Showing 48001 words to 51000 words out of 58121 words

Chapter 17 - MAYYA CE COMPLETE by Mugirat Musa..pdf

Advertisement

12 Jul 2025

2978

ya cika! ".







"ni ba haka naso ba so nayi in kamata yanzu in gana mata azaba,,, sannan daga baya in
kasheta kamar yadda ta kashemin iyayena! ".Cewar Ummaru d'an Sala mafarauci.









Salma tace "kayi hak'uri maigidana zaka d'auki fansar jinin mahaifanka,,, kuma ka daina saka
damuwa da tunanin abinda bana damuwa ba,,, ni nasan komai daren dad'ewa zaka kama
Gwamma ka kasheta har lahira! Lokaci yana nan zuwa ka daina damuwa ".

Ummaru yace "to babu damuwa Ummu Husna,,,, zan daina saka damuwa acikin raina da
zuciyata ".









"da kam yafi baban Husna ka saki zuciyarka,,, komai yanada lokaci kuma zaizo ya wuce kamar
ba'ayi ba ".Cewar Salma cikeda matuk'ar lallashi.









Ummaru yace "tabbas haka ne gaskiyar maganarki ".









Salma ta cigaba da bashi maganganu masu sanyi,,, da kuma lallashinsa da yayi hak'uri
akowane lokaci zai iya kama Gwamma..

*********************




**Bayan shekaru goma ne alokacin ne su Hassan suka girma,,, sunada shekara ashirin da
uku,,,, Suhaila ta samu miji mai k'aunarta tsakani da Allah ya aureta,,, amma saida suka kafta
tashin hankali da bala'i da Iya Gwamma domin nuna tayi ita ba zata aurar da Suhaila ga Salihu
ba,,,, shi kuma dayake yana sonta itama tana sonsa shiyasa ta nace saita auresa,,, babu irin
kashi da zagin da Suhaila bata sha ba akan son da takeyiwa Salihu saboda itama Gwamma so
takeyi ta gajeta a cikin maita! Ita kuma tak'i bin umurninta domin bataga wata ribar da mayyu
suke samu ba idan suka zama mayyu,,, ganin irin haka ne yasa shima Hassan ya bid'i kud'in
aure ya fara kasuwanci,,, ya nemi wata Aisha nan mak'wabciyarsu yayi aurensa,,, sannan ya
kwashi matarsa ya samu wani gida madaidaici ya saye suka shige shida matarsa hankalinsu
kwance..











Iya Gwamma ganin d'iyanta sun watse sun barta akan bala'inta da masifarta,,,, rana guda ta
kama zaginsu tare da tsine musu albarka su suna can gidajensu basusan abinda yake faruwa
ba,,,,, to dayake batada rik'o arayuwarta nan da nan ta fita harakar d'iyan tareda cigaba da cin
naman mutane da aljannu,,, babu tsoron Allah ko kad'an a cikin zuciyarta..






¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤

*CIGABAN LABARI*





Mama Sa'ima da Alhaji Suleiman ganin yawon Maryam yayi yawa,, dole yasa uwar take sakawa
'yarta idanu da hana mata yawon zuwa ko'ina idan ba makaranta ba,,, saboda gudun kada
mayyu su kamata basusan sun riga sunyi fad'a da Iya Gwamma k'usurgumar mayyar da ta
addabi rayuwar mutane shekara da shekaru ba,,, Ummaru ya kasa kamata alamar sai taci
zamaninta,,, shi dai bai hak'ura ba yana nan yana bibiyar rayuwarta kuma yasan yanzu duk
d'iyanta sun gudu sun barta,,, saboda mummunan dabi'ar da take aikatawa wato yin maita da
rikid'e rikid'e da tsafe tsafen da bayada k'yau ko addinin musulunci..









Mama Sa'ima ce zaune tana tsintar k'asa acikin shinkafa,,, Mubarak yana zaune gefenta yana
tayata suna fira cikin natsuwa da kwanciyar hankali..









Alokacin ne Mubarak ya dubi Mama Sa'ima yace "amma yau ana zafi sosai agarin nan,,, baba
yana can kasuwa kuwa gashi akwai rana sosai ".

"zafi ai lokacinsa ne Mubarak ai fita kasuwa ya zama dole ga Alhaji,,, saboda kaga yanzu idan
bai fita ba yaran yanzu masu tsaron shago ba kowanensu keda amana ba,,, sai 'yan kad'an
daga cikinsu sukeda amana da gaskiya ".Cewar Mama Sa'ima.








Mubarak yace "ai Alhaji yanada hak'uri da juriyar zama da mutane,,, musamman idan mutum ya
samu masu tsaron shago ko marasa gaskiya sai yakai zuciyarsa nesa ko ya koresu".







Mama Sa'ima tayi murmushi tace "ai zaman duniya iyawa ne gaskiya idan baka iya zama da
mutane sai zama ya gagareka da mutane,,,,, mutum yazo yana fad'a da mutane kowa ya
tsanesa,,, ai rayuwar da kake ganinta gaba d'aya sai mutum yayi hak'uri da juriya a rayuwa ".











"haka ne gaskiya Mama ni abinda yake bani tsoro da takaici shine,,, yadda zamanin nan namu
ya lalace kowane ka gani ya zama mayye ko mayya,,, saboda tsananin kwad'ayi da son abin
duniya da dogon buri! Ni abin yana cimin tuwo a k'warya bansan yadda abubuwan suke faruwa
ba? ".Cewar Mubarak cikeda jimamin abinda ke faruwa cikin gari.

Mama Sa'ima tayi murmushi taja numfashi,,,, sannan tace "ai lamarin mayyu sai addu'a saboda
yafi k'arfin Al'umma,,, saboda haka koni abin yana damuna babu yadda zamuyi sai hak'uri akan
lamarin mayyu! Sai addu'a da neman tsari daga sharrinsu".
















Mubarak yace "Allah ubangiji ya karemu daga sharrin masu sharri a cikin mutane da aljannu ".

"Amin ya rabbi Mama ".Inji Mubarak.






*BAYAN KWANA BIYU*




Bayan faruwar wannan al'amarin tsakanin Iya Gwamma dasu Fatima,,, na rashin mutuncin da
Fadila tayiwa Iya Gwamma saiya zamo iyayensu Fatima sun hana musu zuwa ko'ina kamar
yadda aka hanama Maryam,,,, domin aran nan da suka kama yiwa su Fadila fad'a kamar zasu
dokesu da yake Fatima tanada tsoro sosai shine ta sanardasu irin abinda ya had'a su da Iya ta
aikesu,,, da kuma rashin kunyar da Fadila tayi mata duk saida ta gaya musu.






To sunsha fad'a sosai rannan akan rashin kunyar da Fadila tayi ma Iya Gwamma,,,,, kamar
abasu mugun kashi saboda abinda Fadila tayima Iya Gwamma,,,,,Fadil yayan Fadila kamar ya
bata kashi akan rashin kunyar Fadila tayi yawa da kuma tsiwarta..









Amma Iyayennasu mata suka hana ya bugeta saboda sunsan bugu baya horar da yara,,, sai
dai addu'a da yawan jama yaro kunne ,,,to wannan maganar dai anan atsakaninsu Iyayen mata
suka bar maganar,, basu sanarda Iyayen maza ba saboda sunsan sune da laifi,,, sannan su
mazajen zasu yiwa fad'a kunsan ance laifin d'a baya wuce mahaifiyarsa.

Ana nan dai kwatsam! Fadila da Fatima rashin lafiya ya kamasu kusan atare,,, ita Fatima amai
da zawo ne takeyi duk ta rame tayi bak'i sannan ta fige babu k'yawon gani,,, ita kuma Fadila
ciwon zazzab'i da ciwon kai ne ya kamata sannan ga wasu k'ananan k'uraje nan da suka fara
fitowa a jikinta,,,ciwon yayi matuk'ar ramar da ita yasa ta fita cikin hayyacinta k'warai da gaske,,
Iyayensu hankalinsu yayi k'ololuwar tashi sosai,,, babu abinda sukeyi sai kukan zuci dana zahiri
ga bak'in ciki da k'uncin rayuwa.........














_Share&Comments_
[7/9, 11:55 PM] Mugiratmusa66:





*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_

*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_



*PAGE 28*






Babu abinda sukeyi sai kukan zuci dana zahiri ga bak'in ciki da k'uncin rayuwa,,, saboda suna
matuk'ar k'aunar d'iyansu da gaskiya basa son ko k'uda ne ya tab'asu idan da son ransu,,, haka
dai suka cigaba da jinyar yaransu tareda da basu kulawa ta musamman,,,, batare da sanin
iyayensu maza ba. Ab'angaren gidansu Maryam itama ta kamu da tsananin rashin lafiya sosai,,, wato ciwon ciki
mai tsananin gaske da hanasu barcin dare shine Iya Gwamma mayya ta tura mata,,, alokacin
da ciwon cikin ya fara tashi Mama Sa'ima da Mubarak hankalinsu yayi k'ololuwar tashi sosai ga
zuciyarsu sai bugawa takeyi da k'arfi da k'arfi! Kallo d'aya xaka yi musu kasan basa cikin
kwanciyar hankali da jin dad'i,,,idan ciwon cikin Maryam ya taso har shure shure takeyi da
kukan zafi da rad'ad'in ciwo,,,, su kuma su Mama Sa'ima babu mai kama wani akan hawaye
kuka kawai sukeyi cike da tsananin damuwa da bak'in cikin rayuwa,,, wata rana idan ciwon ya
lafa mata harda wasa takeyi da cin abinci sosai,,, idan ciwon ya tashi kuwa haka zata kama yin
fisge fisge da shure shure kamar mai aljannu har kumfa ke fitowa daga cikin bakinta,,, saboda
tsananin bala'in sihiri da magagin ciwo,, kunsan wani ikon Allah shine dukansu Allah ya mantar
dasu su sanar da Alhaji Suleiman irin ciwon da yake damunta,,, domin shi bayada masaniya
akan komai duk lokacin da baya nan gida to alokacin ne ciwon Maryam ke tashi..

Aranar nan suna zaune gefe saman tabarma sunyi tagumi,,, ga hawaye sai kwaranya yake
daga idanun Mama Sa'ima,,, shi kuma Mubarak idanunsa sunyi jawur kamar barkono saboda
damuwa da bak'in ciki,,, alokacin ne ya bud'i baki dak'yar yace mata "Mama inaga fa matsalar
nan ya kamata asanar da Alhaji duk abinda ake ciki gameda ciwon Maryam,, idan muka
sanardashi nasan zaice muje asibiti idan mukaje can duk abinda ake ciki gameda ciwon
Maryam zasu sanar damu,,, ko mi ne ne shawararki? ".








Mama Sa'ima ta fyace majina sannan tace "haka za'ayi Mubarak domin barin kashi a a ciki baya
maganin yunwa,,,, kuma ya zama dole babanku yasan wannan abu ".










"nima shine na gani amma munyi shiru munata b'oyon ciwo,,, kamar bamusan zafinta ba idan
shiru yayi yawa gaskiya wani ciwon yana iya shigowa bamu sani ba ".Inji Mubarak cikeda
jimamin rashin lafiyar k'anwarsa Maryam.

Mama Sa'ima ta nisa tace "duk abinda ka fad'a haka ne Mubarak,,, babu k'arya a cikin
maganarka Allah ubangiji yaba Maryam lafiya da itada dukkan kullumin musulmi baki d'aya,,,
amma ni agaskiya wannan ciwon nata yana matuk'ar bani tsoro da fargaba,,, sai ina ganin
kamar ba ciwon Allah da annabi bane ".









"amin Mamanmu kiyi hak'uri karkice haka domin kada kiyi sab'on Allah,,, dukkan abinda kikaga
ya samu bawa to muk'addari ne daga Allah,,, bawa bai isa ya cutar da d'an uwansa bawa ba sai
yardar Allah mad'aukakin sarki,,, shiyasa akeson mutum ya kasance mai hak'uri da tawakalli
akan lamuran duniya,,, da iznin ubangiji Allah Maryam zata samu lafiya ta warke garau kamar
bata tab'a yin wannan cuta ba " .Cewar Mubarak cikeda da tunani da hangen nesa.









Mama Sa'ima tace "haka ne Mubarak Allah ubangiji ya k'ara mana juriya da hak'uri da kuma
tawakalli da dukkan k'addarar da zata samemu,,, ita kuma Allah ya bata lafiya ".








Mubarak yace "Amin ya rabbi ".

Mubarak ya cigaba da kwantar mata da hankali,,, tareda bata hak'uri da kalamai masu sanyaya
zuciyar mai sauraro..










*Allah ubangiji ya bamu d'iya nagari masu tausayinmu ,,,,da yi mana addu'a idan babu mu a
duniya*.










*********************










**Ummaru da Kabiru ne zaune suna firar duniya data mayyu,,, cikeda matuk'ar natsuwa da
kwanciyar hankali..

Kabiru ne ya dubi Ummaru yace masa "abokina kana fa k'ok'ari sosai sai rage mana mayyu
kakeyi a cikin garin nan,, amma har yanzu ka kasa kashe Gwamma mayya wadda ta addabi
rayuwar mutanen gari da k'auyukkan dake kewaye damu ".









Ummaru d'an Sala mafarauci yace "hmmm Kabiru abin ba'a cewa komai wlh,,, kadai sha
kuruminka da yardar Allah k'arshen Gwamma mayya ya kusa zuwa,,,, ai komai b'oye b'oyenta
na kusa kamata in kasheta ai jinin mahaifana bazai tab'a zuba a banza ba ".









Kabiru yace "haka ne gaskiya ai ka rage mana annoba cikin garin Gumi,,, saboda ka kashe
mayyu fiyeda d'ari kaga kuwa sauran da suka rage nasan basuda yawa sosai,,, ai barin irinsu
Gwamma acikin Al'umma bala'i ne da tashin hankali! ".










"wama zai barta a raye cikin duniya,, ai idona idonta k'aryarta ta k'are,,, sainayi mata kisan
gillah saina banbance mata tsakanin wuta da ruwa,,,, har abada babu tausayi ko rahama
atsakanina da ita ".Inji Ummaru d'an Sala mafarauci cikeda tunanin rayuwarsa ta baya tareda

da iyayensa.










Kabiru ya dafa kafad'ar Ummaru cikeda tsananin tausayin abokinsa,,, domin shi har azuciya
yana matuk'ar k'aunar Ummaru.







Sannan yace "kayi hak'uri Ummaru domin shi mai hak'uri wata rana zai cimma nasara da ribar
hak'urinsa,,,,, sannan tabbas da yardar Allah zaka kashe Gwamma mayya kamar yadda ta
kashe maka iyayenka! ".












Ummaru yace "na sani ai shiyasa kaga akullum akowane lokaci acikin shiri nake,,, domin bana
fatar ranar ta riskeni ba ashirye ba saboda irinsu Gwamma shahararrun mayyu dole mutum yayi
musu shirin tunkararsu na musamman ".

"wannan haka yake gaskiya ai rana dubu ta b'arawo rana d'aya tamai kaya ".Inji Kabiru.








Ummaru yace "haka ne tabbas ".











¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤







Ganin irin ciwonsu Fatima yak'i ci yak'i canyewa yasa,,, uwayen hankalinsu ya k'ara d'unguma
sosai gabansu sai fad'uwa yakeyi yana bugawa rassssss! Rasssss!.

Umma Nusaiba ce ta dubi Mama Nafisa cikeda raunin zuciya da damuwa,, tace "Nafisa wannan
ciwon yayi yawa fa ya kamata mu sanardasu baban Fadila domin akaisu asibiti da gaggawa,,,
kada muyi shiru muzo mu rasa yaranmu akan zurfin ciki da gudun laifi wurin mazajenmu ".









Mama Nafisa ta d'ago idanunta da sukayi ja akan kuka da damuwa,,, tace "ai ya zama dole mu
sanardasu komi domin gujewa afkawa cikin nadama da dana sani,,, ni wallahi yanzu k'irjina sai
ciwo yakeyi ga wani abu daya tokare min k'irji mai nauyi,,, sai nake ganin kamar bazasu tashi
ba mutuwa zasuyi! ".








"Subhanalillah! Nafisa ba'a yanke k'auna daga rahamar ubangiji kedai keyi fatar samun sauk'i
da waraka,,,nima hankalina ba kwance yake ba amma ya zamuyi sai hak'uri da dangana,,, da
kuma addu'ar Allah ubangiji ya basu lafiya ".Inji Umma Nusaiba cikeda matuk'ar sanyin jiki da
damuwa.








Mama Nafisa tace "amin amin ya rabbi haka ne gaskiya lamarin duniya sai hak'uri da juriya ".

"bari adauko waya akira d'aya daga cikin mazajenmu ".Cewar Umma Nusaiba ,,,,, ta tashi
tsaye ta shige cikin d'akinta,,ta jima kad'an tana waya da baba Nura tana sanardashi abubuwan
dake faruwa,,, baba Nura yace mata gashinan nan zuwa yanzu yanzun nan karta damu,,, tace
to sannan ya katse wayar ita kuma ta fito waje tace "Nafisa ga baban Fatima nan tafe yanzu je
ki shirya ki fito kafin yazo,, yana zuwa wucewa kawai zamuyi ".








"to yaya Nusaiba ".Inji Nafisa ta tashi tsaye ta shige cikin d'akinta domin ta shirya.









Babu b'ata lokaci su dukansu suka shiryo cikin kayansu masu k'yau,,, suka tsaya jiran baba
Nura bada jimawa ba saiga sallamarsa shida Fadil sun shigo kusan atare suka shigowa daga
cikin gidan matan suka amsa musu sallama ,, babu b'ata lokaci aka kwashi su Fatima aka
sanya cikin motar baba Nura,,,Fadil ya shiga gaban mota su kuma su Mama Nafisa a bayan
mota,, baba Nura yaja motarsa ya nufi hanyar zuwa asibiti..









Suna zuwa asibitin aka amshi su Fatima domin afara basu taimakon gaggawa,,, gadajensu
suna kusaga juna itama Maryam har babanta da mamanta sun kawota asibiti,, baba Nura yana

ganin Alhaji Suleiman suka yi musabaha suka gaisa cikeda matuk'ar girmamawa da nishad'i
sosai..







Umma Nusaiba ce ta dubi Mama Sa'ima tace"a'aaaa Sa'ima kece a cikin asibiti,,, wa ye ba
lafiya? ".







"hmmm Maryam ce babu lafiya wlh ".Inji Mama Sa'ima.







Umma Nusaiba tace "to Allah ubangiji ya bata lafiya mu kuma su Fadila da Fatima muka kawo
basuda lafiya sosai ".







Sai da gaban Mama Sa'ima ya buga da k'arfi d'immmmm sannan ta tattaro dauriya tace "to 'yan
uku duk sun kamu da rashin lafiya alokaci guda,,, Allah ubangiji ya basu lafiya yasa kuma ba
abinda nake tunani bane ya faru dasu ".....
[7/10, 12:17 AM] Mugiratmusa66:






*MAYYA CE*








*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ®*✍
_[Onward together]_



*Written by Mugirat Musa*



*DEDICATED TO SIS NAJER'ART*



_Bismillahir rahamanir rahim_


*MAYYA CE FANS hak'ik'a ina godiya matuk'a da comment d'inku masu dad'i sosai,,, Allah
ubangiji yabar k'auna da zumunci har abada nagode masoyana*


*PAGE 29*




Saida gaban Mama Nafisa ya buga da k'arfi rassssss! Hankalinta yayi k'ololuwar tashi sosai
zuciyarta tana yimata k'una da tafasa,,,, ta mik'e tsaye cikeda matuk'ar fargaba da tashin
hankali tace "ban gane mi kike nufi da Allah yasa ba abinda kike tunani bane ya faru? "."Nima
kaina ya d'aure wlh,,, na kasa gane inda maganarki ta dosa ".Inji Umma Nusaiba cikin tsoro da
fargaba akan rashin lafiyarsu Fadila. Mama Sa'ima tayi shiru na tsawon lokaci sannan can tayi
doguwar ajiyar zuciya tace "yanzu kuwa zanyi muku bayani yadda zaku fahimta sosai,, ina nufin
Allah yasa ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login