Showing 21001 words to 24000 words out of 59972 words
Chapter 8 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf
san kayansu"har suka cimma shopping
mall d'in nan hirar nan dai d'aya ita suke!
í ½í³“í ½í³“28 *'YAR JAMI'A*í ½í³“í ½í³“
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*
Katafaren kantin country mall dai-dai nan beauty ta tsayar da motarta tare da fitowa,haka
xee-xee ta biyo bayanta,ciki suka shige abinsu nan suka shiga b'angaren kaya suka jidi kaya na
axo a gani designers kala-kala don yawancin kayan komai kala d'aya suka d'auka abinda ya
kama jaka da takalmi kai harda jewelries abindai ba'a cewa komi ranar kud'i ya sha
kayi"ma'aikatan wajen su kansu beauty bata barsu a baya ba se datai musu kyakykyawar
sallama bayan sun kawo mata kaya har mota"basu suka isa gida ba sai gab da sallar magrib
inda ta sauke xee-xee a k'ofar gida,nan ta janyo hijabinta cikin jaka ta xumbula tare da janyo
ledar kayanta ta nai ma beauty godiya ta fita har ta cimma gate beauty ta manna mata horn ta
juyo bak'ar leda ta hau nuna mata dake ajeyi a bayan mota,hakan yasata dawowa tana fad'in
kinga na manta kayan da kika ce a baiwa mama ko"nan ta karb'a tana mai k'arai mata godiya ta
wuce"hakanan yasa itama beauty ta tada mota ta nufi gida"
Kamar yadda ta saba haka yau ma ta shiga gida mota sautin kid'a se tashi yake haka tai parkin
a wajen aje motoci tare da manna horn da gudu mai gadi ya taho rik'e da buta a hannu ya xube
gefen marfin motar,booth tq bud'e masa ba magana ya nufi wajen dan yasan aikinsa,da haka ta
fito ta nufi cikin gida"falon shiru ba alamar motsin kowa hakan ya tabbatar mata da umma da
ma'aikatan gidan kowa na wajen sallah sashenta ta nufa itama"murd'a hannun k'ofarta yayi
dai-dai da fitowar ummah daga sashenta rik'e da caxbi tana laxumi"daga ina kike?tambayar
data fito daga bakin ummah kenan"cikin sauri beauty ta juyo dan har ta tsorata da jin murya
bayanta"tuni ta saita nutsuwarta ganin ummah tace shopping naje nayi" shopping??shopping fa
kikace awannan lokacin?in har da gaske kike ina kayan da kika siyo"kafin beauty ta iya cewa
wani abu baba me gadi ya hawo sama nik'i-nik'i da kaya cike bisa hannu"sanin ummah cewa
dady ya d'aure wa beauty bayan rashin aiki se dai ma'aikata suyo yasa bata tanka mata akan
hakanba"gaisheta baba me gadi yayi inda beauty jiki sanyaye ta shige d'akinta yabi
bayanta"gefe guda ya aje mata kayan ya fice"
Sallah ta fara yi duk da dai cikin sauri aka kaita ana ta d'okin bud'e kaya"tana
sallamewa ko addu'a bata samu damar yi ba ta doshi kayan"a hankali ta hau fiddo kayan tana
k'are musu kallo"hannu ta kai ga wata doguwar riga kalar sky blue da ratsin bak'i ajikinsa ta
d'aga ta sama tana k'are mata kallo se kuma can ta nisa tace tabbas wannan rigar dake xa'ai
harka gobe tunda inaga muna da statistic kamar yadda na gani a time table se de kuma long
slip ce" ta nisa kamar me tunanin wani abu se kuma ta basar kawai taci gaba da duban
kayanta"k'ara wayanta ya shiga yi nan ta mik'a hannu ta d'akko a jaka"xee-xee kuma toh
lapiya?tambayar datai kenan sannan ta d'auka"
Beauty dama mama ce tace na kira mata ke a waya"cewar xee-xee"ok toh wani abu de ko?eh
godiya dama xatai miki gata ma kusa bari na bata"nan mama ta karb'i waya suka gaisa da
beauty godiya ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba har ta kai ta ga fad'in ai kullum in kina son
rakiya unguwa zainab tana da cikakken lokaci kixo kuje"itade beauty toh shine kad'ai amsarta
har sukai sallama mama na ta shi mata albarka kafin xee-xee ta amshi wayar su ci gaba da
hira"bayan ta kashe wayar ne ta shiga gyaran kayan ta jere su a wardrobe bayab ta fitarda
complete kayanda xata saka gobe a shiga *jami'a* d'aukar lecture!
í ½í³“í ½í³“29 *'YAR JAMI'A*í ½í³“í ½í³“
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*
í ½í²•
Zaune take bisa stool gaban madubi se shafe-shafe take da alamar fara'a ainun d'auke sama
fuskarta"ta d'au lokaci tana ta kwalliya kamar me shirin xuwa wani party ko dinner"bayan ta
gama ne ta nufi wajen kayan data aje saman gado ta janyo su ta saka kamar yadda ta ware su
daga irin kayan data siyo a fitar su da xee-xee jiya"da kokawa da nishi doguwar rigar nan ta
shige jikinta"se faman haki take kamar wacce ta sha wani aiki"rigar tsaf ta amshi jikinta sosai
duk wasu sak'o da loko na jikinta ya bayyana matuk'a gashi tai mata cif-cif kamar an
aunata"haka ta zura d'an kunne,tare da jaka da takalmi harda k'ara min veil duk black tunda
rigar sky blue ce"ko da beauty takai kallonta ga madubi wani irin ihun jin dad'i ta saki don ita
kanta tasan yau kam abin ba'a cewa komai"gefen gado ta k'arasa ta bud'e k'aramar drawer
dake wajen ta ciro wata jotter me sak'ale da biro ta xura a jaka"sannan ta matsa gefe wajen
ma'ajiyar tirare nan ma tai ruwansa ajikinta"kafin ta zari key na mota ta fito kunne dod'e da
earpiece se kad'a kai take na jin dad'in yadda kid'in ke tsima ta" a falo suka had'e da ummah
cikin sauri ta tsaida kid'an tare da gaisheta a ladabce"da fara'arta ummah ta amsa mata kafin ta
nuna mata dinning table dake cike da kayan bud'e baki"fahimtar abinda ummah ke nufi beauty
tai ba musu ta nufi wajen nan sukai karin kumallo" bayan ta gama tai ma ummah sallama ta fito"
Ko da beauty ta shigo jami'ar office din malam umar ta fara wucewa sai dai ina lokacin bai
k'araso ba da yake safiya ce sosai dan ko 8:00a.m batai ba"dole ta hak'ura bayan ta tura masa
sak'on yanemeta in yaxo da haka ta nufi venue d'in su na ranar"ta jima cikin mota zaune tana ta
kallace-kallacen jama'a mai shiga dame fita se sak'a zancen zuci take"cikin waigenta ne idonta
ya kai ga captain d'insu tuni ta wangale gilashin motar ta shiga kiran sunansa"meenu!meenu!
Da farko ameenu bai lura da kiran da take masa ba sai da wani d'alibi da suke tafiya tare ya ce
masa wai ameenu ba sunanka nake jin 'yar jami'a na kira ba da yake kowa yasan beauty yadda
ya kamata" hakan ya sashi mik'a ma d'alibin takaddunsa akan ya wuce masa dasu ciki kafin shi
ya k'ara so"wajen beauty ya k'arasa nan suka gaisa sai kuma ta nisa tace haba meenu ka shigo
mota mi magana mana xakai tsaye a waje"da farko ya d'an yi shiru kamar baxe shiga ba sai
kuma ya xagaya ya bude motar ya shiga"
A nutse meenu ya d'ago kai ya dubeta yace toh ina jin ki wani abu ne?ita abin ma dariya ya
bata se yayi ta wani mata magana sauri-sauri aduk sanda suka had'u besan yaga suna jimawa
a hira"itama kallon nasa tayi cike da murmushi tace ba wani abu bane illah aikin da kaimin
watannin baya yau ma shi za kai min"wane aiki kuma?cewar ameenu"sunan malamin da zai
d'aukemu statistic nake son ji" wata ajiyar zuciya ya sauke na jin dad'i da Allah yasa ba wani
abun zata sakashi ba don shi sam be son abinda zai had'ashi da ita musamman yanxu da kowa
yasan wace ita a jama'iar"
Saukar lumfashinsa yaxo dai-dai da bata amsa"ehh toh nima dai bansan shiba amma dai dana
tambayi wani tsohon lecturer anan yace d'alibai dai na kiransa sir prince but tak'amai-mai
sunansa se ya shigo lecture zai fad'a mana don haka yake yi kafin ya fara darasi"jin-jina kai
beauty tayi kamar me wani naxari tana k'ara maimaita sunan a zuciyarta"sir prince"sir prince"
ina kuwa na tab'a jin sunan nan a baya?ina ne kuwa?kai bazan iya tunawa ba"may be ma
shima na harka ne ban sani ba"
Ganin yadda ta duk'ufa da tunani ne yasa meenu ya d'an buga kujeranta yace zan iya tafiya
ko?firgigit ta jiyo tana fadin yes meenu zaka iya tafiya nima ai yanxu xan shigo ka samamin seat
kusa da kai bara naje na siyo orbit chewing gum a caferia"toh kawai ya amsa ta ya fice a motan
ita ko ta tada mota ta nufi caferia" A wani k'aramin kanti ta siyo shi tana k'okarin kunna mota kenan ta bar wajen taji ance adawo
lapiya?saurin juyawa tqi taga wanda ke mata magana"murmushi ta saki ganin sir Mutallab tsaye
a gefen motan ta"wanda yake d'aya daga cikin malaman department d'insu kuma na hannun
dama a wajenta dan kuwa lokaci-xuwa lokaci sukan had'u" dole ta fito suka tsaya nan fa hira ta
b'arke tsakaninsu har beauty ta manta da wani abu wai shi lecture!
í ½í³“í ½í³“30 *'YAR JAMI'A*í ½í³“í ½í³“
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*
Kimanin minti 30 beauty na tsaye da sir mutallab suna hira can ya nisa yace au kin ga kin
sha'afantar da ni da dad'ad'an kalamanki ko? gashi kinsa nayi late a lecture da zan gabatar"sai
a lokacin beauty ta tuna da ashe itama fa tana da lecture dole sukai sallama a gurguje ta hau
mota ta nufi venue "wayam kake ganin wajen nan ba alamar mutane kowa ya shiga ciki hakan
ya tabbatar mata da an fara lecture"motar xee-xee ta hango can gefe guda, haka ga kuma wasu
motoci nan sunyi jeri a gefe d'aya"tsakiyar cikinsu inda yayi dai-dai da wata mota ash colour
tasha wanki nan ta aje motan nata ta d'akko jakanta ta fito"
A bud'e ta samu k'ofan hakan yasa ta tura kai ciki ta shige"
Juye ta riske shi ya maida kai ga allo yana ta xuba uban rubuta d'alibai na kwafa"don haka bata
jira wata-wata ba ta shiga taku cikin gadara ji kake kwas-kwas takalmi na k'ara"markern dake
rik'e a hannunsa sir prince ya tsayar da rubutun tare da juyowa yana kallon ikon Allah"inda tuni
hankalin beauty ita ko yayi nisa a neman meenu se can ta hangoshi saman theater ga wata
mace a gefensa"sauri beauty ta shiga yi don taje tai mata masifa na ta zauna mata a
waje"kamar daga sama taji ance"hey lady where are u going there?ba tamabayar ce ta bata
mamaki ba sai dai muryar wanda ta ji"don tabbas ko a mafarki taji wannan voice d'in xata gane
shi bare a fili"juyowa tai don k'ara gaskata abinda taji"kwatsam sukai ido hud'u da prince"kusan
mutuwar tsaye tayi a gun shiko me zai yi prince in ba k'ara had'e fuska ba ya k'ara jefo mata
wata tambayar"tell me about your wristwatch?banbara kwai taji tambayar aiko me xatai in ba
k'udurta raina masa hankali ba nan ta gyara tsayuwarta sosai ta kai dubanta ga agogon dake
sak'ale a hannunta ta shiga magana cikin izzah"wow my wristwatch ix unique and
fashionable"as u guys normally call it one in town"& i'm quite sure small money inside a small
pocket can't afford to handle it"tana kaiwa nan ta d'ago kai cike da murmushi saman fuskarta
tana dubansa"me yarinyar nan take nufi ni talaka ne kome?wato ina tambayar ta lokaci shine
zata juya min da haka aiko zata ga dixgi"xancen da prince ke nanata wa kenan arai"ganin
yadda aji kowa ke jiran jin me xai ce ma ta"nan ya k'ara matse fuska tamau kamar be tab'a
dariya ba sai kuma ya d'an saki murmushi na gefen fuska ya shiga kad'a marker dake dauke a
hannunsa yana fad'in alright class let us solve a small work here before moving to our main
topic of discussion"ido kowa ya bishi dashi ana kallon ikon Allah"a inda prince ya koma gefe da
rubutun shi na farko yayi wani k'aramin arithmetic yace waze iya min solving"wani d'alibi a
gaban seat ya d'aga hannu yace sir let me try"prince yace ok come and try"haka d'alibin ya taso
ya karb'i markern a hannunsa ya shiga solving"bai d'auki wani lokaci sosai ba sai gashi ya
gama ya fitar da amsa da yake d'alibin shi ke d'aukar overall a class din"yace sir na
gama"duban board d'in prince yayi a nutse yaga tabbas abinda yake so ya gani yaron ya
rubuta"nan yace ko zakai min bayanin yadda akai ka samo amsar"tiryan-tiryan d'alibin yayi
bayani abin yayi matuk'ar burge prince nan ya kallo class yace alright class kun gane me yayi
ko?class kowa ya d'auka da yes sir"in banda wata matashiya dake gefen dama gareshi wacce
ta amsa da no sir"dama abinda yayi tsammani za'a samu me fad'a kenan dan yasamu yayi
nasa bayanin nan kuwa ya kallo ta cike da samun karsashi a jiki yace ok lady let me repeat it
clearly"gaban allo ya koma ya shiga nunawa yana bayani daya ke quadratic equation ne sai da
ya gama bayani tsaf sai yace mata ko kinsan dalilin da yasa x=0 & y=10 nan ma dai ta kara
bashi ansa da no sir sai yace toh bara nai miki example da hausa yadda xaki gane sauran aji
ma su k'ara fahimta sosai dan nasan akwai wanda ko an bud'e brain d'insu an zuba karatu kan
bazai d'auka ba"
í ½í³“í ½í³“31 *'YAR JAMI'A*í ½í³“í ½í³“
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*
í ½í²•
kallo ya k'ara kai wa sir prince ga sauran d'alibai dake zaune suna jiran cewarsa cikin
sarrafaffiyar muryar nan tasa mai cike da kwarjini had'i da izzah haka ya fara magana" Hak'ik'a
nin gaskiya ba ya cikin tsarin karatuna yin bayani da hausa don ya zama dole ne shiyasa yau
zan mu ku,kun fahimce ni ko?sauran aji suka amsa da yes sir,sannan yaci gaba da
magana"yana kai nuni da hannu izuwa ga allo"a duk lokacin da ku ka tashi lissafin irin wannan
aiki toh ku d'auki x amatsayin mace mara kamun kai, ita kuma y amatsayin mace mai kamun
kai"a yayin da x mara kamun kai ta gama zagayen ta na duniya zakuga ta tara kud'i masu
d'umbin yawa (anan yayi nuni ga inda x ta samu maki100 a yanda calculation d'in ya nuna) ,har
ta dunga jin cewa kamar ta fi kowa kud'i jama'ar gari kuma suyi ta bibiyarta don neman abun
hannunta,har ta kai wata rana kwatsam sai a wayi gari wannan kud'in nata ya k'are a lokacin da
zaton mutane bai kai ga haka ba"nan ya sauke hannunsa a inda rubutu ya nuna=0, ita kuma y
mai kamun kai za kuga tana ta faman wahala a duniya( ya saita inda aka rubuta y=0) jama'a ko
ta kanta basa bi don a tsammaninsu sam babu wata daraja a tattare da ita har sai an cimma
gab'ar da zatai arziki alokacin ne jama'a zaka ji suna yabo gareta na k'iddige muku sai ta kai ta
kawo wannan x d"in na bibiyar y don samun dacewar rayuwa"don haka jama'a wannan labari
dai na san kun fahimce shi don nai muku shi dalla-dalla"bai kai ga rufe baki ba waje gaba d'aya
ya d'auka da tafi ji kake raf-raf had'i da ihu kai har da shewa na jama'a,kowa na tofa albarkacin
bakinsa akan wannan labari,beauty dake tsaye gaban desk k'afafunta sun kasa rik'eta ga wani
matsanancin sarawa da take ji kan ta ya fara duk don wannan d'an iskan labarin da sir prince ya
bayar ta san ba makawa labarin nan da ita yake"ganin tsayuwar baza tai mata ba ne yasa ta
fara takawa a hankali tana dafe kai kamar wata 'yar giya ta nufo k'ofa dan barin theater d'in,tana
takowa dai-dqi da inda yake tsaye nan ta d'ago fuska cikin zafin nama ta shiga k'ok'arin yin
magana amma ta kasa sakamakon rad'ad'in da kanta ke mata"saurin duk'ar da kanta k'asa tayi
sai ji tai kamar daga sama yana fad'in pls among u ladies someone should help her out kafin ta
fad'i anan may be cough syrup ne ya fara mata aiki,ai ko kamar jira suke class suka d'orar da
wani sabon ihun kafin kace me wajen ya karad'e da hayaniya,xee-xee da ke can saman theater
cikin sauri tai k'arfin halin tasowa ta nufo wajenta nan ta rik'eta adaddafe har wajen mota, bud'e
motar xee'xee tayi ta sanya ta ciki tana mai cewa zaki iya tuk'in ko kuwa?hannu beauty ta d'aga
mata kawai da alamun ta bar ta haka ta koma ciki"ba dan taso ba haka xee'xee ta barta xuwa
ciki don tasan halin beauty indai ta kafe a abu to abarta kawai"
Tunani sosai su kai ta ziyartar beauty ta sak'a wannan ta kunce wancan duniyar duk ta gama
yi mata zafi,sam ta rasa me ke mata dad'i a duniyar nan ace wai yau har ita jama'a zasuyi ma
ihu duk shaharar da tayi a haka zai k'are inaaa wallahi da sake hakan bazai tab'a faruwa da ni
ba"duka takai wa sityarin motar tata da hannu kafin ta kunna motar cikin b'acin rai ta nufi gate ta
bar makarantar!Bayan kimanin awa biyu da faruwar hakan ne sauran d'alibai suka fara
tururuwar fitowa bayan da sir prince ya rufe karatunsa na ranar inda kowa ka ganshi labarin nan
dai d'aya shi ake nanatawa na dizgin da akai wa 'yar jami'a da sanyin safiyar yau, shi ko prince
wani dad'i ne ya lullub'e shi tun bayan fitar beauty daga theater d'in yasan ko ba komai yau
burinsa ya fara cika akanta!
í ½í³“í ½í³“32 *'YAR JAMI'A*í ½í³“í ½í³“
_BY_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*
í ½í²•
Horn! Take