Showing 51001 words to 54000 words out of 58121 words

Chapter 18 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2987

mayya ce ta kamesu ba saboda wannan lokaci na yanzu yanada hatsari sosai,,,
musamman ga yara su rink'a fita yadda suka gadama batare da mayyu sun kamesu ba

"."Hmmm Allah ubangiji yasa ba mayya ce ta kamasu ba,,, dako mun shiga uku mun lalace!
Wayyo ni Allah kaiconmu da wannan mummunan al'amarin daya samemu ".Inji Mama Nafisa
cikeda da tashin hankali da *RUD'ANI*,,,,Umma Nusaiba tayi matuk'ar ajiyar zuciya da k'arfi!
Tace "ina lillahi wa inna ilaihirraji'un! Dako haka ne gaskiya muna cikin matsalar rayuwa,,,
saboda yadda mayyu suke addabar mutane agarin nan ya wuce misali,,, su kashe mutum su
cinye namansa ba'a bakin komai yake ba "."karku damu idan Allah ya yarda abin zai zo mana
cikin sauk'i sosai,,, zasu samu lafiya insha Allahu ".Inji Mama Sa'ima cikeda matuk'ar sanyin jiki
da zullumi,,, Umma Nusaiba tace "to Allah ubangiji ya basu lafiya,,, ya kuma yaye musu abinda
ke damunsu "."Amin ya rabbi ".Cewar Mama Nafisa cikin fargaba da zullumi..






*BAYAN KWANA UKU*




Jikinsu Maryam baiyi wani sauk'i ba gaskiya,,, saboda ciwon ya k'ara tsananta sosai sun k'ara
bak'i da ramewa k'warai da gaske,, duk mai imani idan yayima su Fadila kallo d'aya saiya
tausaya musu,,, musamman akan yadda ciwon yake hanasu barcin dare da iyayensu,,,, idan
ciwonsu ya tashi har kuwwa da kururuwar zafin ciwo da rad'ad'i sukeyi! Duk asibitin gaba d'aya
saiya gameda kuwwarsu da ifface iffacensu,,, kowa da yake asibitin saiya tausaya musu har
zuwa ganinsu akeyi akan matuk'ar tausayawa rayuwarsu Fadila,,, ni kaina ganin yadda suka
k'anjame da ramewa saida suka bani tausayi sosai,,, an canza musu yanayin kamanni sun
koma kamar skeleton babu k'yawon gani,,, ganin haka ne yasa hankalin iyayensu mata da
maza ya k'ara tashi fiyeda misali.










Suna zaune duk sunyi jugum sun fad'a duniyar tunani! Tashin hankali da bak'in cikin ne
bayyane afuskokinsu k'arara saboda rashin natsuwa da kwanciyar hankali duk sun rame sosai.
Can saiga doctor Sageer ya fito daga cikin office d'insa,,, yazo wurinsu Alhaji Suleiman dasu
baba Nazifi ya kallesu na tsawon lokaci yana nazari can ya bud'i baki yace "Alhaji kaine baban

Maryam? "(dayake yasan Alhaji Suleiman tun dad'ewa ).Alhaji Suleiman yace "nine Likita bokan
turai ".Sageer yayi murmushi sannan yace "to ina iyayensu Fatima Nura da Fadila Nazifi suke?
".Sukace"gamu nan "atare da juna.
"OK i want see you now all of you,,, muje office akwai maganar da nakeson in sanardaku mai
muhimmanci ".Inji doctor Sageer bai tsaya jiran jin maganarsu ba,, ya k'ara gaba su baba Nura
da Alhaji Suleiman suka mik'e tsaye sukace matansu su jirasu yanzu zasu fito,,,, su Mama
Sa'ima sukace to babu matsala Allah yasa muji alkhairi,,, baba Nazifi yace "amin "suka nufi
office d'in doctor Sageer da saurinsu.









Suna shiga suka iske doctor Sageer saman kujera ga takardu masu yawa asaman table,,, yana
rubuce rubuce sallamar da sukayi ne yasa ya d'ago kansa ya amsa musu cikin sakin fuska da
walwala,,, yayi musu bismillah dasu zauna saman kujerin dake cikin office d'insa suka zauna.











Yayi musu duba na fahimta da natsuwa sannan yayi ajiyar zuciya yace "Alhaji Suleiman ina
fatar zaku saurareni da k'yau kuyimin fahimta na natsuwa da ganuwa,,, sannan kuyi hak'uri da
irin kalaman da zasu fito daga bakina ".

Alhaji Suleiman ya dubi baba Nura,,, shima baba Nura ya dubi Alhaji Suleiman sannan sukace
atare "insha Allahu zamu fahimceka sannan duk abinda Allah ya k'addara mai k'yau ne ".Shi dai
baba Nazifi babu abinda yace kansa aduk'e yake,,, saboda k'irjinsa sai zafi yakeyi masa sosai
ga wani irin zogi da rad'ad'i da zuciyarsa keyi masa.








Doctor Sageer ya numfasa yace "agaskiya ciwon yaranku bana asibiti bane,,, domin munyi
bincike bincike ta hanyoyi da dama saboda mu gano kan matsalar ciwonsu ko bakin zaren,,,
amma ciwonsu yak'i ci yak'i canyewa sai k'ara cigaba yakeyi saboda haka amatsayina na doctor
ina baku shawarar,,, da kuje gida ku gwada na malamai ku gani ko za'a dace ".








"Alal hak'ik'a munji dad'in bayaninka da yardar Allah zamuje mu gwada na malamai ".Inji Alhaji
Suleiman cikeda matuk'ar sanyin jiki da fargaba.








Baba Nazifi ya bud'i baki dak'yar cikin rashin kwanciyar hankali da tashin hankali! Yace "babu
wani taimakon da zaka iya yi mana ayanzu ".

Baba Nura ya juyo ya dubi baba Nazifi yace "haba Nazifi miyasa bakada hak'uri ne,, bakaji
bayanin da yayi mana bane ko baka gamsu da bayaninsa ba? ".







Doctor Sageer ya tari numfashinsu yace "kayi hak'uri Malam Nazifi insha Allahu idan kuka
gwada na islamic za'a dace,,, kudai ku dage da yawan addu'a akan Allah ubangiji ya basu lafiya
"."Amin amin doctor Sageer mun gode k'warai da gaske Allah ubangiji yabar zumunci ".Inji
Alhaji Suleiman.






"Amin ".Cewar baba Nura doctor Sageer ya basu hannu d'aya bayan d'aya sukayi sallama da
juna,,, sannan su baba Nura suka fice daga office d'insa.








Kai tsaye wurin matansu suka wuce direct batare da b'ata lokaci ba,, suka sanarda iyalansu an
sallamesu daga asibiti sun fara had'a kayansu kenan saiga nurse Umaima ta kawo musu
takardar sallama,,, daga wurin doctor Sageer itace ta tayasu suka gama had'a kayayyakinsu
duka,,, sukayi mata godiya sosai sannan suka shige cikin motocinsu sunka nufi hanyar komawa
gidajensu,,, cikin rashin kwanciyar hankali da jimamin ciwon yaransu.

¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤






Iya Gwamma ce ta aza tukunyar tsafinta tsakar gida,,,,tana ta tsubbace tsubbacenta ga wasu
irin surutai da takeyi na sihiri marasa dad'in saurare da ji,,, wani irin tururin hayak'i da rugugin
tsawa fasss fasss fasss! Ya bayyana da k'arfin gaske ga wata irin razananniyar guguwa ta taso
da k'arfi ta game wurin yadda ko tafin hannu ba'a iya gani akan duhu! Idanun Iya Gwamma
sukayi jawur kamar wuta halshenta ya zazzago ya k'ara tsawo kamar maciji,,, jikinta gaba
d'ayansa gashi ya tsiro zago zago kamar dodanniya! Can dai guguwar ta tsaya cak ta daina
yawo tsawa da hayak'i suka tsaya wuri d'aya,,, tayi nuni da hannunta zuwa cikin tukunyar wani
irin bak'in abu ya shige cikin tukunyar batare da b'ata lokaci saiga photonsu Maryam ya
bayyana k'arara acikin tukunyar,,, duk abinda ya faru dasu tun daga lokacin da ta tura musu
ciwon da kuma kaisu asibiti da komai ma saida ta gani da idanunta!.







Wata irin mahaukaciyar dariya ce ta bushe da ita sannan tace"hhhhhhhh saini Gwamma d'iyar
Talatu k'usurgumar mayya na rantse da jinin mahaifiyata da kuma gadon maita! Yara yanzu
kuka fara wahalar ciwo akan rashin kunyarku,,, musamman ke Fadila babu uban da ya isa ya
hana in kasheki! In kashe ki!! In kashe ki!!! ".







Ta sake karanta d'alamisai na tsafi da sihiri,,, gidan gaba d'ayansa da tukunyar suka kama rawa
da girgiza da k'arfi! Ga wata irin wuta jawur da ta tsago akan tsakiyar tukunyar can batare da
b'ata lokaci ba boka LOK'ORO ya bayyana acikin tukunyar yana k'yalk'yalar dariya sosai!.

Iya Gwamma ta dubesa tace "boka LOK'ORO jikina ya bani na kusa mutuwa,, ajalina ya kusa
gabatowa gareni! Saboda haka saina kashe yaran nan guda uku kafin inbar duniya! ".








Boka LOK'ORO yace mata "tabbas haka ne gaskiya baki fad'i k'arya ba Gwamma,,, kin kusa
mutuwa har abada nima nasan bazasu tab'a barina in rayu ba,,, saboda haka ki zama cikin shiri
domin Ummaru d'an Sala mafarauci yana gab da tunkaroki domin ya kasheki ya d'auki fansar
jinin mahaifansa! "Da wata shegiyar murya tasa kamar tusar kare.






"zan zama cikin shiri akodayaushe ya mai girma boka LOK'ORO,,, na rantse da gadon tsafi da
maita! Shima Ummaru bazai tab'a iya kasheni cikin sauk'i ba saiya sha bak'ar wuya sosai a
rayuwarsa wadda bai tab'a shan irinta ba! ".Inji Iya Gwamma mayya.








Boka LOK'ORO ya bushe da mahaukaciyar dariya yace "karki damu zaki basa bak'ar wahala
kafin ya zamo ajalinki! Kedai kiyi taka tsan tsan da Ummaru d'an Sala mafarauci ".Yana rufe
bakinsa photon dake cikin tukunya ya b'ace b'at kamar k'iftawa da bismillah.

"to ya mai girma boka LOK'ORO zanyi biyayya agareka zan kiyaye da duk irin abinda zai biyo
baya ".Cewar Iya Gwamma cikeda shed'anci da ta'addanci.








**********************







Komawarsu Alhaji Suleiman gida yasa dole kowane daga cikinsu ya tashi tsaye,,, domin ganin
sun nemawa 'ya'yansu magani saboda su samu waraka daga cutar,,, haka yasa sukayi ta
kashin kud'i ana kawo musu magani na malamai iri iri daban daban,, to kunsan ciwo farat d'aya
yake shiga samun sauk'i kuwa da sannu sannu yake shiga,, ganin haka ne yasa hankulan
iyayen suka k'ara tashi sosai! Saboda ana shan magani amma ciwon sai k'ara anzama yakeyi,,
su dukansu aman jini kawai sukeyi sannan basu iya tashi a tsaye a zaune suke kashi azaune
suke fitsari babu k'yawon gani.
Haka iyayen nasu mata suke cigaba da kulawa dasu tareda zubar da hawayen bak'in ciki da
k'uncin rayuwa,,, domin su kansu ciwon yaran har tsoro yake basu saboda aganinsu kamar ba
zasu tashi ba mutuwa zasuyi,,, hmmm duniya ina zaki damu hak'ik'a ta'asar da mayyu sukeyi da
kashe rayuka cikin Al'umma baki d'aya yayi yawa sosai,,, saboda su mayyu da kuke ganinsu
basuda d'igon imani da tausayi ko kad'an a cikin zuciyarsu,,, komai suna iya aikatawa domin
ganin burinsu ya cika,, jama'a mu kiyaye dan Allah mu yawaita karatun qur'ani da addu'a akan
neman tsari daga shairin masu sharri,,, da iznin ubangiji Allah idan mutum ya kiyaye yawan
addu'a da karatun qur'ani babu abinda mayyu ko aljannu zasu iya yiwa mutum da iznin
Allah........
[7/10, 11:50 PM] Mugiratmusa66:





*MAYYA CE*









*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_



*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 30*




Da iznin Allah ba zasu iya cutar da mutum da komai ba,,, saboda haka mu kiyaye mu tashi
tsaye da dagewa da yawan yin azkar,,,, da yardar Allah babu abinda zai iya cutardamu komai
tsafinsa da sihirinsa.







Ciwon Maryam ya tsananta sosai ayanzu,,, duk da yake magani kala kala iri iri daban daban
ake bata domin samun dacewa da waraka,,,, duk ta k'ara lalacewa da k'anjamewa babu
k'yawon gani,,, Mama Sa'ima da Mubarak hankalinsu ya k'ara tashi matuk'a saboda irin wahalar
da Maryam kesha akan wannan ciwo!.

Mama Sa'ima ce zaune tana shafar kan Maryam tana zubar da hawayen bak'in ciki da takaici,,,
domin aganinta kamar ba zata warke daga wannan mummunan ciwon ba,,, Mubarak agefe
yana lallashinta shima kansa idanunsa sunyi jawur jijiyoyin kansa sun tashi rud'u rud'u! Saboda
rashin kwanciyar hankali da tashin hankali,,, amma ganin mahaifiyarsa tana kuka dole yasa ya
b'oye damuwarsa,,, ya tattaro natsuwarsa cikin dauriya yace "kiyi hak'uri Mama ki daina zubar
da hawayenki,,, babu abinda Maryam ke buk'ata yanzu idan ba addu'arki ba,,, sannan cikin
tsanani akwai sauk'i komai mai wucewa ne insha Allah ".







Mama Sa'ima ta d'ago jajayen idanunta,,, b'acin rai da bak'in ciki ne k'arara akan fuskarta tace
"ya zama dole in yi kuka Mubarak,,, idan Maryam ta mutu bansan yadda rayuwata zata iya
kasancewa ba,, duk nice silar faruwar hakan saboda ban hanata fita ba alokacin da zataje wasa
ba ".Ta sake fashewa da wani irin rikitaccen kuka mai cike da k'unci da bak'in cikin rayuwa.







"bakida laifi Mama ina son ki sani komai ya samu bawa muk'addari ne daga Allah,,, sannan
wannan ciwo da ya samu Maryam *K'ADDARA CE* bakida laifi ko kad'an,, ya kamata ki daure
ki sassautawa zuciyarki domin ki samu sauk'in rad'ad'i da zugin da kikeji acikin zuciyarki ".Inji
Mubarak cikeda matuk'ar tausayin kansu da Maryam.

Mama Sa'ima tace "bawai ban yarda da k'addara bane Mubarak,, wallahi na yarda da
k'addararmu amma har cikin zuciyata ina jin tsoron mayyu saboda zasu iya aikata komai,,,
domin babu imani acikin zuciyarsu ".








Mubarak ya dafa kafad'arta yana share mata hawayenta,,, shi kansa zuciyarsa sai tafasa takeyi
da k'una amma ya zama dole ya b'oye damuwarsa,,, agaban mahaifiyarsa domin kada ya k'ara
tayar mata da hankali,,, shi kansa yasha b'oyewa acikin d'akinsa yana zubar da hawayen bak'in
ciki da k'uncin rayuwa,,, ga tunane tunane da fargaba akan ciwon Maryam!.






Ya numfasa sannan yace "ki daina cewa haka Mama mayyu basu isa cutar da d'an Adam ba
saida yardar Allah mad'aukakin sarki,,,, sannan inason ki daure ki dinga hak'uri akan wannan
lamari,,, tabbas zata samu waraka ta warke kamar bata tab'a yin wannan ciwo ba ".







"Mubarak kenan nasan kana cikin damuwa,,, amma kake daurewa kana bani hak'uri tabbas kai
mai albarka ne a rayuwa,,, sannan Alhaji yace zaizo da wani shahararren Malami mai suna
Malam Usama,,, domin shima yayi nasa maganin ko za'a dace ".Inji Mama Sa'ima cikeda
matuk'ar fargaba da zullumi!.

Mubarak ya nisa yace "za ma adace da yardar Allah dama ciwo farat d'aya yake shiga acikin
jiki,,, lafiya kuma da sannu sannu take shiga jiki saboda haka ki kwantar da hankalinki,,, babu
abinda zai faru sai alkhairin Allah ".









Mama Sa'ima taja doguwar ajiyar zuciya da k'arfi! Tace "haka ne gaskiya amma zan daure inga
idan zan iya,,, domin kasan tsakanin uwa da d'a sai Allah ".








"tabbas haka ne Mama amma zaki iya daurewa domin gujewa kamuwa da wani ciwon ".Cewar
Mubarak cikeda tausayi da *SOYAYYAR GASKIYA* na tsakanin uwa da d'a.






Mama Sa'ima tace "to zan gwada Mubarak ".






"dako kin k'yautamin mahaifiyata ".Inji Mubarak.

Mubarak ya cigaba da kwantar mata da hankali,,, tareda lallashinta yana gaya mata
maganganu masu dad'i matuk'a,,, ita kanta taji bak'in ciki da rad'ad'in da takeji acikin zuciyarta
ya ragu sosai saboda Allah ya bata d'a nagari na kowa..







¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤








Suma Fatima da Fadila ciwonsu ya k'ara tsananta sosai,,, duk da yake suna nan suna shan
magani iri iri daban daban daga malamai kala kala,,, amma ciwon sai k'ara cigaba yakeyi,,,
k'urajen da suka fitowa Fadila ajiki sun k'ara girma sosai sai wani ruwa ruwa yake fitowa daga
jikinta mai shegen wari da d'oyi! Bakinta har wani kumfa yake fitarwa akodayaushe akowane
lokaci idan ciwonta ya tashi.
Ciwon Fatima da Maryam yanada sauk'i bisa ga na Fadila! Saboda ciwon Fadila yafi tsanani da
firgitarwa!.








Ganin haka ne yasa hankalinsu Umma Nusaiba ya k'ara tashi matuk'a!.

Mama Nafisa ce take zubar da hawayen bak'in ciki da takaicin rayuwa,,, idanunta har sun
kumbura sosai akan kuka! Ga wani irin abu da takeji daya tokare mata k'irji,,, gabanta sai yawan
fad'uwa yakeyi da k'arfi da k'arfi! Zuciyarta sai zafi takeyi mata sosai.





Shesshekar kuka takeyi tana cewa "wayyo Allah ni Nafisa mun shiga uku mun lalace! Ya zanyi
da rayuwata da wannan mummunan al'amarin daya samemu ".







Umma Nusaiba tana jiyo kukanta da maganganunta ta fito daga sauri cikin kitchen,,, ta nufi
wurin Mama Nafisa tana cewa "haba Nafisa,, haba Nafisa miyasa bakida hak'uri ne,,, miyasa
baki yarda k'addara ba? Ai komai na duniya hak'uri akeyi da kuma dauriya akan abinda Allah ya
k'addari bawa dashi ".






"wallahi yaya Nusaiba ba haka bane,,, zuciyata zafi da rad'ad'in ciwo takeyimin,,, hankalina yak'i
kwanciya gabana sai yawan fad'uwa yakeyi,,, sannan jikina ya bani akwai mummunan k'addarar
da zata samemu! Dan Allah ki fahimceni laifin zuciyata da gangar jikina ce! ".Cewar Mama
Nafisa ta sake fashewa da wani irin rikitaccen kuka,,, mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai
sauraro.

Umma Nusaiba jikinta yayi matuk'ar sanyi da fargaba akan kalaman Mama Nafisa,,, ta faikaci
idon Mama Nafisa ta share hawayen da yake fita daga cikin idanunta!.






Sannan ta tattaro natsuwarta da dauriya tace "kiyi hak'uri Nafisa dukkan tsanani yana tare da
sauk'i,,, komai na duniya yanada farko yanada k'arshe hak'uri da yarda da k'addara shine jigon
zaman duniya,, da yardar Allah zasu samu lafiya ".







Mama Nafisa tasa hannu ta share hawayenta,, sannan tace "shikenan yaya na daina kuka Allah
ubangiji ya basu lafi.........."Bata k'arasa maganar ba suka jiyo kuwwa da kururuwar Fadila mai
matuk'ar tashin hankali! Suka shek'a da gudu suka nufi d'akin dasu Fadila ke kwance,,, suna
zuwa suka iske sai kumfa da jini ke fita daga cikin idanunta,,, sannan idanunta sai k'ak'k'afewa
da juyewa sukeyi akan rad'ad'i da zafin ciwo,,, can dai Fadila ta bud'i baki dak'yar tace "Umma,,
Mama duk abinda nayi muku zamana na duniya ku yafemin,,, sannan ku rok'armin gafararsu
baba su yafemin duk abinda nayi musu! ".Mama Nafisa ta saki wani irin gigitaccen kuka mai
cike da k'unci da tarin damuwa,,, Umma Nusaiba ce ke zubar da hawayen bak'in ciki da k'uncin
rayuwa ta matso kusaga Fadila ta rik'i hannunta tace "a'aaa Fadila ki daina fad'ar wannan
magana bakiyi mana komai ba,, koda kinyi mun yafe miki cuta ba mutuwa bace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login