naje,toh baya nan ita kuma waccen shashashar yaushe zan tura ta jinya,ita da ko hankali bata
cika ba,!dafe kanta unmah tayi don wani irin sarawa da taji yayi kamar zai bar jikinta hakan yasa
sameer saurin fad'in ya isa haka ummah ki daina damuwa kar kema wani abun ya
sameki,yanzu shi yana ina da zama?yana nan kano cikin local government d'in
minjibir!minjibir?sameer ya nanata sunan wajen,a gaskiya ummah bansan wajen ba amma in
bazaki damu ba ni ki wakiltani indai kinga ba wani abu sai naje ni!da sauri ummah ta d'ago kai
tana kallonsa!ajiyar zuciya ya sauke yace eh ummah ni zanje in har kin amince min sai ai mun
kwatance!toh sameer Kar na takura maka aikin naka fa?haba umma karki damu da wannan zan
sanar kuma ko bana nan akwai masu tallafa min don haka ki kwantar da hankalinki,toh shike
nan hakan yayi na gode amma kaga da waccen malalaciyar zata iya ai da kun tafi tare tunda ta
san wajen ba sai ka wahala ba!yamutsa fuska sameer ya d'an yi jin an ambaci mace yace wace
kuma ummah?hajara mana,kai dai Kawai Allah ya sawak'e ma wannan yarinya wallahi ban
tab'a ganin mace sakara irin taba duk ubanta ya gama d'aure mata sai yadda take so ina duniya
zatayi dad'i a haka?cikin fad'a-fad'a ummah ke maganar!wani dogon gauron numfashi sameer
ya sauke lura da yadda ummah ke zayyana halayem yarinyar sak irin na salaha k'anwarsa,toh
amma ya akai duk da jarunta da nake ganin yanzu tattare da ummah ta kasa gyara 'yarta?toh
yanzu mene abunyi?ko dai na tallafa wa ummah ne tunda ga dama ta samu daddy baya nan?
Sameer lafiya dai ko naji kayi shiru haka?jin ya lula wata sabuwar duniyar yana tunani yasa
ummah tamabayarsa!cikin jin kunya irin nasu na maza nan ya shiga susa k'eya kamar mara
gaskiya sannan yace babu komai ummah amma in babu damuwa sai mu tafi tare da ita kawai
yadda nima bazan wahala ba,kuma kinga itama ai taga jikin nasa!sosai hakan yayi wa ummah
dad'i nan da nan ta amsa masa da ai kuwa hakan za'ai bara ta tashi daga bacci sai na sanar
mata zuwa safe sai d'au hanya"kai Allah dai yayi maka Albarka ashe kai rahama ce a gareni
amma k'ememe daddy Ya hanaka shigowa ciki,ai daga yau ka zama d'an gida kuma ana tashi
daga aiki ka yo gida nan ne mahallin cinka da shanka,ni na tsaya maka naga kuma wanda zai
canja hakan!dariya sameer ya saki na jin dad'in kalaman ummah nan yayi mata godiya da
hakan ya kuma nemi izinin wucewa sashensa,ba musu ta yarje masa har da kiran ma'aikata
da'a mik'a masa abinci sashensa! [10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
46-50
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
Misalin k'arfe 9:00p.m kenan a agogon bangon dake mak'ale saman d'akin ummah kallo ta
kai gareshi sannan ta nisa,juyowa tai gefe ta ga hankali kwance beauty na rik'e da waya sai
latse-latse take yi?me kike yi da wayar??ummah ta tambayeta,cak beauty ta tsaya da charting
d'in da take ta d'ago kai a hankali tace ummah gaisawa muke da daddy!daddy kuma?me kike
ce masa?shiru beauty tai ba emm ba em em,toh ki ce masa ya kirani zami magana,toh ummah
sannan beauty ta samu damar ci gaba da latsa yawar ta sanar masa,daga haka ta kashe datan
nata ta sauka akai gaba d'aya,gefen kujera ta maida wayan ta aje don tasan halin ummah
yanzu k'iris take jira ta kwace ta,ba'a d'auki wani tsawon lokaci ba sai ga kiran daddy ya shigo
wayar beauty,hannu ta kai ta d'akko wayar ta ga sunan daddy a jikin wayar,juyawa tai ta kalli
ummah tace daddy ne ya kira!wani dumm ummah taji kanta yayi mata yanzu kenan bazai kirata
a wayar ta ba sai dai ta 'yar ta!haka ta danne damuwarta ta sa hannu ta karb'i wayar!gaisawa
sukai kafin nan suka shiga hira ainun suna k'ara nuna wa juna tsantsar kulawa da rashin juna
da sukai!acikin hirar ne beauty dake can gefe zaune taji ummah na sanar da dady zancen tafiya
har tana ce masa beauty ta rok'i bak'on gidan nan ya kaita ta dubo jikinsa,da mamaki beauty
tabi ummah da kallo har ta kammala wayar,ba abin tai magana ba sai kallo da ido,ke lafiya kika
kafe ni da ido haka?cewar momy"nasan dai kin ji me nake cewa sarai toh dan haka ki shirya
gobe da sassafe zaku tafi minjibir!minjibir kuma ummah?eh minjibir kuma wallahi naji kin kira
dady kin gaya masa wani abu ni dake ne,don haka sai kije ki fara shiri tun yanzu don bansan
kwana nawa zai ce kuyi ba!ba shiri beauty ta mik'e tsaye ta amso wayarta a hannun ummah ta
fice a d'akin!
Da gudu beauty ta fad'a d'akinta kuka sosai ta shiga yi ba ji ba gani sai wani shure-shure take
da hannu ita ala dole an b'ata mata"teddyn ta dake ajiye tsakiyar gado ta d'auka tai cilli dashi
saman mirrow duk wasu kayan kwalba suka zube k'asa,tun tana kukan da sauti har ta gaji ta
fara tsagaitawa dan kanta"kalaman ummah ke ta faman mata yawo akai toh yanzu haka kawai
zata bi wani bak'o k'auye bata ma san waye bane,don kawai an ga daddy baya nan,har kusan
sha d'aya na dare beauty na kwance sai faman mirgine-mirgine take saman gado"
Can wata dabara ta fad'o mata"tabbas zan had'a kayana da zarar mun fara tafiya sai na nemi
na bashi kud'i kawai ya sauke ni a wani hotel d'in in yaje ya dawo sai ya biyo ya d'auke ni mu
tafi!!yes yes beauty ta mik'e tsaye tana murna ta nufi drawer d'inta,duk wani abunda zata
buk'ata sai da ta kammala su a jerin akwati biyu don ko ta batun karatunta bata yi sanin dama
can baya gabanta!
Kiran sallar asuba na farko beauty ta tashi"ita da sallah sai gari ya waye take yi,wanka ta
d'auro kafin nan ta fito ta shirya tsaf ta nemi hijab tai sallah"tana zaune kan dadduma kamar
daga sama ta ji ta fara tariyo abinda ya faru jiya a stop and chop,yanda matan nan su kai mata
tayin shiga k'ungiyarsu,tunani sosai tayi har dai daga k'arshe ta yanke shawarar in har ta samu
zuwa hotel an jima zata kirasu ta shaida musu amincewar ta akan buk'atarsu!
Duk yadda tayi saurin lokaci yayi ummah ta kirata sai gani take lokacin baya ja,sauka k'asa tayi
ta nemi breakfast tayi amma har yi war haka 7:00a.m batai ba, tsuka ta saki ta k'ara haye wa
sama"tana zaune saman stool tana k'ara gyara kwalliyar fuskarta taji turowar k'ofa,ummah ce ta
shigo dan haka cikin ladabi ta gaisheta!shigar jikinta ummah ta k'are ma kallo"doguwar riga ce
light pink sai yalolan gyalan rigar data nad'e kanta dashi"jinjina kai ummah tayi sannan tace tun
d'azu fa ya fito yana mota ke yake jira"jin haka yasa beauty cikin sauri ta aje lip stick d'in dake
hannunta kamar ba ita jiya ke b'ata rai ba,ta shiga jan akwatinta,don yanzu ummah ta hana
kowa yi mata aiki a gidan in banda wanki da guga,ummah ce ta taya ta da d'ayan akwatin har
bakin mota inda ya ajiyeta saitin fitowa daga falo,bud'e taga booth d'in don haka suka zura
akwatunan ciki,jiyowa tai su kai sallama da ummah sannan ta nufi k'ofar gaba na motar ta
bud'e,da yake motar dimm take da duhu ko ina bak'i ne in banda side mirrow na waje baya
ganin na ciki,shiko sameer rik'e yake da waya yana fama zuma revenge game da yake mayan
game ne kawai yaji wani k'amshin turare ya doki hancinsa daga bud'e k'ofar!!!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
51-55
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
A hankali sameer ya d'ago dara-daran idanunsa ya sauke su akan k'ofar motar har lokacin
beauty na tsaye tana k'ok'arin gyara doguwar rigarta don ta zauna,zanen rigar ya k'ura ma ido
yadda yake ta shek'i na tamabarin tauraro(star) sosai ya shagala da kallon zanen kamar daga
sama yaji k'arar demmmmm...Alamun an masa game over kenan, saurin sauke kansa yayi a
phone d'in inda hakan yayi dai-dai da shigowar beauty had'e da tsayuwar ummah a bakin k'ofar
tana fad'in toh sameer Allah ya tsare hanya,da saurinsa ya d'ago kai sama don baiwa ummah
amsa!dass yaga idon mace kafe saman nasa wanda tun kiran sunansa da ummah tayi hakan
yasa ta waigowa taga wannan waye abokin tafiyar tata,what??abinda sameer ya iya fad'a
kenan yana nuna ta da yatsa, beauty da tai saroro kamar wata dutse tana kallonsa,can kuma
cikin razani lokaci guda ta turo k'ofar motar har tana bige ummah da marfin motar haka tayo
waje sai faman haki take kamar wacce tai tseren gudu!ido waje take kallon ummah da take
tsaye tana luliye inda ta bug'e tace ke lafiya haka?bata iya cewa komai ba beauty sai nuni da ta
ma shiga yi da motar!ganin ta kasa cewa ko uffan yasa ummah sunkuyar da kai cikin motar don
ganin ko wani abu ya faru ciki!zaune ummah taga sameer ya dafe kai da hannu!cikin rashin
fahimta ummah ta k'ara nanata maganar ga sameer shima dai yayi shiru!k'ok'arin komawa ciki
beauty tayi,ai kuwa cikin sauri ummah ta rik'o hannunta!ina zaki?tambayar da ummah ta jefo ta
dashi kenan?cikin dak'ilewar murya beauty ta amsa ta da ciki zan koma ummah wallahi na fasa
tafiyar nan ya fito min da kaya na kawai!ciki kuma?akan wane dalili?kafin beauty ta iya bata
amsa suka ji bud'e k'ofar sameer daga d'aya b'angaren yana fad'in emmm ummah dama ba
komai kawai tayi mamaki ne jiya na d'an daki motar ta ban sani ba har ta kasa hak'uri ta fito
tanai min fad'a,sai kuma gashi yau Allah ya had'amu amma babu komai,cikin k'ik'ina da
sark'ewar murya sameer ke maganar!kana ganinshi kaga wanda ke b'oye da wani abu a
rai,k'ara yunk'urowa beauty tai zatai magana nan ma ya k'ara tare ta da cewa,ina ga ummah in
ta shirya kawai mu wuce don kar muyi latti ko?jin an ambaci latti yasa ummah saurin kallon
beauty tace kin de ji kunya wallahi ko ina se kin nuna halinkina rashin hak'uri yanzu gashi dara
ta ci gida,sai ki wuce yanzu ku tafi ai,kasa ko da kwakwkwaran motsi beauty tayi,duk wasu
jijiyoyin kanta sun gama tsayawa cak da aiki,tunani fal sun gama cika kwanyar kanta,toh yanzu
dama wannan shine bak'on dady?wanda ya gama tozartani a bainar jama'a?anya kuwa burin
dana cimma yau zai iya bari na cika shi?toh yanzu ya ma za'ai na iya binshi mu tafi daga ni sai
shi?bata dawo daga duniyar tunanin data shiga ba kamar daga sama taji wuf an finciki
hannunta da k'arfin tsiya an wullata cikin mota,an maida k'ofa an kulle da key,a razane beauty ta
hau jijjiga k'ofar da k'arfi ita ala dole sai ta bud'e,tana kallo haka cikin sauri sukai sallama da
ummah ya shigo motar,bai bi ta kanta ba ya hau kunna motar,batai wata-wata ba ta jiyo kamar
wata zararra ta rik'o hannunsa da yake kan key tace wallahi ka bud'e min motar nan,kar ka
kuskura ka fita a gidan nan ba tare da ka sauke ni ba na dai gaya maka,sauke idanunsa sameer
yayi a karo na farko a hannunsa yaga hannun beauty saman nasa,wani irin kukan kura yayi
kamar wani mayunwacin zaki yayi wurgi da hannunta gefe,yanda taga jikinsa na wani kyarma
tamkar mayak'in soja yasa ta shiga taitayinta ta fara rok'onsa Allah,da annabinsa ya sauketa,da
yake motar duhu gareta sai ya zamana ummah duk wannan dramar tasu ba wadda ta gani haka
ya tada mota hankali kwance ya fice daga gidan yana gyad'a kai!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
56-60
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
Wallahi ka sauke ni, zan maka ihu, Allah zan juyar da kan motar nan kowa ya mutu,wai ba
da kai nake magana ba ka mai dani wofi,kana jina fa? Nace ka tsaya na fita,surutai sosai
beauty keyi,tun tana gunguni har takai ga samun sararin d'aga murya,ganin har lokacin sameer
tafiya yake bashi kuma da niyyar tsayawa yasa ta kwarma wani uban ihu da bashi ba ita kanta
sai data firgita,lura da lokacin ya fita daga wajen mutane ya fara yankar daji yasa shi jan birki ya
maida motar gefen titi ya tsaya,kana ganin sameer kaga wanda yake cike da b'acin rai basai an
gaya maka ba,wani wawan kallo ya jefe ta da shi mai cike da tsana,kusan minti 2 yana mata shi
ganin hakan bazai gama isar da sak'onsa ba yasa shi magana"tur da wayewar gari irin wannan
a wajena,ina ma ace mafarki nake,wallahi da tuni na farka na shiga gari na hau sadaka,don
wannan munin mafarkin yakai matuk'a!kaicona sai gashi wai a zahiri ne,ni ne yau kusa da mace
fasik'a,fajira,wacce bata san k'ima da mutuncin kanta ba,balle kai tunanin samun tsarki tattare
da ita,nikam Allah wadai da mace 'yar Allah bani musha kunin kanwa,wai ya ma akai kika zama
'yar ummah?how??duka yakai a sityarin motar rai b'ace cike da nadamar hakan!
Tun tana danne zafafan kalaman dake fitowa daga bakin sameer har abin ya fara kai ta
mak'ura gashi yak'i ci gaba da tuk'in kuma yak'i yarda ya sauketa,wasu zafafan hawaye ne suke
k'ok'arin gangarowa kumatun beauty cikin sauri ta sharesu dan kar sameer ya ga lagonta ko
kasawarta,juyowa tai cike da tsiwa tace ya isa!ya isa haka malam,ka ishe ni da surutai nace ka
sauke ni ko dole ne sai ka tafi da ni?
Cikin huci sameer ya amsa ta"dole sai na tafi dake,ke kanki kinsan hanyarmu ta sha ban ban in
banda k'addara!hayaniya sosai suka shigayi ya fad'a ta fad'a kamar wasu karnuka,har takai ga
ta big'e masa hannu don masifa,kan uban can!ni kika bige ma hannu?ai sameer be jira ta bashi
amsa ba ji kake fau fau ta ko ina dukanta yake kamar an aiko shi,duk da wuyar dukan da take
sha amma hakan baisa bakin beauty ya rufu ba,sai da yaga yayi mata lilis sannan ya
kyaleta,nan ne kuma tai lamo saman kujerar mota tana maida ajiyar zuciya!
Sai a lokacin ya janyo goran ruwa dake sak'ale a marfin motar ya sha,sannan ya bud'e
motar,hannunsa ya wanke kafin nan ya maida k'ofar ya rufe yata nanata astaqfirulla,shi ala dole
ya tab'a mace(kun ji sameer fa)wata doguwar tsuka ya saki yana fad'in ni dai duk iskancin mace
da makircin ta na fi k'arfinta don ni ba ta shin shaid'anu bane,in ma sune ke bibiyarki gara ki
gaya musu su barki dan nan baza ku sami waje ba,sai a bari sai an koma *'jami'a* sai a ci
gaba,yana kaiwa nan yayi saurin kai hannunsa ga cd rom d'in motar, kaset d'in qira'a ya kunna,
a hankali kake jin muryar sudais na tashi aciki,cikin sanyayyar muryarsa mara sauti haka ya
shiga raira qira'an yana wani kwantar da kai saman kujera,sannan ya tada motar yaci gaba da
tafiya!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*
_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*
61-65
í ½í²•In Devotion to yuh my Dearies:
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*
&
*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*
Duk da ba wani bacci beauty take ba amma haka tai shiru itama dai tana sauraron qira'ar da
haka har bacci ya d'auketa!lura da yadda ta makure kanta waje d'aya sameer yayi,nan da nan
ya k'ara k'arfin ac d'in motar inda ta ko ina kake iya