Showing 33001 words to 36000 words out of 59972 words

Chapter 12 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf

Advertisement

08 Jul 2025

3222

jin sanyi,shi kansa sanyin yayi masa yawa
amma don mugunta haka ya hak'urar ma kansa,can cikin bacci beauty ke jin sanyin a jikinta,
juyowa tai ta kai hannu ido a rufe tana laluben makunnin ac,d'all...taji an kai mata duka a
hannu,wani irin zugi taji hannunta ya d'auka ba shiri ta bud'e ido,kansa na a titi amma yasan
tabbas shi take kallo yace,kar ki kuskura ki bari najasa ta tab'a tsaftataccen abu in ko ba haka
ba,yanzu ki sake shan wani dukan!
K'ara gyara zamanta sosai beauty tayi har tana wani bank'aro k'irji waje ta murgud'o mai baki
tace bismillah d'an halak ka fasa,
Kallo d'aya sameer yayi mata ya k'ara sakin wani tsakin yace kaga balama,wato na dake ki
d'azu kin ji dad'i hankali ya kwanta,har da lumshe ido shine yanzu kike so jikina ya k'ara tab'a
naki ko?toh na gano ki!gaskiya ke akuya ce ko wacce harawa ci kike!God forbid! Wannan irin
rayuwa taki yarinya kamar tashin getto! Marairaice murya tayi beauty uwa mai shirin kuka take nuna kanta da yatsa tace,ni nake son ka
tab'a ni?kai kuwa kasan ni wacece?cikin tsiwa shi ko sameer ya dawo mata da amsa"ahaf ni ko
nasan ko ke wacece,ko ba kece wannan karuwar malaman jami'ar ba? wacce sunanta yayi
k'auri a wajen d'alibai kai har da malamai ko ina ka zagaya *'yar jami'a* duk mutumin banza ya
sanki!bayan wannan sanin akwai wani sani da zan miki ne?don haka ina gargad'inki in kina son
tafiyarmu ta k'are lafiya toh ki iya bakinki kuma ki nisanci zama a inda nake,bata jira taji k'ashen
maganar tasa ba ta juya masa baya har da cire gyalen data yale kanta dashi ta rufe fuskarta!
Murmushin gefen kunci sameer ya saki me cike da mugunta yace dad'in ta dai kin ji a jikinki don
haka in kunne ya ji,toh gangar jiki ta tsira,yana kaiwa nan ya basar da ita ya shiga bin qira'arsa
yana tuk'i!

Har suka isa garin minjibir beauty kwance take fuska rufe,gashi yana son tambayar ta inda zai
shiga amma zuciya tak'i barinshi,can dai da yaga ba haza dole ya k'ara d'aka mata wani
dukan,beauty dake kwance tunani duk ya gama cikata ta sak'a wancan ta kunce wance,tai
firgigit ta d'ago fuska tana cire gyalen fuskarta,dilla malam ni kar ka sake duka na ai ba jaka
bace,shiru yayi mata don yanzu bashi da lokacin biye mata haka,ina zamuyi?ya tambayeta
kansa na kalon gaba,karkato hannunta tayi tana nuna masa kwanar data yanki gefensa cikin
saurin yayi baya da jikinsa sameer can kuma ya kallota yace ke dilla ba sai kin kara kanki da ni
ba da baki zaki min magana!wani abu taji ya kawo mata wuya beauty wai shin me ya dauke ta
haka yake ta wulak'antata?kwanar yasha ya shiga tafiya a hankali don sun shigo gari baya so
ya wuce wajen!tafiya suke tayi ba tare data k'arayi masa magana ba sai ma chewinggum data

fito a jakarta ta jefa baki,ta shiga tauna, har sameer ya kai k'arshen titi beauty bata tanka masa
ba,a k'ufule ya juyo don yaga babu wani sauran gida gma inda suke sai gonaki na mutane, yace
ke wai ina zami yi ne kuma?kwai beauty ta sakar masa ji kake k'as-k'as sannan ta saki wani
kasalallen murmushi tace inda waccen akuyar take nan zaka bi!waige sameer ya shiga yi amma
sam wajen baiga wata alamar ko kaza a wajen ba balle akuya,lokaci d'aya ya fahimci beauty
bak'ar magana ta yi masa,juyowa yayi a b'ace yaga ta k'ara sakar masa wani kwan k'ato,ai bai
san sameer lokacin daya cafko hannunta ya murd'a shi da k'arfin tsiya ba,ihu sosai beauty ta
saki har da d'aga k'afa d'aya sama bayan ido data zaro waje,ji kake tana cewa wallahi baya
ne,kwanar da muka baro ne,waccan kwanar ce fa ta baya,amma ina sameer k'af yak'i kulata sai
da yaga ta ji jiki sannan yayi wurgi da hannun ya juya kan motar suka dawo baya,rik'e take da
hannun tana juya shi da haka tayi ta masa kwatance a nutse har suka isa k'ofar gidan nan tace
toh ka tsaya haka mun zo!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

66-70



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Yi yayi sameer kamar ba ze amsata ba, sai kuma can ciki-ciki uwa mai gunguni yace
toh!k'ok'arin bud'e k'ofa beauty ta shiga yi ta fita don taga alamar sameer bashi da niyyar fita,
taji yace toh sai a kama kai nan dai gidan tsoho ne ba gala ba,wani miyau mai mugun zafi
beauty ta had'e ta gyad'a kai ta fice abinta,kamar jira yake ta fito shima ya fito ya biyo bayanta,
zauren gidan suka shiga tana gaba yana biye har suka cimma tsakar gidan sallama beauty tayi
shiru ba motsin kowa sai data k'ara d'aga sautin nata fiye da wancan sannan ta ji daga can
d'akin dake kallin kusruwar gidan wata dattijuwa ta amsa!
Wana ke ji kamar muryar jikalle?

Eh tsohuwa me ran k'arfe mune!
Toh! yagana ta fad'a tana yaye tsukakken labulen dake sak'ale a k'ofar tana fad'in lalle
marhabun k'araso ciki!ta kai ayar maganar kenan kanta ya kai ga sameer wanda ke mak'ake
bayan beauty!.
Auf ashe da bak'o kuke tare!hannu baba yagana takai saman katifar da ke shinfid'e tsakar
d'akin ta janyo gyalenta ta yale akanta dashi sannan ta k'araso waje,cikin nutsuwa sameer ya
tsugunna ya gaisheta ta amsa hannunta d'auke da tabarma!
Ashe ana ganin ku mutanen birni?cikin farin cikin ganinsu baba yagana ke jefo mata tambayar!

Hmm kaji baba ai yanzun ma wajen tsoho na zo ba ke ba!tana maganar yayin da take
tallafamata wajen shinfid'ar tabarmar!
Yunk'urawa beauty tayi zata zauna baba yagana ta jefota da wani irin mugun kallo tace na bige
ki anan guraren,ke zan wa shinfid'a ko siriki na?gafara can ki ba bak'ona waje ya zauna yau ta
shi nake bake ba!"

Ba beauty ba hatta sameer se da maganar tayi masa mugun nauyi a kai!siriki kuma?nanata
kalmar yayi cike da rashin fahimta,haka nan dai ya iya dai-daita nutsuwarsa ya nemi waje ya
zaune,k'ara gaisawa sukayi nan kuma hira ta b'arke inda sameer ya ji komai game da raahin
lafiyar tsoro dake can cikin k'uryar d'aki ya samu bacci!
"Gafara dai masu gida!e Muryar wani matashi kenan wanda a tsawo bai wuce na sameer ba
ya shigo tsakar gidan rik'e da kekensa mai cike da damin harawa!
Baba yagana ce ta amsashi da gafara dai!tana kallon shi cike da nuna sanayya!
K'eeee.. suka ji ya saki keken k'asa ya shiga nuno su da yatsa yana fad'in kan uban can wazan
gani zaune kamar hajjo?
Sororo hajjo tai tana kallonsa kamar zata iya tuno shi amma ina rashin zuwanta yasa ta kasa
tuna shi!!

Ganin tayi shiru ya sashi k'arasowa ya nemi waje gefen sameer ya zauna nan ya mik'a mai
hannu sukai musabaha sama-sama amma duk hankalinsa naga beauty,baba yagana ce ta
katseshi da hannu tace kai wannan kallo haka d'an ladi kamar baka san taba?washe baki ya
shiga yi yana kai hannu k'eya yana susawa yace"ai baba hajjon ce duk ta canja tayi fari tai gyau
wallhi hala tana shan lemon birni(apple) ne?
dariya duk suka sa har da beauty!jim suka d'anyi da sigar shiru hakan ya baiwa sameer damar
kai kallonsa ga bak'ar agogon dake sak'ale a hannunshi ya duba lokaci inda ya nuna 9:30a.m
da sanyin jiki ya d'ago kai ya kalli baba dake jn gene da garu yace ina ganin baba yagana ya
kamata a tashi tsoho haka yayi kumallo mu je asibiti ko? Don kar lokaci ya k'ure mana"baki
sororo baba yagana ta bud'e baki hangam tabi sameer da kallo can kuma ta nisa tace kai d'an
nan rufa min asiri ina yabon ka sallah kar ka kasa alwala mana,mu yanzu ina mu ina zuwa wani
wajen asibiti kayan yahudu da nasara bakaji jami'an su ana kiransu likita bokan turai
ba?wannan ai sai ka saka mu zama abin fae'e a yankin nan,toh bada niba wai shiga d'akin
mayya!fad'a-fad'a,tsiwa-tsiwa haka baba yagana ke maganar kafin ta kai ga cigaba d'an lami
yayi caraf ya karb'e maganar!

Ai dama wallahi baba ni nasan da walakin goro a miya tunda na yanko kwanar layin nan naga
an kicciye mota gaban shagon sale me rake nasan cewa wa'adin tsoho yazo don na tabbatarda
wannan d'an farin(nan ya nuna sameer da yatsa)uwa aljani ba haka nan yazo ba,toh wallahi
ahir d'inka tsoho sai ya ga aure na don baza kai min haramiyar damun hatsin daya tanadar min
ba yazama na magada!jin yarda d'an ladi ke ta zuro bayani ba ko tsagaitawa yasa beauty rai
b'ace ta daka masa tsawa!

Kai dalla can kai wa mutane shiru,ashe kai har yanzu sokancin nan dai baka bar shiba?har
kana wani d'aga wa mutane murya?toh bara kuji zuwa kamar anyi an gama"


Kin yi kad'an wallahi kin yi tsararo baki isa kizo cikin sanyin safiyar nan ki d'aga mana hankali
ba,ko uwarki ina magana bata ja balle ke!
yau naga waze raba ni da d'an uwana"tana kaiwa nan a magana sai ta b'arke da wani irin kuka
mai cike da k'ara baba yagana kenan, kai kace wani mugun abun akai mata!

Ganin yadda hayaniya ke tashi sosai ga kuka da baba ta saka yasa sameer matsowa kusa
ita ya saisaita muryarshi k'asa-k'asa uwa mai rad'a ya shiga aikin lallashi! Da kyar baba yagana
ta hak'ura ta tsagaita da kukan wanda lura da hakan ya baiwa sameer damar fara yi mata
bayani! [10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

71-75



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*


Ina so kisan wani abu baba mak'asudin zuwan mu gidan nan ba don komai bane illah mu

nema wa tsoho lafiya,babu yadda za'ai muna ji muna gani mu kai shi inda zai wahala,tunda mu
musulmai ne,bisani ma wannan jikarsa ce,maganar asibiti kuma da kika baba shekara nawa
kuna zaune gida ana yin na hausa,wane sassak'e da mad'acin ne ba'a bashi yasha ba?ina ce
duk an gwada amma jikin jiya i yau,kinga kuwa bazamu zuba ido ace haka za'a barshi cikin
wahala ba dole a samu abin yi!kuma ina ganin son da zaki nuna wa tsoho shine ki barshi muje
mu jarraba na baturen ko Allah yasa a dace!


Jimm baba yagana ta d'an yi uwa mai nazarin wani abu kowa ita yake jiran jin abinda zai fito
daga bakinta,kwatsam suka fara jin k'uhul...k'uhul...k'uhul....alamun k'arar tari na tasowa daga
d'akin dake gefensu,cikin sauri baba yagana ta mik'e suka rufa mata baya sukai cikin d'akin!
Kwance suka iske shi yana yunk'urin mik'ewa amma ba hali don wani matsanancin rawa da
jikinsa ya soma va shiri sameer ya k'ara suka dashi bai jira cewar suba yadda yaga jikin tsoho
na gyargyarwa ya sungume shi yayi yayi waje dashi,haka suka k'ara d'ungumowa gaba
d'ayansu suka yo waje banda kuka da kururuwa babua binda baba yagana ke sumbud'awa"
Abakin k'ofar zaure ne suka ci karo da malam sale mai shago wanda kukan baba da ya jiyo
yasashi shigowa ba shiri,ganin yadda aka fito da tsoho ranga-ranga yasa shi shima kwarma
uban salati ya ja gefe ya tsaya,ba wanda ya iya bi ta kansa suka haura sukai waje,cikin aljihu
sameer ya fiddo key ya mik'a wa beauty nan ta bud'e motar ,gidan baya sameer ya zauna shi
da tsoho d'an ladi na k'ok'arin turo kai ciki ya dakatar dashi yace a'a ka zauna gida ka kula da
baba yanzu zamu dawo,badan yaso ba haka d'an ladi ya ja gefe yayi turus!
Juyawar da sameer zai yi ne kicib'is suka had'a ido da beauty dake gefen baba tsaye hannu rike
da mukullin mota"cikin tsawa ya furta mata" ke dalla malama ki shiga ki drivern namu kikai tsaye
akan mu kamar sanda,ba ta bi ta maganar saba duba da yadda jikin tsoho ta tsananta ta nufi
driver seat da sauri ta shiga ta kunna motar,ta nufi asibitin dake k'auyen!

Da idarsu asibitin waje beauty ta samu ta aje motar wanda har lokacin numfashin tsoho ya kasa
dai-daito cikin sauri sameer a bud'e k'ofar ya d'akko tsoho suka fito beauty na take musu
baya,cuncurundon jama'a kad'ai kake hangowa ta ko'ina acikin asibitin ga hayaniya na mutane
duk inda ka juya mara lafiya ne zaune,abinka da ba'ai saba shiga waje haka ba kafin kace me
duk sameer ya rikice ya rasa ina ma zai yi dashi,waje ya gano gefe da wata mata dake goye da
yaro ba kowa cikin sauri ya isa wajen ya zaunar dashi juyowa yayi ya kalli beauty rai b'ace yace
ki kula dashi ina zuwa kuma banda nuna hali!yana kai wa nan sameer ya sakai yayi gaba"
sakayau beauty ta bishi da kallo fuska yamutse uwa mai shirin kuka ta shiga zancen zuci"toh
wai shi wannan me ya d'auke ni akuya ko kuwa tunkiya da duk inda naje sai na bi maza?ba
takai ga baiwa kanta ansa ba ta jiyo tarin tsoho ba shiri ta katse guntun tunaninta ta nufi
wajensa ta na mai sannu!

Bai wani jima da tafiya ba sameer sai gashi ya dawo gefensa wani matashi da alama likitane sai
wasu samari suma dai cikin fararen kaya dake nuna jami'an lafiya ne,ko da suka k'araso
samarin nan cikin sauri da nuna gogewar aiki haka suka janyo gado a wani d'aki dake gefe

damu suka d'aura tsoho suka nufi can wani sashen na asibitin,biye muke binsu har suka isa
wani b'angare da hayaniya ta tsagaita a wajen,office dake ciki suka nufa muna k'ok'arin biyo su
ciki likitan dake biye damu ya d'ago musu hannu badan sunso ba dole yasa suka dakata anan!

Waige sameer ya shiga yi ko ya samu wajen zama can ya hango wasu kujeru da basu wuce 4 a
jere a k'arshe wajen ba take ya nufi wajen yazauna itako beauty ta shiga sintiri tana kai kawo a
wajen!

Har kimanin minti 30 babu alamar motsi ko fitowa daga ciki! gajiya beauty tayi da zagayen dole
ta nemi gefen wata window dake nan ta jingina tana kallace-kallacen jama'ar waje!
Can suka fara jiyo taku na tahowar mutum ido duk suka k'ura wa k'ofar sai gashi d'aya daga ciki
samarin nan ya fito hannunsa d'auke da takarda!mik'ewa sameer yayi da sauri ya nufoshi inda
itama beauty ta yo kansa tana fad'in dan Allah malama ya jikin nasa?bai iya tanka mata sai ma
kallo da yakai ga sameer yace yallab'ai dr.ya rubuto allurai da ruwa da za'a siyo,karb'ar
takardar sameer yayi k'ok'arin yi sai yaji yace dashi,a'a yallab'ai ai wannan aikin ba naka bane
kadai bayar a siyo,lummm sameer ya d'anyi sai kuma can ya wuce gaba yace muje toh wajen!


tafiya suka shiga yi har sun kai k'ofar barin wajen sameer kamar wanda yayi mantuwa ya juyo
ya kallo beauty wacce itama dai su take kallo yace toh sai ki samu waje gashi can ki zauna a
bar lek'en taga don babu abin gani kuma dai a kama kai don nan gidan HIV ne,yana kaiwa nan
yasa kai ya fice abinsa!beauty dake tsaye hannu sak'ale da k'aramar jakarta bata ankara ba taji
wasu zafafan hawaye sun fara kwaranyo mata a fuska wanda sam batasan dalilin hakan ba!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

76-80



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*

Kusan minti biyar kenan da fitar su sai gasu sun shigo rik'e sa ledoji biyu,office d'in saurayin
ya shige shi ko sameer ya dawo nan ya nemi waje ya zauna!

Kawo lokacin beauty na zaune saman kujerar ta duk'e kai k'asa tana nazarin halin da tsoho ke
ciki,
Sallama har sau biyu sameer yayi amma ina beauty tayi nisa a tunani"wasu dai anyi asarar
kud'in tara wallahi ace sallamar ma basu iya amsawa ba"furucin da beauty kenan ta tsinta daga
sameer hakan ya tabbatar mata da sun dawo don haka ta d'ago kai tana kallonsa"kafin daga
bisani ta saki doguwar tsuka had'e da tab'e baki ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya ta juya masa
gyeya! Dariyar k'arfin hali sameer ya saki mai cike da tuhuma sannan ya furzar da wani
zazzafan iska waje yace"Wato in aka ce dai akuya wallahi an gama da kai,don kuwa ita ko ina
sai ta nuna halinta sai dai in bata samu waje ba! Bai kai ga sauke lumfashinsa ba kamar wacce
aka mintsina beauty ta juyo a kufule ta shiga gyad'a masa hannu taba magana"kai malam
shiru-shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne,ko dan kaga tun d'azu ina raga maka shiyasa
kake ganin kai ka isa,toh wallahi ina yi maka kashedi na k'arshe ka fita a harkata tun kafin na
nuna maka kaina a zahiri"
A razane sameer ya mik'e tsaye ya dafe k'irje had'e da fad'in wa iyazu billahi yanzu banda
wannan munanan ayyukan da kika shahara dau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login