Showing 24001 words to 27000 words out of 58121 words
aura
insha Allahu ".
Malam Mamman ya dubeta yana mamakin kalamanta sosai,,, shi kansa yasan Talatu batada
tausayi ko imani amma ji yadda take masa nasiha kamar ta k'warai,,,,,,, amma da yake bayason
ya fara zarginta yasa yayi saurin kauda wannan magana gaskiya.
¤¤¤Malam Mamman yace "tabbas haka ne amma ina cikin damuwa,,, sannan mantawa da
Lawiza alokaci guda abu ne mai matuk'ar wahala sosai,,, amma bazan tab'a mantawa da
Lawiza ba acikin rayuwata ba har abada ".
"haka ne baidace kayi saurin mantawa da ita ba,,,, idan Allah ya bani ciki muka samu d'iya
mace sunan Lawiza za'a saka mata saboda k'aunar da kakeyi mata,,,, amma ka daure ka rage
yawan damuwa saboda kada kamu da wata cutar hak'urin dai shi ne yafi dacewa ".Cewar Inna
Talatu.
Malam Mamman yace "eh mana maganarki haka take nagode sosai da kulawarki gareni,,,
kuma idan Allah ya yarda zan rage sa damuwa acikin raina ".
Inna Talatu tace"da kam yafi Mamman karka damu ai dole in tausaya maka,,, saboda anzama
d'aya tuntuni "...
Inna Talatu ta cigaba da bashi maganganu masu dad'i,,, da nasihohi masu ratsa zuciya da jini..
*** **** *** *****
*BAYAN WATA SHIDA*
••••Bayan watanni shida abubuwa da dama sun faru,,, ciki kuwa harda kamun kurwar da Inna
Talatu keyi tana cinyewa ko ta mayarda kurwar kaza,, rago,, tunkiya,, bunsuru da dai sauran
dabbobin dake cikin duniya to mayyu suna iya komawa kowace irin halittar dabbar da suka
gadama. Inna Talatu ta addabi mutanen gari itada sauran mayyu,,, babu abinda sukeyi sai kashe rayuka
da cin naman mutane,,, mutanen gari duk sun tsorata da kid'emewa akan mayyu idan suka
hangosu daga nesa,,, kowane mutum ko mace zai iya cikawa wandonsa ko bujensa iska k'afa
mi naci ban baki ba! Mutane kowa sai kaffa kaffa yake da d'iyansa saboda gudun kada su had'u
da mayyu su lamshe musu kurwar d'iya ko mata.
Idan matar aure ce tana kaffa kaffa da mijinta domin kada mai afkuwa ta afka musu,,, amma
duk da hakan basu tsira ba domin har gida ake zuwa a lamshe musu kurwa ,,,saidai kaga
mutum ya fad'i k'asa rikcham! Idan yana tsaye idan kuma zaune yake sai aga mutum ya fara
aman jini yana murk'usu,, can ya fara shure shuren mutuwa yana kakarin mutuwa nan da nan
ya rasu! Akwashi gawar mutum ankaishi mak'abarta! Haka abubuwan suke faruwa cikeda
matuk'ar tashin hankali da rikicewa .
Rayuwar garin ta zamo cikin rashin kwanciyar hankali da rashin natsuwa,,, saboda
akodayaushe akowane lokaci mutum za'a iya kame masa kurwa a cinye ya mutu! Shiyasa
mutane basuda natsuwa ko walwala.
***Ab'angarensu Hassi kuwa bayan rasuwar mijinta Lado,,, sukaje itada Mariya ta tayata
zaman idda domin ta d'ebe mata kewar Lado da mutanen gida.
Alokacin ne Hassi duk ta rame tayi bak'i akan tunanin mijinta,,, wata rana har kuka takeyi
saboda tunani da zullumi,,,alokacin idan kaga Hassi saita baka matuk'ar tausayi haka Mariya
zata kama ta tana kuka ,,,tayi mata nasihohi masu sanyi tareda da bata hak'uri akan lamarin
rayuwa,,, haka al'amarin nasu ya cigaba da tafiya hartayi watanni hud'u da kwana goma
kenan,,, sannan ta fita daga takaba tayi wanka fes tayi kamar ba ita ba tareda sanya sabuwar
sutura.
Bayan wani lokacin ne akayi rabon gado sannan Hassi itada Mariya suka koma gidansu da
zama,,,, al'amarin nasu dai komai cikin tausayawa Na'ima da Hassi suke yinsa daga Innarta har
babanta babu maison b'acin ranta,,, duk abinda take so shi sukeyi mata babu shakka,,, shiyasa
Na'ima takeyin sagarci da shagwab'arta babu mai takura mata ko hantararta.
Anan ne wata rana Hassi Allah ya kawo mata miji nagari mai tsananin k'aunarta tsakani da
Allah ya aureta,, sunansa Iliya ba saurayi bane yanada matarsa Dije da yara uku mace biyu
namiji d'aya,,, haka dai akayi auren cikin wadatar zuci da rufin asiri sosai,,, aka kaita gidan
mijinta sukayi zamansu lafiya da Dije.
Da yake Dije mace ce mai halin dattako da karamci,,, kirki da sanin ya kamata shiyasa zamansu
ya zamo abin sha'awa da burgewa,, babu gulma ko tsegumi balantana haukan kishin da bayada
k'yau ko misali..
***** ******** ******
Macijiya ce naga ta fito daga cikin gidan Malam Mamman cikeda da saurinta kamar iska,,, ta
kama tafiya ta nufi wata hanya mai yawan hakukuwa da itatuwa.
Abin mamaki macijiyar tana tafiya tana waige waige kamar mutum,,, can naga ta nufi cikin
sark'ak'k'iya da duhun ciyawa ga k'oramai agefen daji,,, ga itatuwa dogaye manya -manya a
ko'ina cikin k'usurgumin dajin baka iya hango tsawon dajin da girmansa saboda yawansa.
Macijiyar tayi ta tafiya tana ratsa hakukuwa da kuma k'oramai tana wucewa,,, tana kawowa
wurin wani rami mai matuk'ar zurfi da ban tsoro wata irin guguwa ce da bak'in hayak'i ne suka
game wurin nan da nan fass fasss fasss! Tass tass tass saboda tsananin tashin hankali da
bala'i! Abin yakai tsawon minti ashirin sannan ya tsaya cak ya daina,,, saiga wata irin
mahaukaciyar dariya ta bayyana b'ut akayi fitar burgu acikin ramin kamar walk'iya,,, nan da nan
wata irin guguwa mai k'arfi ta zagaye wurin cikeda sihiri da tsafi! Babu abinda ke tashi cikin
guguwar sai kukan namun daji da muryar mutane,,, can dai guguwar ta daina yawo a doron
k'asa.
Wani irin murgujejen k'aton mutum ya bayyana tsulut kamar aljani,,, kallo d'aya nayi masa
amma kamar inyi amai saboda halittarsa babu k'yawon gani,, domin ido d'aya garesa atsakiyar
kai ga kuma k'aho biyu agefen dama da hagu duk jikinsa gashi ne zago zago kamar rago,,
halshensa yakai tsawon k'afar mutum mai tsawo hak'oransa sunada tsini kamar wuk'a,,, fatarsa
bak'ik'irin kamar gawayi. Ya dubi macijiyar da babban murya mara dad'in saurare yace "yake
Talatu ki koma zuwa ainahin siffarki ".
Ai bai rufe baki ba Inna Talatu ta girgiza sannan ta rikid'e zuwa ainahin siffarta ta mutum,,,, ta
dubi boka LOK'ORO tace "ya kai wannan k'urgumin boka mai babban matsayi a cikin duniya,,,
ina mik'o gaisuwata da girmamawa agareka,,, tsawon rai da shahara sun tabbata agareka ".
Boka LOK'ORO ya bushe da mahaukaciyar dariya,, dariyarsa da muryarsa bibbiyu take fitowa
dajin ya gauraye gaba d'aya yana tanbal tanbal kamar zai kife a cikin k'asa !Yace "godiya nake
da gaisuwar ban girma amma inason ki sani Mamman mijinki yana nan yana neman wata
budurwa fara ce tass mai suna Salima da aure,,, yana yawan zuwa wurinta fira yau zai
sanardake yana neman aurenta ance ya turo magabatansa,,, saboda haka ki iya takonki domin
gujewa afkawa cikin wahala da nadama! 'Yarki Gwamma zata gajeki a wurin maita zata shahara
cikin maita da mugunta iri iri daban daban,,, Lawwali bazai gajeki ba saboda halinsu yasha
banbanci dana Gwamma ".
Inna Talatu ta bushe da dariya sosai tace "nagode sosai babban boka LOK'ORO aikinka yana
k'yawo sosai,,, nayi farin ciki sosai 'yata zata gajeni amma ko Lawwali bai gajeni ba babu komai
boka,, sannan ni auren Mamman bai dameni ba domin cinye namanta zanyi ta mutu har lahira
alokaci guda! ".
Boka LOK'ORO yace "aikinki yana k'yau shiyasa nake k'ara sonki saboda bakida imani bale
tausayi,,, saboda ni banason haraka da mai tausayi da sanyin hali sannan idan zaki dawo kizo
da Gwamma domin ta saba da aljannunmu tun yanzu,,, kafin ta zamo shahararriyar MAYYA
gagararriya! ".
"zanzo da ita yah mai girma boka LOK'ORO, ".Cewar Inna Talatu cikeda matuk'ar farin ciki .
Boka LOK'ORO yace "to Talatuwa Innar Gwamma ki tafi zuwa gidanki cikin farin ciki da nishad'i
sosai,, duk abinda kika sama gaba kece zakiyi nasara ki kashe kowa kici naman kowa! ".Yana
gama fad'ar wannan magana ya b'ace b'at kamar k'iftawa da bismillah,, kamar kuma wata
halitta bata tab'a zama a wurin ba.
Inna Talatu tana ganin boka ya b'ace itama ta girgiza sannan ta rikid'a ta koma tsuntsuwa,,, ta
tashi sama ta lulluk'a a cikin sararin samaniya,,, tana ta gudun bala'i da masifaffen saurinta.......
_Share&Comments_
[6/25, 8:12 PM] Mugiratmusa66:
*MAYYA CE*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_
*Written by Mugirat Musa*
*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*PAGE 15*
Tana ta gudun bala'i da masifaffen saurinta kamar walk'iya ce ta gifto ta wuce da sauri,,,,,abin
akwai ban mamaki da matuk'ar al'ajabi akan tsuntsuwar wato Inna Talatu MAYYA...
Haka dai ta cigaba da tafiya har ta iso bayan gidan Malam Mamman,,, abayan gidan akwai
hakukuwa da yawa tana sauka ta k'ara girgiza da k'arfi,,, sannan ta rikid'a zuwa ainahin siffarta
ta dawo mutum sannu a hankali,,,, tana dawowa siffarta ta fito daga cikin hakin ta nufi cikin
gidan Malam Mamman,,, tana shiga cikin gidan ta isko Lawwali wasa kawai yakeyi ita kuma
Gwamma tana cikin d'akin Innarta tana kwana..
Lawwali ya dubi Innarsa yace "Inna sannu da zuwa ".
Inna Talatu tace "yauwa Lawwali ina Gwamma take ne? ".
"tana d'aki tana kwana Inna,,,, sannan da kika fita da safe Gwamma tayi tafiyarta yawon banza
da neman magana ".Inji Lawwali cikeda dad'in baki.
Inna Talatu tace "ya isa bashi na tambayeka ba,,, babu ruwanka da sha'anin Gwamma saboda
haka ka rabani da surutunka na banza ".
Lawwali yace "to Innarmu na daina fa ".
Suna surutu saiga sallamar Malam Mamman ya shigo cikin gidan,,, Lawwali ne ya amsa masa
sallamarsa yana yi masa sannu da zuwa,,,, Mamman ya amsa tareda sa mishi albarka Inna
Talatu tayi masa sannu da zuwa,,, ya dubi Talatu sannan ya amsa gaisuwar da tayi masa...
Malam Mamman yayi gyaran murya,, tareda ajiyar zuciya yace "ina son magana dake Talatu ".
"ina saurarenka Mamman ".Inji Inna Talatu cikeda natsuwa,,, ta mayarda hankalinta kacokam
wurinsa tana kallonsa.
Malam Mamman yace "da farko dai kinsan dai aure nufin Allah ne shine ke k'addara abu tun
ranar gini ranar zane,,, saboda haka na nemi auren wata yarinya mai suna Salima har gidansu
sun yarjemin in turo magabatana asaka rana,,, shi ne nace bari in sanardake abinda ke
faruwa,,, saboda kada kiji abin daga sama zan tura iyayena gobe asaka sati biyu ad'aura
auren,,,, shine nace bari in sanardake ko akwai shawarar da zaki bani ?".
Inna Talatu ta dubesa duba na munafurci da k'ulle-k'ullen makirci,,, tace "Alhmdlilah agaskiya na
tayaka murna da farin ciki sosai,,, Allah ubangiji ya gwada mana lokacin biki lafiya musha bidiri
mu dargwaji kaji,,,, ai shiyasa akeson mutum komai ya samesa yayi hak'uri da juriya domin
babu abinda yakeda tabbas a rayuwa,,,, komai kaga ya samu bawa to muk'addari ne daga Allah
".
"tabbas haka ne maganarki gaskiya Talatu komai na duniya yanada farko yanada k'arshe,,,,
saboda haka ki gayamin abinda ya kamata asiyo kafin biki na dangane da abinci da sauran
abubuwan buk'ata ".Inji Malam Mamman cikeda matuk'ar farin ciki da nishad'i sosai,,, saboda
shi azatonsa Inna Talatu yanzu ta sauko kuma ta gyara halayyarta,,, daga mugun hali zuwa
k'yakk'yawar d'abi'a,,, baisan wannan yana daga cikin tarkon makircinta ba da munafurci irin na
Inna Talatu MAYYA ba ".
Inna Talatu tayi murmushin da iyakarsa a leb'en bakinta baikai zuci ba,,, sannan tayi wata
wawuyar ajiyar zuciya tace "mi kakeci na baka na zuba ka bari har lokacin biki ya k'ara
k'arasowa mana,,, bakada matsala indai nice matarka Mamman aure ne kamar kayishi ".
"tooo.. Too bakomi uwargidana sarautar mata kece Innar Gwamma da Lawwali,,,, kece haske
gidan Malam Mamman ".Cewar Malam Mamman cikeda zolaya da jin dad'i..
Inna Talatu tace "a'aaa wannan kirarin duk ni kad'ai naji dad'i matuk'a,,, mijin Talatu angon
Salima babansu Gwamma da Lawwali ".
Hak'ik'a Malam Mamman yaji dad'i sosai da kirarin da Inna Talatu tayi masa,,, akan farin ciki ya
ciro d'ari biyar daga cikin aljihunsa ya bata k'yauta,,, ta amshe kud'in tana zaginsa tareda da
tsine masa a cikin zuciyarta.
Wata irin tsanarsa ce ta k'ara ninkuwa da kishinsa a cikin zuciyarta,,, ta fad'a cikin zuciyarta
"lallai Mamman zaka tafka babban kuskure a rayuwarka,,, zakasan ni babu mai tabani ya kwana
lafiya in kashe mutum ya mutu har lahira ba'a bakin komai yake gareni ba! Amma da sannu
zakasan ko wa ce ce ni Talatu idan ma ka gano ni *MAYYA CE* naga kanason ka kawomin
tangard'a sai in kasheka! ".Da yaga tayi shiru na wani lokaci,, Malam Mamman ya tab'a Inna
Talatu .
Yace "lafiya dai Talatu ya naga kinyi shiru kina tunani? ".
"lafiya k'alau wlh farin ciki ne yayimin yawa sosai,, shiyasa kaga nayi shiru ina tunani nagode
sosai da wannan k'yautar daka bani mijina Allah ubangiji ya k'ara bud'i na alkhairi ".Cewar Inna
Talatu tana dariyar yak'e da baikai zuci ba..
Malam Mamman yaji dad'in addu'arta matuk'a yayi murmushi yace "amin amin Talatu Allah
ubangiji yabarmu tare har abada ".
Inna Talatu tace "amin amin Mamman ".
**Suka cigaba da firarsu cike da tsananin jin dad'i da nishad'i,, saboda shi Malam Mamman
agaskiya yaji dad'in sauyawar Inna Talatu har cikin zuciyarsa,, bai kawo zarginta ba ko wani
mugun zato akan taba ya yarda da ita ne da zuciya d'aya,,,amma baisan ita munafukar Allah
ba haka bane a cikin zuciyarta ba,,, tana nan tana binsa da mugun nufi da k'ulle k'ullen makirci
da sharri..
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
***Awashe gari da misalin k'arfe hud'u da rabi 4:30pm na yamma magabatan Malam Mamman
ya tura can gidansu Salima.
Anyi musu tarba ta musamman da nuna karamci da dattako,,, hak'ik'a iyayen Salima mutanen
k'warai ne da sukasan mutunci da sanin ya kamata,,, komai cikin sauk'i da wadatar zuci akayisa
ansa sati biyu aranar juma'a za'a d'aura auren Malam Mamman da Salima,,, sun baro gidan
suna masu farin ciki da murna sosai akan yadda aka tarbesu hannu bibbiyu cikin sakin fuska da
fara'a.
Haka dai abubuwan suke tafiya cikeda zalunci da cin amana,, Inna Talatu taje da Gwamma
wurin boka LOK'ORO har ya bama Gwamma maganin maita! Itama ta zama k'usurgumar
mayya,,, uwarta Talatu ta kama kurwar mutane ta cinye ita Gwamma ta kama ta cinye.
Saboda tsabar shahara da gunguma a wurin Gwamma ita idan ta kama kurwar mutane ko
gasawa batayi,,, sai dai taci naman d'anye hakanan batare da ta gasa ba,,, yaro komai
k'ank'antarsa Gwamma tana kameshi mishi inwa (Shadow) ta cinye batare da b'ata lokaci ba.
Ana nan kwatsam!Ana saura kwana d'aya auren? Malam Mamman da Salima,, aka wayi gari
itama ta mutu irin mutuwar Lawiza alal hak'ik'a awannan rana iyayenta da 'yan uwanta sun
shiga cikin matuk'ar tashin hankali da rikicewa! Kowa awannan rana idan ka ganesu sai sun
baka tausayi saboda mahaifiyar Salima har yassuwa zane tayi ta ruga da gudu ta haukace!
Saboda tsananin bak'in ciki da b'acin rai sannan kuma ita kad'aice ke gareta amatsayi 'ya a
duniya.
Mutanen gari 'yan uwa da abokan arzik'i suka bita da gudu,,, domin su kamota suka babbazu
cikin daji suna nemanta,,, sunbi lungu da sak'o na daji har suka gaji amma ko ma kamada ita
basu gani ba ganin mutane da yawa daga cikinsu sun galabaita yasa dole suka juyo sukayo
cikin gari gidajensu .
Haka dai aka cigaba da cigiyarta da nemanta amma shiru babu wani labari,, asanadiyar haka
ne shima baban Salima ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani sai dai atayardashi a kwantar
dashi,,, abubuwan dai babu dad'in ji balantana saurare sun faru mutane sun k'ara tsoracewa
akan al'amarin mayyu,,, saboda kamasu kawai sukeyi suna canyewa jariri ma ko jaririya tun
suna cikin cikin mahaifiya ake kamasu acinye,,,wannan lamarin da gaske yana faruwa ni
Mugirat na gani da idanuna azahirin gaskiya bawai labari kawai aka bani ba.
*Azahirin gaskiya ta'adancin mayyu ya wuce duk wani tunaninku mutane.*.
Malam Mamman da yaji labarin mutuwar Salima saida ya fad'i ya suma,, sannan daga baya ya
farfad'o saboda matuk'ar damuwa da bak'in ciki saida ya kwanta matsananciyar rashin lafiya
sosai,,, duk yayi bak'i ya rame sosai Inna Talatu ke jinyarsa cikeda matuk'ar munafurci tana
lallashinsa tareda basa hak'uri,,,idan kaga yadda take kula dashi da tarairayar miji saika rantse
da Allah batada masaniya akan komai,,, amma awurin nan muguwa ce azzaluma