Showing 48001 words to 51000 words out of 59972 words

Chapter 17 - 'YAR JAMI'A Complete Book Hausa Novels by Aneesa Abubakar Rimi .pdf

Advertisement

08 Jul 2025

3238

iske sameer kwance akan katifa yana waya da ummah
waje ya samu ya zauna har ya gama sannan sameer ya jiyo yace haba mutumina yau ina ka
shige haka daga cewa ka bani waje na kafa soyayyarka azuciyar yarinyar nan kawai sai ka
b'ace sai yanzu?murmushi d'an ladi ya saki yana d'an girgid'a kai ya d'ago idanunsa sama yace
ai yau babbar rana ce agareni kaga kuwa bai kamata nayi wasa da ita ba,tun bayan rabuwarmu
dai ban zame ko ina ba sai wajen aminina d'an mai gari can naje muka sha hira duk na baci
labarin komai game da hajara kai in tak'aice maka labari shine ya bani naira d'ari biyar da na
siyo mana wannan naman!janyo ledar d'an ladi yayi ya mik'o d'aya yace kaga wannan shine
namu shi kuma wancan daka ganshi a k'ulle na gimbiya ne"dariya sameer ya saka can kuma ya
nisa yace Allah mutumina?kace yau dad'i zamu ci,ai tana can shiga ka mik'a mata kafin tai
bacci,washe baki d'an ladi ya shiga yi yana k'ara gyara zaman hularsa akai sannan ya d'akko
ledar ya jiyo ya kalli sameer yace ya ka gani d'an birni!jinjina kai yayi da zummar gamsuwa da
yadda ya ganshi yace wannan kwalliyar tayi mijin hajjo!cike da jin dad'in sunan da sameer ya
kirashi dashi haka ya bar d'akin!
Wai wa yaga 'Yaar jami'a an yi auren k'auye??ai kuwa da musamman zan d'auki katin d'aurin
aure na kai jami'a ko dan asha dariya!maganar da sameer yayi kenan cikin raha bayan fitar d'an
ladi!


Kwance take beauty duk da ba bacci take ba, amma kana ganinta kasan hankalinta baya tattare
da ita tuni ta lula duniyar tunani,har d'an ladi ya zaune nesa kad'an da ita amma bata san da
zaman saba,sunanta daya kira ne ya maido da ita hayyacinta,a d'an tsorace ta d'ago kai gani
d'an ladi zaune gefenta yasa ta saki wata k'aramar tsuka ta koma ta kwanta!gyaran murya ya

fara yi sannan ya mik'o mata ledar!ganin bata karb'a ba yasa shi aje mata ledar ya mik'e zai fita
kenan yaji tace ka dawo ka d'auki ledarka na k'oshi!bai bi ta kanta ba d'an ladi ya fice abinsa
yana mai cike da farinciki na ko ba komai dai ta kalleshi kuma yasan abun sune kawai na mata
na filako amma tana da buk'ata! Baba yagana dake kwance can lungu da gado ta rufa da abin rufa ta bud'e tace in kin k'oshu ji
mik'o min na lashe tunda abin wariyar launin fata ne bai kawo min ba ya biye miki!yamutsa
fuska beauty tayi sannan ta mike zaune ta janyo ledar ta bud'e nama ta gani sai k'amshi ke
tashi nan tai faro da ido tace loh tashi baba mu ci nama ne ashe!haka baba yagana ta sakko
suka nad'i namansu tas suka cinye shi,ruwa suka sha suka koma gado anan ne kuma hira ta
b'arke tsakanisu,tun fara hirarsu babu abinda baba yagana ke wa beauty nasiha dashi in banda
sirrin zaman gidan aure,duk wasu hanyoyi na tarairayar miji da neman soyayya wajen mai gida
babu wanda baba bata labarta mata ba,har takai beauty na mamakin yadda baba tasan wad'an
nan bayanan ita da take k'auye,basu suka tsagaita da hira ba sai can tsakiyar dare suka samu
suka bi lafiyar gado!!




_11:00a.m(na safe)_


Tsoho ne tsaye bakin k'ofar d'akinsa shirye cikin farar shadda da malin malin waxce tasha
guga,Alhaji yayi sallama ya shigo cike da girmamawa haka suka gaisa suka nufi hanyar fita
waje har sun kai zaure Alhaji ya dawo ciki ya nufi d'akin su d'an ladi suna zaune suna hira shi
da sameer koda ya shiga suka gaisa nan ya kalli d'an ladi yace maza ka tashi ka shirya ka
sameni kai d'aya a babban masallacin juma'a na tsakiyar gari!toh d'an ladi ya bisa dashi da
haka Alhaji yayi waje ya basu waje!

A b'angaren baba yagana kuwa tun tashinta asuba take tsaye gaban murhu sai girke girke take
yi ga wata tukunya can k'arama da lokaci zuwa lokaci takan bud'e ta motsata,bud'ewar da tayi
ne na k'arshe taga tukunyar tayi don haka ta juye ta a k'aramin kwano ta nufi d'aki da ita!
Tana shiga ciki zaune ta tarar da beauty tayo wanka tana kwalliya sosai yau kwalliya take
cab'awa abinta na komawa gida,kallo d'aya baba yagana tayi mata ta saki dariya tace lallai yau
ana gayu anan ita kuma wannan kwalliyar fa?juyi tai da ido beauty tana d'aure d'an kwalin
doguwar riga pink data saka,tace wannan kwalliyar komawa gida ce don ni duk na k'agu mu tafi
na huta da surutunki!kwanon baba yagana ta ajiye gabanta sannan tace bari zumud'i nan da
awa biyu zuwa uku zaki tafi gida nina na huta yanzu dai gyara zamanki kici wannan!yamutsa
fuska beauty tayi sannan takai hannu ta bud'e kwanon,kaza ta gani ciki tasha kayan had'i ga
romo jikinta sam babu kayan miki,d'ago kai tayi ta dubi baba tace wannan kuma meye?kaza ce
mana!ku kuma haka kuke dahuwar kazarku anan toh ni dai d'auki kayanki na k'oshi,da jin haka
baba yagana ta samu waje ta zauna,ai kuwa baki isa ba nai miki dahuwa kice kin k'oshi ko ya
ya ne sai kin ci,cewar baba!ba don ta so ba haka beauty ta zura hannu cikin kwano ta d'an
d'eb'o kad'an ta saka baki!cauu...taji abu ya kama bakinta,su beauty abin nema ya samu ai tuni

ta gyara zamanta ta fara kwasar romanta,sai da taci kusan rabi da kwata na kazar nan banda
romo da ta sha ta k'oshi sannan ta ture kwanon gefe guda tace Alhamdullah,cike da jin dad'i
baba ta janye kwanon daga gabanta ta fice abinta ba tare data tanka mata ba!

12:00p.m( na rana)
Busa sarewa da ganguna kad'ai ke tashi ta ko ina,duk unguwa ta karad'e da hayaniya,ko da
sameer ya lek'o ya tambayi baba ko lafiya sai ce masa tayi itama bata sani ba jiran dawowar su
Alhaji take!
Ba'a yi minti 30 da maganar ba sai ga tsoho ya shigo gida da sallama cikin sauri ya nufi
ma'ajiyar tabarma ya d'auka yayi waje"zaure yajeya shinfid'a wa manyan bak'i sannan ya dawo
ciki,sunan yagana ya shiga kira haka ta fito a d'aki da sauri tana lafiya?abincin bak'i zaki mik'o
da alamar fahimta haka baba yagana ta nufi inda ta jere kayam abinci data gama ta jidi mik'a
masa yana fitarwa waje har ya gama!
Bayan wasu mintina da basu fi goma ba sai ga Alhaji ya shigo gida yana kiran sunan
sameer,sameer dake tsugunne gaban k'aramar jakarsa ta kaya yana k'ok'arin zuge zip d'inta
don ya gama shirya kayansa tsaf ya ji muryar Alhaji,amsa shi yayi ya fito hannu rik'e da
jaka"sororo Alhaji yayi yana kallonsa sai kuma can yace ina zuwa haka?susa gyeya yayi
sannan yace dama zan kaita motane kafin ku dawo muyi sallama!ahiyar zuciya Alhaji ya sauke
sannan yace toh ajeta anan gefe kazo muje zaure ana buk'atarka acan!umarnin da aka bashi
yabi haka ya bi bayansa bayan a jae jakar suka nufi zaure!
[10:25am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

156-160



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*


Daga fitar baba yagana bata zame ko ina ba sai d'akinta inda ta tarar da beauty kwance tana

ta waya abinta dariya sosai take yi da alamar wayar da take tana jin dad'inta,waje baba ta samu
ta zauna tana jiran gamawarta,ba wani lokaci mai tsawo ta d'auka ba sai gashi tayi sallama sa
wadda ta kira da zee-zee sannan ta kashe wayar,kallo ta kai wa baba sannan tace ma,aikaciyar
tsoho ya kayi ne?harara baba yagana ta watso mata sai tace saboda kin rai na ni nice
ma'aikaciyar tsohon?dariya beauty ta maida mata ba amsa,gyara zamanta sosai baba tayi
sannan ta juyo ta fuskance ta sosai,sunanta ta kira,beauty ta amsa tana k'are wa wayar ta
kallo"hajara ina so ki nutsu kuma ki saurareni da kyau kisan cewa ita wannan duniyar kome
muke aikatawa dama muk'addari ne daga Allah sannan mafiyawancin abubuwa na rayuwa da
muke ganinsu ba alkhairi bane toh sune mafi Alkhairi a wajenmu amma mu bamu sani ba,don
haka ina yi miki umarni amatsayi na na 'yar uwar mahaifiya a wajenki wacce nasan ko ita
mahaifiyar taki zan gaya mata taji,daki ji tsohon Allah a zamantakewarki ta rayuwa,sannan yi
biyayya ga na gaba dake domin abinda suka hango miki na ci gaban rayuwa ke bazaki tab'a
hango shi ba,nasan yanzu baza ki fahimci me nake nufi ba Amma in kika koma gida ummanki
zatai miki cikakken bayani,a k'arshe ina miki addu'ar Allah yayi miki albarka! Beauty ta amsata
da ameen!
Tana kaiwa nan a maganarta baba yagana ta mik'e ta nufi jerin samirunta dake mak'ale a cikin
kwabot ta zaro wata k'aramar samira bud'eta tayi ta janyo k'ullin dake ciki a rufe a bak'ar
leda,beauty dai na biye da ita da ido har ta dawo ta zauna,hannun beauty ta riko ta saka mata
shi sannan ta maida ta rufe nan tace hajara ki adana wannan zai miki anfani duk ranar da Allah
yasa kika tarr a d'akin mijinki ko bayan rai nane kafin mu'amala ta auratayya ta had'aku ki
tabbata kin jik'ashi da ruwa kin sha"hannu ta kuma kaiwa k'ark'ashin gado inda ta janyo wani
farin mayafi ta yafawa beauty sannan ta saki murmushi tace toh haka yau zaki komawa
ummanki nasan zatai farin ciki in ta ga wannan gyalen jikinki!
Kalaman baba yagana duk sun gama d'aurewa beauty kai inda kunya ta gama lullub'eta dan jin
maganar baba ta k'arshe na abinda ta bata,don duk wasansu basu tab'a magana irin haka ba!



Suna cikin wannan hali ne suka ji shigowar tsoho da Alhaji,sunan yagana suke kira baki
d'ayansu dan haka cikin sauri ta fito tana tambayar ko lafiya?Alhaji ya tambaye ta ina yaran
suke?suna cikin d'aki! Yana jin haka ya shiga kiran sunayensu a tare,sameer ne ya fara fitowa
d'an ladi na rik'e da hanunsa gaba d'ayansu fuskokin nan babu alamar annuri,sai can ga beauty
ta fito rike da jaka a hannu,tsoho na ganin yanayin beauty sam babu alamar damuwa ko b'acin
rai a tattare da ita cike da zolaya yace lallai yaran zamani wato ke farin cikin tafiya ma kike ki
barni ko?itama dai cikin wasan ta maida masa da ehh mana ni daman duk a k'age nake na
koma garin mu,dariya tsoho ya saki sannan ya tsagaita tak'aitacciyar nasiha yayi musu sosai
mai tsuma jiki inda duk ciki jan hankali ne da hak'uri ga al'amuran rayuwa sannan ya sanar dasu
cewa basu kad'ai zasu tafi can ba har da Alhaji da wasu mutanen!toh kawai suka amsa da shi
sannan suka fiddo kayansu baba yagana na rik'e da hannunta har suka fito waje!

Cincirindo na mutane da motoci,beauty ta soma gani tun fitowarta inda nan take gabanta ya
yanke ya shiga fad'uwa cike da d'unbin mamaki ta kalli baba tace wannan mutanen fa haka
baba?da yake baba yagana ta shirya ma amsa wannan tambayar tuntuni don tasan ba makawa

sai ta afku nan take ta bata amsa da nad'in sarauta akayi shiyasa kika ji unguwar ta rikice Alhaji
aka baiwa muk'ami don haka in kunje can gida an nutsu sai ki masa tayin murna!toh ta amsa ta
dashi da haka ta kaita har inda motar sameer take ta bud'e ta shiga gidan gaba ta zauna,haka
tana kallon Alhaji ya shiga wata mota doguwa fara tare da wasu jama'a kana ganinsu kaga
mutane 'yan alfarma,inda d'an ladi ya rako sameer har bakin mota sukai sallama beauty na
masa bankwana amma yadda yayi shiru uwa bai ji taba don haka itama ta basar don ta lura da
yanayin nasu gaba d'aya yai sai a hankali,ko b'acin ran rabuwa da juna ne oho musu!



Tafiya suka shiga yi cikin nutsuwa haka yake tuk'in inda motoci uku ke bayansa a jere,tun
bayana shigarsu mota babu wanda ya iya ko da kwakwkwaran motsi baran tana
magana,dukkan ninsu tunani tsagwaronsa ke cinsu sak'a wannan kunce wancan haka har suka
yi nisa sosai a tafiyarsu,k'ishi daya taso masa ne ya janyo ruwa faro dake gefe dashi ya bud'e a
hankali ya shiga sha,d'agawarsa ta k'arshe ne yasa shi kwarewa da sauri ya sauke ruwan ya
shiga tari,jin yadda yake ta faman tari da alama ya kware da yawa ya saka beauty d'ago kai ta
sauke dara-daran idanunta akanshi ba tare da wani tunani ba tace masa sannu ya
sameer!banza yayi da ita uwa bai ji mai take cewa ba yaci gaba da tarinsa,ko zaka tsaya da
motar ya fad'a maka?a raunane ya d'ago kumburarrun idanunsa ya sauke su akanta,kallon da
yake watsa mata kad'ai ya isa ace tasha jinin jikinta,d'auke kai tayi daga kansa ta maida kan titi
wanda hakan baisa ta tsaya da maganarta ba taci gaba,hmmn yanzu dai ba da bane da zaka
kashe mota ka jibgeni,kuma kar kai tunanin abinda kai min abaya yanzu zan d'auke shi,wallahi
bazan k'ara tsayawa wani namiji ya tab'a lafiyar jikina ba,kar kaga na saurara maka dama can
saboda tsorona da Alhaji ne amma kaga yanzu yadda na d'akko hanyar gidan nan komai ta
fanjama-fanjam,cikin b'acin rai da d'acin zuciya haka kalaman beauty ke dokar
kunnuwansa,wato wani wawan damk'a daya kai hannu yayi mata saman kanta cikin zafin nama
ya kai gab da gaban motar kenan zai buga,kamar daga sama ya ji maganganun baba yagana
na dawo masa ....kaji tsoron Allah kuma ka sani hajara ta zama abin kiwo a wajenka......a sulale
ya iya zare hannunshi daga kanta wanda tuni beauty ta gama sakin jiki taji inda kanta zai
kasance taji an sake ta,hannunsa ya buga jikin sitiyarin motar yace"wallahi an cuce ni"an
cuceni"why me? Dariya beauty ta saki ganin yadda yake ta faman haki kamar wani
mayunwacin zaki,fari tai da ido kamar yana ganinta tace Allah dai ya kiyaye maza basuyi abun
kunya ba,in banda matsoraci wake dukan mace?dariya ta k'ara sakar masa,inda abin duniya ya
gama cika sameer CD na motar ya kunna ya k'ure k'arar motar k'ira'ar sudais ta hau tashi sosai
ya shiga binsa ko ya samu sassauci a zuciya!
[10:25am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

161-165

💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*


Misalin k'arfe 12;00p.m(na rana) a agogon hannun sameer wanda yayi dai-dai da shigowarsu
gidan dady a parking space ya aje motar haka sauran motocin suma suka aje nasu!bara dai na
wullar da kwallon mangwaro na huta da k'uda haka beauty ta fad'a tare da bud'e marfin motar ta
fita abinta,hanyar shiga babban falo ta bufa ta kai hannu kenan zata bud'e k'ofa taji an riga ta
turo k'ofa matsawa tai da baya gudun kar ta bige ta tsaya tana jiran ganin mai fitowa,ido ta zaro
waje da gudu kumaa ta fad'a jikinsa dady ta gani tsaye ai kuwa ta shiga rero kukan shagwab'a
tana bubbuga k'afa a k'asa,idan ran dady yayi dubu tuni ya gama rikicewa don babu abinda ke
dagula masa lissafi irin kukan beauty,tambayarta ya shiga yi ko lafiya amma sam tak'i tanka
masa,Alhaji da mutanen wajen haka sukai sororo suna ganin ikon Allah ganin abin nasu ba mai
k'arewa bane yasa Alhaji yayi k'arfin hali ya k'araso wajen ya daka mata tsawa don yanzu ba
halin dukan matar wani,dole ta janye jikinta daga na dady tabi gefe ta shige gida da
gudu,babbar rigar jikin dady ya shiga gyarawa yana cike da fara'ar gani amininsa mahaifin
sameer da d'an uwansa har da wasu mutum uku daga danginsa,cikin girmama juna haka ya
k'arasa wajensu suka gaisa tare da yiwa juna murnar abinda ya had'a tsakani,haka sameer
shima ya fito kai a k'asa ya gaida dady ya amsa,iso dady yayi musu dasu k'araso ciki nan suka
d'unguma suka nufi falo,sameer dake tsaye yana k'ok'arin yin sashensa kamar yadda ya saba
yaji Alhaji ya rik'o hannusa yana nuna masa hanyar falo dole ba don yaso hakan ba ya bi
bayansa suka nufi ciki,ji yake a halin yanzu babu abinda yafi buk'ata irin kad'aituwa ba tare da
wani ya shiga lamarinsa ba amma ya ya iya da lamarin Alhaji!.


A babban falo suka sauka nan hira sosai ta b'arke a tsakaninsu bayan nan ummah ta fito suka
gaisa da yake tun safe tana kitchen da ma'aikata ana had'a abincin tarbar bak'i,nan da nan
kuma aka shiga jere kayan ciye-ciye da tand'e-tand'e,sameer dai ido kad'ai yake iya binsa dashi
don gaba d'aya tunaninsa baya wajensu,ga wani uban tagumi daya dasa kamar wanda akaiwa
mutuwa,lura da hakan dady yayi nan ya kalloshin sosai yace sameer ki zaka je ciki ka d'an
watsa ruwa ne?dady bai gama rufe bakinsa ba kamar dama jira yake sameer yace ehh
dady!yana kaiwa nan ya mik'e ya nufi waje sai sashensa!

_4:00p.m (na yamma):_
Sameer ne kwance saman gado ya rufa da bargo duk da ba bacci yake ba amma dai idonsa a
rufe yake,ya ji an bud'e k'ofar d'akin an shigo,bargon dake rufe a jikinsa yaji an yaye an shiga
daddab'ar shi a hankali ya bud'e idanunsa karaf ya sauke su akan na Alhaji,cike da mamaki
Alhaji ya k'ara kai hannunsa a wuyan sameer inda yaji zafi, meke damunka sameer?tambayar
da yayi masa kenan!lumshe ido sameer yayi nan take kuma ya bud'esu ya sauke akan Alhaji,
ya bashi amsa da babu komai!jinjina kai yayi na alamun bai gamsu da maganar sameer don
haka yace toh tashi zaune muyi magana,ba musu sameer ya zauna ya zuba ido yana
sauraronsa,sunansa ya kira samee sannan ya ci gaba da magana,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login