Showing 9001 words to 12000 words out of 59972 words

Chapter 4 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf

Advertisement

08 Jul 2025

3232

in banda murmushin nan de data k'ara cilla masa ya cab'e da girgixa mata kai don
mugunta"!har ta d'an ci taxarar tafiya sai ta waigo tace wanene office no nashi!"cikin sauri yace
kina xuwa 2floor ki mik'e shine na k'arshe se ki fad'a da k'afa biyu ki fito da......hannu beauty ta
d'aga mishi da haka ta nufi ciki gadan-gadan!.

Ab'angaren xee-xee kuwa koda ta iso jami'ar bata xame ko ina ba illah masallaci nan ta shiga
kamar yadda ta saba ta hau fito da kaya daga jakanta"batai k'ok'arin sanya wa ba se data ga
jama'an da suka shigo suma dan buk'atun su sun fita sannan ta shiga k'ok'arin sauyawa daga
doguwar riga ta atamfa dake jikinta da dogon hijabin ta har k'asa xuwa wassu shegun k'ananan
kaya riga da wando gara ma rigan iya kar kwiwace!gyale mara nauyi ta yale a kanta tare da
k'ara 'yar powder da jan baki a bakinta"kafin kace me tsaf ta gama canja ma kanta halitta baka
ce ita ka gani d'axu cikin kaya na mutunci ba"!me da wad'ancan jaka tayi nan ta kammala tsaf ta
fito ta nufi lecture hall nasu kamar yadda ta kira aka sanar da ita a inda xasu yi ranar"jama'a ke
ta shiga ciki hakan ya sa itama tai parkin car nata gefe ta xari wani k'aramin jotter na ta da biro
se wayoyinta a hannu ta fito ta nufi ciki waje ta samu ta xauna kamar yadda ko wane d'alibi ke
nema"bata wani jima da shiga ba se ga wani matashin malami ya shigo captain na biye dashi
da kayan karatunsa"saman stage ya tsaya nan kaji ajin yayi wani irin tsit kamar ruwa ya cinye
saboda shiru da akai"!kowa mamakin da yake toh ina prof KAS d'in bashi xe shigo mana ba?ko
de an canja tym table ne?ko kuma yana da wani uxuri babba?amma kuma ai shi ba ma'abocin
fashi bane"?"!



📓15 *'YAR JAMI'A*📓📓
_By_ *HERWWERH JIDDERH*

*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*

💕

Washe garin ranar beauty kwance take tana maida ramuwar gajiyar jiya ummah ta shigo ta
sameta"tashinta ta shiga yi sanin tabbacin cewa batai ko sallar asuba ba"a hankali beauty ta
shiga bud"e idonta"firgit tai ta mike xaune ganin ummah duk'e kanta"murxa idanu ta fara yi tana
fad'in ummah ina kwana?ina kwana kuma kin yi sallah ne? Emm emmm ummah nima bansan
lokaci yayi haka ba fa?oya toh maxa tashi ki shiga bayi abu har past 7;00a.m ace baki sallan
asuba ba anya kuwa hajara kina son hutu cikin kabari kuwa"?fuska ya mutse beauty ta fara
kallon ummah taji an fara maganan lahira wanda sam baya cikin abinda beauty ke so ana
magana"hannu ta kai ta dod'e kunnenta ta mike ta nufi bayi"tsaye ummah tayi tana dubanta har
ta rufe kofan sannan ta nisa tace oh ni kam Allah de ya shirya wallahi"ace yarinya kamar tashin
gidan arna kwata-kwata lissafinta ba ibada in anyi magana shi kuma ubanta ya chafke da
bala'insa shi a dole me san 'ya"tana sambatun ta ummah da haka tayi waje".
Har ta k'arasa d'akinsa nan ta iske dady xaune gaban mirrow yana taje kanshi daya ke daga
wanka ya fito"karasawa tai gabanshi ta kai hannu ga Cumb nashi nan ya saki mata ta shi
sharce masa kan a hankali tana shafanshi da hannunta cike da kulawa".ganin yadda take yi ne
cikin burgewa daddy ya lalubo phone nashi dake aje saman mirrow d'in bata ankara ba taji
k'es-k'es-k'es dady na snapping nata d'agowan da tai tana dariya ne ya k'ara yi mata wani se ya
xamana duk yafi ko wannen ciki kyau"wow dear luk wannan pic d'in yayi kyau"duk'owa ummah
tai itama tana kallo nan ya lakato mata hanci da kan phone d'in dady yace dix pic will be my
new screen saver".dariya ummah tasa tare sa kamo hannunshi da alamun ya mik'e haka ba
musu ya ko tashi ya biyo bayanta har gaban wardrobe d'insa nan ummah ta shiga nema masa
kayan sakawa"cikin lafiyayyar shadda wacce tasha aiki ummah ya shirya dady ga hula ta kafa
mai akai"ya fito fes"ware hannu dady yayi tako fad'a jikinsa ya manna mata peck a kuncinta
yana fad'in dear banga macen data kaiki iya kula da namiji ba"kinsan kome na farin ciki
naa".how i wish others will come and copy from u my dear"tana murmushi ta d'ago kai tace ok
kar kai late maxa muje kai breakfast sarkin xolaya"har ta juya da xummar fita dady ya k'ara riko
hannunta cak ta tsaya haka ya k'ara so gabanta ya wani langwabar da kai cikin nata yace Trust
me dear Allah kin iya kome akaina".yanda yayi maganan ma abun dariya ya bata kamar wani
k'aramin yaro nan umma ta saki dariyanta a fili"sosai suke dariya haka ta rike me hannu tana
cewa ok i trusted your words swytynah let go".
Xaune take ummah gefen dady inda yake cin abincinsa ita ko tana taya sa hira!sakkowqn
beauty suka hau ji daga saman matattakala tana ta rera wak'anta na "shakira i'm live"har ta
k'araso dinning d'in da gudu ta nufi dadynta ta fad'a kanshi har se da kujeran ya d'an ja
baya"cikin sauri ummah ta mike ta daka mata tsawa"ke meye haka?bakki da hankali ne?hannu
dady ya d'aga mata da xummar ta yi shiru amma ummah sam tak'i jinsa"baxa ki tashi daga
kansa ba wai?kaga shashashar banxa?haka ake gaisuwa a garinku?ni na rasa wallahi yaushe
yarinyar nan ta xama haka?
A hankali beauty ke raba jikin nata dana dady ga hawaye nan shar ya gama cika kuncinta"nan
ta d'ago kai tana kallon dady can ta nisa cikin kuka tace"dady u see ko?kuma bara kace komi

ba ?in na nuna caring akanka ai min fad'a?in nayi ignoring mayi maka magana kai kuma kace i
hated u?so ya kuke so nayi?bata jira maganan shiba ta juya baya da gudu rike da karamin jaka
a hannunta se file nata tayi waje tana wani kwarma ihu kamar wacce aka daka".cikin sauri dady
ya mike ya biyo bayanta har wani tuntube yake yi a kofa yana kiran beauty?beauty?pls beauty
nah wait kinji ba haka bane?amma ina kafin ya kai ga cimma parkin space tuni beauty ta fixgi
motanta tayi waje" dafe kai kawai dady yayi cike da takaicin abinda ya faru"shi ya rasa ma me
xeyi wa ummah ya huce"ga wani irin gudu da yaga 'yar tasa nayi"Allah yasa de kar wani abu ya
same ta"tunani ne ya fad'o masa hannu ya saka cikin aljihu ya xaro waya nambar beauty ya
shiga nema amma gashi yana ruri tak'i d'auka"ran nan nashi gaba d'aya ba dad'i".cikin murya
k'asa-k'asa yaji kamar daga sama ance dady ina kwana?waige ya kai gun se lokacin ya tuna da
jiya fa cikin dare yayi bak'o d'an amininsa".murmushin dole ya k'irk'iro ya jefa masa nan suka
gaisa yake tanbayarsa akan mahaifin nasa".lura da yanayin da dady ke cike yaso yi nan ya ke
tambayar dady ko lafiya?ehh toh ka gane dama beauty ce ta fita da mota a guje kuma bana son
tana irin wannan gudu kar wani abu ya sameta gashi ina ta kiran nambarta tayi fushi tak'i
picking call na"bansan ya xanyi ba".cike da mamaki matashin ke kallon dady yadda duk ya
damu akanta"ajiyan rai ya saki kafin yace ok dady ka sake trying layin nata mana"no baxan
sake ba nasan bara ta d'aga ba i know her se de ko na baka nambar se kai ka kira tunda bata
san namber naka ba"?jinjina kai yayi nan ya xaro phone nashi ya shiga karb'ar lambar".kira biyu
yayi mata amma duk da haka batai picking ba".idan ran dady yayi million toh ya gama b'aci
k'arfin hali kawai yayi yace masa ka wuce wajen aiki kawai ba damuwa bari na shiga ciki"yana
kaiwa nan ya nufi ciki".
Cikin mota ya shiga yana k'ok'arin tada mota yake wata xuciyar ke raya masa ya k'ara gwada
layin mana ko xe samu"a hankali ya danna nambar"kara yake yi sosai har gashi ya kusa
katsewa se jiyayi karaf an d'auka".
Toh me ma xan ce mata?abinda ya fara sak'awa a rai kenan!hello who ix on d line?beauty tai
maganan cikin fad'a"jin yanayi da ta karb'esa yasashi watsa mata magana shima cikin
fad'a"STOP D CAR"I said STOP IT" keeeee... kake iya jiyowa alamar tsayiwar mota cikin
waya"wata ajiyan rai me k'arfi ya saki jin haka kafin ya nisa' jin shiru ya biyo baya ne yasa ya
d'an katse shirun tattausan voice nashi me cike da ixzah ga haiba ya fara riskan kunnen beauty
inda ya fara da"pls take it easy mana wannan speed da kike gudu dashi haka yayi yawa"ko
bak'ya son ran kine?so in bak'ya so ki aje shi akwai masu so"yanxu ina so ki tafi a hankali har ki
k"arasa inda xaki kinji beautyn dadynta".?tsintar kanta tai da amsa shi da toh"yana jin haka
kuwa ya kashe wayan yana wani murmushin jin dad'i ko ba kome ya san dady xe ji dad'i in ya
fad'a masa ta rage gudun".
Abangaren angel kuwa ita abin ma mamaki ya bata wai ya akai ma ta d'aga kiran unknown
number ita da bata haka kuma har ake bata command tana amsa"can kasan ranta kuma tace
no ba command bane may be ya hange ni ina gudu ne yaga baxe iya bari na naci gaba da
hakan ba se yayi protecting na"but ina ya sami number na kuma waye ma?tambayar kanta ta
shiga yi amma ta kasa samo amsa tuna cewa akwai aiki babba da xata gudanar yau a scul d'in
yasa ta tsaida tunani ta lalubi wayan nata ta kallon number d'in kafin ta shiga contact nata tai
saving no da *MY PROTECTOR* haka tai saving badan wani abu ba se dan kariyar da take
kawowa ya bata a yanxu".mukullin motar ta tayar ta shiga tuki abinta a hankali kamar yadda
*PROTECTOR* Ya nema har ta isa bakin kofar JAMI'AR.

📓19 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE


Da isarta gida ummah ta tarar zaune a falo rik'e cajbi tana lazumi se gwaggo atika da ke zaune
k'asan kafet tanai mata gyaran k'umba(farce)"--daddy wanna beat me bcox i gonna
party"--shine baitin wak'an dake d'auke bakin beauty da haka ta shigo falon tana ta faman
gyad'a kai uwa wata shurwa"gaba d'aya juyowa sukai suna bin ta da kallon mamaki"har
tsakiyan falon ta k'araso rik'e da waya a hannunta se airpiece data sak'ala a kunne"
Hannu tasa ta zare shi a kunne sannan ta k'araso gaban momyn a kasalance ta zauna
gefenta tace umma na dawo".toh sannunki"ummah ta amsata a tak'aice"sanin halin ummah ya
sa ta mik'e ta nufi sama abinta" hooo hooo hoo!!Allah de ka shirya wallahi yanxu kai magana
cibi ya zama k'ari"cewan ummah tana me allah wadai da hali irin na 'yar tata!"ameen de gwaggo
atika dake duk'e ta fad'a".
Da shigarta d'aki ruwa kawai ta iya watsawa nan ta haye gado hannu d'auke da file
nata".zama tai a tsakiyan gadon nan ta shiga bud'e file d'in a hankali tana nazarin sunayen data
gani a ciki"gefe guda kuma ta janyo wayanta ta shiga laluben number datai mata aciki".sai da ta
kira lecturers har tara(9) aciki"abin jin dad'in sai gashi duk 'yan kamun ludayi ne kowannen su
yayi na'am da batu na beauty"dan Allah ya bata baiwar iya sarrafa harshe sosai".wasu a ciki
kuma koda tai saving number d'insu a phone nata se ta lura da suna chart ai ko nan da nan ta yi
musu magana suka ko biye mata(abin nema ya samu).kamar yadda malam umar ya sanar da
ita cewa duk halayensu d'aya ne na bin mata in banda dattijon nan prof.KAS se ko gashi hakan
ne". Ko me ta tuno kuma se ta shiga ci gaba da binciken file d'in wanda har ta k'arashe bata
gani ba"!kallo ta kai ga madubin dake lik'e a bango a d'akin sannan tace toh in de haka ne
wannan file d'in is incomplete tunda ban ga number sir.prince ba kamar yadda naji zee-zee ta
ambaci sunansa d'azu"toh ko de shi ba na faculty namu bane borrowing d'inshi akai daga wani
deparent din?any away zuwa dare naji daga bakin dattijon can".ruri wayan ta ya d'auka tana
dubawa ko taga saleem ne wani d'an abokin dady ne wanda suka had'u ran birthday nata "da
murmushi d'auke samalan fuskanta ta amsashi a waya nan hira ta b'arke tsakaninsu har kana
iya jiyo dariyanta sosai a wayan da alama de hira yayi dad'i" a karshe ne ya ke nuna mata yana
son had'uwarsu a wani guest house na mahaifinshi ba musu kuwa ta amince da buk'atan nasa
don dama haka take so badan komi take son mu'amala da saleem ba se dan ko a 'yq'yan masu
hannu da shuni su kansu suna fad'ar kud'i da jan aji na saleem se de shi matsalarsa d'aya bin
mace me aji".bayan ta katse wayan ne beauty tai wani d'an k'aramin shewa cike da murna tana
fad'in ko banza de duniya zata sanni da kai kuma se na tabbatar da na raba ka da kowace
mace se ni d'aya tilo".

â—†Wannan kenanâ—†

_Daren ranar:_
Zaune yake a d'aki saman kujera ya d'an kishingid'a kai kamar me nazarin wani abu se yaji an
bud'e k'ofan nan hankalinshi ya koma ga k'ofan dan ganin waye" dady ya gani ya shigo cikin
manyan kanya"da saurinsa ya mik'e zaune cike da kunya ganin yadda dady ya same shi daga
singlet se short"kai sunkwi yayi yana d'an sosa k'eya har dady ya k'araso ciki". Ina wuni daddy??ya fad'a da fara'ansa.lafiya lau sameer ya zaman kad'aici da kuma aikin
naka hope de baka facing wani problem ko? Eh daddy babu ko d'aya se de wallahi daddy garin
nan ya cika zafi".da dariyarsa dady yake kallonsa jin maganar da yayi yace toh in banda abin
sameer ai ko ina kake da air conditioner kaga de d'akinka,falo cikin mota kuma na tabbata office
d'inka ma da akwai"ido ya d'an kaikaici daddy da kallo da sigar na'am da batun nasa yace eh
daddy amma weathern mu yafi na nan dad'i d'azu dawowa na ai ina tsakar gida shan iska"!
Jin yadda sameer ya kira tsakar gida hankalinsa a kwance yasa daddy sauyawa gami da
neman guri ya zauna"haka shima sameer ya nemi gu ya zauna".
Emm sameer"dady ya kiraye shi" dama ina so mi wata magana da kai".kana ji ko d'ana?eh
sameer ya fad'i yana me k'ara gyara zamansa sosai" ka gane dama ba wani abu bane'illah kaga
ita beauty wallahi mace ce wacce bata son ganin jama'a hasali ma bata son jin hayaniya ko
wanin bak'uqar fuska"tun tashinta haka take yanxu zaman ka a waje ze iya janyo min matsala
ko ma yasa ta fushi"kasan rigimar yara"shine nace wai ko in ze yiyu kawai se kana zaman ka
d'aki ko falo koma kai fitanka wajen shak'atawa tunda muna dasu anan kam da yawa"kaji d'ana
na kai na"murmushi dady yake haka shima sameer ya me da me cike da mamakin maganan
dady yace ba komi dady zan kiyaye"
Har suka gama hiransu dady ya yi me sallama ya fita amma sam sameer hankalinsa ya kasa
kwanciya tunaninsa d'qya maganar dady"yanxu dan yarinya k'arama bata son jama'a se dady
ya hau ya zauna bama yayi mata fad'a ko neman hanyar gyara ba"toh amma kuma ai ummah
ba k'arama bace bara ace tana da k'aramar yarinya kode jika ce a gidan dady ke nuna mata so
haka?hala shiyasa da na nuna ina son mu gaisa da ummah dady ya hana?Ganin bame amsa
masa tambayoyin nasa yasa shi tashi ya rage wutan d'akin yabi lafiyar gado".






📓18 *'YAR JAMI'A*📓📓
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*


kamar yadda kullum wajen yake cike da jama'a toh yau ma de haka"bata wani b'ata lokaci ba

da isarta wajen ta nufi wajen waiters d'in abincin wajen ta k'arashe siyawa gaba d'aya kamar
yadda ta saba ta kuma umarce sa da yau ma duk wanda yaxo a bashi abinci kyauta a kuma
sheda masa da *'yar jami'a*ta riga ta biya kud'in,take away tayi itakam dan cunkoson wajen
baze barta ta iya cin abinci wajen ba"ta fito a wajen kenan ta waiga ido a car nata me xata
gani?wani car yayi blocking nata a wajen"cikin b'acin rai ta dawo cikin restaurant d'in rik'e da
key nata ta na gyad'awa!
Waiter! Waiter ta kira sunan a tsawace"fahimtar muryan wace yasa shi saurin fitowa a wajen
nasu rik'e da serving plate yayo wajen ta yana fad'in hajiya wani abu kike so"?
Wani kallo ta wurga me cike da tsiwa tace wani blind man d'in ne mara ganin komi yayi wrong
parkin a waje?cike da rashin fahimta waiter ke kallonta can ya nisa yace wallahi hajiya ban sani
ba amma bari na tambaya"duk abin nan da ake jama'an wajen naji abin ka da d'alibai da son
gulma"se k'us-kus suke suna tambayan juna ko de wannan ce 'yar jami'an da ake fad'i?wasu ko
na cewa ai kam ta cika sunanta da gani akwai naira se de ba tarbiyya".ganin ze b'ata mata
lokaci a gun yasa ta sauke wani gauran numfashi ta kallo shi tace look waiter kayi saurin nema
min blind man d'in da yayi min blocking ma mota na ina jira a waje".tana kaiwa nan ta fice"
Cikin sand'a waitern ya lek'a waje ko ze gane motan waye"ai ko da alama ya fahimci me
ita"rik'e baki yayi cike da mamaki na yadda ze je ya samu sir. prince yace gaya masa sak'on da
aka bashi".
Waige ya hau yi gefe ai ko can gefe ya hango wani student wanda akasari kullum shike rik'e
da jakan sir. prince inde xasu shigo wajen da saurinsa ya k'arasa wajensa ya d'an tab'o shi da
hannnu"dan Allah malam minti d'aya yayi maganan yana matsawa gefe ba musu kuwa ya taso
yaxo wajen shi yace ok ina jinka"dama kaga motan sir. ne a waje kuma ya rufe ma hajiya
hanyar fita shine nace toh ko za kai mai magana ya d'an janye"ido d'alibin ya zaro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login