Showing 27001 words to 30000 words out of 58121 words

Chapter 10 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf

Advertisement

12 Jul 2025

3006

batada
tausayi da tauhidi ko kad'an,,, ita fa arayuwarta bata yarda da k'addara ba indai akan kishiya ce
da cikar burinta.





_Agurguje please._









Bayan wasu kwanaki Malam Mamman ya warke garau ya cigaba da harakokinsa,,, tafiya tayi
tafiya Malam ya nemi wata mai suna Jummai da aure itama dai ana sauran kwana d'aya da

auren ta rasu!.
Sai da Malam Mamman ya nemi mata d'aid'aya har guda bakwai suna mutuwa,, sauran matan
sune Karima, Labiba,, Nuratu,, Ummu,,, Lantana,, Falmata,,, Laraba,, Zainabu,,, duk garin gaba
d'aya ya d'auka Inna Talatu *MAYYA CE* saboda alokacin basusan Gwamma ta fara maita ba .









Suka zama abin gudu da tsoro a cikin garin gaba d'aya,, babu mai zuwa inda take daga 'yan
uwan Malam Mamman har nata kowa gudun ceton ransa yakeyi,,, ko ahanya ne aka tsinkayo
Inna Talatu daga nesa sai kaga kowa ya watse domin ceton ransa,,, tun Malam Mamman bai
fara yarda da maganar mutane fa har yazo ya fara yarda da maganarsu,,,aiko arana nan ne
yayi mata mugun bugu sosai yana zaginta.









Ya dawo kamar ba Mamman ba yana yi mata walak'anci da rainin wayo iri iri daban daban,, shi
kanshi alokacin wani tsanar Inna Talatu ne ya dirar masa a zuciya,, yanason ya saketa amma
yana ganin idan yayi haka bai dace ba .








Ganin irin abubuwan da Malam Mamman keyi mata na walak'anci da duka sosai,, tabbas taga
alamar idan batayiwa abin tufkar hanci da wuri ba zai iya tona mata asiri cikin mutane.

Nan da nan batare da b'ata lokaci ba Inna Talatu ta kama kurwar Malam Mamman,, ta mayarda
ita zakara ta cinye d'anye bata tsaya gasawa ba to aranar saida taci kusan fara goma zama
guda bayan ta Malam Mamman cikon na goma .








Ina lillillahi wa inna ilaihirraji'un!!! Washe gari da safe mutanen gari suka shiga cikin
matsananciyar tashin hankali da bala'i babu abinda sukeyi sai kuka da ifface ifface ,,saboda
bayan Mamman mutum tara ne suka rasu alokaci guda idan kayi duba zuwa ga jama'a zakaga
mutane idanunsu jawur,,, fuska duk ta kumbura sosai bak'in ciki duk ya bayyana a fuskokinsu
k'arara,, haka dai akayi jimami da bak'in cikin rasuwarsu Malam Mamman kowa ya watse.







Ganin da Lawwali yayi mahaifiyarsa ta kashe masa mahaifi! Yasa ya tashi tun kafin ayi sallar
asuba ya gudu ya koma wurin k'annen mahaifinsa Labbo,, aka wayi gari Inna Talatu ta nemi
Lawwali sama da k'asa ta rasa........

_Share&Comments_
[6/28, 1:56 PM] Mugiratmusa66:





*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_



*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 16*





Inna Talatu ta nemi Lawwali sama da k'asa ta rasa a cikin gidan,,, nan da nan hankalinta yayi
k'ololuwar tashi cikin kid'ima da fargaba,, haka dai ta daure ta cigaba da harakokinta na cin

naman mutane,, Gwamma itama ba baya wurin kamun inwar kurwar mutane tana cinyewa
d'anye ba babu tausayi ko rahama acikin zuciyarta ko kad'an,,,mutane sai k'ara tsoracewa da
katsewa akan lamarin mayyu sukeyi...








**Inna Talatu ce da Gwamma zaune suna tattaunawa akan yau,,, wa ne gari zasuje kamun
inwar kurwar mutane suje can batare da b'ata lokaci ba,, Inna Talatu ce ta dubi Gwamma tace
"Gwamma har yanzu bakijin labarin ina Lawwali yaje ya b'oye ba,, acikin garin nan
wai?".Gwamma ta karkace baki tace "Inna ayau da dare da naje kamun inwar kurwar mutane,,,
na ganshi acan gidan baba Labbo yana b'oya saboda kada ki ganshi wai ".Inna Talatu ta bushe
da dariya sosai tace "hmm to ai ko ya gudu ya b'oye can bai tsira ba,, saboda idan inason inci
naman jikinsa abu ne mafi sauk'i a wajena ".






Gwamma tace "nima naga wautarshi Inna ai kamun inwar Lawwali shan ruwa ma yafisa wuya
sosai,, abinda ya aikata rashin wayo ne babba ".










Inna Talatu tace "yaje yayi tayi fa sannan ina son inja miki kunne ki rik'e wannan haraka ta maita
hannu bibbiyu,,, saboda muddin kinayinta babu mai rainaki cikin mutane kowa shakkunki zai
dinga yi,,, domin inason ki shahara da gunguma fiyedani inason duniya tasan da zamanki ".

Gwamma tace "zanyi iya bakin k'ok'arina kuma zan kasance mai biyayya ga boka LOK'ORO
,,har sai burinmu ya cika Inna bana wasa a cikin wannan sana'ar gado wato maita !"





"zaki ko shahara sosai da zama gagararriya acikin mutane da aljannu,,, babu wanda ya isa ya
tab'aki ".Cewar Inna Talatu cikeda matuk'ar farin ciki da murna sosai..





Gwamma tace "naji dad'i sosai Inna dazan shahara a duniya ".







Inna Talatu tace "ba zakiji dad'i sosai ba sai nan gaba kad'an,, idan shahararki ta bayyana a
cikin wannan gari ".






Gwamma tace "to Innata ta kaina".

Haka dai suka cigaba da shawarwari ta yadda zasu b'ullowa al'amarin kamun inwar kurwar
mutane,, da kuma yadda zasu gudanar da komai cikin sauk'i....








¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤







*BAYAN SHEKARA BIYAR*




**Abubuwa da dama sun faru acikin wad'annan shekarun da suka wuce,, ciki kuwa harda
kamun kurwar mutane dasu Inna Talatu keyi suna cinyewa,, domin abin nasu yayi tsamari sosai
sun hana shak'at da jin dad'i a cikin gari,, mutum bayada halin ya fito daga cikin gidansa ya
dad'e yana a cikin kasuwa face sun kamesa,, ganin sun addabi rayuwar mutane yasa kowa
yake addu'ar Allah ubangiji ya kawo k'arshen Inna Talatu MAYYA.
Saboda har yanzu basusan Gwamma ta zama k'usurgumar *MAYYA CE* shahararra a wurin
mugunta da cin naman mutane,, domin ayanzu tanada shekara goma sha takwas Lawwali kuwa
sha shida,, tamafi Inna Talatu mugunta saboda ita har naman aljannu ci takeyi saboda ta
shahara da gunguma akan maita! Tana alak'a da dodanni wurin abokanka,,, batada tsoro ko
shakku uban kowa duk abinda takeso shi takeyi.








Ganin da mutane sukayi kashe rayukan da akeyi agarin nan yayi yawa,, yasa dole suka fara
takon sak'a da Inna Talatu sukayita d'ana mata tarko tana tsalkewa,,, domin duk abinda sukeyi

tana ganinsu cikin tsafinta,,, ganin abinda suke mata yayi yawa sosai.










Yasa dole wata rana da misalin k'arfe 10:00am na safe,,, bayan sunyi karin safe itada Gwamma
tace mata zataje can wurin boka LOK'ORO,, ta tsaya ta fake gida yanzu zataje ta dawo,,,
Gwamma ta nuna mata babu matsala saita dawo.
Inna Talatu ta shirya sannan ta saka kai tayi wucewarta zuwa wurin boka LOK'ORO..








********************






Inna Talatu ta girgiza ta rikid'a ta koma kaza sannan ta kama hanyar zuwa cikin k'usurgumin daji
mai duwatsu,, dajin da boka LOK'ORO ke rayuwa acikinsa na tsawon shekaru,,, tana isa inda
yake ta girgiza sannan ta rikid'a zuwa siffarta ta ainahi,,, wata irin mahaukaciyar guguwa ce ta
ratso kusa gareta tana girgizawa da zagayarta na wani lokaci kad'an,, can dai komai ya tsaya
cak guguwar ta daina yawo ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma boka LOK'ORO,, idanunsa sunyi
jawur kamar barkono jijiyoyin kansa sun tashi rud'u rud'u halittar yanayin jikinsa duk ya chanza,,
ya bud'i baki yace mata "nasan mi yake tafe dake Talatu,, amma ki sake gayamin da bakinki
saboda wak'a abakin mai ita yafi dad'i ".

"ya maigirma boka LOK'ORO abubuwa da dama sun faru acikin wannan lokacin,,, mutane
yanzu so suke su kasheni har abada,, sunyi d'anamin tarkuna har sun gaji ina tsallakewa,, ka
sanardani ta yadda zan k'ara kare kaina".Inji Inna Talatu cikeda matuk'ar sanyin jiki.








Tana gama fad'in wannan maganar boka LOK'ORO ya bushe da mahaukaciyar dariya sosai,,
wanda sanadiyyar hakan saida k'asa ta kama rawa yace"Talatu babu wani taimakon dazanyi
miki domin alk'alami ya riga ya bushe,, mutuwarki ta kusantoki! Ajalinki yana zuwa agareki
kwananki ya kusa k'arewa ".





Hankalin Inna Talatu ya d'unguma sosai zuciyarta sai bugawa takeyi da k'arfi da k'arfi,,
rayuwarta idan har tayi dubu to ta b'aci sosai,, ta d'ago idanunta jawur tace "boka LOK'ORO wa
ye zai kasheni sannan ya zamo ajalina? ".






"Sala mafarauci k'anen baban Lado shine zai kasheki! Amma ba'a cikin sauk'i zai kasheki ba
'yarki Gwamma itama ta kashesa,,, sannan abin yazo ya zamar musu gaba mai tsananin gaske
itada Ummaru d'an Sala mafarauci,,kinga kuwa bakida damuwa domin ak'alla ko kinyi k'aranci
kinci naman mutane fiyeda dubu 'yarki Gwamma taci d'ari ".Inji boka LOK'ORO yana dariyar
mugunta da rashin tausayi!.

Inna Talatu ta bushe da dariya sosai sannan tace "hak'ik'a nayi matuk'ar farin ciki da wannan
maganar taka boka LOK'ORO,,, aini burina ya cika koda ya kasheni saboda 'yata ta zamo
shahararriyar *MAYYA CE* gagararriya acikin mutane da aljannu,, saboda haka banida fargaba
ko shakku akanta ".





Boka LOK'ORO yace mata "tabbas haka ne Talatu ,,,ki tafi zuwa gidanki na barki lafiya ".






Yana gama fad'ar wannan magana ya b'ace b'at kamar bai tab'a wanzuwa a wurin ba,,, Inna
Talatu tana ganin boka LOK'ORO ya tafi itama ta rikid'a ta zamo kaza ta k'ara gaba domin zuwa
gida...








¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤





Inna Talatu ta koma gidanta ta cigaba da harakokinta itada Gwamma,, amma bata sanarda ita
abinda boka LOK'ORO yace ba na gameda da mutuwarta ba,, saboda kada ta tayar mata da
hankali.
Haka dai suka cigaba da rayuwarsu ta cin naman mutane da aljannu,,, cikeda matuk'ar
kwanciyar hankali.

*BAYAN KWANA BIYU*





Bayan kwana biyu da faruwar magana atsakanin Inna Talatu da boka LOK'ORO,, bayan sun
tashi da safe ne sun karya Inna Talatu tace ma Gwamma zataje daji domin ta d'ebo
ganyayyakin da zata had'a wani magani,, Gwamma ta nuna mata babu matsala saita dawo,,
Inna Talatu ta shirya tayi cikin k'urgumin daji Gwamma tana ganin ta fita itama tayi wurin kamun
inwar kurwar mutane da satar kayan jama'a har cikin gida.









Inna Talatu ce ta shigo k'usurgumin daji mai duhu da yawan itatuwa,, yanada manyan duwatsu
babu abinda ke tashi cikin dajin sai kukan tsuntsaye dana namun daji daga ganin halittar dajin
kasan ba za'a rasa k'wamak'wanmai acikinsa ba.
Inna Talatu ta falfala da wani azababban gudu tana hawa saman wannan icce ta sauka tahau
wancan bishiya,, haka dai ta kama yawo acikin dajin cikin tsafi da sihiri harta kallama had'a
ganyayyakin da suka kawota,, ta juyo ta kama hanyar zuwa gida tana tafiya tana wak'e
wak'enta.




Tayi nisa da tafiya kenan kwatsam! Sai taga Sala mafarauci agabanta kamar an jefosa,,
hannunsa rik'eda kwari da bakansa ga kuma kibiyar halbi a d'ayan hannunsa,, jikkarsa ce goye
abayansa ya kamo namun daji irinsu,, kura,, damo,, zomo da maciji.

Inna Talatu taja tayi tsaye turus gabanta sai bugawa yakeyi da sauri da sauri,, ta daure ta
dubesa da jajayen idanunta b'acin rai k'arara ya bayyana akan fuskarta tace "kai Sala mafarauci
lafiya ka taremin hanya,, mi kake nufi ne dani wai? ".







Sala mafarauci yace "kasheki zanyi Talatu saboda na dad'e ina d'ana miki tarko kina
tsallakewa,, kin addabi mutanen gari da cin namansu saboda rashin imaninki ko jariri baki bari
ba,, yau zan kawo k'arshen rayuwarki da zaluncinki! Ayau komai naki zai zama tarihi ".








"k'aryarka tasha k'arya Sala mafarauci ayau kaine zaka zama gawa bani ba,, sai dai uwarka ta
haifi wani d'an idan tana raye amma ba kaiba,, ayau zaka d'and'ani d'acin mutuwa kwanciyar
kabari shine yafi dacewa dakai a yanzu babu b'ata lokaci ".Inji Talatu cikeda matuk'ar tashin
hankali da bala'i!.




Sala mafarauci yace "lallai kuwa ayau zakiyi nadamar duk abinda kika aikata saina banbance
miki tsakanin k'arya da gaskiya! ".






Yana rufe bakinsa suka afkawa juna da azababban fad'a mai cike da rikitarwa da tashin hankali!
Sara da suka kawai suke kaima juna cikin matuk'ar juriya da zafin nama.

Sala mafarauci yayita amfani da kwari da bakansa yana kaimata hari tana kaucewa,, sannan ya
sareta da takobi ta kauce ya sari iska,,, kibiyarsa ya jefa mata ta kama kallon kibiyar da
idanunta,, siririn haske ya bugi kibiyar ta juya domin ta chake Sala mafarauci ya kauce cikin
zafin nama da juriya,, haka itama tayita jefo masa abubuwan sihiri irinsu wuta,, mashi,, wukake
k'anana yana tsallake tarkonta.









Sun dad'e sosai suna azabtar da juna duk sun yiwa juna rauni sosai,, jini sai zuba yakeyi daga
jikinsu akan fad'a,, amma duk da hakan basu daina ba Sala mafarauci ganin yayi Inna Talatu
MAYYA tana batun kashesa a banza da yofi! Dole ya k'ara tattaro dauriya da hakurinsa ya sake
afka mata cikin zafin nama ya sanya takobinsa yana ya sare mata kai ,,ai kuwa yana sare kan
Inna Talatu jini ya kama bulbulowa kamar teku mai ambaliyar ruwa.





Wani irin rugugin tsawa ne ya bayyana dajin ya kama rawa da girgiza komai na cikinsa ya kama
da wuta!,, Namun daji da tsuntsaye suka kama gudu domin ceton ransu,, alal hak'ik'a Sala
mafarauci yaga abin mamaki da al'ajabi akan mutuwar Inna Talatu,, yasa hannunsa ya d'auki
kan Inna Talatu da ya rabuda gangar jikinta yasa acikin jikkarsa ,,,yana sakawa wani k'aramin
rami ya bayyana akusa da jinin jikin Inna Talatu,,, abin mamaki jinin ya dinga shiga cikin ramin
har ya k'are tsab sannan gangar jikin Inna Talatu ta k'ara matsawa agefen bakin ramin.







Jinin yana k'are shiga ramin,,, ramin ya rufe kansa kamar bai tab'a bayyana a wurin ba,, Sala
mafarauci ya juya zuwa hanyar zuwa gida yana tafiya yana tangad'i kamar mashayi,,, ga jinin
Inna Talatu duk yayi masa faca faca a jiki ga wani zafi da rad'ad'in ciwon da taji masa sosai,
akafarsa ta dama harta zaftari namansa babba yana shillo,,, dak'yar da bala'in dauriya ya kawo
gidansa yana kawowa bakin garka ya fad'i k'asa rikcham ya some.

*Ab'angaren Gwamma kuwa bayan ta tafi wurin sace sacenta da kuma kamun inwar kurwar
mutane,,, ta jima sosai a wurin kamun kurwar mutane sannan daga baya ta dawo gida tayi
wanka tana jiran dawowar Inna Talatu.




Tana, zaune taji gabanta ya buga da k'arfi rassssss! Hankalinta yayi k'ololuwar tashi sosai
zuciyarta tana yi mata k'una da tafasa sosai,,, haka kawai taji hawaye sun zubo daga idanunta
jijiyoyin kanta sun mik'e tsaye rud'u rud'u halittar jikinta gaba d'aya ta chanza kammani,, safa da
marwa kawai takeyi a cikin d'akin ita kanta ta rasa dalilin dayasa hankalinta yayi matuk'ar tashi
sosai,, zuciyarta tana yi mata suya da tafasa sosai .......















_Share&Comments_



*Muje zuwa*
[6/28, 4:34 PM] Mugiratmusa66:






*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_



*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 17*






Zuciyarta ta kama tafasa da k'una sosai,, hakan ne ya tabbatarwa Gwamma akwai mugun abun
da zai faru marasa k'yau ko ya faru ,,,hankalinta ya sake tashi ta dubi agogo bango ganin har
Inna Talatu MAYYA ta zarce kusan awa biyar awaje,,, bata dawo gida ba gashi ita kad'ai cikin
gidan babu mai shigowa ko lek'owa ganin mahaifiyarta ta jima sosai a waje,,, yasa ta yanke
shawarar bari ta bita can inda taje ta nemota ta dawo gida,,, sai da Gwamma tasa tsintsiya ta

k'ara sharen gidan sannan tayi musu girki domin tarbon dawowar mahaifiyarta,,, tana kamalla
komai da komai ta sake wanka ta shirya cikin tufafinta masu dama dama,,tana shiryawa ta
d'aga hannunta sama tana sambatu na tsafi da sihiri ta jima sosai tanayi,,,, saiga wani bak'in
abu ya bayyana yana zagayarta can naga ya shige cikin jikinta ta rikid'a ta koma tsuntsuwa fara
tass,,, tana komawa tsuntsuwar ta fito filin gida ta bud'e fikafikkanta ta tashi sama ta lulluk'a a
cikin sararin samaniya tana ta matsiyacin gudu kamar aljana..














**********************





**Ab'angaren Sala mafarauci kuma bayan ya fad'i k'asa abakin k'ofar gidansa ya suma,,, duk
jikinsa jinin Inna Talatu ne da kuma mugun raunin da taji masa hak'ik'a ya zubar da jini fiyeda
kima,, ya dad'e kwance a k'asa babu wanda ya gifto can saiga Ummaru d'ansa da yayansa
Labaran baban marigayi Lado sunzo bakin k'ofar gidan zasu shiga ciki,,, suna kawowa suka
iske Sala mafarauci cikin jini kwance a k'asa ya suma,, sukaja suka tsaya,, baba Labaran ne
yace "Subahanillah Ina lillahi wa inna ilaihirraji'un! Sala ne akwance cikin jini Ummaru,, ko
namun daji ne sukayi masa haka amma bamu sani ba ".Ummaru yace "anyah kuwa baba
namun daji basu tab'a yima babana ba wannan mugun ta'addanci ba,, akwai dai abinda yake
faruwa dashi "."wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login