Showing 33001 words to 36000 words out of 58121 words
Chapter 12 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf
ta iske har boka LOK'ORO ya
bayyana yana jiranta.
Ta dubesa da idanunta jawur kamar barkono,, b'acin rai da bak'in ciki ne suka bayyana k'arara
akan fuskarta,,, ga hawaye yab'e yab'e a fuskarta tace "boka LOK'ORO ya kashemin
mahaifiyata ya zanyi da rayuwata boka?,,, na zamo marainiya banida uwa banida uba wallahi
wallahi duk wanda yakeda sa hannu ko yayi farin ciki da mutuwar mahaifiyata,, duk saina
kashesu! Gaba d'ayansu in yaso kowa ya d'and'ani zafin mutuwa da rashin uwa,,,gasu can sai
walima sukeyi suna murna da farin cikin mutuwar Talatu MAYYA ".
Boka LOK'ORO yace "kiyi hak'uri Gwamma zaki d'auki fansar jinin mahaifiyarki,, yanzu nan zan
k'ara miki k'arfin tsafi da sihiri wanda zaki iya yak'ar kowane mahaluki a cikin duniya! ".
"ina son ka bani k'arfin sihirin da babu wanda zanji tsoronsa a cikin wannan duniyar mai cikeda
bak'in ciki ".Inji Gwamma tana zubarda hawayen bak'in ciki da k'uncin mutuwar mahaifiyarta!.
Boka LOK'ORO ya bushe da mahaukaciyar dariya mai cikeda rugugin tsawa da bak'in hayak'i!
Yace "yanzu kuwa zan baki sihirin da zaki kashe kowa kici naman kowa yadda kike so,,, sannan
idan kika kashe Sala mafarauci ya mutu Ummaru d'ansa zaiyita farautarki kamar yadda sukeyin
farautar namun daji! Saboda haka kiyi taka tsan- tsan da Ummaru domin shima hatsabibin yaro
ne da zai gaji ubansa a farauta ".Yana gama fad'ar wannan magana ya dinga feso mata wani
irin abu mai tsananin haske,,, shi kuma abin ya kama shiga cikin jikinta sosai yana kuma
zagayarta da sauri da sauri!.
Hasken saida ya shige cikin jikinta tsab sannan komai ya dawo dai dai,,, "ki tafi gida Gwamma
ki kashe duk wanda kike ra'ayi babu wanda ya isa ya hana ki sai Ummaru d'an Sala mafarauci,,
saboda haka ki bishi a hankali sannu ki samu ki kawardashi a doron k'asa kafin ya zamo
ajalinki! ".Yana kawo k'arshen maganarsa ya b'ace b'at kamar bai tab'a sauka a wurin ba.
"to mai girma boka LOK'ORO zanyi biyayya agareka matuk'ar ina raye,, sannan zanyi taka tsan-
tsan da Ummaru d'an babban mak'iyina a duniya,, na rantse da girman tsafina saina kashe
duka dangin Sala mafarauci muddin ina raye a cikin duniya! ".Inji Gwamma tana gama fad'ar
wannan kalmar ta rikid'a ta koma tsuntsuwa,,, ta tashi sama tana masifaffen gudu a cikin
gajimare,, tun ana hango tsuntsuwar har ya zamana ko hangota ba'ayi ta riga ta b'ace a cikin
sararin samaniya..........
_Share&Comments_
[6/28, 6:03 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 19*
Ta b'ace a cikin sararin samaniya tana masifaffen gudu harna tashin hankali,,, ta jima sosai tana
gudu sannan ta kawo gida ta sauka a saman roofing na gidan,, sannan ta sauko a cikin tsakiyar
gidan wanda ya zamo mallakinta ayanzu,,, bada jimawa ba ta rikid'a zuwa ainahin siffarta
Gwamma tana mai bak'in ciki da takaicin yadda aka kashe mata mahaifiya zama guda,,, ta nufi
randar ta d'ebo ruwa tayi wanka fes.
Sannan ta gama shiryawa taci abincin da ta girka tunda safe,,, sannan ta nufi wurin inda take
aje kurwa mutane kusaga randa ta d'auko fa ru (grasshoppers) kusan shidda ta lak'umesu a
cikin bakinta,, batareda ta tsaya gasawa ba aiko tana cinyesu duka sai wata irin kuwwa da
kururuwar mutane kawai yake tashi! Gwamma ta rufe kunnuwanta domin kada ta kurumce ga
wata irin iska da guguwa mai k'arfi dake zagayar gidan sosai,,, hankalinta kwance dayake tasan
babu abinda zai iya tunkararta da fad'a ayanzu,,,bayan komai ya lafa ta tashi daga inda take
zaune tanata huci da bak'in rai akan yanzu ta rasa kowa nata idan ba Lawwali ba,,, tasha
alwashin koda zatayi yawo tsirara sai taga bayan dangin Sala mafarauci da zuri'arsu baki
d'aya,,,saboda ya sanyata cikin bak'in cikin da har abada ba zata tab'a warkewa ba idan har
bata kashesa ba,,, bata huce takaici ba sannan kuma masu murna da farin ciki da kuma masu
yin walima akan mutuwar mahaifiyarta saita kashe musu mata ko d'iya,,, domin su d'and'ani irin
kwatankwacin zafi da rad'ad'in da ta jiya a cikin zuciyarta,,,,bazata tab'a yafewa duk wanda
yakeda sa hannun acikin mutuwar Inna Talatu MAYYA ba,,,,shiyasa yanzu taji zuciyarta tana
k'una da tafasa sosai wani irin zugi da rad'ad'i ne zuciyarta,,, ga wani turirin bak'in ciki daya dafe
mata kan zuciya wani abu takeji yana tokare mata saman k'irji kamar an aza mata dutse babba.
Can dai ta kwanta saman gadon Ummanta tana zubar da hawayen bak'in ciki da na rashin
uwa,, ga wani zogi da zuciyarta keyi saboda damuwa,, haka dai tayi shiru tana tunanin
rayuwarsu ta can baya itada mahaifiyarta Inna Talatu da mahaifinta Malam Mamman...
**********************
**Acan cikin gari kuwa bayan mutanen sun gama yin walima da cin abincin walimar ,,,kowa ya
watse tareda kama gabansa,, saboda yanzu mutane sun saki jikinsu sai murna sukeyi da
mutuwar Talatu MAYYA,, wasu ma har gidan Sala mafarauci suke zuwa suna yi masa gaisuwar
ya jiki dana ban girma sannan ya d'auko kan Inna Talatu da ya fille ya nuna musu ,, saboda
tsananin jarumtakar daya nuna da kuma k'ok'arin da yayi wurin kashe k'usurgumar mayya
gagararriya irin Inna Talatu,,, wadda akan shahararta ba kowa ke iya fad'a mata maganar banza
ba..
Ganin maitar tayi sauk'i k'warai bayan mutuwar Inna Talatu MAYYA,, yasa mutane suka saki
jikinsu kowa ya cigaba da sha'aninsa da kuma kulada iyalinsa,,, kodayaushe mutum zai iya
fitowa acikin tsakar dare batare da fargaba ba ko shakku ba,,, idan kaga yadda mutane suka
dawo cikin natsuwarsu da walwalarsu sai kayi mamaki sosai,,, mutane suka cigaba da gudanar
da rayuwarsu cikeda matuk'ar kwanciyar hankali da kuma gudanar da kasuwancinsu..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
*BAYAN SATI GUDA*
Bayan sati d'aya da mutuwar Inna Talatu MAYYA,, Gwamma ta wartsake ta share maganar
kashe Sala mafarauci saboda batason ayi saurin gano ta zamo shahararriyar mayya,,, domin
tasan hakan ne zai iya tona mata asiri da wuri yasa mutane su ganota cewa ita d'in mayya ce,,,
saboda haka ne taba zuciyarta hak'uri da dangana tana kula da duk wani motsi na Sala
mafarauci,,, duk inda ya shiga akan idanun Gwamma yake tana hankalce dashi da duk wani
motsinsa,, idan tari Sala mafarauci yayi akan idon Gwamma idan abinci yakeci akan idonta ne,,
in tak'aice muku babu wani motsin da zaiyi ba'a kan idanun Gwamma ba..
**Washe gari da safe misalin k'arfe 9:30am na safe,, Gwamma ta tashi tunda tayi sallar asuba
ta share gidan gaba d'aya tsab sannan ta aza ruwan zafi asaman murhu ta d'ibi na wanka,,
sauran ta barsu domin ta had'a shayi mai kauri.
Bayan ta shiga wanka ne ta fito ta sanya doguwar rigarta,, sannan tazo kitchen ta juye sauran
ruwan zafinta a kofi tana juyewa ta shige cikin d'akinta,, ta d'auko kayan shayi da biredi ta had'a
shayinta mai kauri tana sha da biredi,, haka dai ta cigaba da cin abincinta cikin natsuwa harta
kammala,, tana gamawa taje wurin murhun wuta ta d'auko fara biyar ta cinyesu zama guda,,
saida kuwwar mutane da kururuwarsu ta bayyana na tsawon lokaci,, bayan komai ya lafa ta fito
bakin k'ofar d'akinta ta shimfid'a tabarma ta zauna shiru tana nazari da tunanin lamarin duniya
da zamantakewar rayuwa gaba d'aya..
Can dai da jimawa saiga sallamar baba Labbo ya shigo har cikin gidan batare da wani shamaki
ba,, Gwamma ta tsura mishi jajayen idanunta tun kafin ya k'araso kusa gareta yana k'arasowa
ya samu wuri ya zauna kusa ga Gwamma,, yana kallonta yana mai tsananin jin tausayinta
saboda gata marainiya kuma d'iya mace ita kad'ai acikin gidan,,, dak'yar ta bud'i baki ta
gaidashi ba domin ranta yaso ba ya amsa mata cikin sakin fuska da walwala.
Sannan ya dubeta cikin tausayawa da k'aunarta amatsayinta na d'iyar yayansa yace "Gwamma
ya mukaji da hak'uri na rashin da mukayi? ".
Gwamma ta kauda kanta cikeda matuk'ar takaici da jin haushinsa,, tace "mun gode Allah ya
zamuyi duk abinda Allah yayi mai k'yau ne ".
"haka ne 'yata inason kiyi hak'uri ki maida komai ba komai ba,,, Allah ubangiji da ya baki su
yaya Mamman da Talatu amatsayin iyayenki shine zai chanza miki da sauyi mafi alkhairi,,
sannan ki sani dukkan mai rai mamaci ne kowa lokacinsa ne kawai yake jira,, burinmu dai Allah
yasa mu cika da imani muna musulmai ".Inji baba Labbo cikeda matuk'ar tausayi da lallashi.
Nasihar nan da yakeyi mata saida taji an fama mata tsohon ciwon da ya riga yayi mata k'urji
acikin ciki,,, ta d'ago rinannun idanunta jawur dasu tace "haka yake baba ".
Baba Labbo yace "saboda haka amatsayina na babanki k'ane ga mahaifinki Mamman,,nake
umurtarki da ki dawo gidana da zama saboda bai dace ba kina yarinya budurwa kina zaman
kanki ke d'aya acikin gida,,, bak'ya tsoron kada wani abu na cutarwa yazo ya cutardake ko yayi
miki wata illa,, sannan akwai matasa masu shiga har cikin gidan mutane suna musu fyad'e da
k'arfi da yaji,,, saboda haka ki tashi yanzu ki kwaso kayanki bazan bar gidan nan ba sai k'afata
k'afarki ".
"to baba yanzu zan shiga cikin d'akin in had'o kayana saimu wuce zuwa gidanka ".Cewar
Gwamma.
Baba Labbo yace "ina jiranki d'iyar albarka shiga ki had'o kayanki ".
Tace "to baba ".Ta tashi sannu kamar abin arzik'i ta shige cikin d'akinta,, tana shiga bada jimawa
ba ta rikid'a ta koma macijiya mai kai biyu idanunta jawur kamar wuta bakin nan nata wargajeje
gudan k'ato,,, macijiyar tayi zuruf zuruf ta fito wurin baba Labbo,, baba Labbo bai hankalta da
macijiyar ba saida yaji ana lasar masa tafin k'afafuwa,,, naji yana cewa "wai wa ne irin k'waro ne
ke lasarmin k'afafuwa ",,,yana gama magana yana juyowa idanunsa ya sauka akan macijiya,, ai
kuwa ya zabura da k'arfi! Yana kuwwa sosai da kururuwar neman agajin mutane,, itama
macijiyar tana ganin zai shek'a da gudu ta bisa da gudu tana fitar da halshenta.
Ai kuwa yana ganin ta biyosa ya k'ara gudu tareda k'ara rikicewa! Yana hawayen ganin mutuwa
k'iri k'iri,,, ya kama zagayar filin gida saboda tsananin rikicewa da d'imaucewa! Babu abinda
yakeyi sai zubar da hawayen tsoro,, macijiyar ta kama binsa harda hawa takeyi saman jikinsa
tana k'ara tsoratardashi,, can naga baba Labbo ya buga wata gigitacciyar k'ara da kuwwa mai
ban tsoro!.
Saiga kashi da fitsari tsuluttt tsuluttt tsuluttt sun fito daga cikin wandon baba Labbo,, ashe wai
zawo yakeyi amma da yake yana cikin tsoro ne da firgici baisan yayi ba,, ya cigaba da zagayar
gidan yana kukan bak'in ciki da takaici can ya bud'i baki yace"na tuba dan Allah kiyi hak'uri
bansan Inna Talatu tabar miki mai gadinki bane,, nasha aradu bazan koma dawowa cikin gidan
nan ba har abada,,, sai yaga macijiyar ta bushe da mahaukaciyar dariya tace "idan ka sake
dawowa acikin gidan nan saboda ka tafi da Gwamma,, saina kasheka har abada! "."bazan ma
koma dawowa ba kiyimin rai banason in mutu yanzu inbar iyalina ".Inji baba Labbo sai wari da
d'oyin kashi da fitsari yakeyi. "Naji! Naji tsohon munafiki fita ka bani wuri,, kafin in chanza
ra'ayina in kasheka a banza ".Cewar macijiyar cikeda matuk'ar hasala sosai,, ai kuwa baba
Labbo ya shek'a da gudu saida ya buge kansa abango gidan ya fad'i k'asa d'immm! Sannan ya
tashi da sauri ya falfala da gudun bala'i yana fesa zawo da fitsari,, babu abinda ke tashi sai b'urr
b'urr b'urr yana gudun ceton ransa.
Tun yana gudun ceton ransa har ya kawo gungu samari ya wucesu da gudu,, suna lafiya lafiya
Malam Labbo amma ina yayi nisa bayajin kira ganin haka ne yasa samarin suma kowa ya
cikawa wandonsa iska suka shek'a da gudu ,,,suna biyar bayan Labbo.
Suna gudu har suka iso majalisar dattijawa suna firarsu cikin natsuwa ,,su Labbo sukayo cikinsu
da gudu harda take cikin wani daga cikinsu sukayi yana kuwwa da k'arfi da kuka ,,,dattijawa
suka runtuma da gudu da babbar rigunansu harda wanda aka takawa ciki shima ya mik'e
zumbur ya kama gudu da k'aton cikinsa kamar k'warya.
Haka dai suka kama gudu nan kamar ransu zai fita,, kowane daga cikinsu ka duba bakin rai
bakin fama yake gudu!. Nishinsu da sawun takalminsu kawai ne ke tashi ruduuu ruduuu d'iiiiiiiiii.
Maigari ne zaune da dogarawansa da sauran mutanen gari suna fira,, ga kwanonin tuwo nan da
miya aje agefe rufe sannan ga ruwan yamin da aka kawowa Maigari domin ya kaiwa awakin
matarsa,,, suna tsaka da firarsu saiga su Labbo da samari,, dattijawa sun shek'o da gudu sunyo
cikinsu aikuwa aka d'unguje Maigari ya fad'a cikin kwanon tuwo shida wani dogarinsa,, ga hula
da rawanin maigari agefe sai kuwwar zafin ciwo da neman agaji sukeyi shida dogarinsa,, d'ayan
kuma ya fad'a cikin miya duk jikinsa ya b'aci sosai da ruwan miya shima sai kuwwa yakeyi yana
murza idanu da laluben hanya saboda duk miyar ya shige masa acikin idanu.
Saura mutum uku suka fad'a cikin ruwan yami suna iyo dayake irin babbar roban nance wadda
ke iya d'aukar mutane kusan hud'u,, sunsha ruwan yami sunyi tsamo tsamo suna kuwwar
neman ceto da agajin gaggawa,, robar da taji nauyin bala'i ta fashe fasss suka kasa tashi a
k'asa sai kuwwa sukeyi,, wad'anda suka tsere ko waiwayo su basayi sunata kansu! Wad'anda
suka fad'a cikin ruwan yami suka tashi dak'yar suka kama Maigari duk ya k'one a hannu da
fuska sai kuka yakeyi,, suka shigardashi cikin gidansa dayake a k'ofar gidan suke zama,,
sauran kuwa daga baya mutanen gari ne suka ciccib'esu suka kai kowa gidansa..
**********************
Macijiyar ta koma mutum wato ainahin siffarta Gwamma sannan ta sake rikid'a ta koma kaza,,,
ta fito daga cikin gidanta ta nufi gidan Sala mafarauci,, tana tafiya sannu sannu a hankali harta
kawo bakin k'ofar gidan ta kalli k'ofar da idanunta wani farin haske ne ya fito daga idanunta ya
bugi k'ofar ta bud'e kanta tayi zuruf zuruf ta shige cikin gidan Sala mafarauci da saurinta.........
_Share&Comments_
[7/2, 7:36 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 20*
Ta shige cikin gidan Sala mafarauci da saurinta,, tana shiga bata tsaya b'ata lokaci ba sai cikin
d'akin Sala mafarauci da Inna Yashe sunata barcin rana,, ashe kafin taxo itace tayi amfani da
tsafinta ta sanyasu barcin rana,,, batareda b'ata lokaci ba Gwamma ta kamayin wasu surutai na
tsafi ba'a jima saiga wata irin mahaukaciyar guguwa da k'arfi! Tana zagayarsu Inna Yashe na
tsawon lokaci can naga guguwar gaba d'ayanta ta shige cikin jikinsu kaf,,, tana gama shigewa
Gwamma mayya tayi amfani da sihiranta ta b'ace a cikin gidan baki d'aya kamar wani halitta bai
tab'a wanzuwa a cikin gidan ba,,, ta barsu nan kwance suna barcin sihiri da tsafi..
Bayan wasu awanni saiga sallamar baba Labaran da Ummaru atare suka shigo cikin gidan,,
bawai tare suke ba baba Labaran ya had'u da Ummaru ne a hanyar dawowa gida shine yace
bari ya biyosa saboda ya k'ara ganin yadda jikin d'an uwansa yayi sauk'i sosai,, suna zuwa
sukayi sallama basu amsa ba baba Labaran ya umurci Ummaru daya shiga cikin d'akin yaga
shin lafiya,,, Ummaru bai tsaya wasa ba ya shiga yana shiga ya tayar dasu daga barci yana
cewa "baba lafiyarku k'alau kukeyin barcin rana? ".Suka kalli juna Sala mafarauci da Inna Yashe
sunajin maganarsa amma sun kasa mayarda martani,, ganin haka ne yasa Ummaru ya sake
tambayarsu sukayi shiru,, dalilin haka da sukayi ne yasa hankalin Ummaru ya d'unguma
gabansa ya dinga bugawa da k'arfi dummmmm! Yaji wani irin d'aci da zafi a cikin zuciyarsa ga
wani abu ya tokare masa mai nauyi a k'irjinsa,, can dai ya tattaro dauriya da hak'urinsa ya fito
bakin k'ofa ya kira baba Labaran yace "masa baba kazo kaga wani abu ".To Ummaru ".Inji baba
Labaran tareda shigowa cikin d'akin,, yana shiga shima saida gabansa ya bada rasssss! Yace
"Sala lafiya naga kunyi shiru ne? ".Babu amsa ai kuwa baba Labaran da Ummaru suka dubi
juna cikin tsoro da fargaba akan rashin maganarsu Inna Yashe.
Babu b'ata lokaci suka ga naman sassan jikin Sala mafarauci ya fara rabuwa filla filla,, kamar
yadda kukasan ake raba sassan naman kaza idan za'a dafa misali k'afa daban kai daban
bayanta da fiffikenta daban,, suka tsorace da rikicewa babu abinda ke tashi kuwwa da
kururuwar Sala mafarauci cikeda matuk'ar zafi da rad'ad'in mutuwa,, ga jini sai bulbulowa yakeyi
kamar an yanke sa! Ummaru da baba Labaran suka fashe da wani irin matsiyacin kuka mai
cikeda bak'in ciki da tashin hankali ,, ga Sala mafarauci da Inna Yashe suna cikin mayuwacin
hali amma basuda ikon taimakonsu! Sala ya