Showing 15001 words to 18000 words out of 58121 words

Chapter 6 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf

12 Jul 2025

2937

kwana hud'u da faruwar wannan mummunan al'amari,,, mutane kowa ya cigaba da
harakokinshi...



Inna Talatu ta cigaba da musgunawa rayuwar Malam Mamman tareda ci masa mutunci da
tozarci,,, kullum kullum da irin kalar walak'ancin da zata masa kowace safiya idan garin Allah ya
waye,,, bayada natsuwa da kwanciyar hankali masifar safe daban ta rana daban ta dare da
daban,,, bata ganin mutuncinshi da girmanshi ko kad'an. Har takai ta kawo Malam idan zai
dawo gidansa har fargaba da tsoronta yake ji,, ta zame mishi ciwon ajali ya rasa yadda zaiyi da
ita bayada natsuwa da kwanciyar hankali ko kad'an,,, a cikin kwanakin nan idan kaga yadda
Malam Mamman ya rame sai kun tausaya mishi,,, har ta kai ta kawo ko abincin gidan nan bata
aje mishi sai dai yaci acan kasuwa gurin masu sayarwa,, amma haka bawan Allah nan yake
hak'uri matuk'a da ita,,, ganin yayi tana shirin kashe shi tunda sauran ranshi yasa dole ya fara
neman wata bazawara mai suna Laweeza a cikin unguwarsu da aure..




Inna Talatu MAYYA ta ji labarin neman auren Laweeza da yakeyi amma da yake k'usurgumar
*MAYYA CE*,,,sannan kuma ta san muguntar da zata k'ulla yasa ko a fuska bata damu ba bale
a cikin zuciyarta..





***Wata rana Malam Mamman ne yayi wankansa sannan ya d'auko shaddarsa sabuwa a cikin
kayansa yasa,,,, ya feshe jikinsa da turare sannan ya dubi kanshi a madubi yaga ba laifi ya jawo
k'ofar d'akinsa ya kulle da padlock,,, ya fito filin gida Inna Talatu tana zaune tana gyaran
shinkafar da zata yi tuwo da ita gasu Gwamma da Lawwali zaune gefe suna wasarsu cikin
kwanciyar hankali..



Inna Talatu tana ganin irin wankan da Malam Mamman ya d'auka ga k'amshi sai tashi yakeyi na
turarensa,,, ta yi masa walak'antaccen kallo mai cike da raini ta ja mugun tsoki mtsssss! Sannan
tace "Mamman mai budurwar zuciya ina zaka je? ".Tayi masa tambayar rainin wayo..

Ya juyo ya kalleta da yake yasan tambayar raini ne ta yi masa,,, yayi murmushin mugunta yace
"wurin masoyiyata matata mai son farin cikina,,, tana gudun b'acin raina ta iya kalamai masu
sanyaya zuciyar masoyi gata da tarbiya da biyayya,,, ga ta d'iyar mutanen k'warai alal hak'ik'a
nayi matuk'ar dace da samun mace ta gari Talatu,,, idan kina zuwa zan kaiki gobe ku gaisa da
ita saboda tun yanzu ku saba da juna ".




Hali zanen dutse! Hak'ik'a maganganun Malam Mamman sun matuk'ar k'ona zuciyar Inna
Talatu,,, babu abinda zuciyarta keyi sai suya rayuwarta idan har tayi dubu to ta b'aci sosai..





Ta bud'i baki tace "Mamman kenan mi kake ci na baka na zuba? Wato bazawarar da kake nema
itace mai kirki ni ce mara kirkin ko,,, itace d'iyar mutanen k'warai ni ce d'iyar mutanen banza ko
itace wadda ta iya kalamai ni ban iya ba? To ka rubuta a takarda ka ajiye wlh wannan auren
muddin ina raye ba zai tab'a yiyuwa ba! Na fika iya shege na rashin mutunci da hatsibibanci ".




"tabbas ta fiki duk abinda na lissafa harda wanda ban fad'a ba ta fiki,,, sannan baki isa ki
hanamin k'ara aure ba Talatu ba zaki hana inji dad'i ba kamar yadda kowane magidanci mai
mata biyu keji ,,,idan naga kina son b'atamin gida sai in sakeki ki koma gidanku! ".Cewar Malam
Mamman cikeda matuk'ar zafin rai da haushi..







Inna Talatu tace "to sai mi idan ka sakeni nifa ba irin wad'annan matan bane wad'anda ake

tsoratarwa da kalmar saki,,, so kake ka kawo wata a cikin gidan nan kazo kana iskanci da ita
agaban 'ya'yanka kana tab'a mata nono ko,,, bazai tab'a yiyuwa ba nadai gaya maka gaskiya ".





Malam Mamman yace "sai nayi abin nan da bakiso ko na sadu da ita idan har na aureta ai halat
na aikata ba haramun ba,,, ke kinyi kad'an ki haramta min abinda Allah ya halat min ba kuma ko
mutuwa zakiyi saina k'ara aure! ".






"hmmm haka kace? To mu zuba mu gani ni da kai shege ya fasa,,, wanda yaji tsoro ya janye
d'an wuta ne a tsakaninmu".Cewar Inna Talatu cikeda son tashin hankali..




Mal. Mamman yace "mahaukaciya wawuyar jahila! Ai kece 'yar wuta kuma shegiya dama ai
mace idan bata biyayya ga mijinta sunanta 'yar wuta,,, kinyi 'k'arama wlh da ki hana min rawa
gaban hantsi,, banda lokacin karya irinki! ".Yasa kai yayi tafiyarsa zuwa inda zaije..





"kaine k'aton kare kuma jahili! Wallahi zaka gane bakada wayo ko dabara,, zan nuna muku ni
murucin kan dutse ce ni ban fito ba saida na shirya,,, ni ce ajalinku da kai da ita! Hmmmm yaro
baisan wuta ba sai ya taka andaiji kunya ana son ayi aure adinga yi mata iskanci da tambad'a
yara suna kallo,,, ni ba zan bari a lalata min yarana ba ".Inji Inna Talatu cikin jin haushinsa..




**********************

Malam Mamman naga yazo baki k'ofar gidansu Laweeza ya samu yaro ya aika domin ayi masa
sallama da ita,,, can yaro ya fito daga cikin gidan yace masa tana zuwa Malam Mamman ya
bashi naira ishirin yaron ya amsa yayi godiya ya wucewarsa yana jin dad'i sosai.
Bayan mintuna kad'an saiga Laweeza ta fito daga cikin gidan tana tafiya cike da yanga da
natsuwa,,, tana isowa wurin Malam Mamman ta gaidashi ya amsa cikin fara'a da murmushi..



Nayi duba zuwaga fuskar Laweeza ashe k'yakkyawa ce bak'a ba tilin ba,,, tanada doguwar
fuska tareda da dogon hanci ga madaidaicin bakinta,, wanda ya k'ara mata k'yawo sosai..




Malam Mamman ya nisa yace "Lawiza ".




Tace"Na'am ".Tana wasa da yatsun hannunta.




Yace mata "ina son ki bani dama in turo magabatana asa mana rana,,, saboda kinga ni da ke
ba wannan ne karo na farko da zamuyi aure ba ke kin tab'a aure harda yaro ni inada mata
harda yara biyu,, saboda haka mu ba yara bane da zamu tsaya b'atawa kanmu lokaci ,,,shin
miye ra'ayinki game dani kina sona kin aminta naturo magabatana? ".



Lawiza tace masa "na amince amma ina tsoron abinda zaije ya dawo,,, saboda naji ana fad'a
agari cewa matarka masifafffar mace ce mafad'aciya sannan kuma ance ana zarginta da
maita!.....

_Share &Comments_
[6/21, 9:56 PM] Mugiratmusa66:





*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_



*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 10*



Lawiza tace "na amince amma ina tsoron abinda zaije ya dawo,,, saboda na ji ance matarka
masifaffiyar mace ce mafad'aciya sannan kuma ance ana zarginta da maita a cikin garin nan,,,
kaga kuwa dole hankalina ya tashi sosai in dai domin fad'a ne to abin da sauk'i saboda saina

kulata ne zamuyi sa'insa ni kuma ba zan kulata ba idan Allah ya yarda ".





"hmmmm wannan maganar ta maita da akecewa matata tana yi ba gaskiya ba ne,,, wannan
zance ne na mak'iya da mahassada wad'anda basu son mutum a rayuwa ko cigaban
mutum,,,,lafiyar matata k'alau kawai dai mafad'aciya ce shi ne gaskiyar magana ".Cewar Malam
Mamman cikin taushin murya da lallashi..




Lawiza tace "to shikenan na yarda ka turo a sanya mana rana ".





Malam Mamman yace "yanzu naji maganar k'warai Lawizata amma ko gobe ina baki shawarar
ki daina yarda da maganar mutane,,, domin su mutane iyawa dasu sai ubangiji duk abinda
kakeyi saika samu wanda ya kusheka yakejin haushinka,,,, saboda hassada da bak'in ciki a
cikin jinin d'an Adam yake".




Lawiza tace "ai kuwa karka damu komai ya wuce na daina yarda da maganganun mutane,,, ni
ke aure ba mutum duk wadda ta kawo tseguminta ko anyi ance zanyi kunne uwar shaggu da ita
harta gaji ta k'ara gaba ".






"dako kin k'yauta mana wlh,, sannan karki damu jibi zan turo manyana wurin babanki saboda
haka ki sanar da su da wuri,,, ga wani 'yan chanji inbaki farin cikin rayuwata ".Fad'ar Mlam
Mamman yana washe mata hak'oransa da suka gogu da aswaki zad sha'awa,,, ya mik'a mata
kud'i da kuma bak'ar leda..

Lawiza tasa hannu ta karb'a cikeda matuk'ar kunya da k'aunarsa,,,sannan tace "nagode sosai
Allah ya saka da alkhairi ".






Mal. Malam Mamman yace "Amin amin rabin jikina,,, to ni zan wuce gida yanzu ki gaida
mutanen gidanku ".(Ka ji su Malam an iya lobaiya da kashe murya).





"zasu ji mijina Allah ya kiyaye hanya ya tsare min kai ".Cewar Lawiza cikeda nuna kulawa da
soyayya.




Ai kuwa wannan addu'a da ta yima Mal. Mamman ba k'aramin masifar dad'i yaji ba,, wani irin
sanyi ne yabi jinin jikinsa yace "Amin babina ".Sannan ya kama hanyar zuwa gidansa,, ita kuma
ta shige cikin gidansu ..





********** ******* ****

***Ab'angaren gidansu Hassi bayan anje ankaisu Lado gidansu na gaskiya shi da sauran
mutum hud'u,, da suka rasu rana d'aya..





To bayan Hassi tayi barci mai tsawo daga baya saita falka daga barcin,,, tana tashi da hamma
ta tashi daga barci Mariya ce ta d'ebo abinci da ruwa masu sanyi ta kawo mata,, Hassi ta yi
bismilla ta fara cin abincinta sai da taji tayi nak sannan ta wanke hannunta ta sha ruwa sosai,,,
Inna Lami ce ta had'a mata ruwan wanka ta taimaka mata ta yi wanka sannan aka d'auko kala
d'aya tsofaffi daga cikin kayan Mariya aka bata ta saka...




Zuwa anjima da daddare da Malam Abubakar ya dawo gida,, bayan sun kammala cin abincin
dare ne Malam Abubakar yayi gyaran murya yace "Hafsa ".



"Na'am baba ".Cewar Hassi cikin mutuwar jiki da fargaba..



Mal. Abubakar ya dubeta cikin tausayinta da tsantsar k'aunar 'yarsa yace "ina so ki saurari
abinda zan gaya miki da k'yau,,, ki fahimci maganata cikin natsuwa da kaifin tunani kinsan da
cewa komai ya faru da bawa muk'addari ne daga Allah kuma babu wani mahaluk'i a cikin
wannan duniya,,, da ya isa kaucewa k'addararsa Allah ya riga ya rubuta a cikin littafinmu duk
irin abubuwan da zai samu mutum tun daga farkon haihuwarsa har zuwa mutuwarsa,,,, ana son
musulmi na k'warai yayi imani da k'addara mai k'yau ko mara k'yau,,, sannan duk abinda Allah
ya baka a matsayin aro na wani lokaci daga baya ya amshi abinsa zakiji ciwo Hassi? ".






Hassi ta gyad'a kai cikin matuk'ar sanyin zuciya da zullumi! Ta bud'e baki tace "a'a baba ".

Malam Abubakar yace "kiyi hak'uri da duk abinda zakiji Hafsa domin Allah yana tare da masu
hak'uri,,, ubangijin da ya baki Lado a matsayin miji ya k'addari aurenku ya kuma k'addari
samuwar Na'ima a tsakaninku batare da sisinku ba,,, ya amshi ran Lado domin ya fiki sonshi
aronsa dama ya baki ".


Hassi tana jin wannan maganar ta fashe da wani rikitaccen kuka mai ban tausayi,,, hankalinta
yayi k'ololuwar tashi zuciyarta sai k'una da rad'ad'in zafi sosai takeyi mata ..





Inna Lami ce ta rungumeta tana lallashinta da fad'a mata kalamai masu sanyi a cikin zuciya,,
tana cewa "kiyi hak'uri hafsa kiyi ta fad'ar wannan kalma ina lillahi wa inna ilaihirraji'un!!!
Alhumma ajirni fi musibati wa'akhalufni min khari minha,,, da yarda Allah zakiji sauk'i cikin
zuciyarki Allah ubangiji ya jik'an Lado ya gafarta masa zunubbansa ".




"kiyi hak'uri yaya Hassi ki daina kuka addu'a kawai ce yaya Lado ke buk'ata a gareki,,, ba kuka
ba saboda kukan mai rai akan mamaci azaba ne kuma masifa ne,,, ki tausayawa mana ki daina
kuka 'yar uwata saboda nima zaki iya sakani kuka ".Cewar Mariya idanunta sun cicciko da
ruwan hawaye..





Inna Lami tace "ki daina kuka ki saurari maganarmu kuma ki fahimcemu Hafsa,,, duk abinda
kika gani daga Allah ne sannan ina son ki sanar dani waye kike cewa ta kashe Lado d'azu
alokacin da ya fad'i k'asa yana aman jini? ".

Mal. Abubakar yace "tabbas muna son muji wani bayani a cikin bakinki,,, sannan d'azu wa ce
irin magana ce kikaso gaya min da baki samu dama ba? ".





Hassi ta d'ago jajayen idanunta wad'anda suka kumbura akan zubar hawaye,, ta bud'i baki
dak'yar tace "tabbas ba mutuwa akeyiwa kuka ba sabo ne akeyiwa kuka ,,,baba,, Inna,, Mariya
hak'ik'a na yarda komai ya faru da bawa muk'addari ne daga Allah kuma mutum bai isa ya
gujewa k'addararsa ba,, Lado ya riga ya zamo ginshink'in rayuwata kuma jigona ni da 'yata
mantashi alokaci d'aya yanada matuk'ar wuya agareni sai dai a sannu sannu cikin wani lokaci,,,
ku dai tayani da addu'a Allah ubangiji ya k'ara sanyaya zuciyata tareda hak'uri da juriyar
rashinsa,,, yanzu kuwa zan baku labarin abinda ya faru da marigayi kafin ya rasu....... ".Nan da
nan ta basu labarin da Lado ya bata kafin ya rasu,,, na gamuwarshi da karya alokacin da ya fito
waje domin yayi fitsari...







Babu abinda bata gaya musu ba kamar yadda dai ya sanar da ita..





Tana gama bada labarin suka saka salati atare,,, da kuma fad'ar kalmar ina lillahi wa inna
ilaihirraji'un!!! Duniya ina zaki damu wannan ai rashin imani ne,, anya wasu mutane suna tuna
mutuwa kuwa,, anya mutane suna tuna kwanciyar kabari da hisabi kuwa,,, anya wasu mutane
suna tuna cewa komai daren dad'ewa zasu koma ga Allah ubangijin talikkai? ".Cewar Inna Lami
cikeda matuk'ar tashin hankali da jimami..






Mal. Abubakar yayi huci mai zafi da ajiyar zuciya yace ".wannan magana taki akwai alamun
k'amshin gaskiya a cikinta na cewa *MAYYA CE* ta kama Lado,,,, amma kuma sanin gaibu sai

Allah idan ma itace mun barta ga ubangijin sammai da k'assai wanda baya kwana baya angaje
shi zai miki *SAKAYYA* tun anan duniya Hassi,, saboda haka ki share hawayenki ki tashi kuje
da Mariya gidanki kiyi takaba acan domin haka ne yafi dacewa ".





"wannan gaskiya ne maganarka ".Inji Inna Lami cikeda matuk'ar tausayin Hassi..






"ya zamo dolena in kiyaye dokokin ubangijina yi muku biyayya ya zamo wajibi agareni iyayena,,,
zan tashi in koma gidan Lado inyi takabata acan kamar yadda kuka umurceni amma dan Allah
ku tausayamin ku sakani a cikin addu'arku ku rok'armin akan Allah ya sanyamin hak'uri da
dangana na rashin Lado ".Cewar Hassi yayinda take zubar da hawayen bak'in ciki da k'uncin
rayuwa..







Mal. Abubakar yace "karki damu akodayaushe muna yi muku addu'a Hassi,, ki sani albarkarmu
da aminci yana tare daku a duk inda kuka shiga a cikin fad'in duniyar nan,, Allah ubangiji ya
tsaremin ku yayi muku albarka ".





Mariya tace "Amin ya rabbi baba ".Tana share hawayen da ke fitowa daga idaniyarta.






Inna Lami tace "Allah ya sanya miki hak'uri da dangana akan wannan k'addarartaki,,, ki sani ku

masu albarka ne akodayaushe akowane lokaci,,, kuma kuna tareda aminci da yarda Allah
saboda haka ku tashi ku tafi gida kafin dare yayi k'warai,, Mariya jeki d'auko Na'ima tana cikin
d'aki ku wuce ".





Mariya tace "to Inna ".Ta tashi tsaye ta shiga cikin d'akin ta d'auko Na'ima,,, tasa zanen Inna
Lami tsoho ta goyata a bayanta.






Itama Hassi dole tasa ta mik'e tsaye suka yima iyayensu sai da safe,,, iyayen suka k'ara sanya
musu albarka tareda yi musu fatar alkhairi a rayuwa,,, sannan su Hassi suka nufi gidan marigayi
Lado..






*********************





***Ab'angaren Malam Mamman kuwa bayan ya dawo daga wurin Lawiza yarinyar da yake son
ya aura,,, to aranar sai da sukayi fad'a har na tashin hankali da Inna Talatu,, saboda har kwalar
rigarsa ta rik'e tareda sa hannunta ta shak'e mishi wuya sosai cike da son kasheshi.
Yayi amfani da k'arfinshi na zama namiji ya b'anb'are hannunta dak'yar ga wuyansa,,, bai b'ata
lokaci ba ya kashe ta da wasu mahaukatan maruka hud'u masu rai da lafiya,,, wanda sai da
jinta ganinta suka d'auke na wucin gadi ga wani mahaukacin zafi da rad'ad'i da yake fitowa
daga kuncinta..

Haka dai rikici da tashin hankali ya cigaba da gudana a cikin gidan Malam Mamman,, wata rana
har dambe take cewa tayi dashi cikeda matuk'ar masifa da bala'i shi dai saidai ya ceci kansa
domin har makami ko takobi take d'auka tace saita kasheshi,,, haka dai zaiyi dabarar amshe
makamin sannan yayi mata matsiyacin duka wanda sai tayi fitsari da tutu cikin wando saboda
bak'ar wahala,, amma ba zai hana gobe tayi mishi rashin kunya ba ko tace zatayi dambe dashi..







**Malam Mamman ya aika magabatansa a gidansu Lawiza aka saka ranar aurensa da Lawiza
nan da sati biyu masu zuwa.
A wannan ranar Malam Mamman ji yayi kamar anyi masa bushara da gidan aljanna akan
tsananin farin ciki da murna sosai,, akan murna ya siyo kwalin minti da chewgam yana rabawa
'yan uwa da abokan arzik'i tare da sanar musu da lokacin aurensa..






Hak'ik'a 'yan uwa da abokan arzik'i sun tayashi murna matuk'a tareda yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login