Showing 54001 words to 57000 words out of 59972 words

Chapter 19 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf

Advertisement

08 Jul 2025

3227

da ta tabbatar da an rufe darasin d'alibar gefenta na shirin tashi
rik'o hannunta tayi ta zaunar da ita,hak'urin abinda ya faru a baya beauty ta rok'a tare da nuna
nadamarta akan hakan,da ya ke yarinya ce mai sauk'in kai nan take ta yafe mata,su beauty dai
har da karb'ar lambar waya kafin su rabu!
Kayan karatunta beauty ta had'a itama ta nufo waje da shirin fita inda anan ne kuma kowa ya
fahimci wace acikin hijabi sakamakon shigowarsu ba d'alibai kamar yanzu da yawa kafin kace
me,cece kuce da gulmace-gulmace suka fara yawo,kowa na tofa albarkacin bakinsa,wasu dan
tsabar gulma har lek'e suke dan tabbatar da abinda suke zargi,ganin haka cikin sauri beauty
har tana tuntub'e haka ta fito a ciki ta nufi bayan theater kamar yadda sameer ya shaida
mata,can gefe ta hango motarshi don haka ta nufi wajen,tana k'ok'arin bud'e motar taji kamar
daga sama an kirs sunanta cikin kid'ima ta juya me zata gani? K'unyar nan da suka sameta
wani lokaci a baya a stop and chop har sukai mata tayin shiga k'ungiyarsu,take suka shiga nuna
mata wani mugun salo suna kashe mata ido,bata jira wani abu ba tai azamar bud'e k'ofar kamar
wacce aka wullo ciki haka ta fad'o ta rufe k'ofar tana ta faman mai da numfashi!


K'arewa 'yan matan nan kallo sameee yayi tas sannan ya dawo da kanshi wajenta,ita dai kallon
nata yayi bai iya ce mata komai ba ya tada mota ya bar wajen,cikin nutsu haka yake tuk'in
motar yana zagaya makarantar har ya kai ga muhalin da yake son zuwa,waje ya samu ya
tsaida motar ya fito a ciki sannan ya sunkuyar da kai yace mata fito,haka beauty ta fito don ta
fahimci inda ya kawota ta bi bayansa suka nufi ginin dake gine a wajen,basu tsaya ba sai da
sameer ya kai ga office d'in Prof KAS,nan yayi sallama aka basu izinin shiga suka shiga,zaune
suka sameshi ciki kamar kullum yana nazarin littafi,gaisawa sukayi cikin girmamawa amma
fuskar beauty ta kasa b'oyuwa a gareshi,duk da sameer ya bashi labarin komai da safe,don
haka sai bai yi mamakin ganin 'Yar jami'a cikin wannan shiga ta kamala ba,sameer ne ya juyo
cike da izzah ya watso mata wani irin mugun kallon da ya sa tuni tasha jinin jikinta,sunkwi da kai
tayi kafin yace baki iya bada hak'uri ba ne? A sukwane beauty ta zube k'asa ta shiga rok'on
Allah prof ya gafarta mata abinda ya faru a tsakaninsu,cike da mamaki prof yake girgiza kai na
jin dad'in Alk'awarin da sameer ya d'auka masa na cewa sai ta durk'usa da k'afafunta ta nemi
gafararshi,yau ga 'yar jami'a k'asan gwiwoyinta,haka dai prof ya amsa mata sannan yayi musu
nasiha sosai game da zamantakewar aure,bayan nan kuma suka fito zuwa gida inda a kan
hanyarsu na koma gida ne sameer ke tambayarta akan 'yan matan da ya gani,beauty bata
b'oye masa komai ba haka ta kwashe labarinsu ta bashi,tab'e baki kawai yayi da jin haka ya ci
gaba da tuk'insa!


Haka rayuwa ta ci gaba tsakanin beauty da sameer kullum shi yake kaita makaranta kuma ya
d'akko ta tun jama'a basu gano komai tsakaninsu ba har suka gano,bayan da kuma ya nema
mata malamin islamiyya kullum bayan sallar magriba yake zuwa nan gida suyi karatu,haka
takan ware wani yanki na dare tana bitar karatunta,duk da babu wata kafa tayin anfani da waya
gashi yanzu zee-zee ta daina shugowa makaranta kuma sameer ne ke kaita ya kuma dawo da

ita babu damar ziyararta don ba wani hira ke shiga tsakaninsu dashi ba!a b'angaren ummah
kam abin ba'a cewa komai don kullum da had'i na musamman da ake wa beauty hakan yasa
duk ta ciko tai wani haske abinta!

A kwana a tashi ba wuya, yau ya zama ranar da su beauty zasu farar jarabawar k'arshen
zangon karatu (wato 2 semester exams),tun safe ta gama shirinta tsaf,haka suka tafi a mota
tana ta bitar karatunta sosai sameer yake yaba kwazo irin na beauty,kullum haka take fama da
wannan karatun indai zasu tafi don ranar da bashi da aiki a jami'ar dole don ita yake shiga,da
haka har ta gama jarabawarta!
[10:26am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

181-185



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*

Wayewar garin yau ta kasance asabar,sameer na zaune saman kujera cikin d'akinsa daga shi
sai singlet da short yana zuma revenge game hankalinsa sosai ya raja'a a game d'in yaji
knocking,k'afa ya d'na buga k'asa da alamun rashin son tsayuwa a game d'in sannan ya danna
pause ya mik'e kanshi tsaye ya nufi bakin k'ofar don yasan bazai wuce Ali driver bane da yake
jininsu yazo d'aya yanzu kusan kullum suna tare a d'aki yana masa tad'i,hannu yasa ya bude
k'ofar lokaci guda kuma yana fad'in you are late... bai iya tsaida numfashinsa ba karaf idanunsa
suka sauka akan beauty dake tsaye cikin kamala hankalinta naga hijabin da take 'yan
wasanninta dashi,jin an bud'e itama yasa tai saurin d'ago kai,sak'onni suka fara saukarwa
junansu ta ido cike da mamaki,har wani kyarma jikinta yake sanin bata tab'a ganin sameer cikin
yanayin irin haka ba yasa tayi saurin kai hannu fuska ta rufe tace kazo dady na kiranka!tan
kaiwa nan da gudu beauty ta ruga ciki cike da jin kunya,kamar wanda aka tsayar sameer ya bita
da kallo har ta shige ciki sannan ya maido da dubansa anan murmushi ya saki mai cike da
d'unbin tambaya yana susa kai,komawa ciki yayi ya zuro jallabiya a sama sannan ya fito!

Kwance beauty take saman cinyar dady yana wasa da gashin girarta,inda ummah na gefensu
zaune tana binsu da kallo,sameer yayi sallama fallon ya shigo kai k'asa ya k'araso ciki,gefe ya
tsugunna ya gaishesu kafin nan dady yayi masa iso daya zauna a kujera!bayan ya zauna ne
dady ya kira sunansa a hankali sameer ya amsa shi cike da ladabi,cigaba dady yayi da
magana" Dama na kiraka ne badan komai ba sai dan na ji meye shirye-shiryenka game da
beauty nah saboda a halin da ake ciki ta gama jarabawa kuma kamar yadda mahaifinka ya
shaida min da zarar ta gama zaku tare,wannan shine mak'asudin kiran naka!
Eh dama dady ina shirin da nake nayi sallah azahar dama na shigo nan domin na sanar maka
akan cewa sati mai zuwa zamu wuce abuja tunda ranar asabar mukayi passing out na bautar
k'asarmu, cewar sameer da har kawo yanzu kansa na duk'e k'asa!jin jina kai dady yayi sannan
yace toh Allah ya kaimu lokacin!ummah ta amsa shi da ameen,shiru dai beauty take duk jinta
take wani iri tun bayan shigowar sameer wanda kawo yanzu hira suke tayi a tsakaninsu banda
ita can taji dady ya lakato hancinta yana fad'in yanzu zan huta da rigima,sai kije can kiyi ta
masa shagwab'ar taki!cuno baki gava tayi uwa mai shirin kuka tace dady ni d'in ko?yadda tayi
maganar a shagwab'ance yasa dukkansu sakin wata dariya,sameer ne ya mik'e yana k'ok'arin
barin waje dady ya kira sunansa,har lokacin dariya na d'auke saman fuskarsa yace tsaya ta
biyo ka can ku bamu waje muyi magana da mahaifiyarku!hannu yasa dady ya shiga d'agota
tana nok'e kai wani kallo da ummah ta watso mata yasa tuni tasha jinin jikinta tayi tsum ta mik'e
tana wani cuno baki gaba ta bishi sukao waje!

Tafiya yake sameer tana biye dashi har ya shiga d'akinsa gaban gado ya samu ya zauna ya
barta anan tsaye,ganin bai yi mata tayin zama ba yasa itama neman waje gefe k'ad'an dashi ta
zauna har lokacin hannunta na rik'e da gefen hijab d'inta tqna 'yan wasanninta dashi!
Wayarsa sameer ya janyo yaci gaba sa game d'inshi wanda a zahirin gaskiya kana ganinsa
kansan hankalinsa da inda ya raja'a yana cikin haka yaji an masa game over,take ya saki wani
guntun tsaki yayi cilli da wayar saman gado,sai kuma shiru ya biyo baya!ganin wannan shine
karo na farko da masoya biyun suka tab'a keb'e kansu sai ya zamana fargaba ta mamaye
su,k'arfin hali sameer ya d'anyi ya katse shirun nasu da cewa?kin yi shiru kamar bakya
magana?ganin yadda yayi maganar cike da izzah yasa ta maido masa amsa dai-dai da
tambayarsa"ai naga wajen daga ni sai kai kar nai magana yau ma ya zama laifi,shiru sameer
yayi maganar ta d'an so ta dake shi don ya fahimci inda ta dosa haka ya ci gaba da magana
yana fad'in"ai yanzu kin girma baran dake ki ajiki ba sai dai a zuci?baki bud'e beauty ta juyo
tace a zuci kuma?ai dad'in ta dai ita zuciya ba'a ganinta bare ka illata min ita"har wani yamutsa
fuska take yayin maganar"wanda hakan ya baiwa sameer damar sakin wani guntun murmushi
sannan yace ni ko a gani na kafin na kai hannu jikinki zuciyarki na fara kaiwa,domin idan baki
manta ba ranar da kika fara shiga lecture a jami'a bayan kin gama kin shiga econs faculty
wanda har ki ka fad'arwa wani kyakykyawan matashi wayarsa,alokacin basarwa kawai nayi na
wuce sanin cewa dana jima tsaye zaki iya suma don azabtaccen kamun da nai wa
zuciyarki,haka ne?yanda yayi tambayar yasa beauty tsuke fuska tamau tamkar bada ita yake
ba, tabbas ta tuna yadda taji lokacin da tayi karo dashi don har tana iya kwatanta kyawun
fuskarsa a idonta!dariya sameer ya soma sosai ganin ya gama gano lagwanta,da haka kuma

sannu a hankali hira mai k'arfi ta fara shiga jakanin masoyan biyu,damar da sameer ya samu
ne yasa shi labarta wa beauty abinda ya faru cikin satin inda ya shaida mata cewa an kori
malam umar daga jami'a sakamakon wata sabuwar d'aliba da yayiwa ciki,iyayenta suka k'i
yarda sannan ya sanar mata yasa an chafko principal tare da discipline master yanzu haka
suna hannun jami'an tsaro kafin a tura su kotu!
Shiru beauty tayi tare da juyar da walwalarta zuwa fushi,tausayi tsagwaronsa kake iya hangowa
a idanunta ga wani mak'alallen hawaye dake shirin zubowa!
Take sameer ya dawo gabanta ya tsugunna had'e da tarba hannunsa a fuskarta yayi sauri
tarbar hawayenta a hannunsa,a hankali ya shiga share mata yana lallashinta,sai daya tabbatar
da samun nutsuwarta sannan ya tallabo kumatunta ya shiga magana"Ban yarda a gaban idona
ko abayana ki zubar da hawaye ba,kamar yadda ban yarda ki sake wata rayuwa nan gaba ba
tare da ni ba, a baya na jahilci kai na game dake ashe abin ba haka yake ba,shiyasa a kullum
nake d'aukar abinda ya faru akanki matsayin k'addara a gareki,a kullum ina godewa Ameenu
don ya zamanto aboki na gari shine yayi ta nuna min yin hak'uri da juriya don samun alkhairin
abu,yanzu princess d'ina gani tsugunne gabanki ina neman yafiyar laifina!
Da jin haka beauty tayi saurin rik'o hannayensa ta shiga yi masa nuni da ya tashi amma sam
sameer ya k'i ala dole ta iya furta masa ta yafe!


godiya sosai yayi mata sannan ya shiga yi mata nasiha"inda aciki yake cewa" hajara yau na kira
sunanki akaro na farko ba dan komai ba sai dan na sanar dake abinda jami'a ta k'unsa,ki sani
ita jami'a da aka kira sunanta mahad'ace ta kowanne irin abu hala mai kyau ko akasin
haka,muhalli ne na kazo nazo da mutumin kirki da na banza duk zuwa suke kuma kowa da
manufarsa,yawancin iyaye ko jama'ar gari sukan kawo cewa a jami'a ko wane masha'a da
alkhaba'i ke faru,wanda ba hakan take ba,tarbiyya ana fara tane tun daga gida,rashin samun
kyakykyawar tarbiyya kamar wata k'ofa ce na bud'e b'arna ga al'umma,kinga wasu matan sukan
yi anfani da jikinsu,wasu kuma suyi an fani da kud'i haka ma daga mazan yake shiko malami
buk'atarsa d'aya kuma da ya samu toh ya wuce wajen,amma kinga duk da haka akwai na Allah
wad'anda a komai nasu tsantsar gaskiya da rik'on amana suka saka a gaba,kamar dai Prof
KAS,saboda haka na yanke shawarar canja miki jami'a sakamakon fahimta da nayi yanzu kin
kasa sakewa da nan d'in,mutanen ciki kamar dodonni kike ganinsu,sanadin canjawa da kikayi
kina ganin kamar kowa na miki kallon 'yar jami'a ta baya,bayan mun koma abuja zaki ci gaba da
zuwa jami'a kuma karatu zaki yi har sai kin gaji tun da dai matar tawa ta kira kanta 'yar
jami'a!duka na wasa beauty ta kai masa yayin da yayi saurin gocewa yana dariya!jan hankali
sosai sameer ya yi mata kafin ya canja labarin zuwa yadda shagalin dinner d'insu zai kasance
wani satin!
[10:26am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

186-190

💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Kome aka sa wa lokaci toh alal hak'ik'a sai yazo,yau take asabar wanda shirye-shiryen
tafiya tsaf sun gama had'uwa,a inda dady yayi musu jagoranci,ali driver ya kai su airport suka
wuce abuja,ko da suka isa can sameer ne yayi wa dadynsa waya aka zo aka d'auke su,sai dai
ummah tuni ta gama tsara inda zasu sauka gidan babbar aminiyarta inda a can ne 'yan uwanta
da abokan arzik'i zasu taru,dole ba don yaso rabuwa da beauty ba sameer ya sauke su acan
kafin ya wuce gida,bayan isarsa gida ne sameer ya iske ameenu da tun ranar litinin ya taho don
ya shirya masa yadda dinner zata kasance,wanda ya tarar tuni an gama komai lokaci kawai ake
jira!

_8:00p.m(na dare)_

Dandazon motoci ne na alfarma kana ganinsu kaga zallar ajiyar naira aciki ke ta faman
tururuwar shigowa gidan can tsakiyarsu wata doguwar mota ce bak'a tasha wanki sai kyalli take
wanda da alama ango ne aciki,haka suka jero suka yada zango a tsakar gidan,yadda
abokansa ke fitowa daga motoci cikin kaya na alfarma wanda suma dai sukai ankon shadda
blue wanda ita kad'ai zai gaya maka cewa bikin manya ne,hira da dariya kawai kake iya jiyowa
ta kowane yanki,sameer dake cikin mota zaune ne ya fito a tare wani irin ihu suka sake ganin
ango yasha wanka na had'uwa shadda black ce sanye jikinshi tasha zubin aiki golden colour
d'an senegal,sai hula da takalminsa duka baki,hannun nan sanye da agogo itama golden,tattare
a lallausar farar fata irin ta sameer abin dai ba'a cewa komai,zagaye shi suka zo sukayi kowa da
irin tashi salon tsokanar can ameenu ya lek'o ta cikin mota da yake shi ya tuk'o sameer yace
ango lokaci na tafiya fa akira amarya ko naje na fito da ita!wani kallo sameer ya wurga masa sai
kuma can yace toh ai sai kaje ta fito da ita mu gani,gaba d'aya waje aka sa dariya wasu na
fad'in jealousy!! Abin shina sai ya dawo yana bashi dariya dole ya zura hannu cikin aljihu ya
fiddo waya ya shiga laluben lambarta,bugu biyu ta d'auka nan ya shaida mata zuwansu,ko me
ta fad'a daga d'aya b'angaren ya bata amsa da ok my princess;da haka ya kashe wayar aka ci
gaba da hira ana jiran k'arasowarsu!

Wani lokaci kad'an bayan wannan hayaniya ce ta 'yan mata had'e da gud'a kake jiyowa wanda
duk dangin ummah ne na yola da ta sanar dasu bikin suka xo sai kuma 'yammatan gidan da
suka fito ga wani k'amshin turare daya lullub'e gidan tun bayan fara fitowarsu,inda 'yan matan
amarya suka sanya beauty a tsakiyarsu duk kan ninsu sanye da anko,baka iya hango komai
daga shigarta,tafiya suka shiga yi basu zame ko ina ba sai jikin motar sameer inda suka zagaya
suka shigar da ita sannan suma suka nufi sauran motocin suka shiga,duk wani zumud'i da
rikicewa sameer ya gama yinshi burinsa kawai yayi ido hud'u da gimbiyar tasa don haka cikin
sauri shima ya bud'e motar ya shiga" watabarakallahu ahsanal khaliqeen"abinda sameer ya iya
fad'a kenan jikinsa na kyarma ya matso daf da beauty ya kai hannayensa biyu ya d'ago ta daga
sunkwi da kai da tayi,karaf suka had'a ido wani shu'umin kallo suka shiga jefar junansu dashi
inda ko wannensu baki d'auke da murmushi na farin ciki" a haka ameenu ya ja motar saura na
biye dashi suka bar gidan,yayin da a hankali beauty ta maida dubanta k'asa tace ni kam ka bar
kallo na haka"daga k'asan zuciyarsa ya sako wata dariyar had'e da k'ara matsowa sosai ya
matse jikinta da nashi,shinshina k'amshin jikinta ya shigayi,yanda yake bin wuyanta da
shinshina yasata fara janye jikinta tana tureshi taji can kamar mai rad'a yana fad'in ki barni naji
k'amshin matata ko kuma yanzu labari ya canja,ya zatayi da sameer ta san halinsa idan ya fad'i
magana dole ba dan taso ba ta barshi ya ci gaba da abinda yake inda sak'onsa ke ziyartar
kwakwalwarta tana karb'a!




Karya kwanar da akai ne aka shiga wani k'aya taccen hotel ya tabbatar da beauty da an
k'araso wajen inda cincirindo na motoci suka rigaya suka cika wajen,a bakin event hall d'in
ameenu ya tsaida motar a inda sameer ya fito ya zagayo ya bud'e waa beauty k'ofa ya rik'o
hannunta k'am kamar wacce za'a kwace masa take masu nan da nan aka fara ruwan d'aukar
hoto sai alokacin sameer ya iya k'are mata kallo wanda ita ma dai doguwar bridal gown ta saka
bak'i wuluk ta bi jikin nan nata,sai head d'in ta golden da takalminta,sosai beauty tayi kyau,don
duk yawancin hotunan sameer na kallonta ake yi,lura da haka yasa ta d'an b'ata fuska tanai
masa rad'a ka kalli mai camera mana !shima ya rad'a mata nak'i wayon!dariya suka sa a tare
kamar daga sama taji ana mata magana ta baya inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login