Showing 1 words to 3000 words out of 58121 words
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 1*
Wasu yara ne ke wasa su uku,,, yaran bazasu wuce shekara goma sha uku ba zuwa sha hud'u
.'Dayar ce mai suna Fatima ta dubi 'yan uwan wasanta Maryam da Fadila,,, tace "Maryam ya
kamata muje gida yanzu fa,, mun dad'e sosai muna wasa gashi rana ta fara fitowa ".Fadila tayi
charab ta chafke maganar tana hararar Fatima,, sannan tace "ke idan kin gaji da yin wasa ne
mu bamu gaji ba,, saboda haka ga hanya nan ki wuce zuwa gida babu wanda ya tareki ".Fatima
ta dubi Fadila duba na rashin son fad'a,, tace "haba Fadila dad'ina dake akwai saurin fushi,, ni
dama wasa kawai nakeyi muku na fad'i haka ne saboda kada a nememu arasa a gida "."To wa
ne aiki ne zamuyi idan muka koma gida,, nidai gaskiya ban gaji da yin wasa ba ".Cewar Fadila
cikeda rashin son maganar.
Sai asannan ne Maryam ta dubi Fadila tace "ya isa Fadila abar maganar,, kada abin ya zamar
muku fad'a a tsakaninku muji kunya. Amma ai gaskiya Fatima ta ke fad'a ba k'arya ba ".Fatima
tace "k'yaleta Maryam ai ya riga ya wuce adaina tunawa "."To shikenan babu komai ai ".Cewar
Maryam dayake ita yarinya ce nutsattsiya mara son magana sosai,, sunyi shiru dukansu na
tsawon lokaci,,, can dai Fadila ta katse musu shurun tace "ku zo mu fara 'yar chahu muna
gamawa muyi gida ko,, amma nice ta farko ".Fatima da Maryam suka gyara zamansu domin suji
dad'in wasar,, Fatima tace "ni ce ta biyu "."Ni kuma ta uku ".Inji Maryam cikeda natsuwa da
kwanciyar hankali.
Suna tsakar wasarsu cikeda matuk'ar jin dad'i da nishad'i sosai,,,daga ganin yadda sukeyin
wasar suna cikin walwala da farin ciki. Sun jima sosai suna wasa can dai suna batun tashi
gidajensu,,,,saiga Iya Gwamma tazo wucewa zuwa gidanta. Ta zo zata wuce ne sai kuma ta
dawo baya wurinsu Maryam,,, suna ganinta suka durk'usa su uku suna cewa "Iya ina kwana,,
ya gida?.Lafiya k'alau 'yan uku masu kamada juna,, kuma 'yan matan gobe mi kukeyi anan ne?
".
Suka had'a baki wurin cewa "wasa mukeyi Iya Gwamma,, mi zamuyi miki Iyarmune ko wani abu
kikeso mu siyo miki ne?".Iya Gwamma ta tsura musu idanu na wani lokaci tana kallonsu,, irin
kallon na k'urilla da bai dace ba. Baki da hanci ta saki tana musu kallon kwad'ayi,,, da k'urilla
nason cimma wani buri nata. Can dai da k'yar ta daure ta b'oye damuwarta da kwad'ayinta,,tace
"muje gidana in baku kud'i ku siyomin biredi da madara shagon Mande ".
Fadila tayi saurin cewa "to Iya su Fatima ku tashi muje gidan Iya mu amshi kud'i,, mu siyo mata
biredi da madara ".Maryam da Fatima jikinsu duk yayi mugun sanyi tsoro da fargaba ya
bayyana a cikin zuk'atansu,, su kansu basu so zuwa ba amma babu yadda suka iya. Kamar
suce basu zuwa ba amma ba zasu iya kallon tsabar idon Iya Gwamma ba,, suce ba zasu iya ba
saboda ko banza tayi jikoki dasu. Can dai Fatima ta tattaro dauriya tace "to Fadila, Maryam
tashi muje mana kinyi shiru lafiya dai? ".Maryam itama ta mik'e tsaye tace "Lafiya k'alau Fatima
".Tana kakkab'e jikinta da yayi k'asa saboda wasa,, su ma su Fatima suka kakkab'e jikinsu,, Iya
Gwamma ta dubesu tace "ku wuce muje zuwa gidan na gaji da tsayuwa ".
Suka ce "to Iya ".Iya Gwamma ta sasu agaba suna tafiya,, ita kuma ta tsaya abayansu tana
k'are musu kallon k'urilla tasa lasar baki da fitar da halshe,,, su Maryam suna tafiya suna fira
cikeda matuk'ar jin tsoro da fargaba akan abinda kan iya faruwa dasu. Saboda maganar
gaskiya da sunsan Iya Gwamma ce zata biyo ta inda suke,,, da tuni sun cikama bujensu ko
zanensu iska. Domin Iya Gwamma ta shahara wurin maita da kuma sata a cikin unguwarsu,,,
babu wanda baisan da zamanta ba sannan babu inda sunanta baije ba akan ita *MAYYA CE*.
**********************
*****Acan gidansu Maryam kuwa Mama Sa'ima ce zaune da yayan Maryam mai suna
Mubarak,,,, suna firarsu ta tsakanin uwa da d'a. Yaya Mubarak ne ya dubi Mama Sa'ima yace
"Mama tun d'azu muna fira banga giftawar yarinyar nan Maryam ba,, wai ina taje ne kuma? ".
"Hmmm Mubarak sun fita tun d'azu itada su Fatima,, gashi yanxu har azahar tayi basu dawo ba
".Inji Mama Sa'ima fuskarta tana bayyanar da damuwa.
Saida gaban Mubarak ya buga da k'arfi,, ya bada rasssss! Sannan ya tattaro natsuwarsa wuri
d'aya,,, domin kada ya tashi hankalin mahaifiyarsa. Ya dubeta duba na natsuwa ya tausasa
halshensa,, yace "Mama ki kwantar da hankalinki Insha Allahu suna waje suna wasa,,, kuma
yanzu nan zanje ince su dawo gida hakanan. Ai wasan ya isa yau sai kuma gobe ".
"Da kako k'yauta Mubarak kayi sauri kaje kace ta dawo gida hakanan,,, saboda ina tsoron kada
Alhaji ya dawo bai sameta gida ba. Nasan ni zai azama fad'a ni kuma ban aiketa ba wurin yin
wasan banza ba ".Cewar Mama Sa'ima cikeda damuwa da tsoro..
Mubarak ya dubi uwar yace "ki daina damuwa Mama yanzu nan zan turo k'eyarsu,, insha Allahu
Alhaji ma bazai san ta fita ba ".
Uwar tace "to Allah yasa tun can ka fara dukan shegiya domin Maryam agaskiya batajin
magana,, kullum ina gaya mata idan ta fita wasa ta daina kaiwa azahar bata dawo gida ba.
Amma tayi kunnen uwar shaggu da maganata saboda tana son babanku ya sani gaba ya cimin
mutunci,,, wallahi yau kam sai jikinta ya gaya mata zata yabama aya zak'inta ".Ta fad'a cike da
jin haushin Maryam.
Mubarak ya mik'e tsaye sannan ya dubi mahaifiyarsa,, cikeda lallashi yace "kiyi hak'uri Mama
Maryam bazata koma dad'ewa awaje ba,,, yanzu zanje in korosu su dawo gida wlh amma dan
Allah kada ki duketa Mamanmu ".
"Naji bazan duketa ba ,,, saboda kai ka haifarmin 'yar ko Mubarak ".Inji Mama Sa'ima cikeda
sababi da masifa.
Mubarak ya sassauta murya yace "ba haka bane Mamanmu,, ganin nayi bugu baya magani sai
dai addu'a da nasiha Allah ubangiji ya shirya mana zuri'armu. Kuma ya huci zuciyarki yake
mahaifiyata,, kiyita hak'uri damu wata rana sai labari ".
Jikin Mama Sa'ima yayi matuk'ar sanyi akan maganar Mubarak,,hak'ik'a tasan duk abinda ya
fad'a gaskiya ne babu k'arya acikin maganarsa. Kuma tasan Mubarak yaro ne mai natsuwa da
iya kalamai masu dad'i da kwantar da hankali ga mai sauraronsa,, sannan yanada kaifin tunani
da hangen nesa,, Mama Sa'ima ta numfasa tace "na hak'ura Mubarak Allah ubangiji yayi muku
albarka,,, sannan ya shirya mini ku shirin addinin musulunci ".
"Amin Mamanmu,, toni zan wuce yanzu ".Cewar Mubarak.
Maman tace "Allah ya kiyaye hanya Mubarak yasa kayi saurin ganosu ".
Mubarak yace "Amin ".
Yaja k'ofar gidan ya bud'e tareda da fita,,, domin ya koro su Maryam su dawo gida hakanan..
**********************
Su Maryam suna tafiya suna fira har sukazo bakin k'ofar gidan Iya Gwamma,,, sukaja suka
tsaya suna jiran harta iso dayake sun fi ta saurin yin tafiya kunsan abu da tsohuwa. Suka zauna
suna hutawa can saiga Iya Gwamma ta iso tasa makulli ta bud'e musu k'ofar gidan,,, ta
umurcesu dasu shiga cikin gidan dayake yara ne sosai babu wanda yasan ciwon kansa. Suka
kutsa kai zuwa cikin gidan tareda Iya Gwamma,, suna shiga babu kowa cikin gidan sai
komattsai da raggad'ud'an Iya Gwamma. Babu abinda ke tashi cikin gidan sai k'amshi soyen
nama da k'arnin jini,,, dayake su Maryam yara ne babu abinda suka fahimta gameda Iya
Gwamma .
Iya Gwamma ta tura ganbun d'akinta ta shiga cikin d'akin,,, ta d'an jima sosai sannan ta fito da
kud'i ga hannunta d'ari uku da hamshin. Taba Fatima kud'in tana shafar hannun Fatima da wayo
da wayo,,, tace "gashi ku siyomin biredi na d'ari da hamshin madara ta naira d'ari,,, inada sugar
da bonbita naira d'arin da ya rage ku d'auka na baku "..
Fatima tace "mun gode Iya amma da kinbar kud'inki,,, ki k'ara ki sayi wani abu ".
Iya Gwamma tazo wurin kan Maryam tana shafa cikin dabararsu ta mayyu,, tace "Ayya 'yar nan
k'yautace na baku kuma ba'a maida hannun k'yauta baya ".
"dallah rufe mana baki! Munce kibar kud'inki amma kinzo kinata damunmu da surutunki na
banza,, bamu son kud'inki ko ana amsar k'yauta dole ne "Inji Fadila cikeda fitsara da tsiwa.
Iya Gwamma ta dubeta cike da tsananin mamakin rashin tsoronta,, ta bugi Fadila da wasa tace
"amma yarinyar nan bakida kunya,, kinsan koni wa cece nayi fa jikanya dake yarinya".
Fadila itama ta dunk'ule hannunta cikeda rashin kunya,,, tayima Iya Gwamma mugun bugu a
bayanta. Saida Iya Gwamma ta zabura da k'arfi! Tana mamakin k'arfin hali da rashin tsoro irin
na Fadila. Fadila ta harari Iya tace "ina ruwana da kin yi jikanya dani tsohuwa,,, sannan sanin
koke wa cece bayada wani amfani gareni! ".Tana murgud'a bakinta.
Hak'ik'a Fatima da Maryam sunyi matuk'ar jin tsoro da firgita! Akan abinda Fadila tayima Iya
Gwamma,,, babu abinda jikinsu keyi sai makarkatar tsoro da fargaba. Can dai cikeda masifar
tsoro suka had'a baki wurin cewa "dan Allah Iya kiyi hak'uri wallahi haka Fadila take da tsiwa ".
Iya Gwamma idanunta sukayi jawur saboda b'acin rai zuciyarta sai tafasa takeyi akan bak'in
ciki,,, jijiyoyin kanta sukayi rud'u rud'u akan b'acin rai. Can tayi ajiyar zuciya na bak'in ciki ta
daure tace "babu komai yaran nan amma ta sani taci alfarmarku,,, da wallahi bazata sake yima
wani rashin kunya ba,,,amma ta je duniya ce zata ga abinda zai biyo baya! "".
"Mtsss aikin banza! Babu abinda zan gani sai alkhairin Allah,, kurwata kur! Kici kanki kisha
bak'in ruwa ".Cewar Fadila tana tofar da yawu,, cikeda masifa da bala'i. Su Maryam ne sukaja
hannunta da k'arfi suna bata hak'uri,, suka nufi hanyar zuwa shagon Mande suna tafiya Fadila
tana ta masifa da bala'i,,, haka suka kama bata baki suna lallashinta. Suna isa shagon Mande
dole tayi shiru suka siye abinda ya kaisu sannan suka juyo zuwa gidan Iya Gwamma.
Suna dawowa suka ba Iya Gwamma aikenta,, sannan su Fatima suka k'ara bata hak'uri akan
abinda ya faru. Ta nuna musu babu komai ai tareda yi musu godiya sosai. Sannan sukayi
juyawarsu zuwa gidajensu. Bayan fitarsu ne Iya Gwamma ta k'yalk'yale da dariyar mugunta
harda fad'uwa k'asa akan makirci,, can tace '"hak'ik'a Fadila kin kawo kanki gidan mutuwa! Sai
kinsan kinyi mini rashin kunya. Ko 'yan uwanki da basuyi min komai ba,,, bazan tab'a k'yalesuba
balantana ke mara mutunci,, zakiyi nadamar abinda kika yimin a rayuwarki! "Hhhhhhhh haka dai
Iya Gwamma ta cigaba da surutunta na son ganin bayansu Maryam..........
_More comment more typing_
_Mugirat Musa_
,
[6/21, 9:53 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 2*
***Iya Gwamma ce ta kama surutunta na hauka,, mai cikeda bak'in ciki da b'acin rai akan
abinda Fadila tayi mata. Can naga Iya Gwamma ta shiga cikin wani d'akin da yake gefen
d'akinta da take barci da saka kayayyakinta,, tana shiga ciki ta fito da wata k'warya cikeda jinin
mutane. Ta samu wuri saman tabarma ta zauna tanata sambatu da maganganu irin na masu
sihiri da tsafi,,, ta jima tanayi saiga rugugin tsawa da hayak'i! Suna bayyana ruwan jinin dake
cikin k'warya suna chanza kala daga ja zuwa kore-kore. Nan da nan naga ruwan jini sun fara
tururin tafasa,, kamar an azashi saman wuta. Nayi duba zuwa ga idanun Iya Gwamma sunyi
jawur kamar barkono,, ga jijiyoyin kanta sun mik'e tsaye rud'u rud'u halittar jikinta gaba d'aya ta
chanza,, ko'ina a cikin jikinta gashi ya k'ara tsawo zago -zago kamar k'aho,,, bakinta babu
abinda ke fitowa sai wuta mai mugun zafi. Can naga tayi wasu d'alamisai na tsafi saiga
photonsu Maryam su uku ya bayyana a cikin k'warya,, suna tafiya zuwa gidajensu. Iya
Gwamma tayi duba cikin k'waryar jini da idanunta jawur kamar kan jaki,,, tace" saina kasheku!
Saina cinye namanku d'anye yara! Zan nuna muku ba'a yima mayyu rashin kunya akwana
lafiya,,, hhhhh na kama kurwarsu ni Gwamma jikar mayya d'iyar *MAYYA* .Saina banbance
muku atsakanin aya da tsakuwa,,, k'ananan marasa kunya kawai daku! ".
Haka dai ta cigaba dayin sambatunta,, tana tofe -tofe a cikin k'warya. Saiga inwar kurwarsu
Fadila ta bayyana a cikin k'warya,, Iya Gwamma ta k'yalk'yale da dariyar mugunta da kuma farin
ciki mara misaltuwa na cikar burinta....
**********************
Su Fadila suna tafiya suna firarsu cikeda walwala,, kamar babu abinda ya faru dasu agidan Iya
Gwamma. Basu jima sosai ba suka had'u da yaya Mubarak,, bayan sun kawo wajen garkar
gidajensu. Yaya Mubarak ya dubesu cikeda matuk'ar mamaki yace "Yara manyan gobe ina kuka
shiga ne,, tun d'azu nake zagayar gari nemanku ".
Maryam da Fatima suka sunkuyar da kansu cikeda fargabar da irin amsar da zasu bashi,,, tsoro
da fargaba ne ya bayyana k'arara akan fuskokinsu. Su biyu ne suka dubi Fadila domin
sunsanta wurin rashin tsoro da dauriya,, da iya tsara k'arya da gaskiya akan lamarin rayuwa.
Fadila ce ta numfasa tareda k'yafta musu idanu akan su saki jikinsu,, kada yayi saurin gano
abinda zata furta k'arya ne. Su Maryam suka gyad'a mata kai alamar to,, duk da yake babu
abinda sukeyi sai wuru -wuru da idanunsu alamun rashin gaskiya duk ya bayyana a fuskokinsu.
Fadila ce tayi murmushi mai k'ayartar da fuskarta tace "yaya Mubarak wasa mukaje gidan
k'awarmu Hassana,, shiyasa ne kayi nemanmu baka ganmu ba ".
Mubarak yayi shiru na minti biyu yana nazarin maganar Fadila,, amma acikin zuciyarsa ko
kad'an bai aminta da maganarta ba. Domin kuwa kallon d'aya yayi musu ya gane basuda
gaskiya,, amma dayake shi ma d'an zamani ne ya nisa sannan yace "Ok ba matsala amma dan
Allah ku daina dad'ewa awaje,, wurin yin wasa domin kuwa yanzu zamanin nan namu ya lalace.
Akwai abubuwa da yawa da zasu iya cutar daku wanda bana fatar haka,, saboda zuciyata
bazata iya d'aukar hakan ba ".
Fatima taja dogon numfashi tace "insha Allahu yaya zamu kiyaye maganarka,, ai domin muje
gidansu Hassana ne yasa muka dad'e sosai".
"haka ne gaskiya yaya Mubarak ai da tun d'azu mun dawo gida ".Cewar Maryam.
Mubarak yace "to 'yan k'annena na yarda daku nasan ba zakuyi abinda za'a ce Allah yayi
wadaran da halinku ba,, saboda haka ku wuce zuwa gida ".
Fadila tace "zamu kiyaye yayanmu karka damu ".
"Allah yasa da gaske kukeyi ".Inji Mubarak.
"Amin Yayanmu ".Cewar Fatima da Maryam atare cikeda sanyin jiki. Yaya Mubarak saida ya
raka Fatima da Fadila har bakin k'ofar gidansu,, dayake gidansu d'aya baban Fatima shine
yayan baban Fadila. Bayan yah Mubarak yaga shigewarsu cikin gidansu,, yazo yaja hannun
Maryam yana yimata nasiha tareda maganganu masu lurassuwa cikin hikima da iya magana..
**********************
Mubarak ne da Maryam suka shigo cikin gidan,, tareda da furta sallama a bakinsu. Mama
Sa'ima ta amsa musu yayinda take k'ok'arin kwashe sharar da ta kammala yanzu nan,,, tasa
parker ta kwashe sharar tana zubawa cikin kwandon shara. Alokacin ne Mubarak da Maryam
suka k'araso cikin tsakar gida,, suka samu wuri suka zauna saman tabarma. Mubarak ya dubi
Mama Sa'ima yace "sannu da aiki Mamanmu "."Yauwa Mubarak".Inji Mamansu bayan ta fito
daga wurin kwandon zuba shara,, ta zauna kusaga Maryam ta harareta tace "sannu Maryam
sarkin yawo,, Mubarak gidan uban wa kagansu? ".
Maryam ta sunkuyar da kanta cikeda matuk'ar tsoro da fargaba! Tace "Mama dan Allah kiyi
hak'uri gidansu Hassana mukaje wasa ".
"tabbas haka suka gayamin Mama,,,tayi ba dai-dai ba ayi mata hak'uri bata sakewa ".Cewar
Mubarak.
Mama Sa'ima tace "naji Mubarak amma wallahi Maryam ki kiyayeni ! Inba rainin wayo da
hankali ba,,, ki fita daga cikin gidan nan tun safe baki dawo cikin gidan nan ba sai yanzu bayan
azahar. Saboda bak'yajin maganata to zan gayama babanki nasan shi ,,,zakijin maganarsa
saboda kinajin tsoronsa mara jin magana kawai ".
Maryam ta fara zubarda hawaye ,,,muryarta tana rawa tace "na tuba Mama ki rufamin asiri kada
ki gayama baba,,,,wayyo wayyo Allah! Wayyo kaina wallahi Allah bana k'arawa komi kikace shi
zanyi Mama. Yaya Mubarak ka taimaka ka k'ara bata hak'uri kaji ".
Yaya Mubarak ya dubeta cikin tausayawa da k'aunar k'anwarsa,,, yasa hannu ya jawota ya
rungumeta a jikinsa yana lallashinta. Yace "ya isa ya isa Maryam share hawayenki Mama zata
hak'ura kinji,, kuma idan Allah ya yarda bazan bari ta gayama Alhaji abinda ke faruwa ba ".
"To Yaya ".Cewar Maryam tana shessheka tana ajiyar zuciya,, saboda kukan da tayi.
"to tashi uwar son jiki kije kiyi wanka sannan kici abinci,,, nidake ne a cikin gidan nan matuk'ar
kikace bazakiji maganata ba,,,,sai rayuwarki tayi matuk'ar b'aci sosai wawuya wadda bata san
ciwon kanta ba"..Inji Mama Sa'ima cikeda matuk'ar b'acin rai